Skip to content
Part 14 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

“Haba Alhaji, ta ya za ka ce Aisha ba ta da gaskiya alhali ba ka ji ta bakinta ba?”

In ji Mommy da take ganin ana shirin jibga ma Aisha laifi.

Cewa Alhaji Usman ya yi,

“To idan tana da gaskiya ta yi magana mana, tunda ba wani ya rufe mata baki ba.”

Shiru Mommy ta yi tare da maida dubanta ga Aisha da ke ta raba idanu, ai kuwa sai ga tsantsar rashin gaskiyar da Alhaji Usman ya faɗa a tare da Aishar, hakan ya ƙara kulle ma Mommy baki, don ba ta son a ce ga abin da ɗiyarta ta yi.

Aisha kuwa burinta bai wuce ta ji me Khamis da har yanzu kansa ke ƙasa zai ce ba, ai kuwa Alhaji Usman na sake bashi izinin magana gabanta ya shiga sabon faɗi.

Sai da Khamis ya ɗago kansa sannan ya ce,

“Alhaji har yanzu Aisha a matsayin matata take, kuma da shirin tafiya da ita na zo. Sai dai ina son ku yi mata faɗa ta ji tsoron Allah, kuma ta guji ƙawayen banza.”

Wata irin sassanyar ajiyar zuciya Aisha ta sauke, don a yadda Khamis ya yi fushi ta ɗauka sakinta zai yi. Kallon shi ta yi tare da lumshe idanu, cikin ranta kuma tana jin babu nagartaccen miji kamar shi a zamanin yanzu. ya kama ta dumu-dumu da laifi, amma sai ya rufa mata asiri, kuma ya kasa rabuwa da ita.

‘Allah ka yaye mini kishin da ke son raba ni da mijina.’ Abin da ta faɗa a ranta tare da buɗe idanu ta dubi mahaifanta.

Basu wani ɓata lokaci ba suka shiga yi mata faɗan ƙawaye, musamman Mommy da ta san da zaman Zuzee, cewa ta yi,

“Wallahi Aisha ki fita batun ƙawaye, kin ga wannan ƙawar taki Zuzu take ko wa? Allah idan ba ki rabu da ita ba sai ta raba ki da wannan nagartaccen mijin naki.” Alhaji Usman ya ce,

“Au har yanzu suna tare?”

Mommy ta ce,

“Ko kwanaki har nan gidan ta iske ta.”

Aikuwa ta inda yake shiga ba tan yake fita ba. Sai da ya nuna mata zallar ɓacin ransa akan Zuzee, kuma duk akan kunnen Khamis.

Samun kansa ya yi cikin tuhumar Zuzee, musamman da ya ji mahaifan Aisha sun dage suna ta yi mata faɗa a kan ta.

‘In kuwa har sun haɗu a ranar da Aisha ta zo, to ko ita ce ɗayar munafukar?’

Khamis ya tambayi kansa a zuci, tunawa da halin kirki da kuma kamun kan Zuzee da ya sani ya kasa gazgata zuciyarsa, cewa ya yi a ransa ‘Ko ma wace munafuka ce yau da gobe za ta bayyana ta.’

Maida hankalinsa ga faɗan da mahaifan Aisha ke mata ya yi, in da ya ji suna faɗa mata muddin ta rabu da shi to har ta mutu ba za ta samu kamarsa ba.

Kuma suka nuna mata ta ji tsoron Allah a rayuwarta, duk da ba su san me ta yi ba, asali ma ba sa son ji, don zai iya zame musu damuwa. Sun mata faɗa sosai, daga bisani suka yi mata umarnin ta haɗa kayanta ta bi mijinta.

Khamis ya ji daɗin yadda mahaifan Aisha suka yi mata faɗa, wanda dama albarkacinsu ne ta ci, saboda yana matuƙar ganin girmansu.

Amma da ba don su ba, ba zai sake ta ba, kuma ba zai ce ta dawo mishi gida ba sai ya wahalar da ita, tunda shi ma ya iya muguntar.

Fita Alhaji Usman da Khamis suka yi farfajiyar gidan. Nan Alhaji Usman ya ƙara yi mishi nasihar ya zama adali ga iyalansa, don wani lokaci rashin adalcin namiji ke sa matarshi kangarewa. Godiya Khamis ya yi mishi, daga bisani Alhaji Usman ya dawo cikin gidan.

