Ƙaddara ɗauke take da shafuka mabambanta, daga zarar wannan shafin ya rufe wani shafin ne zai buɗe.
Allah ya kan jarabci bayinsa da abubuwa masu tarin yawa, wani lokacin ma har bawa ya ji ya sare kaman ba zai iya cimma gashi wajen ganin farin ciki ya wanzu a fuskarshi ba.
Kasancewar mu musulmai ne, yasa muka yi imani da Allah sannan muka rungumi rayuwa a duk yadda ta zo mana ko da kuwa ace ta zo ne tamkar tafiyar kunkuru a dokar daji.
Ihu mai tsanani ta saka tana wani irin gurnani kamar Zakanya, ta ko ina gumi. . .