Skip to content
Part 18 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Tunda suka ɗauki hanyar Katsina Maryam take bacci, sakamakon allurar da Dini ya yi mata. Ba ita ta farka ba sai da suka zo roundabout ɗin Welcome to Katsina. Rikici ta so sanya musu a motar, Hajiyarmu da ke gefenta ta shiga ririta ta kamar ƙwai, har Allah ya sa gaba ɗaya motocin suka isa unguwarsu Maryam lafiya.

Duk da zuwansu Maryam ba na lafiya bane, amma hakan bai hana duk wanda ke gidan murnar zuwansu ba, saboda samun arziƙin sauka lafiya. Cike gidan yake da duk wani ɗa da aka haifa a gidan. Dangi na kusa da maƙwafta ma duk sun zo tarbar Maryam da suke ta jimamin halin da aka basu labarin ta shiga.

Yadda mutanen gidan suka ga Maryam a natse sun yi tsammanin ta samu lafiya. Sai da ta fara magana da Hajiyarmu ne jikinsu ya yi sanyi, inda ta ce,

“Wai Hajiyarmu biki ake ko suna?”

Saboda ta gan su cike da gidan. Ga kuma yara can daga gefe suna ta guje-guje.

Maido mata tambaya Hajiyarmu ta yi,

“Me kika gani Maryam?”

Cewa ta yi,

“Na ga gidan cike da dangi da maƙwafta ne.”

Domin ba wanda ba ta gane fuskarsa ba, Hajiyarmu ta ce,

“Duk sannu da zuwa suka zo yi miki.”

Shiru ta yi tare da kallon su ɗaya bayan ɗaya, duk wanda ta haɗa ido da shi sai ta yi mishi dariya. Su Asma’u kuwa tuni sun fara kuka, ba kuma wanda ya ce musu don me, saboda kowa ya girgiza da ganin halin da Maryam ta ke ciki. Musamman mahaifiyarta da ta ɗauki nauyin cikinta na tsawon wata tara, bayan ta haife ta kuma ci gaba da rainon ta har ta kai shekaru ashirin a duniya sannan ta aurar da ita, shi ne kuma daga gidan auren aka maido mata ita mahaukaciya, duk da ita lafiyayya ta basu.

“Maryam haka Allah ya yi dake?” Ta faɗa bayan ta dafa kafaɗun Maryam, cikin ranta kuma tana jin wani irin tashin hankalin da bai misaltuwa. Sha’anin soyayyar uwa da ɗa abu ne mai girma so sai .

Sauran yayyenta maza kuwa sallallami wasu suka shiga yi, wasu kam sai dai suka yi gum saboda kaɗuwa da ganin halin da ƙanwarsu ke ciki.

Sosai kaɗuwarsu ta ba su Rahama tausayi, don suma sun samu kansu a cikin irin wannan yanayin.

A falon babansu Maryam suka sauka, saboda ya fi faɗin da zai ɗauke su. Khamis da Rahama ne akan kujera two seater, Hajiyarmu da Hajiyarsu Haupha kuma akan kujera three seater, inda suka sa Maryam a tsakiya.

Babansu Maryam da Mamansu kuma kowane akan kujera one seater. Sauran ‘yan gidan mata zaune a ƙasan carpet, mazan kuwa duk a tsaye suke sun raɓu a gefen kujerun, saboda da an gaisa ficewa za su yi.

Sannu da zuwa da kuma jajen halin da Maryam ta shiga suka yi ma juna. Ita kuwa sai raba idanu take. Babban yayansu Alhaji Kabir da ke zaune a hannun kujerar da Mamansu take ta duba, shi ma dubanta ya yi,

“Ƙanwata.”

Murmushi ta yi mishi tare da faɗin,

“Alhaji Yaya, na same ku lafiya?”

Ya ce,

“Lafiya lau, ya jikin?”

Idanunta a kan Khamis da ke ta kallon ta ta ce,

“Da sauki, ciwon da ke a cikina ya warke, shi kuma ɗan da na haifa ya rasu.”

Vikin raunin murya ta ƙarasa maganar, wanda duk sai da ta ba kowa tausayi.

“Allah ya jiƙan shi, ke kuma Allah ya baki lafiya.”

Ta ce,

“Amin Alhaji Yaya.”

Bayan duk an yi musu sannu da zuwa, Khamis da Rahama suka yi ma mahaifan Maryam gaisuwa ta musamman. Sai da Mamansu Maryam ta ɗauke idanunta a kan Maryam da ke ci gaba da raba idanu a ɗakin sannan ta amsa gaisuwar da suka yi mata. Babansu Maryam ne ya ce ma Khamis,

“Ya Ƙoƙarin kula da lafiyar Maryam?”

Don tuni Hajiyarmu ta shaida musu yadda Khamis ke ta ƙoƙarin fiddo kuɗaɗe yana badawa domin Maryam ta samu ingatacciyar lafiya. Murmushi kawai Khamis ya yi, saboda shi gani yake wajibinsa ne kula da Maryam. Godiya Babansu Maryam da Alhaji Kabir suka yi mishi.

Tun maganar da Maryam ta yi da Alhaji Kabir bata sake magana ba, tsammanin babansu Maryam har yanzu nutsuwar na nan.

