Skip to content
Part 11 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

A ɓangaren Aisha kuwa. Sosai kalmomin da Khamis ya faɗa mata suka yi tasirin gaske a zuciyarta. Ci gaba da nanata faɗar su ta yi a zahiri da kuma baɗini duk don ta gane tsakanin ita da shi waye mai laifi. Shin ita ce ta daina kula da kanta, ko kuma shi ne da ɗaɗin amarci gami da asiri suka hana shi ya ga ƙoƙarin da take yi? Duk da ta san cewa ta yi rauni wurin kulawa da kanta, amma raunin bai kai yadda zai ga gazawarta ba.

Maganganun Aisha ne kuma suka yi mata dirar mikiya a cikin zuciya, inda Aisha ke nuna mata bai kamata mace ta yi fushi don mijinta ya faɗa mata gazawarta ba, abin da ya fi dacewa shi ne ta binciki ina gazawar take sai ta gyara.

Tambaya ce ta jefa ma kanta, inda ta ce,

‘To wace irin kula ce Abban Haneef yake so na yi ma kaina?’

Wani sashe na zuciyarta ne ya gwasale tambayar ta hanyar faɗin, ‘Ba wata kula da za ki yi ma kanki, kawai asiri ne aka yi mishi don ya daina ganin haskenki, kuma ai ga zahiri nan kin gani a ɗakin Maryam.”

Wannan magana ta ƙarshe da ta yi da zuciyarta ne ta rinjayi tambayar farko. Lallai akwai abin da Maryam ta yi ma Khamis wanda ya sa yake ganin gazawarta, tunda a can baya kafin ya ƙara auren bai taɓa kushe ta ba, sai ma ɗinbin yabon da take samu a wurinshi.

Wata irin tsanar Maryam ce ta ci gaba da taso mata a zuciya, domin a nata zargin Maryam ɗin ce sanadin wargajewar farincikinta.

‘Dole na ɗauki mummunan mataki a kan waccan shegiyar yarinyar.’

A fili ta faɗi haka tare da ɗora ƙafarta ɗaya akan ɗayar, kasantuwar zaune take a kan sofa.

“Toh wane irin mataki ne ya dace?”

Ita kanta bata sani ba, saboda bata yarda ta je wurin wani malami ita ma a yi mata asirin ba. Sannan ta ƙi yarda ɗari bisa ɗari akan gazawarta da Khamis ya faɗa bare ta gyara.

Tsunduma ta yi a cikin hanyar nema ma kanta mafita. Ba ta kai ga yin nisa ba ne Haneef ya dakatar da ita lokacin da ya shigo cikin ɗakin da gudu.

Miƙa mata game ɗin da ke hannunsa ya yi wanda Maryam ta siyo mishi.

“Mammy kalla, har na gama Level Three.”

Aisha na jinshi, amma gani take kamar kula shi zai iya datse mata mafitar da ta fara sama ma kanta ta bin shawarar Zuzee, ko kuma ta gyara kanta duk da ita bata ga abin da za ta gyara ba.

Ɗan bubbuga jikinta Haneef ya yi shi da Haneefa da ke riƙe da ƙatuwar ‘yar bebe, wadda ita ma tana cikin tsarabar da Maryam ta yi musu.

“Haneef na faɗa maka bana son takura.”

Aisha ta faɗa tana duban shi.

Ɗan marairaicewa suka yi, Haneef ɗin ne ya ce,

“Sorry Mammy, game ɗin kaɗai za ki gani.”

Duba fuskar game ɗin Aisha ta yi ta ga ‘Level complete’ ɗago dubanta ta yi,

“Na gani to a wuce falo.”

Da gudu suka ruga falo, tana jin sa’adda Haneefa ke cewa ,

“Yaya ka bani nima na yi.”

Haneef ɗin kuma na faɗin,

“To bari na gama wannan level ɗin.”

‘Yar gajeriyar ajiyar zuciya Aisha ta sauke tare da ci gaba da karɓar saƙon da zuciyarta ke aiko mata.

“Duk in da gazawa take zan gyara, ƙorafin kuma zan rage.”