Ɗakin Mommy ya samu Aisha, Mommyn na yi mata wani faɗan, daga bakin ƙofar da yake tsaye ya ce,

“Maza ki je gashi can yana jiranki. Kuma wallahi duk ranar da mijinki ya sake maido ki to kada ma ki zo nan gidan, tunda kin sauya daga Aishar da muka sani.”

Jiki a mace Aisha ta fito daga ɗakin Mommy, abu biyu ne a ranta. Murnar komawa ɗakinta, da kuma tsoron rashin sanin matsayin da za ta kasance a tare da Khamis a yanzu.

A cikin mota ta iske shi, da alamun ita kaɗai yake jira. Cike da fargaba ta buɗe gidan gaba ta shiga, ba tare da ya kalli inda take ba ya ja motar suka fice daga gidan.

Zuciyar Khamis cike da sosuwa yake tuƙin, kuma dalilin shi ne na rashin sanin yadda zai yi rayuwa da Aisha a yanzu, shi dai ya san ba zai iya sake mata ba, saboda laifin da ta yi ya tafiyar da kaso mai yawa na yardar da ya yi mata.

Ita ma ɗin a cunkushe zuciyarta take, kunyar Khamis ce mamaye da ita.

‘Yanzu da wane ido zan ci gaba da kallon mijina?’ Tambayar da ta yi ma kanta kenan, ba ta da amsa, saboda zai yi wahala wannan laifin ya wuce, sai dai kawai a riƙa kallon kallo.

Har suka isa gida ba wanda ya tanka ma wani, sai dai saƙe-saƙen da kowannen su ke yi a zuci.

Tunda Aisha ta fito a motar ta ji wani irin daɗi a ranta. Lallai gidan miji daban ne, musamman mijin da zuciya ke so.

Shigarta falo ta yi daidai da fitowar Maryam daga ɗakinta. Ras! Gaban kowacce ya faɗi. Kishi ne ya taso ma Maryam a zuciya, ji ta riƙa yi ina ma Aishar ta dauwama a gidansu, saboda da ba ta nan gidan ya fi yi mata daɗi.

Aisha ma tsanar Maryam ce ta cigaba da taso mata. Wadda tuni akwai ta a ranta, sai dai rashin cimma burinta na zubar ma Maryam da ciki ya ƙara ta’azzara ta.

Yaƙe Maryam ta yi mata tare da ɗan hugging, lokaci ɗaya kuma ta ce,

“Oyoyo Umman Haneef.”

Murmushi mai sauti kaɗai Aisha ta yi, wanda kuma iyakar shi baki, sannan ta ce,

“Mai ciki! Na same ku lafiya?” Maryam ta ce,

“Alhamdulillah lafiya lau.”

Khamis ne ya shigo falon, hakan ya sa Maryam ta koma wurinsa. Cikin karyayyiyar murya ta yi mishi sannu da zuwa, hannunsa cikin nata ya amsa, lokaci ɗaya kuma ya bi Aisha da idanu lokacin da ta shige ɗakinta.

Maido dubansa ya yi ga Maryam ya ce,

“Kin ga na daɗe ko?”

Girgiza kai ta yi.

“A’a.”

Kafe ta da idanu ya yi, sai ya ga ta yi jirin-jirin, sosai ya fahimci kishi ne ke cin ta, don haka ya ja ta ɗakinta suka zauna a gefen gado.

Tambayar ta abinci ya yi, sai ta ce, “Ba ka ci a gidan surukan naka ba?”

Maido da ita kan cinyarsa ya yi tare da faɗin,

“An mini tayi na ce A’a.”

Tambayar sa ta yi,

“Saboda me?”

Sai da ya haɗe musu fuskokinsu sannan ya ce,

“Na fi son na ci a tare da babyna da kuma Mom ɗinsa.”

Hannunsa na shafar cikinta ya ƙarashe maganar. Zai janye hannun daga cikin ne ta riƙe shi tare da faɗin,

“Lallai kana ji da babynmu.”

Cike da son ta ya ce,

“Ai faɗi ɓarnar baki ma, ni na san babu wasu kalmomin da za su iya fasalta son da nake ma cikin nan naki, sai dai kawai na bar ma zuciyata.”

Ko bai faɗa ba ta yarda, saboda tunda ta samu cikin soyayyar da yake mata ta nunku sau ba adadi. ‘Yar dariya ta yi sannan ta ce, “Uhm, Allah ya sa dai kada soyayyar da kake mini ta koma kan babynmu.”

Ya fahimci me take nufi, kuncinta ya ɗan ja yana dariya.

“Za ki yi kishi da ɗan da kika haifa kenan?”