Ce mata ya yi,

“Maryam ba a gaishe da Baba?” Baki ta turo tare da faɗin, “Gaisuwar da na yi maka fa?”

Ya ce,

“Yaushe kika gaishe ni?”

Tamkar ƙaramar yarinya ta ce, “Jiya mana.”

Gaba ɗaya yaran da ke wurin ba wanda bai yi dariya ba. Masu hankalin kuwa ƙunci da tausayin Maryam suka shiga.

‘Yar ƙara ta fasa kamar ƙaramar yarinyar da aka ƙwace ma alewa, lokaci ɗaya kuma ta da kalli Hajiyarmu da ke gefenta tare da nuna yaran,

“Kin gani ko suna mini dariya.” Haƙuri Hajiyarmu ta bata, sannan ta kori yaran waje. Gwalo da dariya Maryam ta raka su da shi. Sauran manyan ma duk fita suka yi, sai Alhaji Kabir kaɗai.

Mamansu Maryam da ta kasa jure ganin halin da ɗiyarta ke ci sai ta fashe da kuka. Khamis da Rahama kuwa sai dai suka yi ƙasa da kansu saboda suma suna jin makamncin irin abin da Mamansu Maryam ke ji.

Alhajinsu Maryam ne ya ce mata, “Toh hwa! Kuka kuma?”

A yadda ya ƙarashe maganar shi ma kamar zai yi kukan.

“Alhaji dubi yadda ‘yata ta koma, hauka kenan ko?”

Alhajinsu Maryam ya ce,

“Na gani. Addu’a za mu yi mata.”

Maryam na ganin mamanta na kuka ta dubi Hajiyarmu.

“Kalla, kuka take.”

Hajiyarmu ta ce,

“Na gani Maryam.”

Maryam ta ce,

“To me aka yi mata?”

Amsa ta bata da,

“Saboda ba ki da lafiya ne.”

Shiru Maryam ta yi daga bisani ta ce,

“Idan na warke za ta daina kuka?”

Hajiyarmu ta ce,

“Eh.”

Maryam ta ce,

“Toh Allah ya bani lafiya, nima bana jin daɗin yanayin da nake ciki, kullum ciwon kai, ga aiki a jikina. Don ma wancan mutumin yana kula da ni.”

Ta nuna musu Khamis.

Wani irin tausayi ta ba kowa. Mamanta kuwa ji ta riƙa kamar ita ke ciwon. Kuka mai isarta ta yi, duk kuwa da kawaicinta a kan ‘ya’yanta, amma sai gashi ta kasa jure halin da Maryam ke ciki.

Bayan fitar kowa a ɗakin ne Alhajinsu Maryam ya yi mata magana saboda su kaɗai aka bari. “Haba don Allah, addu’ar samun lafiya za ki yi mata ba kuka ba.”

“Alhaji sai da na ce Maryam ba za ta auri mai mata ba, amma ta kafe sai shi, yanzu ga abin da ya same ta nan.”

Ya fahimci so take ta jingina ciwon Maryam ga aikin kishiya, don haka ya ce,

“Camfa mata ciwo za ki yi?

Ita fa ƙaddarar bawa a rubuce take, ko ina Maryam ta ke sai ta kamu da wannan lalura tunda Allah ya sanya ta a zanen ƙaddararta, don haka ki daina wannan magana ma.”

Gargaɗi ya yi mata sosai a kan kada ta sake zargin wani game da ciwon Maryam, saboda hakan na iya sa ta rasa imaninta.

Habawa! Ai sai dai idan ba mace ba, tana keɓewa da twin sister ɗinta Hajiyarsu Haupha, da kuma Hajiyarmu a falon Mamansu Maryam ɗin ta ce musu,

“Wallahi ban yarda da ciwon Maryam ba.”

Hajiyarmu ta ce,

“Ba ke kaɗai ba, wannan ja’irar kishiyar ta Maryam zargin ta nake wallahi.”

Hajiyarsu Haupha kuwa ta ce, “Uhm! Ai don ma baku ga yadda ‘yar banzar yarinyar nan ta kama kanta a asibiti ba.”

Labarin liƙin da Safara’u ta so ɓallewa a asibiti ta faɗa musu, da kuma yadda Aishar duk ta rikice, kuma kowa ya lura da hakan, sai dai kawai suka basar kamar ba su gani ba.

Hajiyarmu ta ce,

“Su da ke cewa Katsinawa na da asiri, sai gashi sun ɓige suna yi suma.”

Mamansu Maryam ta ce,

“To dama sharri ne fa, duk wadda za ki ji ta kafe ana asiri to ɗayan biyu, ko dai tana yi, ko kuma kishi ke damunta don an auri mijinta.” Sai da Hajiyarsu Haupha ta yi ‘yar dariya sannan ta ce,

“Wallahi fa, kuma ina ne ba a asiri? Ni ban ce matan Katsina ba sa asiri ba, amma ba duka ba, don wata ko roƙon Allah ba ta taɓa bada kuɗi aka yi mata ba, sai dai ta yi da kanta, to bare kuma gidan boka.”

Hajiyarmu ta ce,

“Gane mani hanya dai, kuma idan muka ce za mu yi asirin da ake jifar mu da shi ba sai sun raina kansu ba.”

