Skip to content
Part 20 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

A Katsinan Dikko kuwa, tuni an san da zuwan su Khamis, don haka ne ma Hajiyarmu da su Zahara’u suka shirya liyafar arziƙi wadda za a tarbe su da ita. Su ne kuma suka fi kowa son Maryam ta koma ɗakinta, saboda ta ji sauƙi yadda ba za ka taɓa cewa ta taɓa yin fama da lalurar gushewar hankali ba, sai idan abin ya ɗan bijiro, shi ma ba wani daɗewa yake ba take komawa hayyacinta.

Ganin ta samu lafiya da kuma ƙaƙƙarfan uzurin da mahaifan Khamis suka kawo ne ya sa babansu Maryam ba ta damar komawa ɗakinta, a cewarshi ma ta ƙarasa samun lafiyar a can, tunda shi sauƙi ɗan a hankali ne.

Maman Maryam kuwa ta kafe a kan ‘yarta ba za ta koma a ƙarasa kashe mata ita ba. Inda ta shiga zuga Maryam har ta cusa mata ƙin komawa, don ta faɗa mata Khamis bai sonta tunda har ya guje ta bayan ya san matarshi ce ta yi mata asiri, kuma bai dawo ba sai da ya ji ta samu lafiya, don haka gangar jikinta yake so ba ita ba, Maryam na jin haka ta ce ita da gidan Khamis har abada.

A maganar Mamansu Maryam cewar Khamis bai tsiri zuwa Katsina ba sai da Maryam ta samu lafiya gaskiya ba haka bane, an dai yi daidaito da samun lafiyarsu shi da Maryam ɗin a lokaci ɗaya. Kuma a lokacin ne ya ji ba inda yake son zuwa sai Katsina domin ya ga matarshi, ba tare da tabbacin ta samu lafiya ba.

Duk wani mai faɗa a ji ya yi ma Mamansu Maryam magana akan ta janye batunta na cewar Maryam ba za ta koma ba, amma ta ƙi saurarsu, abin da ma take cewa shi ne,

“Ba wani ya yi mini naƙudar Maryam ba, don haka ba mai iko a kanta.”

Tabbas sun yarda ita ta yi naƙudar Maryam, sai dai batun iko a kan Maryam ɗin ne suka nuna mata ba ita kaɗai ke da shi ba, don haka ne suka shiga gyaran Maryam, yadda za ta ƙara ƙima a idon mijinta idan ta koma ɗakinta. Hajiyarmu ce ta ɗauki nauyin gyaran duk kuwa da tsufanta. Magungunan mata masu gyara lafiyar auren mace ta shiga haɗa ma Maryam tana sha, da Maryam ɗin ta tambaye ta,

“Na miye?”

Sai ta ce magungunan kariyar jiki ne. Yanzu kam Maryam sai a hankali, tunaninta ragagge ne, don haka da ƙanƙanen abu sai a kifar da ita.

Daga cikin magungunan akwai wanda Maryam ta maida ruwan shanta, kuma daɗinshi ya sa take shanshi ba ƙaƙƙautawa saboda zaƙi ya fi yawa a ciki, masu ɗacin kuwa sai an yi da gaske, da yake Hajiyarmu ta fi kowa sanin kanta sai ta lallaɓa ta har ta shanye.

Batun zuwan Khamis kuwa yanzu ko a jikinta, saboda mahaifiyarta ta rage cusa mata tsanar komawa gidansa.

Biye take da duk wani gyara da ake mata. Tuni kuma ta kwance kai tare da zuwa saloon, ƙunshi mai ɗaukar hankalin mai kallo ta je aka yi mata. Daga ƙarshe da ita aka shirya ma su Khamis nau’ukan abinci.

Kowa gani yake Maryam ta sauko, sai da ta dubi abincin da suka gama girka ma su Khamis ta ce, “Ni wallahi bana son zuwan mutumin nan.”

Baki kowa ya buɗe yana mata kallon mamaki, gashi dai babu wasa a cikin maganarta, sai dai kuma yadda ta bada kai ana shiryata ya nuna kamar son ranta ne ta faɗa a yanzu.

Ba wanda ya sa baki a maganarta gudun tada musu rikici.