A narke ta ce,

“A’a ni ban ce ba, mai son uwa ai ya so ɗanta.”

Ya ce,

“Hakane Mairo. Soyayyar ɗa daban, soyayyar mata daban. Kuma soyayyar mata ce ke sa a so ɗan da za ta haifa ko?”

Kai Maryam ta ɗaga, ya ce,

“Toh ina bala’in son ki Maryam, so kuma na haƙiiiiƙa.”

Rungume shi ta yi, cikin ranta kuma tana jin wani irin farinciki, farincikin da ya mantar da ita takaicin dawowar Aysha a gidan.

“Nima ina sonka mijina”

Ta faɗa tare da ci gaba da nuna mishi son da take mishi a fili. Sai da suka wadatar da juna da soyayya sannan suka faɗa banɗaki suka yi wanka.

Bayan sun kimtsa jikinsu ne Maryam ta kawo mishi dinner. Bayan ya gama ne yake faɗa mata tunda tana iya girki yanzu, to Aisha ba za ta sake yi mata girki ba.

Maryam da ma haka take so, ba za ta yi ma Aisha butulci ba don har ga Allah tana girkin da take so. Sai dai tana lura da yadda Aishar ke jin haushin ta mata girki, ita kuma ta kwana da miji, to wannan ne ba ta so, da daɗi da ba daɗi za ta daure ta riƙa yi da kanta.

Kimtsa wurin da Khamis ya gama cin abinci ta yi. A tsammaninta ɗakinta zai kwana, sai ta ga ya kwashi wayoyinsa tare da faɗin, “A maido Haneefa ku kwana a tare ko?”

Marairaicewa ta yi tare da shigewa jikinshi ta ce,

“Ba a nan za ka kwana ba?”

Kwantar mata da kai ya yi a ƙirjinsa tare da yin magana ƙasa-ƙasa ya ce,

“Sorry, kin ga mako ɗaya muna tare, ki bari ita ma na je wurinta.” Maryam ba ta yi musu ba, adalci shi ne abin da take son mijinsu ya ginu a kai, cewa ta yi,

“Ba damuwa, a maido mini Haneefar a nan.”

Khamis ya ji daɗin haka, riƙe ta yayi a ƙirjinsa na wani lokaci, bayan wasu ƴan daƙiƙu suka rabu da juna.

Ɗakin Aisha ya nufa, inda ya same ta zaune a gefen gado ta yi jugum. Raɓawa ya yi gefenta ya ɗauki Haneefa da ke ta sharar bacci, daga bisani ya ce mata,

“Ki same ni a ɗakinta.”

Bai jira jin me za ta ce ba ya wuce ya kai Haneefa ɗakin Maryam. Sai da Maryam ta hargitsa mishi lissafi sannan ta rabu da shi. Cikin wata irin murya ya ce,

“Haba Mairo!”

Dariya ta kama yi ciki-ciki sannan ta ce,

“Na bar ma uwargida ta ƙarasa aikin.”

Shagwaɓewa ya yi kamar wani yaro,

“Don Allah.”

Cewa ta yi,

“Sake kusanto ka kamar shiga hurumin madam Indo ne, don haka ka je ta ƙarasa maka aikin.”

Duk yadda ya so Maryam ta zo jikinsa amma ta ƙiya. murmujewa ya yi tare da faɗin,

“Za ki zo hannuna.”

Ficewa ya yi daga ɗakin yana dariya tare da ja mata ƙofar.

Key ta sanya sannan ta kwanta zuciyarta cike da kewar mijinta.

Khamis na shiga ɗakinsa ya ji ƙamshin turaren Aisha na tashi, da alamu ta shigo ta fita.

Kwantawa ya yi yana lissafin yadda zai buɗe sabon shafin zama da Aisha. Ji ya yi ta turo ƙofar, idanunsa a kanta har ta shigo ɗakin.

‘Kyakkyawar mace mai nagarta, amma kishi na neman halaka ta.’

Cikin ransa yayi wannan maganar.

Ita kanta ɗin ta san kwana a ɗakinsa kamar goguwar laifinta ne, don haka ta yi shirin bacci cikin doguwar riga mai ɗaukar hankali. Kuma da alamun rigar ta ɗauki hankalinsa, saboda kallon da ta ga yana yi mata lokacin da ta shigo.

Gabansa ta durƙusa tare da ruƙo hannunsa.

“Abban Haneef.”

Shiru Khamis ya yi domin bai zaci haka ba.