Cike da ƙunar zuciya suka yi ta maganar. Zagin da aka ce Katsinawa na yi kuwa sai da Hajiyarmu ta ɗuɗɗura ma Aisha shi.

Rahama kuwa tuni ta saje cikin dangin Maryam kamar sun saba da juna, saboda ba ta cika baƙunta ba. Bayan sun cika cikinsu ne suka dasa hira a ɗakin Hajiyarmu, har da Maryam kuwa a ke hirar, tsokana kuwa sun sha ta, wani wurin ta ba mutane tausayi, wani wurin kuma ta ba su dariya.

Khamis ma shi da su Auwal hirarsu suke ta yi a ɗaki. Sai dai tare da tunanin Maryam zuciyar Khamis ke samun damar bugawa, don haka wata hirar ma bai sanin me suke faɗa.

Bayan fitar su Auwal ne ya kishingiɗa kan doguwar kujerar da yake zaune. Hotunan Maryam ne ke ɗebe mishi kewar kaɗaici, don haka kai tsaye photos ya shiga ya kalli mai isar shi.

Bayan ya gama kallon pics ɗin ne ya lumshe idanu, duniyar tunanin abin da ya faru jiya tsakaninsa da Maryam a asibiti. Inda yana shiga wurinta ta fara ƙoƙarin ɓoye fuskarta. Zama ya yi a a bakin gadon ya ce,

“Ke mijinki ki ke gudu?”

Ɗauke hannunwanta daga fuskarta ta yi tare da yin magana cikin tsiwa,

“Na ce ka daina ce mini mijina.” Maƙe kafaɗa ya yi alamun ba zai daina ba, maraicewa ta yi tare da haɗe hannaye.

“Don Allah.”

Cewa ya yi,

“Ba zan bari ba sai kin yi mini wani abu.”

Lokaci ɗaya kuma ya nuna mata kuncinsa, sannan ya ce,

“Kiss.”

Ido ta ɗan zaro,

“Ba kyau mace ta taɓa namijin da ba nata ba.”

Ganin tana son ƙin yi ya ce,

“To kuwa ba zan daina kiranki matata ba.”

Bai tsammaci za ta yi ba, sai kawai gani ya yi ta lumshe idanu tare da bashi hot kiss a kunci, tana shirin janyewa kuwa ya rungumo ta, lahewar da ta yi a jikinshi ne ya bashi damar daidaita zamansa a kan gadon.

Ɗan ƙaramin bakinta ya sumbata tare da yi ma kyakkwar fuskarta ƙuri, ita ma ɗin nutsuwa ta yi tare da ci gaba da kallon shi.

Cikin yanayi mai ɗauke da zallar so da ƙaunar ta ya ambaci sunanta,

“Maryam.”

Amsawa ta yi,

“Na’am.”

Sai da ya ɓoye mamakin amsawarta a natse sannan ya ce, “Mece ce matsalarki?”

Kamar za ta yi kuka ta ce,

“Ni ban sani ba. Amma wani mutum ne ke son raba ni da kai.” Fuskokinsu a haɗe ya ce,

“Ni wa?”

Ta ce,

“Mijina.”

Wani irin farinciki ne ya mamaye Khamis, tsammaninsa ta warke, don haka ya shiga nuna mata tausayawar da yake mata bayan ya maido ta a jikinsa.

Ce mishi ta yi,

“Na haihu ko?”

Ya ce,

“Eh.”

Ta ce,

“A kan idanuna aka kashe yaron, kuma wannan mutumin da ke cewa shi ne mijina ya kashe shi.” Tare da kuka ta ƙarashe maganar.

Faɗuwar gaba ce ya samu kansa a ciki, don lamarin Maryam akwai wani abu a ƙasa, kuma idan har ya gane yadda abin yake hukuncin da zai ɗauka ba zai yi ma duk mai hannu a ciki daɗi ba.

Lallashin ta ya ci gaba da yi, inda ya ce,

“Duk wanda ya kashe moki ɗa ya je shi da Allah.”

Tare da ci gaba da faɗa mata kalmomi masu daɗi. Bacci ne ya ɗauke ta, fatan farkawa cikin aminci ya yi mata. Sai dai ina, da wani kalar rikici ta farka wanda ya yi sanadiyyar sanya kowa zubar da hawaye.

Duk da girman Khamis, don yanzu haka shekarunsa arba’in da uku, amma tuna wasu memories na rayuwarshi da Maryam na sanya shi kuka. Yanzun ma hawaye ne suka gangaro mishi, a ƙasan ranshi kuma yana jin ko nawa ne zai iya kashewa in dai Maryam za ta samu lafiya, don haka tun a ranar ne aka shiga shawarar wurin mai maganin da za a kai Maryam.

Ƙanwar babansu Maryam mai suna Asabe ce ta kawo shawarar a kai ta wurin uwar mijinta, saboda tana bada maganin ciwon iska, mahaifiyar Maryam ba ta so ba, amma don kada Asabe ta ji ba daɗi sai ta amince.

Washe gari da ƙarfe taran safe Khamis ya ɗauke su a mota suka tafi, Hajiyarmu da Mamansu Haupha sun san gidan, don haka basui nemi ɗan jagora ba.