Sai dai Hajiyarmu ta ce mata, “Saboda me?”

Cewa ta yi,

“Haka kawai ba na son komawa tare da shi.”

Murmushi kawai Hajiyarmu ta yi tunda ba wata hujja a zancenta.

Kamar daga sama ta ji shewar Zahara’u tana faɗin,

“Yeeee ga twinny nah!”

Saboda suna wata iriyar kama da Haupha, ga su kuma age mate.

Maryam ta san Haupha ce Zahra’u ke ce ma Twinny, cike da murna ita ma ta fito daga kitchen, ai kuwa sai ga Hafsat da Ruƙayya ta yi arba da su. Maƙalƙale su Maryam ta yi tana wata irin murna saboda ko da take cewa ba za ta koma gidan Khamis ba, amma shi da ‘yanuwansa suna ranta. Kuma su ma ɗin ba ƙaramar murna suka yi da ganinta ba. Su duka biyun Maryam ta haɗa ta rungume, lokaci ɗaya kuma tana faɗin “Oyoyo ƙawayena, na yi kewar ku ba kaɗan ba.”

Ruƙayya na murna ita ma ta ce, “Mun yi kewarki Anty Maryam.” Bayan Maryam ta zame jikinta daga nasu ne ta ce,

“Ni ma Rukky, ina su Ummana?” Hafsat ta ce,

“Duk lafiya lau suke.”

Faɗin farincikin da suke ta yi ma ɓarnar baki ne, saboda akwai alaƙa mai kyau a tsakanin Maryam da duk ‘yanuwan Khamis, saboda tana ba su damar zuwa gidansa su yi yadda suka ga dama, saɓanin Aisha da suke ma laƙani da Kura, daga ke sai ‘ya’yanki. Dawowar Maryam KT sai da gidan ɗan’uwansu ya fara gagararsu, don Aisha ta fara tsirar watsi da su idan suka je gidan, mafarin suke ta fatan dawowar Maryam domin su samu ‘yanci a gidan yayansu.

Maryam na cikin yi ma Haupha magana ne ta ji sallama, wani irin faɗuwa gabanta ya yi saboda duk inda ta ji muryar mai sallamar za ta iya gane shi. Cikin wani irin yanayi Maryam ta yi mishi kallo mai ɗauke da mabanbantan manufofi, lokaci ɗaya kuma gabanta na ci gaba da faɗuwa.

A zahiri kam Khamis ya mata kyau da kwarjini, duk da ‘yar ramar da yake da ita.

Shi kuwa baccin mahaifa da ‘yan uwan Maryam da ke tsaye a wurin ba abin da zai hana shi rungume matarshi. Kewa da tausayi, so da kuma ƙaunar ta ne suka taru suka cika mishi zuciya.

Sannu da zuwa su Zahara’u suka yi mishi, ya amsa cikin yanayi mai ɗauke da farincikin ganin matarshi ta samu lafiya.

Ɗakin Mamansu Maryam suka shiga, sannu da zuwa aka yi musu, su kuma suka yi musu fatan samunsu lafiya. Wani abu da ya ɗan taɓa zuciyar Khamis shi ne yadda ya ga mamansu Maryam na ƙoƙarin ɓoye damuwar da ke ranta, amma ta kasa. Itama Maryam ɗin ya lura da yadda ta ɗan haɗe rai, don suna gaisawa ta fito daga ɗakin.

Sosai Khamis ya tsargu, don haka ne ma ya fito daga ɗakin.

Hajiyarmu ya taras a tsakar gida, don itama kunyar yanayin Mamansu Maryam ya sa ta fitowa. Ƙara gaishe ta Khamis yayi, bayan ta amsa ne yake tambayar ta baban su Maryam, don tunda ya shigo bai ganshi ba, faɗa mishi ta yi tafiyar bazata ce ta kama shi, amma yanzu yana hanyar dawowa ma.

Fatan dawowa lafiya Khamis ya yi mishi, daga bisani kuma ya yi mata maganar Maryam, inda ya ce,

“Na ga mutuniyar ta samu sauƙi sosai.”

Hajiyarmu ta ce,

“Ai Alhamdulillah, Maryam kam lafiya ta samu, sai dai abin da ba a rasa ba.”

