Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Kishin Miji by Farida Musa (Sweery)

Ƙaddara ɗauke take da shafuka mabambanta, daga zarar wannan shafin ya rufe wani shafin ne zai buɗe.

Allah ya kan jarabci bayinsa da abubuwa masu tarin yawa, wani lokacin ma har bawa ya ji ya sare kaman ba zai iya cimma gashi wajen ganin farin ciki ya wanzu a fuskarshi ba.

Kasancewar mu musulmai ne, yasa muka yi imani da Allah sannan muka rungumi rayuwa a duk yadda ta zo mana ko da kuwa ace ta zo ne tamkar tafiyar kunkuru a dokar daji.

Ihu mai tsanani ta saka tana wani irin gurnani kamar Zakanya, ta ko ina gumi ne ki fita daga jikinta tamkar wacce aka watsa ma ruwan zafi. Dishi-dishi take gani saboda azabar kishin da ya turnuko ya yi kane-kane a zuciyarta.

“Aure Abdul ɗin ne zai yi aure? Kai ina ba zai yiwu ba duk abun da na ɗauki shekara da shekaru ina yi ya tashi a banza kenan? Ummi ki ce mun mafarki nake yi don Allah ki mare ni ko zan tashi daga wannan mummunar mafarkin da ya fi mutuwa zafi da tsayawa a rai”.

“Hasbunallahu! Zuby don Allah ki dawo hankalinki ki nustu mu san abun da muke yi wannan koke-koken ba zai kare mu da komai ba sai wani sabon tashin hankalin”. Ummi ta faɗa wa aminiyarta cikin kwantar da muryar don ganin ta fahimci abun da take faɗa mata.

Riko ta sosai Zuby tayi tamkar wacce ta zauce gabaɗaya ma ta rasa me zata fada saboda zuwa mata a ba zata da abun ya yi.

“Ummi kina gani fa wai da Umma za’a haɗa baki a munafunce Ni har Abdul ya kai kuɗin aure amma ban sani ba? Saboda nayi shiru shi ke nuna ba zan yi abun da na ga dama ba? Wallahi auren nan ba zai ɗauru ba idan kuma har ya ɗauru sai na salwantar da duk wacce tayi kuskuren auren Abdul don sai na saɓauta rayuwarta na mayar da ita abun kwatance ta yadda babu wasu iyayen da zasu sake yarda su ba da auren ɗiyar su ga Abdul”.

Share hawayen da ke kwaranya daga idanuwanta tayi ta tashi jiki a sanyaye ta shiga toilet binta da kallo kawai Ummi take yi.

A halin yanzu kallon zautacciya take yi wa Aminiyar tata saboda bata ga alamar hankali a tattare da ita ba ko kaɗan, ta san Zuby na da tsafin kishi amma bata ɗauka abun ya kai haka ba ko dan basu daɗe da sanin juna ba ne shiyasa.

Tana zaune a wajen tana karanta wasikar jaki har Zuby ta fito daga toilet ɗin ga dukkan alamu wanke fuskarta tayi.

Baki Ummi ta ringa ringa bata har rana ta faɗi, sannan tayi mata sallama ta tafi gidanta, da ke jere da gidan Zuby ma’ana makwabtan juna ne. Makwabtakan shine silar amintar tasu tun bayan da su Zuby suka yi ƙaura suka dawo anguwar.

Ƙarfe shida daidai yaran suka fara buga ƙofar gidan tsawon minti biyar suna bugawa kafin aka zo aka buɗe a zafafe ta riƙo Haidar ta kifa masa dundu a baya, “dan ubanka ban ja maka kunne a kan yi mun knocking irin na mahaukata ba? Idan ka buga ƙofa sau ɗaya ba zaka iya jira na zo na buɗe ba sai ka cika anguwa da ƙara kowa yasan ka dawo? Shege mai kama da aljanu” ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

Haidar ɗin da take yi wa kwallagwazo ƙanzil bai ce ba ban da kafe ta da ido da ta yi ga dukkan alamu ya riga da ya saba da masifarta.

Sim-sim-sim suka shige ɗakin su jikinsu a sanyaye idan ka cire Haidar da baya daukan duk abun da take yi, ga dukkan alamu ya gama raina mata wayo.

“Mtssss!” tsaki ya ja yana girgiza kai ji yake kaman ya shaƙe Ammin Farra wato Zuby.

“Me ya faru kake tsaki kuma?” Hisham, wato yayan shi ya tambaye shi.

“Na rantse da Allah idan na girma saboda matar nan zan zama soja na harbe ta kowa ma ya hu..” Hisham Bai bari Haidar ya ƙarasa maganar ba ya toshe masa bakinsa saboda jin takun tafiyar Ammin Farra.

Buge hannun shi ya yi yana yi masa wani duba saboda Haidar ba dai zuciya ba.

“Kai Hisham idan ka cire uniform ɗin ka je ka dafa muku taliya kuma kar ka kuskura ka ɓata mun kicin”.

To kawai ya ce mata saboda kaf a cikinsu yafi mata biyayya duk da shekarunsa ba zasu fi goma sha ɗaya ba.

A falon ɗakinsu ta ci karo da Farha “ke kuma ki wuce ciki ki tattaro uniform ɗin Farra ki wanke”.

“Aunty jiya fa na wanke” buge bakinta tayi da bayan hannunta ta ce “don ubanki yaushe kika yi girman da zan saki abu har ki tsaya kina musa mun?”.

Riƙe baki Farha ta yi hawaye na tsiyaya daga idonta sosai dukan ya shige ta, amma babu yadda ta iya tunda ba ramawa za ta yi ba.

Kai tsaye Zuby ta buɗe gate ɗin gidan ta fita zuciyarta na ta ingiza ta akan abubuwa da yawa duk wanda tayi a baya sai tana ganin su ba komai ba ne yanzu zata tashi akan ƙafafuwanta tayi abun da ya dace ko da kuwa kisan rai ne sai tayi shi a yau, don imaninta ya riga da ya guje ba ta jin komai a zuciyarta sai takaicin abun da Ummi ta faɗa mata akan Abdul.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×