Ita kuwa gabanta ne ya riƙa faɗuwa saboda shirun da ya yi, gani take kamar har yanzu bai huce daga fushin da yake da ita ba.

“Abban Haneef don Allah ka yafe mini a bisa kuskuren da na aikata, In Sha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba.”

Cikin muryar kuka ta yi wannan magana, wadda kuma umurni ne na mahaifiyarta, cewa idan sun dawo gida ta bashi haƙuri, hakan zai ƙara mata ƙima a idonsa.

Jikin Khamis ne ya yi sanyi, shiryuwa da nadamarta ita yake fata, don haka ne ya tashi zaune, tare da ƙare ma fuskarta kallo, ya ɗauka zai ga hawaye na zuba, sai ya ga fuskar ƙamas, abin da ranshi ya bashi wannan kukan bai kai zuci ba. Sai da ya ɓata ‘yan daƙiƙu kafin ya ce,

“Aisha aikin gama ya gama fa, kawai ki yi ƙoƙarin gyara rayuwarki. Sannan da ban yi haƙuri ba ma ba za ki dawo gidannan ba. Abin da kuma nake son ki sani ni ba zan raba ki da yi mana hidima ba a ranar aikinki, duk abin da ki ka girka Maryam za ta ci, sai dai ki ji tsoron Allah, idan ki ka cutar da ita ke da Allah.”

Shiru ya yi, wanda ya ba Aishar damar faɗin,

“In Sha Allahu ba za a sake ba.” Cewa ya yi,

“Allah ya amince, tashi ki yi kwanciyarki.”

Jiki a sanyaye ta kashe fitilar ɗakin, sannan ta zo nesa da shi a kan gadon ta kwanta. Gaba ɗaya jikinta faɗa mata yake Abban Haneef bai yi haƙuri ba, don a yadda ta san shi idan har ya haƙura, to da dariya faɗan zai ƙare.

Cikin bazata ta ji ya kira sunanta, tana amsawa ya ɗora da cewa, “Matso jikina ki kwanta.”

Hannu ta sa ta share hawayen da suka gangaro mata, sannan ta koma cikin bayansa ta kwanta, hannunta da ke zagaye da shi ya riƙe yana ɗan wasa da shi.

*******

Zuzee kuwa tunda Aisha ta shaida mata ta koma ta nemi baccin da ta fara ta rasa. Wani irin zafi ne ya cika mata ƙahon zuciya, wanda bai rasa nasaba da hassada gami da baƙinciki, burinta shi ne Aisha ta dauwama a gidansu, don tunda ta ji Khamis ya ƙi zuwa wurin Aishar ta fara murna saboda Aishar ce ba ta so, tana tare da ita ne kawai don ta rusa mata rayuwa gami da salwantar mata da farincikin da take jin haushin ita ba ta da shi.

A zahirin gaskiya Zuzee Khamis take so, rashin yadda za ta yi ne ya sa ta komawa son Abdul. Ta kuma ɗaukar ma ranta in dai Aisha ba ta koma ba, to ko da tsafi ne sai ta auri Khamis, toh gashi kuma tun ba a je ko ina ba Aishar ta koma.

Zaune ta tashi a kan ɗan gadonta, tare da zabga ashariya cikin ranta. ‘Wallahi ko ana ha maza ha mata nima sai na ɗanɗani zumar da Aisha ke lasa, mace ce ita, nima mace ce, don haka ba dalilin da za ta fi ni damawa a rayuwa. Dole ne na ɓullo mata ta wata hanyar da zan kai ta na baro.’

Cikin ranta take magana, tare da yin ƙwafa a fili.

Mahaifiyarta da ke kwance a kan katifa ce ta ji alamun kamar a zaune take, ɗan ɗaga kanta ta yi tare da haskawa da fitilar wayarta mai botira,

“Wai zaman me ki ke yi ba ki kwanta ba.”

Kakkaɓe kakkaɓen ƙarya Zuzee ta shiga yi.

“Wani abu ne nake jin kamar yana cizo na.”

“Hmm, gado ne sai kin ga dama ki gyara, ba dole ƙwari su maƙale miki ba.”

Maman su Zuzee na faɗin haka ta koma ta yi kwanciyarta.

Ita ma Zuzee ɗin kwantawa ta yi, sai dai muguwar hassadarta ba ta bari ta rubtsa ba.

Washe gari ko karin kumallo ba ta yi ba ta ɗauki mayafi.

“Sai ina tun da wannan farar safiyar?”

Nahaifiyarta da ke tsakar gida a gaban murhu tana dama koko ta tambaye ta.