Abin da ta faɗa a fili lokacin da ta ga bin tsohuwar shawarar Aisha ita ce mafita, domin da tsohuwar zuma ake magani.

Sai dai kuma ta ƙuduri muddin Khamis bai karɓi canjinta ba to daga shi har Maryam zasu ga kalar nata wulaƙancin.

Jiki ba daɗi ta fito falo saboda ta daina jin hayaniyar yaranta. Taras da Haneefa na bacci a ƙasan carpet ta yi, Haneef kuma har yanzu game na hannunsa yana wasa.

Cike da takaici ta dubi corridor ɗin ɗakin Maryam, Kishin da ya turnuƙe ta ne ya sa ta faɗin, “Wallahi dole ma na ɗauki mataki.”

Maida dubanta ga Haneef ta yi “To game din ya isa haka.”

Duƙawa ta yi ta saɓi Hannefa, Haneef kuma ya bi bayanta suka nufi ɗaki. Kwantar da Haneefa ta yi a saman gado. Shi kuma Haneef ta shimfiɗa mishi katifa a ƙasan carpet.

fitowa ta sake yi ta kashe fitilun falon, sannan ta koma ɗakinta ta kwanta. Sai dai bacci bai samu ƙarfin ɗauke ta ba sai da ya nemi taimakon hawaye masu zafin gaske. Kukan baƙincikin samun tazara a tsakaninta da mijinta ta sha, bata taɓa tunanin za ta samu kanta a irin wannan yanayin ba.

Khamis kuwa tunda Maryam ta zo hannunsa yake jin ko first night ɗinsu albarka, saboda a wancan karon tsoronsa ta ke, yanzu kuwa ta ci dubu sai ceto.

Washegari bayan sallar asuba suna kwance a kan gado suna fuskantar juna, hannun kowannensu na zagaye da jikin ɗan’uwansa. Murya ƙasa-ƙasa Khamis ya tambaye ta.

“Wai me aka baki a Katsina ne?”

Maido mishi da tambaya Maryam ta yi cikin muryarta mai daɗi, “Kamar ya me aka bani?”

Duk da ta fahimci inda ya dosa, saboda tun cikin daren yake ta yi mata sambatun da ta daɗe da fahimtar inda ya dosa.

Lumshe idanu Khamis ya yi, ƙasan ransa kuma yana tuna irin farincikin da ya samu wurinta a daren jiya, wanda zai iya rantsewa bai taɓa samun irinsa ba,

“Toh Aljannar nan ce dai kika sake mayar da ni Princess.”

‘Yar dariya Maryam ta yi tare da gode ma ‘yan’uwanta da suka jajirce wurin gyara mata aure. Musamman Anty Zainab da ta dafa mata Kazar Nonon raƙumi. Kazar da idan mata suka yi riƙo da ita ba za su sake siyen tarkacen kayan mata ba, domin tana bin jiki tare da ƙara ma mace ɗanɗano marar misaltuwa.

Ce mishi ta yi,

“Ni ba abin da suka bani.”

Ɗan girgiza kai ya yi.

“Anya kuwa, kin ƙara test fa?” Yana dariya ya ƙarashe maganar tare da ƙara shigar da ita jikinsa.

Ta san irin wannan yanayin dole wani abu ya faru, don haka ne ta sake masa dukkan jikinta. To bayan komai ya kammala kuma sun yi wanka sun kimtsa, sai yake ce mata,

“Dole na biya tukuicin wannan zuma da na sha.”

Dariya kai Maryam ta yi, don ta ɗauka wasa ne. Tunawa ta yi da buɗe mata ɗaki da alamu suka nuna an yi. Ta so ta danne, sai dai tsoron kada a sake ya sa ta yi mishi magana bayan ta zauna gefensa akan gado.

“Uhm ɗakina, sai na ga kamar an buɗe shi lokacin da na tafi Kt.”

Faɗuwa gaban Khamis ya yi, bai yi niyyar yi mata maganar ba, sai dai tunda ita ta mishi, dole shi ma ya yi mata.

“Nima na gani Mairo, amma kada ki damu, na ɗauki matakin da ba za a sake ba.”