Wani abin mamaki shi ne, aljanun da matar ke aiki da su na takawa suka ce sihiri ne aka yi ma Maryam don a raba ta da mijinta, Hajiyarmu ta ce,

“Wane marar Imanin ne yayi mata sihirin?”

Ƙin faɗa suka yi saboda da a tsarin aikinsu ba sa faɗar wanda ya yi sihirin.

Magungunan sha da hayaƙi ta bada, sannan Khamis ya ɗauko su. Ana faɗa ma bansu Maryam ya ce “Ku rabu da zancen aljanu, don sun saba ƙarya.”

Khamis ma bai wani yarda ba. Idan kuma har da gaske ne wa zai yi mata asiri? Don ba ya tsammanin Aisha ta san gidan wani malami bare har ta yi ma Maryam asiri, idan ma ta sani to imaninta da ya sani ba zai bari ba.

Rahama kuwa tana ji a ranta ta ce,

“Zancen Safara’u ya fara zama gaskiya.”

Dangane da Maryam kuwa, sabon yaƙi aka fara da ita don ba ta son shan magani. Hayaƙin ma da an ce za a yi ta fara kururuwa cikin gida kenan, Hajiyarmu ta ce,

“Baccin ciwo, wallahi babu mai takura ma ‘yata.”

Aisha kuwa kamar ta taka dutsen arfa saboda tafiyar Maryam. Ita a hasashenta ma babu ranar warkewar Maryam bare ta dawo, saboda Malam ya faɗa mata wannan ciwo na Maryam sai dai mutuwa ta raba ta da shi.

A ranar da gidan ya zama daga ita sai yaranta kuwa sai da Jamsy ta zo taya ta murnar Maryam ta bar gida. Jamsy ba ta daɗe da zuwa ba Zuzee ma ta sallamo.

A ƙasan carpet suka baje hajar hirarsu yadda za ta yi musu daɗi a falon. Jamsy da ke kallon tsantsar farinciki a tare da Aisha ta ce, “Aisha buri ya cika, sai wani nishaɗi kike yi.”

Dariya Aisha ta yi.

“Ai kishiya bala’i ce Anty Jamsy, dole na yi nishaɗi tunda Allah ya nisanta tsakanina da ita.”

Saboda ba ta da matsalar komai a rayuwa sai ta Maryam.

Zuzee ta ce,

“Ai tuni aka so nisanta ki da ita, kika riƙa kawo mana wasu ƙabli da ba’adi.”

Aisha ta ce,

“Lokacin sheɗan na ɗan ƙauye kenan.”

Karɓewa Jamsy ta yi da faɗin, “Yanzu kuwa ya zo birni ya waye ko?”

Aisha na kwasar dariya ta ce, “Wallahi kuwa. Ba shaiɗan ba ni kaina na zama ‘yar gari a wannan harkas, zan iya kashe ko nawa ne don ganin na hana Maryam zaman lafiya, saboda tunda aka sa ranar aurenta da mijina har aka yi auren hankalina bai kwanta ba, don haka ita ma ba zan bari hankalinta ya kwanta ba madamar tana tare da mijina.”

Jamsy ta ce,

“Ke ce ai kika bari aka kai haka, amma da kin so ai ko auren ba za a yi ba, idan ma an yi to sai kin so su zauna lafiya.”

Hirarsu mai cike da miyagun ƙulli suka sha. Ƙarfe ɗaya saura kuma su Haneef suka dawo school. Jamsy ce ta jawo Haneef saboda kyawunsa na birge ta, sai da ta kalli Aisha sannan ta sake kallon shi ta ce,

“Amma wannan fuskar ta babanshi ce ko?”.

Inda ke yi ma Zuzee ƙaiƙayi ne Jamsy ta sosa mata, yanzu haka tunanin Khamis take a ranta, saurin cewa ta yi,

“Ai har Haneefar ma, ba ki ga sun fi ta kyau ba?”

Aisha na dariya ta ce ma Zuzee, “Wato kina nufin Abban Haneef ya fi ni kyau ko?”

Zuzee ta ce,

“Wallahi ya fi ki.”

Tabbas Khamis ya zarta Aisha kyau, sai dai don tana mace ne ba kowa zai gane ba.

Tuni Jamsy ta zaunar da Haneef a gabanta, hannayenshi ta riƙo tare da faɗin,

“Ai kuwa na yi ma Mubeena kamun miji.”

Don da gani idan Haneef ya girma zai yi kyau da kwarjini.

Mubeena ce ɗiyar da Jamsy ta fi so, saboda ita kaɗai ce mace a cikin jerin ‘ya’yanta biyar, gashi ta biyo Jamsyn kyau da farar fata.

Sai dai kuma ba’a fatan ta biyo halinta, wanda duk da wasa Jamsy ke ce ma Haneef ta ma ‘yarta kamun sa, amma tsoron mugun halinta ya sa Aisha yin dariyar yaƙe kawai, cikin ranta kuma ta ce,

‘ Allah ya tsari ɗana da auren ‘yarki.”

Saboda in dai Mubeena ta biyo halin Jamsy toh duk wanda Allah ya haɗa ta da shi ya shiga uku, Aisha ba ta daɗe da sanin ta ba, amma na’ukan mugayen halayenta da ta sani ba sa ƙirguwa.

