"Haba Alhaji, ta ya za ka ce Aisha ba ta da gaskiya alhali ba ka ji ta bakinta ba?"
In ji Mommy da take ganin ana shirin jibga ma Aisha laifi.
Cewa Alhaji Usman ya yi,
"To idan tana da gaskiya ta yi magana mana, tunda ba wani ya rufe mata baki ba."
Shiru Mommy ta yi tare da maida dubanta ga Aisha da ke ta raba idanu, ai kuwa sai ga tsantsar rashin gaskiyar da Alhaji Usman ya faɗa a tare da Aishar, hakan ya ƙara kulle ma Mommy baki, don ba ta son a ce ga abin. . .
Nice one
Allah ya taimaka
amin