Bai faɗa mata wanda ya shiga ba, haka ita ma bata tambaye shi ba, tunda dai ya ce ya ɗauki mataki magana ta ƙare. Tashi ta yi ta nufi kitchen. Inda Khamis kuma ya shige ɗakin Aisha.

Wanka ya taras tana yi ma Haneefa a banɗaki. Haneef kuma cikin uniform yana home work a ƙasan carpet.

“Daddy Ina kwana.”

Haneef ya gaishe da Khamis, amsawa ya yi tare da zama akan kujera.

Idanunsa akan tarin litattafan da ke gaban Haneef ya ce,

“Home Work ɗin ne sai yanzu ka ga dama ko?”

Shiru Haneef ɗin ya yi, lokaci ɗaya kuma yana ɗan taunar pencil ɗinsa, saboda ya san Khamis bai son Home Work ya kwana, saboda ko ba komai zai hana yaro fita school da wuri.

Da ɗan faɗa Khamis ya sake cewa, “To me kake jira, ka wani tsaya kana kallona?”

Da hanzari Haneef ya maida hankalinsa ga Home Work ɗin.

Aisha da Haneefa ne suka fito daga banɗakin. Haneefa da ke ɗaure da towel ta gaishe shi, Khamis na ‘yar dariya ya ce, “Lafiya lau Mamana, kin dai yi Home Work ko?”

Amsa Haneefa ta bashi da,

“Eh Daddy, Anty ta yi mani jiya.” Lokaci ɗaya kuma ta zo gafensa ta zauna.

Ko kusa fuskar Aisha ba walwala a cikinta, gaishe da Khamis ta yi bayan ta zauna a gefen gado. Shi kuwa fuskarsa a sake ya amsa. Complain ɗin rashin yin Home Work ɗin Haneef ya yi mata.

Cewa ta yi,

“To zai riƙa yi da ya dawo In Sha Allahu.”

Khamis ya ji daɗin yadda ta karɓi laifinta.

Ji Aisha ta riƙa yi kamar ta tada mishi tsohon zance, wani sashe na zuciyarta ne ya kwaɓe ta inda ya nuna mata ta bar shi kawai, lokacin yin maganar zai zo a nan gaba.

Mai ta shafa ma Haneefa tare da shirya ta cikin uniform. Viju milk da kuma biscuit ta saka ma yaran a school bag ɗin kowanne.

Miƙewa Khamis ya yi gami da kama hannun yaransa suka fice falo. Ita kuma a nan suka barta saboda ta ce ba yanzu za ta yi breakfast ba.

Breakfast ɗin suka yi, bayan sun gama Maryam ta sanya ma Haneefa ɗan guntun milk hijabinta, wanda ya yi daidai da coffe brown ɗin skirt ɗinta. Uniform ɗin iri ɗaya ne da na Haneef.

Waje Khamis ya tura yaran ya ce su jira shi bayan duk sun ɗauki school bag ɗinsu.

Jawo Maryam ya yi jikinshi tare da haɗe musu fuskokinsu, cikin taushin murya ya ce mata,

“Kallon fuskarki sa wa yake na ji kamar kada na fita.”

“Uhm.”

Kaɗai ta ce tana ‘yar dariya.

Tambayar ta ya yi,

“Me za ki dafa mini?”

Amsa ta ba shi da,

“Abin da ka fi so.”

Sake tambayarta ya yi,

“Toh me na fi so?”

Cike da rangwaɗa ta ce,

“Tuwo miyar yauƙi.”

Ɗago da kansa ya yi yana ‘yar dariya.

“Sosai ki ka fahimce ni, to ki yi mini mai daɗin nan da kika saba yi, sannan miyar ta ji man shanu.”

Cewa ta yi.

“An gama ranka ya daɗe.”

Ci gaba da kallon sa ta yi, sai ta ga ya ƙura mata idanu, a cikin idanun kuma tana karantar tsantsar ƙaunar ta a tare da shi.

Tuna mishi da su Haneef ta yi don ta ga kamar ya manta da su.