Batun yadda suka baro mutanen gida Hajiyarmu ta yi mashi, ya ce, “Duk suna lafiya, kuma suna gaida ku.”

Hajiyarmu ta ce,

“Muna amsawa.”

So yake ya zauna ya huta, don haka cikin zolaya ya ce ma Hajiyarmu,

“Ɗakina a buɗe yake ko? Zan shiga.”

Hajiyarmu ta san inda yake nufi.

Tana dariya ta ce,

“Eh a buɗe yake Malam Khamis.”

Ta nan cikin gidan ya shiga ɗakin Auwal. Sosai ɗakin da mai ɗakin suke birge shi, kasantuwar Auwal na son gayu, shi ya sa komai nashi tsaftsaf. Wani irin ƙamshi mai ratsa zuciya ne ke tashi a cikin ɗakin.

Zama Khamis ya yi akan kujera, hularsa da ya cire ya aje, lokaci ɗaya kuma ya jingina da bayan kujera. Lumshe idanunsa ya yi tare da shaƙar daddaɗan ƙamshin da ke yawo a cikin iskan ɗakin.

Khamis bai yi mamakin yadda Maryam ta ƙi sakar mishi fuska ba, tunda ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba. Amma ɗaure fuskar da mahaifiyar Maryam ta yi mishi ya tsaya mishi arai duk da a hasashenshi don ya ɗauke musu ƙafa ne.

A fili ya ce,

“Ai Allah ya san ba da son raina na ƙi zuwa ba.”

Saboda tsoro ya fara kama shi.

Idanunsa a lumshe ya ji motsin mutum ya shigo. Daddaɗan ƙamshin da ya daki hancinsa ne ya sanya shi buɗe idanun.

Maryam ce tsaye cikin indigo ɗin doguwar riga, wadda aka ƙawata adonta da stones masu ruwan silver. A yadda take ta ɗaure fuska ne ya fahimci zuwan ba da son ranta bane, domin Hajiyarmu ce ta matsa mata wai ta zo ta yi ma mijinta sannu da zuwa tare da bashi abinci.

Kafe ta ya yi da idanunsa, ita kuma kanta na ƙasa, lokaci ɗaya kuma tana jujjuya basket ɗin da ke hannunta.

Shi kam ko dai kyau aka ƙara ma Maryam? Don ta yi fari da kuma ƙiba. Ita kuwa kwarjini yake yi mata, shi ya sa ba ta iya haɗa idanu da shi.

“Ƙaraso mana tawan.”

Ya faɗa cikin nuna kulawa, shiru ta yi kamar ba ta ji shi ba, bai kuma damu da shirun ba, don tuni babansu Maryam ya faɗa mishi ta canja, wani lokaci magana ɗaya ba ta yi mata.

Tashi ya yi tare da ƙarasawa gabanta, basket ɗin ya karɓa, sannan ya ruƙo hannunta ɗaya, aikuwa gabanta na wata irin faɗuwa ta biyo shi, don gaskiya a yanzu tsoronsa take ji, kuma ba yin kanta bane.

A gefe ya aje basket ɗin, sannan suka zauna kan kujera suna fuskantar juna. Cike da son ta ya dafa kafaɗunta,

“Maryam.”

A hankali ta ɗago ta dube shi, Khamis mijinta, wanda take yawan mafarkin ya zo kusa da ita ne yanzu a gefenta.

“Kin kuwa gane ni?”

Ya tambaye ta, murya ciki-ciki ta ce,

“Na gane ka mana, mijina ne da ya daina nema na.”

A shagwaɓe ta ƙarasa maganar.

Ƙara sassauta murya ya yi,

“Sorry, ba da son raina na daina neman ki ba, ni ma irin rashin lafiyarki na yi, ba ki ga na rame ba?”

Ita kaɗai ta san kalar azabar da ta sha, don haka ba ta fatan irin wannan lalurar ta samu wani, cike da tausayinsa ta ce,

“Da gaske?”

Duk da ta ga ramar da ya yi.

Cewa ya yi,

“Allah kuwa, amma da sauƙi, ke fa ya jikin naki?”

Ta ce,

“Nima da sauƙi sosai.”

