A Katsinan Dikko kuwa, tuni an san da zuwan su Khamis, don haka ne ma Hajiyarmu da su Zahara'u suka shirya liyafar arziƙi wadda za a tarbe su da ita. Su ne kuma suka fi kowa son Maryam ta koma ɗakinta, saboda ta ji sauƙi yadda ba za ka taɓa cewa ta taɓa yin fama da lalurar gushewar hankali ba, sai idan abin ya ɗan bijiro, shi ma ba wani daɗewa yake ba take komawa hayyacinta.
Ganin ta samu lafiya da kuma ƙaƙƙarfan uzurin da mahaifan Khamis suka kawo ne ya sa babansu. . .