“Yara na jiranka fa.”

“Ina sane da su.”

Ya faɗa tare saka bakinsa cikin nata. Sun ɗauki dogon lokaci a haka, sai da suka ji muryar Haneef na faɗin,

“Daddy za mu yi latti.”

Sannan suka rabu da juna.

Har bakin mota ta raka su sannan ta dawo ciki. Aisha kuwa akan idonta Khamis da Maryam suka ci tsayuwarsu a falo lokacin da ta fito za ta shiga kitchen, sai dai baƙinciki da kishi ne suka maida ta ɗaki tare da ci gaba da kai kawo a tsakiyar ɗakin.

A zuci ta riƙa faɗin,

‘Anya zan iya zama da yarinyar nan a gida ɗaya?’

Don in dai za ta riƙa ganin irin wannan abun to zuciyarta za ta iya bugawa, ko kuma ta ɗauki mugun matakin da ba zai yi ma kowa daɗi ba. Ƙarar wayarta ce ta katse mata kai kawon, wurin wayar da ke kan mirror ta je tare da ɗaukan kiran.

“Hello Zuzze ina jin ki.”

Daga can Zuzze ta tambaye ta,

“Ya ake ciki ne?”

Aisha ta ce,

“Kin san dai idan waccan yarinyar na gidannan hankalina ba zai kwanta ba, kullum da sabon salon da za ta tsiro, yanzu haka sai da yara suka yi latti, ta riƙe Abban Haneef a falo tana mishi karuwanci.”

Daga can Zuzee ta ce,

“Ke ba ki iya karuwancin bane? Wani abin fa har da laifinki.” Kamar Aisha za ta yi kuka ta ce, “Wane irin laifina? Bacin da hannunki kika ɗauko mugun abin da ta ƙumshe a ɗaki.”

Daga can Zuzze ta ce,

“To duk abin da ta iya kema fa kin iya, sai dai idan ba za ki yi ba.”

Aisha ta ce,

“To me zan yi?, Ni dai zan roƙi Abban Haneef ya canja mini gida kawai, wataƙila idan bana ganin ta hankalina zai fi kwanciya.”

Ko kusa bata samu goyon ban Zuzee a kan maganar canja gida ba, saboda Zuzeen ta fi son ganin Aisha a damuwa don ta samu hanyar da za ta kai ta ta baro.

A nan kuma Zuzzen ta ƙara tunzura ta wai kar ta ci duk wani abin da Maryam ta dawo da shi, Aisha ta ce,

“Ya ma za a yi na ci, ai tunda na ga wannan abin na ji ko ruwan hannunta bana iya sha, yarana ma don bani da yadda zan yi, shi ya sa ma nake son a raba mana gida.”

Sosai suka sha maganganunsu waɗanda duk a kan nema ma Aisha mafita ne.

Gaba ɗaya ita kishi ya hana ta bin alƙibla guda ɗaya, yanzu kuma ji take ba za ta iya yin abin da Khamis ke so ba, saboda ko ta yi ba za ta burge shi ba saboda asirin da take zargin Maryam ta yi.

Yau da wuri Khamis ya dawo domin cin abinci da rana, ya so haɗuwa da ahalinsa baki ɗaya su ci abincin, sai dai Aisha da ta sanya tutsun ita sai anjima.

A falo suka zauna cin abincin shi da Maryam da kuma yara. Tuwon da ya fi so ne Maryam ta yi mishi, sai miyar kuɓewa busasshiya da ta ji nama da kuma man shanu.

Daga shi har yaran duk santi suka riƙa yi, Haneef da ba ya raina daɗin girki ya ce,

“Wallahi Anty kin iya girki.” Maryam ta ce,

“Kai Haneef!”

Ya ce,

“Wallahi kuwa!”

Hannefa kuwa ba baka sai kunne.

Albarka da yabo kuwa ta sha su a wurin Khamis, ta kuma ji daɗi don abin da kowace mace ke fata ne daga wurin mijinta.

Aisha da ke takure a ɗaki ta ji motsin shigowar Khamis da yara.

Ƙaƙaro murmushi ta yi ta aje a fuskarta lokacin da suka shigo.