Nutsuwar da ke ratsa kowannen su ce ta sa wurin ya yi shiru, shi dai har yanzu ya kasa ɗauke idanunsa daga fuskarta mai ɗauke da annuri, ita kuwa tsoro da jin haushin shi sun tafi, sai dai wata sabuwar kunya da ta mamaye ta. Har cikin ranta take jin kallon da yake mata, wasa ta ci gaba da yi da dogayen yatsunta da suka sha ƙunshi na jan lalle. Ba ta ankare ba sai gani ta yi ya kama hannayen ya kai su ga hanci tare da lumshe idanu yana shaƙar ƙamshin da ke fita daga jikinsu. Ƙuri ta yi mishi, sai ta ji wani sabon son shi na zagaye jini da ɓargon jikinta. ‘Allah ka bar mini mijina’ ta faɗa a ranta tare da kasa ɗauke idanunta a kanshi.

Shi kuwa sai da ya shaƙi ƙamshi mai isar shi sannan ya buɗe idanun, cikin nata ya saka su, lokaci ɗaya kuma ya sumbaci hannun.

Gani yayi ta lumshe idanu alamar ta ji sumbar har a ranta,

“Maryam, kin yi kewa ta ko?”

Kai ta ɗaga,

“Uhmm.”

Ya ce,

“Ni ma na yi kewarki sahibar ruhina.”

Murmushi mai cike da farinciki ta yi. Ɗora hannunta ɗaya a kan tafinsa ya yi , sannan ya cigaba da shafar ƙunshin da ɗayan hannun, cikin kasalalliyar murya ya ce, “Ƙunshinki ya yi min kyau.”

Cike da jin daɗin yabon ta ce, “Allah?”

Yana ‘yar dariya ya ce,

“Allah kuwa.”

Ta ce,

“To duk don kai na yi.”

Matse hannun ya yi gam ya ce, “Na gode Mairona.”

Cire mayafin da ke kanta ya yi, wanda ya yi sanadiyyar bayyanar kwantacen gashinta da ya sha gyara, cike da zaƙuwa ya zare ribbon ɗin da ke ɗaure da gashin, hannayensa duka ya sanya a kan yana shafar gashin ya ce,

“Shi ma gyaran gashin duk don ni?”

Kai ta ɗaga mishi alamar,

“Eh.”

Ya ce,

“To dawo jikina na yi miki godiya.”

Samun kanta ta yi cikin tashi tsaye, shi kuma ya taimaka mata ta dawo jikinsa. Wani irin yanayi mai cike da mutuwar jiki suka samu kansu a ciki. Soyayya da ƙauna ba wanda basu gwada ma juna ba. Tun suna a kan kujera sai gashi sun dawo ƙasa

Tana maƙale a jikin Khamis ya ce, “Lokaci mafi daɗi shi ne lokacin da nake tare da ke.”

Cusa kanta ta yi a ƙirjinsa tana ‘yar dariya. Kulawa mai rai da lafiya suka ba juna, har sai da Maryam ta ji ba za ta yadda Khamis ya koma ba tare da ita ba.

A can cikin gida kuwa Auwal ya susuce a kan Hafsat, kasantuwar bai taɓa ganinta a zahiri ba sai yau, ko lokacin da suka je gano Maryam ba su samu haɗuwa ba saboda shi Abuja ya wuce, sai ranar da zasu dawo KT ne ya biya ya ɗauko su.

Sun daɗe suna chat a waya, sai dai Auwal bai samu damar bayyana mata sirrin zuciyarsa ba saboda wasu keɓantattun dalilai nasa. Amma daga ita har shi suna son juna, kuma suna yin hira mai kama da ta soyayya, sai dai ba soyayyar ce ba.

Ita ma ɗin a yau ne ta ga Auwal face to face.

Kuma ganinsa ya sa ta jin ina ma abotarsu ta koma soyayyar da za ta kai su ga aure, don Auwal ya kai namijin da kowace mace za ta yi sha’awar ya kasance abokin rayuwa a gare ta.

Zaune suke a ɗakin Mamansu Maryam ana ta hira, sai dai su biyun ba su cika sa baki a hirar ba, sai dai aikin satar kallon juna da suke.