Marairaicewa Zuzee ta yi kamar ba ta da lafiya.

“Asibiti, yau ce ranar da likita ya ce in koma.”

Da yake mamansu ta san da batun asibitin sai ta ce,

“To, ki sha kokon mana kafin ki tafi.”

Yamutse fuska Zuzee ta yi.

“A’a na ƙoshi.”

Fatan dawowa lafiya mahaifiyarta ta yi mata sannan ta wuce.

Tun zuwan farko da Zuzee ta yi asibiti likita ya sallame ta, shi ma Malaria ce ta kai ta. Ta yi ma mahaifiyarta ƙaryar sake komawa ganin likita ne duk don ta samu ƙafar yawo.

Kai tsaye gidan mutuminta ta nufa. Shi ba wani babban malami ne ba, amma iya aikinsa ya sa mata na zuwa a wurinsa. Yanzu haka Zuzee ta iske wasu mata biyu masu zaman kansu a zaurensa, domin kowacce fuskarta ta ci bleacing, ga wasu matsattsun riga da skirt a jikinsu.

Sai da ya sallame su sannan ya juya wurin Zuzee da abin duniya ya dame ta.

“Yaya dai ranki ya daɗe?”

Ya faɗa yana ta washe haƙoran gaba.

Hannu Zuzee ta kai kanta ta gyara ɗaurin ɗankwalinta mai taken ture ka ga tsiya sannan ta yi ƙwafa,

“Wai ka san shegiyar nan ta koma jiya?”

Tunda ta fara magana ya kafe ta da idanu yana cigaba da washe baki, sai da ta kai ƙarshe sannan ya ce,

“Ke don Allah! Yanzu duk girman laifin da mijin ya kama ta tana shirin aikatawa sai da ta koma?” Zuzee ta ce,

“Wallahi Malam. Ba zan ɓoye maka ba bana son Asha, kishi nake da ita, don a duniya ba namijin da nake so sama da mijinta, to ina gudun kada duniya ta zage ni ne shi ya sa ban kutsa kai a rayuwar shi ba, daga ƙarshe na koma ma wannan miskilin yayan nata, shi ma na ga mugun hali ne da shi, wanda madamar na same shi sai na gyara ma shege zama.”

Shi kam tsiwar Zuzee birge shi take, shi ya sa idan tana magana baya sa mata baki sai ta gama.

“Yanzu faɗa mini, ya kike so a yi ne?”

Ya faɗa tare da gyara zama, lokaci ɗaya kuma ya ci gaba da zana ƙasar da ke gabanshi.

“So nake in tura ta ta bi malamai, daga bisani in tona mata asiri aurenta ya mutu, ni kuma in shige ɗakinta ko da bala’i.”

‘Yar guntuwar dariya ya yi, lokaci ɗaya kuma ya ɗauke idanunsa daga kan ƙasar ya dube ta. “Muddin ki ka koya mata bin Malamai to ke ma ba za ki zauna lafiya da ita ba.”

Cikin isa Zuzee ta ce,

“Kai na fi ƙarfinta wallahi.”

Ya ce,

“To duk da haka dai wannan ba mafita ba ce, ki ci gaba da bata shawarwarin da za ta ga kamar kina sonta. Sauran aikin kuma ki bar mana zamu ƙarasa.”

Fuskarsa a murtuke ya ƙarashe maganar, duk don ta gane babu wasa a cikinta.

Shewa Zuzee ta yi don ta yarda da maganar sa.

“Aikuwa na gode, muddin kuma ka yi mini aiki a kanta to zan ƙara maka akan tukwuicin da nake baka.”

Gira ya ɗaga mata sannan ya ce, “Nima da na ƙara miki wani aikin a kyauta.”

Hira suka ci gaba da yi, a nan ya ƙara ba Zuzee wasu laƙunƙuna na farinjini, godiya ta yi mishi, sannan ta tafi.

Tana tsaye a bakin titi kuwa sai ga Abdul ɗin gidan su Aisha ya faka motarsa a gaba kaɗan da ita. A tsammaninta don ita ya tsaya, mafarin ta ƙarasa wurin motar, sai dai yana ganinta bayan ya fito a motar ya ƙara murtuke fuska.

“Yaya Abdul ina kwana.”

Ta faɗa tana kisisina, sheƙeƙe ya kalle ta, sannan ya amsa da, “Lafiya.”

Tare da tsallaka titin ya barta nan.