A ƙasan carpet ɗin da take zaune nan Khamis ya zauna, yaran kuma ya maida su falo don magana yake son yi da mahaifiyarsu.

Nannaɗe ƙafa ya yi yana ƙare mata kallo, lallai maganarta ta tabbata, indai tana ganin Maryam to bata da sauran walwala.

Sunanta ya kira,

“Aysha.”

Bayan ta amsa ya ce,

“Maryam ta dawo walwalarki ta tafi ko? Yanzu ke da Maryam wa ke da gida?”

Sosai ta ji tambayar,

“Wa ke da gida?”

Shiru ta yi tana nazarin amsar da za ta bashi.

Bai jira ta nazarto amsar ba ya ce, “Gida naki ne, miji naki ne, yara ma naki ne Aisha, amma sakacinki da kishi ya sa wata na son raba ki da su, kuma kin kasa gane sakacinki ne, sai ma kike kallon kamar an tauye miki haƙƙi, baccin babu ko ɗaya.”

Faɗa sosai ya yi mata wanda ya ratsa duk wata gaɓa ta jikinta, babban abin da ya fi taɓa mata zuciya shi ne ta tsaya sakaci gashi nan za a raba ta da gidanta.

Za ta iya jajircewa ta gyara rayuwarta, amma in dai tana ganin Maryam toh fa kishi ba zai barta ba, don haka da za a raba su har abin da Khamis bai za ta ba zai gani. Duban shi ta yi cikin raunin murya ta ce,

“Abban Haneef kishin ka nake, bana iya jurar ganin wata a gidan nan, don Allah tunda kana da hali ka raba mana gida.”

Kallon mamaki ya shiga yi mata, bai taɓa tunanin Aisha za ta sakarce haka ba. Ko kusa babu ra’ayin raba ma ahalinsa gida, don haka ya ce,

“Ba zan miki ƙarya ba, bana da ra’ayin raba iyalina gida biyu. Kuma ma da kike maganar kishi sai ki bari ya hana ki ɗaga darajarki? Ai na ɗauka a wurin nuna bajinta ake nuna kishi, ki yi fin abin da ta yi, ba wai ki shige ɗaki kuma ki ce wai kishi ki ke yi ba”.

Ido ya rufe ya ci gaba da faɗa mata gaskiya, ba tare da damuwa da yadda za ta ɗauki gaskiyar ba. Nan ya barta tana matse-matsen ƙwallar da ta fito.

A yau ɗin ne kuma ya ya ƙuduri cika ma Maryam alƙwalin da ya ɗaukar mata ba tare da ta sani ba.

Ɗakinta ya shiga ya tarar za ta shiga banɗaki ta yi alwalla, faɗa mata ya yi ta shirya da an yi la’asar za su fita. Tambayar shi ta yi,

“Ina za mu je?”

Ya ce,

“Wani wuri.”

Fita ya yi daga ɗakin suka nufi masallaci shi da Haneef.

Ita ma alwala ta yi tare da gabatar da sallah. Tana gamawa ta ɗan ƙara yin make-up. Gyalenta da waya ta ɗauka tare da zura takalma ta fita.

Ya san dama a shirye zai iske ta, duban gyalenta ya yi ya ce,

“Hijabi za ki saka.”

Ɗan ɓata rai ta yi tare da shagwaɓewa ta ce,

“To gyalen fa me ya yi?”

Ya ce,

“Ni dai na ce ki saka Hijabi.”

Ba don ranta ya so ba ta koma ta ɗauko hijabi blue ta saka, flat shoe ɗinta ma kalar hijabin ne.

Tana fitowa Khamis ya ce,

“Yanzu na ji batu.”

Cewa ya yi su fita ita da yaran, saboda yau Alhamis ne ba Islamiyyar yamma.

Ɗakin Aisha shi kuma ya shiga da nufin faɗa mata inda za su je, sallah ya taras tana yi, cewa ya yi, “Mun fita ni da Maryam da yara.” Sannan ya juya ya tafi.