Waya Auwal ya ci gaba da dannawa, Hafsat ba ta ankare ba sai ji ta yi kira ya shigo a wayarta, dubawa ke da wuya ta ga Auwal ne. Da idanu ta bi shi har ya fice daga ɗakin yana ‘yar dariya.

Sake kiranta ya yi, aikuwa sai ta shige bedroom ɗin Mamansu Maryam.

Ɗaga kiran ta yi tare da zama a kan stool,

Daga can ta ji ya ce,

“Hafsyna.”

Idanu ta ɗan zaro tare da faɗin “Yau kuma?”

Daga can ya ce,

“Yep, ai yau special day ce a gare ni, saboda a yau ne zan isar da saƙon zuciyata a gare ki.”

A hankali ta lumshe idanu, kasantuwar abin da ta daɗe tana jira kenan, wani irin so take yi ma Auwal wanda ba ta iya misalta shi, daga can ya ce,

“Hafsyna.”

Ta ce,

“Na’am Yayana.”

Ya ce,

“Kin yi shiru.”

Cikin taushin murya ta ce,

“Ai kai nake sauraro.”

Murmushi ya yi tare da faɗin, “Ok, to saƙon zuciyata gare ki shi ne I love you with all my heart, fatan nima za ki so ni.

Idanu Hafsat ta lumshe tare da ƙanƙame wayarta, ba ta san lokacin da ta yi gaugawar faɗin “Love you too dear.” ba

Tana jin lokacin da ya bugi iska ya ce,

“Yes.”

Sirrin zuciyarsa ya ci gaba da fallasa mata, inda ita ma ta faɗa mishi nata sirrin zuciyar, cewar ta daɗe tana son shi, kawai jira take ya fara faɗa. Sai da dai suka fahimci juna sannan suka yi sallama.

Tana fitowa Ruƙayya ta shiga tsokanarta, don tun Auwal na nan ta fahimci komai.

Auwal kuwa samun Mamansu Maryam ya yi a kitchen ya faɗa mata Hafsat yake so, don haka ta isar mishi da saƙonshi a wurin Babansu.

Mamansu Maryam ta ce,

“Haba Auwal, ina shirin raba Maryam da su, shi ne kuma za ka wani ce kana son su?”

Lallaɓa ta ya shiga yi tare da nuna mata wani abu ba zai samu bawa ba sai idan Allah ya hukunta, kuma nagartar Khamis ta ci a yi mishi uzuri, tunda shi ma lalurar nan ta shafe shi, kuma sun ga dil tunda ya rame sosai.

Mamansu Maryam ta ce,

“Auwal idan ina da damar ƙara ma Khamis ɗiya, to wallahi zan ƙara, matsalar ta matarshi ce, yanzu baccin Allah ya dubi Maryam da idanun Rahama ai da ta mutu.”

Kai Auwal ya jinjina, lokaci ɗaya kuma ya shiga tunanin irin mawuyacin halin da Maryam ta sake shiga, lokacin da ciwon ya taso, hauka tuburan ta riƙa yi, sai da Allah ya taimaka suka kai ta wurin Malam Ahmad, wanda aka kai Jummai lokacin da su Alhaji Lauwali suka so sanya ta a ƙungiyarsu ta matsafa.

Da taimakon Allah, Malam Ahmad ya raba Maryam da wannan asiri da aka yi mata har ta samu sauƙi.

Cewa Auwal ya yi,

“Gaskiya ne Mama, amma yana da kyau mu sa a ranmu cewa damar ƙarshe ce matarshi ta samu. Kuma tunda an gane muguwa ce kin ga akwai ɗaukar mataki kenan.” Maganganu masu nutsar da zuciya Auwal ya yi mata, har Allah ya sa ta sauko.

Ɗakin Baban su Maryam ta shiga, don bai jima da dawowa ba. Samun Hajiyarmu ta yi a ɗakin suna magana kan komawar Maryam.

Kishi kumallon mata, duk girman mace tana da shi, kuma idan ya motsa sai ta nuna.

Hajiyarmu ba ta ji daɗin shigowar Maman su Maryam ba, cewa ta yi “Hmm! Magana fa muke a kan lamarin ɗiyarmu, don haka ki bamu wuri mu ƙarasa.”

Ita ma Mamansu Maryam ɗin kishin ne cike da ranta,

“Nima batun ɗana na zo da shi, ko za’a hana ni zama?”