Wani shago ta hange shi ya shiga, gululun baƙincikin yarfin da ya yi mata ne ya tokare mata zuciya. “Ɗan banza mai baƙin hali.”

Ta faɗa a fili, sannan ta shige Napep ɗin da ta tsaida.

Aisha kuwa tuni abubuwa sun canja, ta fahimci matsayi da ƙimarta sun ragu a wurin Khamis, ba ta kuma yi yunƙurin dawo da su ba saboda cutar kishin nan tana a ranta.

Tsakaninta da Maryam kuwa kowa ya san ba son ta take ba, to wannan ƙiyayya da take mata ta ƙaru kuma ta fito fili, saboda tunda ta dawo ta canja takunta. ‘Yar hirar da suke yi da Maryam ɗin dama ba ta Allah da Annabi ba ce, da kuma ta ga ta kasa cimma baƙin ƙudurinta a kan Maryam sai ta daina. Idan zasu haɗu a ƙofar allura Ausha ba ta ko kallon Maryam.

Itama Maryam ɗin da yake miskilar kanta ce sai ta daina kula ta, yadda Aishar ke shan ƙamshi haka ita ma take sha, a cikin ranta kuma ta riƙa cewa ‘Ba ni na kar zomon ba, ratayar ma ban san wanda aka ba mawa ba, don haka kishiya ba ta isa in bi ta ba.’

Sai dai wani salon Maryam shi ne, ‘Yar tsamar da ke tsakaninta da Aisha ba ta hana ta ci gaba da kula da su Haneefa ba. Duk wani abu da zai faranta ran yaran Maryam na yin shi ko a gaban waye.

Wannan abu kuwa na ci ma Aisha tuwo a ƙwarya, domin ta lura da yadda yaran ke ƙara son Maryam, sannan ga matsayi a wurin Khamis, don da bakinsa yake faɗa mata yadda Maryam ke ma yaransa yana jin daɗinsa, baki kawai ta taɓe, ta kuma ƙudiri janye yaranta kamar yadda ta samu shawara daga wurin Jamsy da kuma Zuzee, don har yanzu suna tare a chat, saboda ta kasa gane su ne manyan maƙiyanta.

Duk wani abu marar kyau da za ta aikata ba ta neman shawarar danginta, sai dai su Zuzee.

Zaune Maryam take a falo ita da yaran suna kallo, kasantuwar cikin Maryam ya shiga wata na bakwai, ta shi ma ya fara yi mata wahala.

Aiken Haneef ta yi kitchen ya ɗauko mata kofi za ta tsiyaya lemu. Tana ji kafin ya shiga kitchen ɗin Aisha ta kira shi.

“Anty zan ɗauko ma kofi.”

Haneef ɗin ya ce. Daga can Aisha ta ce,

“Tunda Anty ta fi uwarka sai ka je ka ɗauko mata.”

Yaron ya san gatse, don haka ya je kiran mahaifiyarshi.

Maido shi ta yi a kan ya kira mata Haneefa. Tambayar shi Maryam ta yi,

“Ina kifin?”

Cewa ya yi,

“Mommy ta hana ni.”

Ajiyar zuciya mai nauyi Maryam ta sauke sannan ta ce,

“To da kyau.”

Tashi Haneefa ta yi tare da bin bayan Haneef. Suna zuwa Aisha ta zaunar da su tare da sassauta murya. Cusa musu tsanar Maryam ta shiga yi, inda ta ce,

“Me yasa ku ke son zuwa wurin waccan?”

Haneef ne ya ce,

“Mimmy tana da kirki ai.”

Haneefa kuma ta ce,

“Tana ba mu wayarta mu yi game, kuma tana bamu sweet.”

A yadda Aisha ta ga soyayyar Maryam a tare da yaranta ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ƙudurtar raba su da Maryam ta yi a ranta, cewa ta yi,

“Waccan da kuke gani fa muguwa ce.”

Idanu duka suka zaro.

Haneefa ta ce,

“Muguwa Mommy?”

Aisha ta ce,

“Eh mana, ba ta so na, ba ku ga kwana bakwai bana nan ba?”

Suka ce,

“Eh.” a tare.

Ta ce,

“To ita ce ta sa Abbanku ya kore ni, ta ce sai ta kashe mu.”

Nan fa ta yi ta kitsa ma yaranta mugun abu, cikin ɗan lokaci ta sanya musu tsanar Maryam, inda ta ɗauko musu wannan ƙaho da layu da Zuzee ta aje, ta nuna musu, ta kuma faɗa musu Maryam ce ta sanya aljannu su aje shi wai za’a kashe su.