Bai wani ɓata lokaci ba ya shiga mota suka tafi, Maryam dai da ta ga an doshi wata hanya da bata sani ba ta ce,

“Wai ina zamu je don Allah?”

“Sayar da ku zan yi.”

Ya bata amsa a taƙaice.

Dariya ta tuntsire da ita ta ce, “Haba dai sayarwa.”

Yana dariyar shima ya ce,

“To tsaya ki gani.”

Haneef da dama ya san wannan hanyar, ɗan leƙowa ya yi daga bayan da suke shi da Haneefa ya ce,

“Daddy hanyar wurin motocinka ne ko?”.

Tun kafin Khamis ya ba shi amsa Maryam ta ga sun iso KHAMIS AND BROTHERS MOTORS.

Duban shi ta yi ta ga yana ‘yar dariya tare da faka motar. Maryam ta yi zaton ko hanya ta biyo da su wurin, sai ji ta yi ya ce “To mun zo.”

Gaba ɗaya suka fito daga motar, Haneef da Haneefa suka yi cikin jerin motocin don wurin ba baƙonsu bane.

Ido Maryam ta zuba ma ƙayatattun motocin da ke jere a filin wurin, samun kanta ta yi cikin yi ma mijinta addu’ar Allah ya tsare arziki.

Cikin wata rumfa suka ƙarasa. Nan yaran Khamis suka ci gaba da gaida Maryam, kasa amsawa ta yi saboda duk sun girme ta, sai dai ita ma ta maido musu da gaisuwa.

Khamis ne ya tambayi ɗaya daga cikin yaransa mai suna Sani,

“Ina makullan motar nan da na ware?”l

Hannu Sani ya zura cikin aljihu tare da zaro makullan, sai da ya ɗan russuna kai sannan ya ba Khamis. Duban Maryam ya yi tare da miƙa mata.

“Gashi ciki ki zaɓi ɗaya.”

Kallon rashin fahimta ta yi mashi.

Da ya lura da kamar bata fahimce shi ba ya ce,

“Ga motoci can guda biyu, ki zaɓi ɗaya a ciki, duk iri ɗaya ne, colour ne kaɗai ya bambanta.”

Tamkar mafarki haka Maryam take jin maganar, dariya ko kukan farinciki wanne ya kamata ta yi? Yau ita ce za ta mallaki motar kanta.

Ba tare da damuwa da Yaran Khamis su biyu ba ta rungume shi tare da yin shiru.

Su kuwa sai dariya suke, sosai halin kirkin ubangidansu ke birge su, ɗayan mai suna Lawal ya ce ma Sani,

“Haka fa ya yi ma Uwargida gab da ƙarin auren sa.”

Sani ya ce,

“Ai motar uwargidan ma ta fi tsada.”

Lawal ya ce,

“Wannan ma ba daga baya ba.”

Maryam kuwa tuni Khamis ya ja hannunta sun tafi wurin motocin ƙirar Honda guda biyu da ke jere. Fara da kuma Maroon ne kalolin motocin, kalar Maroon ɗin ta ɗauka.

Buɗe mata Khamis ya yi to ki shiga, cikin mutuwar jiki ta shiga motar, wasu irin hawayen farinciki ne suka gangaro mata.

Ɗan leƙowa Khamis ya yi,

“Wai kuka kike?”, hannunsa ta riƙo.

“Dole na yi kuka, mijina ya sa ina jin kamar na fi sauran mata.”

Sassauta murya Khamis ya yi.

“Kin manta ke kika fara sanya shi ya ji kamar ya fi sauran maza.” Maganganun ƙauna da yabo ya ci gaba da faɗa mata, waɗanda take jin kamar kada ya daina.

Ita bata iya tuƙi sosai ba, shi ɗin ne ya tuƙo motar suka ɗauki hanyar gida.

Haneefa ta ce,

“Daddy motar waye?”

Khamis ya ce,

“Ta Anty ce, za ta riƙa ɗaukar ku kuna fita yawo.”

Murna suka kama yi, su in dai za a fita to basu da damuwa.

Aisha na falo ta ji ƙarar buɗe gate, ɗan ɗage labulen window ta yi. Gabanta ne ta ji ya faɗi lokacin da ta ga sabuwar mota.