Ta faɗa fuskarta ɗauke da dariyar yaƙe.

Dariya baban su Maryam ya yi tare da faɗin,

“A’a ga wuri zauna.”

Zama ta yi suka kama yi ma junansu dariya, saboda sun fahimci me ke damunsu.

Maganar Auwal na son Hafsat ta yi musu, Hajiyarmu ta ji daɗi saboda tana fatan Allah ya ba Auwal mace tagari, kasantuwarsa mai biyayya ga mahaifa.

Sai dai Hajiyarmu ta ɓoye jin daɗinta akan lamarin Auwal da Hafsat, shaguɓe ta yi ma Maman su Maryam, inda ta ce,

“Au abin son kai ne kenan, kin kafe basa tafiya da ‘yarmu, shi ne ke za ki basu naki ɗan?”

Cewa Maman su Maryam ta yi, “Lamarin ɗana da ‘yarku ba ɗaya bane, don haka kowa ma ya yi ta ɗansa.”

Sun fahimci inda ta dosa, cewa suka yi,

“Tunda kin ce haka mu dai mun shirya maida ‘yarmu ɗakin mijinta.”

Baki ta taɓe gami da faɗin,

“Allah ya sa hakan ya fi alkhairi.” cike da jin daɗin saukowarta suka ce,

“Amin.”

Don gaskiya Maman su Maryam tana da sauƙin kai, takaicin zaluncin da aka yi ma ɗiyarta ne ya sa ta gwada ɓacin ranta.

Batun maganar Auwal da Hafsat kuwa tuni babansu Maryam da Hajiyarmu suka yi na’am da shi, sai dai fatan Allah ya ida nufi.

A tsakar gida kuwa, Zahara’u ce ke ma Maryam tsiya, wai tunda ta shige wurin miji ta yi shiru. A tsiwace Maryam ta ce,

“Eh ɗin, wani ma ya je wurin nashi mijin.”

Dariya su duka suka yi, Zahara’u ta ce,

“Kar dai a yi mana gorin miji, muma auren nan kaɗan ya rage mu yi shi.”

Hajiyarmu ce ta tsinkayi maganar lokacin da ta zo wurin da suke zaune, ganin Maryam na turo baki ta tambaye ta,

“Ya aka yi ‘yata?”

Kamar Maryam za ta yi kuka ta ce,

“Wai Zahara’u ke cewa na shige wurin miji na yi shiru.”

Asma’u ce ta yi saurin faɗin,

“To awaye kajin birni, sai kin faɗi kenan.”

Haupha na wata irin dariya ta ce, “Ahaf! Maryam ce fa, Allah dai ya ƙara mata lafiya kawai.”

Hannun Maryam Hajiyarmu ta kama, lokaci ɗaya kuma tana kallon Hafsat, cikin ranta tana yaba nagarta da kyawun surukarta.

Jan Maryam ta yi,

“Mu je Hafsat.”

Asma’u ta ce,

“Hafsat kuma?”

Daburcewa Hajiyarmu ta yi,

“Wai, Maryam nake son faɗa.” Dariya suka yi suna faɗin, “Hajiyarmu ta yaba da surukarta”, Rufe fuska Hafsat ta yi tana dariya, Hajiyarmu kuwa tuni ta ja hannun Maryam tana dariyar itama.

Ɗaki suka shiga, zama Maryam ta yi a kan kujera, Hajiyarmu kuma ta nufi fridge ta ɗauko mata lafiyayyen tsumi mai sanyi, wanda aka haɗa shi da sassaƙen ɓaure, miƙa mata kwalbar ta yi, da yake Maryam na son shi ta yi saurin karɓa.

“Hajiyarmu ina son wannan abin, yana da daɗin sha.”

Hajiyarmu ta ce,

“Ke kuwa zuma da mazarƙwaila ne, sai sassaƙen ɓaure da rake, da kuma kayan citta da kanimfari ne a cikinsa.”

Sai da Maryam ta ɗauke bakinta daga jikin kwalbar sannan ta ce, “Haba, dole yake yin daɗi. Amma wannan garin sam bana son shi.” Hajiyarmu ta ce,

“Babanbaɗe ko?”