Haneefa a tsorace ta ce,

“Ni dai ban sake kwana a ɗakinta.”

Aisha da haka take son ji ta ce “Yauwa my daughter.”

Maryam kuwa hana Haneef ɗauko mata kofin da Aisha ta yi ya tsaya mata a rai, lemun da take son sha ma ta ji duk bata buƙata saboda ta lura wani sabon makirci Aisha ke son ƙullawa, musamman da ta ga ta kira Haneefa.

Tashi ta yi daga falon ta koma ɗakinta. Ba ta shakkar duk abin da Aisha za ta yi, sai dai ba ta son ta ƙule ta ne har ta fito da asalin nata rashin kirkin.

Zama ta yi a ƙasan carpet tare da miƙe ƙafafu, saboda ta fi jin daɗin wannan zaman.

Cikinta da ya fara motsi ta taɓa, cikin ranta ta ce ‘Allah ka sauke ni lafiya, domin na wuce gorin ‘ya’ya.’

Yara kuwa sun ɗauki huɗubar da uwarsu ta yi musu sun riƙe. Gaba ɗaya sun daina zuwa ɗakin Maryam, falo ma sai idan Maryam ɗin na ɗakinta suke fitowa.

Ita ma Maryam ɗin tuni ta zuciya, ko ba su daina zuwa wurinta ba dama ba za ta neme su ba.

Yaran ne ke ta wasa a falon, can sai Haneefa ta ce ma Haneef, “Yaya, in ce bamu ƙara zuwa ɗakin Anty tunda muguwa ce ko? Asiri ta ke.”

Shiru Haneef ya yi yana duban Maryam da a kan kunnenta Haneefa ta yi magana.

Gaban Maryam na wata irin faɗuwa ta murɗe ma Haneefa kunne,

“Ke, me uwarku take cewa a kaina?”

Zafi da kuma tsoron Maryam ɗin ne suka sa Hanneefa sakin ƙara, da gudu Haneef ya ruga ɗakin Aisha, a bakin ƙofa suka yi kiciɓus saboda ita ma ta ji kukan. A tsorace ya ce,

“Mommy ga Anty can na dukan Haneefa.”

A fusace Aisha ta ƙaraso falon, tun kafin ta isa gaban Maryam ta ce, “Ke! Ahir ɗinki da taɓa mini yara wallahi!”

Maryam da takaici ya zo ma wuya ta yi magana cikin sababi,

“Dama me zan ji idan na taɓa yara, Uwarsu ce daidai ni, ita zan taɓa, kuma na taɓa banza.”

Da sauri Aisha ta kai mata cafka tana shirin cakumar ta, baya Maryam ta ja ta ce,

“Alo tsiya alo danja! Amma kada ki fara gigin taɓa ni. Na fahimci cutar kishi ce har yanzu ta ƙi rabuwa da ke, kuma ban ga laifin cutar da ta maƙale miki ba, tunda mijinki a ka aura. Dole ki yi kishi, amma ina shawartar ki da kada ki yi na hauka wanda zai raba ki da Allah.”

Sosai maganar Maryam ta sa Aisha jin kamar raddi ne ta yi mata a kan zubar mata ciki da ta yi yunƙurin yi, baƙaƙen manganu masu zafi Aisha ta ci gaba da faɗa mata.

“Ke har kina da bakin ce ma wani ya ji tsoron Allah, munafuka gandun matsafa, kuma wannan shegen cikin naki idan ba ki yi sannu ba sai na sa kin haife ɗan banza ba da shiri ba.”

Shewa Maryam ta buga tare da faɗin,

“Ni ba zan zagi yaranki ba don na san darajar Ubansu. Amma ki sani cikina ya fi ƙarfinki, li’ilafi ƙuraishin, aniyarki ta bi ki ‘yar banza.”

Khamis da tun a farfajiyar gidan ya jiyo hayaniyar su, falo ya shigo da sauri. Sallallami ya shiga yi tare da faɗin, “Lafiya?”

Maryam na ganinshi ta fashe da kukan kissa tare da nuna mishi Aisha,

“Wai Aisha ce ta tara yaranta ta na faɗa musu ni muguwa ce kada su sake cin abin hannuna, wai zan kashe su.”

Wani irin kallo Khamis ya yi ma Aisha, don shi ma yaran sun faɗa mishi a hanyar dawowarsu daga makaranta, ya bari sai ya dawo ne ya yi mata magana.