Aisha ba ta son duk abin da zai cutar mata da ‘ya’ya. Ta manta da idan ka cuci ɗan wani kai ma sai an cuci naka.

Khamis da take son mallakewa ita kaɗai ai ɗan wata ne, Maryam ma haihuwarta aka yi, yadda ta ke son ‘ay’yanta haka suma mahaifansu ke son su duk da sun girma.

Don haka idan ba gaugawar dawowa hayyacinta ta yi ba, to abin da ta yi ma mijinta sai an yi ma ɗanta, kuma duk abin da ta yi ma kishiya ga shi can an yi ma

‘yarta, ko ba a yi irin abin da ta yi ba, to dai ko ta wane hali sai Allah ya jarabci ‘ya’yanta. Ita da yin mugun aiki, ‘ya’yanta da karɓar sakamako.

Cigaba da tsokanar Haneef Jamsy ta yi,

“Kai kana son ‘yata?”

Haneef na da wayau, ya kuma fahimci me take nufi, dariya kawai ya kama yi.

Ko kaɗan Aisha ba ta son wannan wasan, tsoronta kada ‘yan Amin su amsa ta shiga uku, cewa ta yi, “Lallai kina ji da Haneef tunda kike son ba shi ‘ya.”

Jamsy ta ce,

“Idan kin ji so ɗaya kenan. Yana da siffar da idan ya girma mata za su yi rububin shi, to gwara tun wuri na kame ma ‘yata.”

Dariya su duka suka yi, Jamsy ta kuma cewa,

“Kuma dai ba zan ɓoye miki ba ya fi waccan ‘yar taki mai gajeren hanci kyau.”

Saboda Haneefa fuskar Aisha gare ta, ɗazu son Khamis ne ya rufe ma Zuzee idanu har ta cewa Haneefa ma Khamis ta biyo.

Sai da Zuzee ta ɗan samu nutsuwa sannan ta ce,

“Wallahi kuwa Anty Jamsy, ni sai yanzu ma na gane yarinyar uwarta ta biyo.”

Tsaye Haneefa ta ke a kusa da Aisha, ta na jin Jamsy da Zuzee sun rufar mata ta kama turo baki. Jawo ta Aisha ta yi jikinta.

“Zo nan ‘yata, rabu da su.”

Sai da Zuzee ta ɗan taɓo Haneefa sannan ta ce,

“Ai dama ke kaɗai ke son ta, sai kuma ki ji da ita, mu dai Haneef ne namu.”

Sosai suka sha raha, daga nan kuma Aisha ta koma Kitchen.

Yamma na yi kuwa suka fice gidan baki ɗaya a motar Aisha. Islamiyya suka fara biyawa suka aje yara. Gidan Jamsy suka nufa tare da aje ta a bakin gate ɗin gidanta.

Daga nan sai wurin Malamin da Zuzee ta ce za ta kai ta, don a cire ma Khamis tunanin Maryam, yadda idan ya dawo ba zai sake marmarin komawa wata Katsina ba.

Tuni Malamin ya san da zuwansu Aksha, saboda sun tsara kashe mu raba shi da Zuzee da kuɗin da suka shirya tatsa a wurin Aisha, kasantuwar ba ta san kan abin ba.

“Aiki Ga Mai Ƙare Ka.”

Shi ne sunan da Zuzee ta ce ma Aisha ana kiran Malamin da shi, kuma ba haka bane, ita ta ƙirƙiro shi kawai. Magaji ne sunanshi saboda shi ya gaji babanshi koyarwa a makarantar allon gidansu wadda take nesa kaɗan da gidan da yake.

Ɗakinshi na zaure suka shiga tare da zama kan kodaɗɗen jan carpet ɗin da ya shekara shida shimfiɗe a ɗakin. Wanda kuma masallacin unguwar ne aka bashi carpet ɗin a lokacin da suka canja sabo.

A daidai lokacin da shi ma zai zauna ne ya ce ma Zuzee,

“Zuzu tamu, kwana biyu.”

Zuzee ta ce,

“Wallahi sai a hankali.”

Ya ce,

“Jikin ko garin?”

Ta ce,

“Duka, ka san akwai wani da na daɗe ɗauke da son shi a ƙirjina, to shi nake so a damƙe mini tunda kamar Yayana Abdul ba ya yi na, so nake ka yi mar jan kamu, don bana son shi ma ya watsa mini ƙasa a ido.”

Aisha ba ta san mijinta ne Zuzee ke so ba, dariya kawai ta yi, cikin ranta kuma ta ce,

‘Baki da dama.’

Cewa Magaji ya yi,

“Ki kawo kuɗi a yi miki aiki.” Zuzee ta ce,

“Ina fa na gan su, ko da yake ga ƙawata nan na kawo maka, ƙila ta sa ni a jaka.”

Duban Aisha ya yi yana mata kallon wawiya, a idanu ga ta cikakkiyar mace kuma mai wayau. Amma wanda ya zauna da ita zai fahimci remote control ɗin ƙawaye ce, don ya san labarinta a bakin Zuzee.

Gaisawa suka yi, sannan ya ci gaba da zana ƙasar da ke gabansa, bayan ya gama ne ya kuma ɗaga kai yana karanto wasu ɗalasimai na ƙarya.