Maryam ta ce,

“Eh shi.”

Hajiyarmu ta ce,

“Ai kuwa yana gyara mace, shi da wannan hatsabibiyar zumar.” Maryam ta ce,

“Ai zumar ba laifi tana da daɗi.” Hajiyarmu ta ce,

“Tunda tana da zaƙi ba.”

Maryam na dariya ta ce,

“A’a, kawai ina zuba mata nono da ice block ne, sai in ji ta yi daɗi, amma hakanan ba ta da daɗin sha.”

Maganar kayan matan suka ci gaba da yi, nan Hajiyarmu ke faɗa mata anjima za ta ci kazar da aka dafa da sassaƙen malmo, Maryam na dariya ta ce,

“Ba kya bari na hakanan, ko rannan na ci ‘yan shila fa.” Hajiyarmu ta ce,

“Ai ba lokacin da zan barki ‘yata, gyara shi ne mace, idan ba ta iya ba to ta rako mata.”

Maryam ta ce,

“Gaskiya ne Hajiyarmu.”

Sai da suka gama maganar kayan matan, sannan Hajiyarmu ta yi mata maganar Khamis, inda ta ce, “Kun gaisa da mijinki ko?” Maryam na dariya ta ɗaga kai, Hajiyarmu ta ce,

“Shi kaɗai zai koma ko?”

Maryam na jin haka ta yi maza ta ɗago kai, sai dai ba ta yi magana ba. Sosai Hajiyarmu ta fahimci ta sauko. Nasiha ta ci gaba da yi mata akan ta bi mijinta sau da ƙafa. Kuma halinta na iya zama da miji ta ƙara ƙaimi duk da ita gwana ce, Hajiyarmu ta ce,

“Ki ƙara ƙaimi, kin san haushin zamanki jarumar mace ne ya sa kishiya huce haushinta a kanki, don haka kada ki sa wasa.

Kuma ko da wasa kada ki bi hanyar da ita ta bi, kin gani dai biyayya ce kika yi har miji ya ƙaunace ki, to ki ƙara akan wadda kike yi. Batun tsafta da gyaran jiki ma kada ki sa sanya, ahir ɗinki da cushe-cushen kayan mata a gabanki, ruwan ɗumi da ganyen magarya ya wadace ki, sai kuma wani magani wai shi MAI KABBARA da zan ba ki, zan faɗa miki yadda zaki yi amfani da shi, sai kuma wasu ingantattu waɗanda ba su ɓata gaban mace.” Godiya Maryam ta yi ma Hajiyarmu akan ingantaccen gyaran da take mata.

Sosai kuma aka samu kyakkyawar fahimta tsakanin Khamis da Mahaifin Maryam saboda shi mutum ne ɗaya da rabi. Batun magar Auwal ma an yi ma Khamis ɗin, aikuwa ya ce,

“Hafsat ta yi sa’ar miji.”

Tare da alƙawarin zai sanar da mahaifansu.

Tunda an samu wannan fahimta, to kuma a bin da ya rage shi ne Maryam ta koma ɗakinta. A shirye take dama, duk wani gyaran jiki ba wanda ba ta yi ba. Kayanta kuma tuni ta yi parking ɗinsu a wuri ɗaya.

A ranar tafiya kuwa kuka ne ta sha shi, mahaifiyarta ma ta yi kukan rabuwa da ita saboda Maryam tana da shiga rai.

Har sun zauna a mota ne ta kira Khamis, cikin ladabi ya fito, cewa ta yi,

“Khamis ga amanar Maryam nan a karo na biyu, don Allah ka kula mana da ita.”

Cewa yayi,

“In sha Allahu Mama.”

‘yan maganganu suka yi, sannan suka yi sallama.

Hajiyarmu da yayarsu Maryam tare da matar Kabiru ce suka shiga baya, Maryam kuma ta shiga gaba kusa da mijinta.

Auwal ne ya ɗauki su Hafsat da su Asma’u suka ɗauki hanya.

Baban su Maryam da ke jin kewar Maryam ya ce,

“Allah ka sauke su lafiya.” Mamansu Maryam ta ce,

“Amin.”

Sannan suka shigo gida su da sauran yara.