Aisha da ta ga ɓacin rai tsantsa a fuskar Khamis ta ce,

“To ƙarya na yi mata, ba muguwar ba ce?”

Maryam ta ce,

“Wallahi Allah ya isa tsakanina da ke.”

Tana kuka ta ƙarashe maganar.

Haƙuri Khamis ya shiga ba Maryam, da hannunsa ya share mata hawaye ya ce,

“Sorry baby, Allah ya san ai ke ba muguwa ba ce, ni ma da ke mijinki na yaba da nagartarki, don haka ki barta da Allah.”

Yana faɗin haka ya kama hannun Maryam ɗin ya ce,

“Mu je.”

Ƙin tafiya ta yi, ya ce,

“Ko sai na ɗauke ki ne?”

A ƙirjinsa ta kwanta cikin kissa ta ce,

“Ai mun maka nauyi.”

Ya ce,

“Ke da wa?”

Cikin muryar yara ta ce,

“Ni da jalilinka.”

Murmushi kawai ya yi sannan ya ja hannunta suka tafi ɗaki.

Aisha kuwa kishi ne ya zo mata wuya, da wani irin mugun kallo ta bi su har suka shige ɗaki.

Ba ta matsa daga inda take ba Khamis ya fito,

“Wallahi Aisha kin ji kunya a rayuwarki, ke mai tabo ba a ce miki muguwa ba sai ita?”

“Hmm akwai babban marar kunya ma irin ka, a gaban ‘ya’yanka za ka tsaya wata na maka karuwanci”

Murmushin takaici ya yi ya ce, “Kema ai ba a hana ki ba, kuma tunda matata ce ba ubanda ya isa ya hana ni. Sharri kuma ki ci gaba da yi, amma ina gargaɗinki da kada ki ƙara ɓata mini mata a wurin yara.”

“Ɓatawa ba zan fasa ba wallahi, yadda waccan ta raba ni da farincikina ita ma sai na raba ta da nata.”

Maganganu ta shiga faɗa ma Khamis, yana maida martani ta jawo Haneef da duk a kan idonsu komai ya faru,

“Ka ga irin cin fuskar da ubanku ke mini saboda waccan muguwar.”

Rufe bakinta ya yi daidai da saukar zazzafan mari a kumcinta.

“Ni za ki ɓata a wurin yarana? To wallahi kina gab da gamuwa da fushina.”

“Fushinka fushin Allah ne?, Mugu azzalumi.”

Bai bi ta kanta ba ya ja hannun yaransa suka fice waje.

Kuka Aisha ta shiga yi, kafin ka ce me ta ɗauko mayafi za ta bar gidan.

Kiciɓus suka yi da Maryam a falo, aikuwa Maryam ta rafka guɗa, “Sai ni ‘yar mutan KT, mai sa kishiya ta bar gidan miji ba da shiri ba.”

Kukan kura Aisha ta yi ta yo kanta, Allah ya taimake ta Khamis ya shigo da gudu ya janye ta.

“Kina taɓa ta sai ranki ya ɓaci.”

Ya faɗi a fusace.

Gululun da ke tokare da wuyan Aisha ne ya fashe, tana wani irin kuka ta ce,

“Abban Haneef ka ji tsoron Allah, ka faɗa ma matarka ta fita a idona, idan ba haka ba sai na kashe ta.”

A yadda Aisha ta ƙarashe maganar kai ka san ba cikin hayyancita take ba. Ci gaba da magana ta yi da faɗin,

“Meye nata a nawa, na fito me ya sa ta tsokane ni?”.

Khamis da ke jin kukan Aisha har a ransa ya dubi Maryam,

“Me ya sa kika tanka mata? Maryam zan aje komai a gefe na ɓata miki rai wallahi, bana son iskancin banza da wofi.

Me ya sa kuke son sa mini hawan jini ne?”

Faɗa ya shiga zazzaga musu su duka, ya kuma nuna musu duk wadda ta sake yi mishi faɗa wallahi sai dai ta tafi gidansu.

Ɗaki Aisha ta ja yaranta. Maryam kuma ta shige ɗakinta tana turo baki. A zatonta Khamis zai biyo ta. Aikuwa sai ya wuce ɗakinsa shima.

A daren ranar ma ɗakinsa ya kwana shi kaɗai, washegari kuma tunda safe ya fice ya bar musu gidan. Yara ma sai dai ya turo Sani ya kai su school.

<< Kishiyar Katsina 13Kishiyar Katsina 15 >>

1 thought on “Kishiyar Katsina 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×