Zuzee kuwa gumtse dariyarta ta yi, tana kallon shi, saboda gaskiya a aikinsa bai cika karanto irin wannan ba.

Sai da ya gama sannan ya dubi Aisha yana mazurai,

“Kawo sunan mijin naki, za a yi miki aikin da za ki mallake shi ke kaɗai, ta yadda idan ya baro Katsina ba zai sake komawa ba.”

Mamaki ne fal da ran Aisha, ita ba ta faɗa mishi abin da ya kawo ta ba, amma sai gashi ya faɗa, ko da yake ƙila Zuzee ta faɗa mishi. Duban Zuzee ta yi tana son sanin idan ita ta faɗa mashi.

Zuzee na lura ta ce,

“Kin ga aikin Manya ko?”

Kai Aysha ta ɗaga tare da maida dubanta ga Malam.

“Sunan mijina ka ce ko?”

Ya ce,

“Eh, ki ba da cikakken sunansa.”

Ta ce,

“Khamis Abdullahi.”

Rubuta sunan Khamis ya yi da larabci a gaban wani raƙumi da ya zana a kan ƙasar, sake tambayar ta ya yi,

“Sana’ar me yake yi?”

Ta ce,

“Siyar da motoci, kamfaninsu mai suna Khamis And Brothers na nan idan ka wuce General Hospital.”

Dakatawa da rubutun da yake akan ƙasa ya yi tare da rumtse idanu, saboda ya san Khamis jan sani. Duk Zakkar da Khamis ke fitarwa a kowace shekara yana da kaso a ciki, Khamis kuma ya gaji bashi Zakka ne a wurin mahaifinshi, shi ma ya gaji karɓa ne a wurin mahaifinshi. Badawa da karɓar Zakkar duk gado ne, wanda ake yi ma Almajirai sadaka. Kuma ko a kwana uku da suka wuce sun yi waya da Khamis, inda Khamis ɗin ke bashi hakuri cewar matarshi ce bata da lafiya, da ta ji sauƙi zai neme shi da yardar Allah.

Ganin ya yi shiru ne Zuzee ta ce, “Ya dai Malam?”

Hannu ya ɗaga mata, sai da ya gama wasu sambatu sannan ya ce, “Magana nake da aljannu, sun faɗa mani kalar aikin da za a yi.”

Cike da jin daɗi Aisha ta tambaye shi,

“Me suka ce?”

Faɗa mata ya yi za su yi aikin da kansu, saboda sai an shiga duniya neman magani.

Wasu layu da turare ya ba ta ya ce ta tona rami a gidan ta binne, sai garin magani kuma ya ce ta sa mishi a abinci. ba ta yi jayayya kan cewar aljanu za su ƙarasa aikin ba saboda ta ga yadda aka yi da Maryam.

Tambayar shi kuɗi ta yi, ya ce, “Sadakar kuɗin turare da na maganin za ki bada.”

Lissafi ya yi mata dubu ashirin da biyu, ita kuma ta bashi dubu ashirin da biyar don murna.

Suna tafiya ya riƙe haɓa tare da tuntsirewa da dariyar mugunta, saboda duk shaiɗancinsa ba zai iya yi ma Khamis asiri ba, a fili ya ce,

“‘Yan iskan banza da wofi.”

Zuzee dama kallon ta kawai yake don ya ɗaukar ma ransa ko ana ha maza ha mata sai ya aure ta.

Kwanansu Khamis uku a Katsina sannan suka dawo. Tuni kuma ya sha sinadaran da Aisha ta sanya mishi a zoɓo, wanda magungunan zafi ne ba tare da ta sani ba.

Shi kuwa kamar maye ya dawo, don rabon da ya kusanci mace an yi sati, don haka Aisha ta sha ƙwazzabar sa. Sosai ya ji daɗin kasancewa da ita, don haka ya shiga nuna mata farincikinsa a gare ta.

Ita kuwa gani take aikinta ne ke ci, don ba ƙaramar soyayya suke sha ba. Kuma duk abin da ta ce tana so yi mata yake.

Sai dai bai fasa tunanin Maryam da kuma yawan buga waya a Katsina ba, banda kudaɗen da yake turawa akai-akai.

Photos da vedios ɗin Maryam kuwa kullum sai Zahara’u ta turo mishi, ba wannan ba har chat suna yi da Maryam, wanda ba abin da take sai shirme.

Aisha kuwa kamar za ta mutu don kishi, wato ta haukacen ma son ta yake, don a ko ina nuna zallar kewar Maryam yake yi.

Yanzu haka suna zaune a falo ya buɗe voice ɗin Maryam tana mishi shirme.

Haɗe rai Aisha ta yi,

“Ni kam ga mai lafiya, ko miye na damuwa da wata mahaukaci ya.” Saboda ba tun yau yake mata haka ba.

Sosai ya ji zafin mahaukaciya da ta ce

“Aisha Maryam ɗin ce Mahaukaciya?”

Ta ce,

“To mece ce idan ba mahaukaciyar ba.”

Cikin fushi ya ce,

“To ba zan ɓoye miki ba, wallahi idan ki ka sake kiran ta da mahaukaciya sai ranki ya ɓaci.”

