Tunda suka ɗauki hanyar Katsina Maryam take bacci, sakamakon allurar da Dini ya yi mata. Ba ita ta farka ba sai da suka zo roundabout ɗin Welcome to Katsina. Rikici ta so sanya musu a motar, Hajiyarmu da ke gefenta ta shiga ririta ta kamar ƙwai, har Allah ya sa gaba ɗaya motocin suka isa unguwarsu Maryam lafiya.
Duk da zuwansu Maryam ba na lafiya bane, amma hakan bai hana duk wanda ke gidan murnar zuwansu ba, saboda samun arziƙin sauka lafiya. Cike gidan yake da duk wani ɗa da aka haifa a gidan. Dangi na kusa da ma. . .
Ina son ƙaran bayani akan kishiyar Katsina.