Da gudu yaran suka shigo, har rige rigen faɗa suke,

“Daddy ya ba Anty Mota.”

Tamkar saukar Aradu Aisha ta ji maganar, sake leƙawa ta yi ta window, Ai kuwa ta hango Khamis rungume da Maryam a cikin motar.

Take Tuwon da take ci ya fice mata akai. Kasa yarda ta yi sai da Khamis da Maryam suka shigo.

Maryam na wani irin farinciki ta riƙe hannun Aisha.

“Umman Haneef ki taya ni godiya, Abban Haneef ya bani mota.”

Idan aka ce Aysha ta faɗi adadin faɗuwar da ganbanta ya yi a wannan lokacin ba za ta iya ba. Sannan ko kyauta aka sa mata akan ta danne kishinta shi ma ba za ta iya ba.

“Mota dai?”

Ta faɗa tare da ɗan zare idanu.

Khamis na ganin yanayinta ya wuce, da idanu ta bi shi har ya shige ɗakinsa. Maido dubanta ga Maryam ta yi.

“Lallai kin gode, Allah ya sanya alkhairi.”

“Amin.”

Maryam ta ce tare da yin godiya, ta kuma nufi ɗakinta.

Kitchen Aisha ta wuce ta wanke hannu, tana fitowa kuma ta nufi ɗakin Khamis, zaune ta same shi a gefen gado yana waya, sai da ya gama sannan ta ce,

“Uhmm Abban Haneef, Amarya ko shekara bata yi ba amma ta sha mota.”

Ɗan guntun murmushi ya yi tare da faɗin,

“Ai ta cancanta ne.”

“Uhm, ta ce, sannan ta ɗora da “Kai Madalla, to ina taya ta godiya.”

Ficewa ta yi daga ɗakin, Lallai abin da Zuzee ke faɗa na cewa Maryam za ta iya dawowa da asiri ya fara tabbata, duka kwananta uku da dawowa ya yi mata wannan alkhairin, ita kuwa sai da suka shekara shida da aure ne ya bata motar farko.

Zuzee ta Shaida ma a WhatsApp, Zuzee ta ce,

“Aisha sau nawa zan faɗa miki? To abin da ya fi mota ma kina ƙumshe a ɗaki za ki ji tana shewar ya bata.”

Ban fa Zuzee ta shiga yi mata ingiza mai kantu ruwa.

Maryam kuwa ta yi farinciki marar misaltuwa, kuma ta faranta ma mijinta fiye da zato. Sannan ta faɗa ma danginta, sun taya ta murna, wasu kuma sun bugo ma Khamis sun masa godiya.

Ba’a gama murnar sayen mota ba kuma Maryam ta kama rashin lafiya. Da zuwansu asibiti doctor ya bata P test, bayan result ya fito kuma aka ce ciki ne.

Murna wurin Khamis ba a magana, Aisha kuwa wani lodin takaicin ne ya turnuƙe ta. Duk da ta fara gyara ɓarakar da ke tsakaninta da Khamis.

Sai dai zafin wannan ciki na Maryam na neman ya sake maida ta ruwa, kasantuwar cikin Maryam mai laulayi ne, komai bata iyawa.

Samun Aisha ya yi a ɗaki ya ce, “Don Allah ki karɓi girki kafin ta samu sauƙi.”

Kamar abin arziƙi Aisha ta karɓa, sai dai girkin ne kaɗai ta ke yi. Da dare kuma sai Khamis ya shige ɗakin Maryam.

Aikuwa da ta gaji ta ce,

“Ba fa za ta saɓu ba, bindiga a ruwa, wato bata iya girki, amma tana iya kwana da miji.”

Haƙuri Khamis ya ci gaba da bata, da yake so take ya barta ta je unguwa sai ta haƙura ta yi girki a ranar.

Shi kuwa don ya saka mata da alkhairi tana tambayar shi za ta je gidansu ya ce,

“Na amince Indodo.”

<< Kishiyar Katsina 10Kishiyar Katsina 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×