Ta ce,

“An ce mahaukaciya.”

Ya ce,

“Ke tafi can, shashasha kawai.”

Masifa ta shiga yi wai don me zai ce mata shashasha, ya ce,

“Ke a wane dalilin ne za ki ce mata mahaukaciya?”

Faɗa suka yi sosai, wanda ya cire mata gamsuwa da aikin Malamin Zuzee, saboda ita dai bayta ga wani canji ba, duk ranar Allah sai ta haɗiyi baƙinciki akan Maryam duk da ba ta nan.

Ɗaki ta koma tare da kiran Jamsy a waya ta faɗa mata so take a cire ma Khamis tunanin Maryam, Jamsy ta ce,

“Ke ma a maida shi Raƙumi da akala mana.”

Aisha ba za ta iya irin wannan asirin ba, don za’a gane bin malamai ta ke.

Cewa ta yi,

“Ko me za a maida shi in dai akwai Maryam a ransa, to hankalina ba zai kwanta ba, don haka a fara raba shi da ita.”

Haka kuwa aka yi. Mahaɗa suka yi, inda suka je gidan Malam.

Wani baƙin magani ya bata, ya ce da jinin al’adarta za ta haɗa, sannan ta sanya mishi cikin wani abu mai ruwa ya sha.

Aisha na ba Khamis wannan maganin bai sake yi mata maganar Maryam ba, asali ko tuna Maryam baya son yi saboda wani kalar tashin hankali ke samunsa idan ya tuna sunan.

Wannan sihiri ba son Maryam kaɗai cire mashi ba, hatta kuzari da ƙarfin halinsa duk ya rasa su, kasantuwar kowane lokaci kansa ke ciwo, ko fita ya yi baya wani taɓuka komai a harkar kasuwancinsa. Gidansu kuwa sai ya ƙulla satika bai je ba don baya son su tada mishi zancen Maryam. Suma ɗin kamar asirin ya shafe su, don ba mai nemansa bare ya tambaye shi halin da Maryam ke ciki.

Aisha kuwa karenta take ci babu babbaka ita kaɗai a gida, sai kuma danginta da su Zuzee idan sun zo. Cikin ɗan lokaci ta ƙara kyau da ƙiba, saboda tana samun yadda take so a gida.

Sosai kuma ta lura da Khamis bai son batun Maryam, amma don son zuciya da ta mila ta sha iska sai ta yi mishi maganar duk don ta ji daɗi.

Yanzu haka samun shi ta yi a falo yayi jugum, gefenshi ta zauna tare da faɗin,

“Lafiya?”

Kamar wanda ke tsoronta ya ce, “Kaina ke ciwo.”

Cewa ta yi,

“Ayya, sannu.”

Ya ce,

“Yauwa.”

Shiru ya yi yana saurarar yaransa da ke ta wasa a waje.

“Ni kam ya wajen Maryam.”

Ta faɗa cikin kisisina, tsaki ya yi, “Oho! Ni ina na san halin da take ciki.”

Gira ta ɗaga tana dariya,

“Kamar ya ba ka san halin da take ciki ba?”

Ya ce,

“Ke ni na gaji, can mahaifanta su ci gaba da yi mata magani, idan ma bata warke ba sakar musu ‘ya zan yi.”

Wannan shi ne burin Aisha wanda take fatan ya cika!

********

A Katsina kuwa jimami biyu suke yi. Ciwon Maryam da ke tafiya yana dawowa, sai ta yi kamar ta samu sauƙi, sai kuma ciwo ya dawo sabo. Duk da maganin da suke ta nema.

Sai kuma ɗauke musu ƙafa da Khamis yayi, ba zuwa ba aike.

Wayar ma da yake kira ya daina. Sosai abin ya damu kowa. Hajiyarmu ce ta ce ma Alhajinsu Maryam,

“Ni kam Alhaji kun yi waya da Khamis?”

Ya ce,

“Na kira bai ɗaga ba.”

Ta ce,

“To Allah ya kyauta.”

Su mutane ne masu zuciya, ko da Khamis ya daina neman su ba su sake neman shi ba suma. ‘Yan gidansu Khamis ɗin ma ko sun kira ba ɗagawa suke ba saboda sun fusata da yawa.

Su dai fatansu Maryam ta samu lafiya, don haka suka shiga nemar mata magani, sun kuma je wuraren masu magani da yawa, magana ɗaya ce asiri aka yi ma Maryam. Babansu Maryam ya ce “Duk wanda ya yi don kansa.” Saboda lafiyar ‘yarsa ya fi so ba toƙale-toƙale ba.

Zuzee kuwa ba ta san Aisha ta canja wurin magani ba sai da ta je gidan Jamsy take faɗa mata. Masifa Zuzee ta riƙayi tana faɗin, “Aisha ta munafunce ni.”

Jamsy ta ce,

“Rabu da shegiya, ki bi ta a yadda take nuna miki.”

Don kullum suka yi magana da Zuzee sai Aishar ta riƙa zuzuta maganin Magaji.

Shirin yaƙi da Aisha ta shiga yi don ba ta ƙaunar Aisha ta ji daɗi ita kaɗai. Akwai wani sabon sim card ɗinta da ta daɗe da siye.

Ɗora shi ta yi a waya ta kuma shiga kiran Khamis a duk lokacin da ta san yana gida.

Duk sa’adda ya ɗaga ya ji muryar mace sai ya kashe, saboda gudun kada Aisha ta hargitsa mishi lissafi.

Sai idan ya fita ne yake samun damar kiranta saboda har sun fara sabawa a waya, duk da ba soyayya suke ba, amma Zuzee ta yi salon da ta samu mazauni a zuciyarshi, don shi har ga Allah yana son mace fiye da ɗaya, to ba Maryam, shi ya sa Zuzee ta samu kanshi cikin sauƙi, sai dai har yanzu bai san ita ce ba, saboda ta ce mishi sunanta Aydah.

Matsalar kenan, in dai namiji na da sha’awar mace fiye da ɗaya, to duk ƙulumboton mace ba za ta hana shi ƙara aure ba, ko ta hana shi, to waje fa akawai matan banza. Don haka da kishiyar waje ɗaya, gwara kishiyoyi uku a gida.

Kallon shawaraki Zuzee ta riƙa yi ma Aisha. Ita kuma magaji na mata kallon shawarakin saboda duk lokacin da ta ce ya yi mata aiki a kan Khamis bai yi, sai dai kawai ya cinye mata kuɗi.

Burinta a kan Aisha shi ne ta ƙumsa mata takaici, don so take ta ji ta fara kawo mata ƙarar Khamis. Ƙaimi ta ƙara a wurin tura mishi zafafan texes, da kuma kiransa a kowane lokaci.

Aikuwa ba a je ko ina ba Aisha ta fahimci da wani abun da yake ɓoye mata a waya.

Ido ta ci gaba da sanya mishi, sai kuwa ga kiran Zuzee a wayarsa lokacin suna tare a ɗakinsa. Shi ba soyayya yake da Zuzee ba, don haka bai ji shakkar ɗaga wayar ba, don so yake idan sun gama ya ba Aisha labarinta, saboda ta fara cika masa ciki.

“Ranki ya daɗe.”

Ya faɗa yana duban Aysha da ta game bangon gabas da na yamma.

Daga can Zuzee ta ce,

“Tare da naka.”

Shammatar shi Aisha ta yi ta fizge wayar,

“Da wace shegiya ce kake waya?” Da yake Khamis ɗin ya zama mijin ta ce sai ya ce,

“Ni fa ba soyayya muke ba, ita ce ta liƙe mini.”

A fusace Aisha ta ce,

“Ni za ka mayar gara, na samu na rabu da waccar karyar ‘yar katsina, shi ne za ka jajibo mini wata, to wallahi ba ka isa ba.”

Kalmar’ Katsina’ ce ta sa gabanshi faɗuwa, sosai yake son tuna abin da ya manta wanda ya shafi Katsina.

‘Maryam.’

Ya faɗa a zuciyarshi tare da yin shiru.

Sababi ta riƙa yi, amma ya yi banza da ita, aikuwa sai ta ƙara harzuƙa.

“Wato za ka maida ni shashasha ko?”

Hakuri ya ba ta. Sannan ya roƙeta ta bashi wayar.

Sai da ta ɗauki lambar sannan ta miƙa mishi wayarshi.

Suna haɗuwa da Zuzee ta labarta mata, Zuzee kuwa ta murtuke fuska.

“Kada ki yarda ya yi miki sakiyar da ba ruwa, in dai suka ƙara waya a gabanki to ki kwankwatse ‘yar iskar wayar.”

Aisha ta ce .

“Hmm, ki bar ni da shi kawai. A ƙasan ran Zuzee kuwa murna ce fal. Sosai ta ƙuduri sai ta raba Aisha da Khamis ma baki ɗaya, don duk da ba soyayya suke ba, amma ta fahimci shi mutum ne mai daɗin mu’amala.

Khamis kuwa ya koma sukuku, kullum sai faɗuwar gaba akan lamarin Maryam. So yake ya samu damar yin tunaninta a natse, amma firgici ya hana shi. Ya kuma rasa wane irin firgici ne wannan.

Samun damar zuwa gidansu ya yi, sai dai ba kowa sai mai aiki.

Daga nan wurin kasuwancinsa ya wuce. Jingim ya yi a cikin rumfa. Wata irin faɗuwar gaba ya samu kansa da yi,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.” Ya riƙa furtawa, har sai da faɗuwar gaban ta yi sauƙi.

Abokinsa mai suna SP Ameer Sarki ne ya yi sallama wurinsa.

Khamis ya saba tsokanar sa da, ‘Ɗansanda abokin kowa.’

Amma yau sai dai ya miƙa mishi hannu kawai suka gaisa.

“Ya dai Mijin Maryama?”

Cewar SP Ameer cikin sigar tsokana, saboda suna tsokanar juna.

Jin sunan Maryama ba ƙaramin girgiza zuciyar Khamis ya yi ba, ce ma Ameer ya yi,

“Mijin wa ka ce?”

Ameer ya ce,

“Mijin Maryama.”

Khamis ya ce,

“To akwai matsala…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kishiyar Katsina 17Kishiyar Katsina 19 >>

1 thought on “Kishiyar Katsina 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×