*****

Tafiya su Khamis ke yi, lokaci ɗaya suna ta hira abinsu, Hajiyarmu kuwa sai sanya su dariya take. Haba! Yo da hantsi ya fara duban ludayi sai kowa ya yi tsit, Hajiyarmu da ƙanwar babansu Maryam ma bacci suka kama yi, Hadiza matar Kabiru kuwa ta ɗauki waya ta ci gaba karatun littafi.

Shirun da suka yi ne ya ba Khamis damar riƙo hannun Maryam ya ɗan matsa, suna haɗa idanu ya ce, “Ki yi bacci.”

Maƙe kafaɗa ta yi, ya ce,

“Saboda me?”

Ta ce,

“Ba na iya bacci a irin wannan lokacin.”

Sariya ya yi, suka ci gaba da hirarsu ƙasa-ƙasa.

A ɓangaren Aisha kuwa ba ta san yau ne Khamis zai dawo ba, don haka ba wani shiri da ta yi na tarbar mijinta. Khamis ya ɓoye mata ne don gudun yin wani mugun abun, saboda yanzu ta zama abin tsoro.

Su Jamsy da Zuzee da wasu ƙawayensu ne cike da gidan suna ta shewa, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Bayan sun gama shewar ne Jamsy ta ɗauke su a motarta suka nufi gidan Malam, domin karɓo maganin da za a cusa ma Khamis son Aisha, saboda Aishar ta ga alamun Khamis ɗin ba ta ita yake ba, don tunda ya tafi Katsina, kwana uku kenan, amma duka sau biyu suka yi waya.

Baƙin labari Malamin ya faɗa mata a lokacin da suka keɓe, cewar Khamis na hanya kuma tare da Maryam zai dawo.

A rikice Aisha ta ce,

“Don Allah Malam kada ka bari ya dawo da ita.”

Wani ƙaton madubi bokan ya duba, aikuwa ya ce shi bai ga Maryam ɗin ba ma bare ya haɗa ta da aljanu su kora ta daji, ko da ya ganta to kuma garkuwar jikinsu ita da Khamis ta yi ƙarfi, amma ta bari zai yi aiki na musamman a kansu.

Sosai Aisha ta kaɗu da jin maganar malamin ko kuma in ce boka, domin malami baya duba bare tsafi. Ɓoye damuwarta ta yi ta yadda su Zuzee ba za su gane ba, saboda ta fara fahimtar akwai munafuntar juna a tsakaninsu. Daga gidan bokan suka wuce aka aje ƙawayen Jamsy. Aisha da Zuzee kuma ta maido su gidan Aisha tare.

Tunda Aisha ta baro gidan bokan gabanta ke faɗuwa, sai dai ganin motar Khamis a cikin gidan ya sanya mata tashin hankalin da ya fi na gidan boka.

A gigice ta tambayi mai gadi, “Abban Haneef ya dawo?”

Tuni Sule ya fara tsanar Aisha, amsa ya ba ta da,

“Eh Hajiya.”

Cikin ransa kuma yana fatan Khamis ya ɗauki mugun mataki a kanta. Sake tambayar shi Aisha ta yi,

“Shi da wa ya dawo?”

Idanunsa na cikin na Zuzee da ke ta maƙyaftai ya ce,

“Shi da Amarya, sai kuma danginta da su Innata Ruƙayya.”

“Mun shiga uku.”

Faɗar Zuzee tare da dafe ƙirji, Aisha ta ce,

“Ke fa miye naki na shiga uku, ni dai da waccan matsiyaciyar ta dawo ke da shiga uku.”

Zuzee ji take Aisha ba ta fi ta tsanar Maryam ba, saboda Maryam ɗin ita ce rayuwar Khamis.

Gaba suka ƙara, Zuzee ta kafe ba za ta shiga ba, saboda ba ta son Khamis ya san ita ce ke kai Aisha ta baro.

Aysha kuma ta ce,

“To wayarki fa?”

Zuzee na tuna ta’adin da ke cikin wayarta, wanda indai Aisha ta gani to ƙarshen alaƙarsu ya zo, saboda layin da ta ke kiran Khamis yana cikin wayar, kuma ta san yadda Aisha ke yawan kiran layin don ta gane mai bibiyar mata miji.

Ba arziƙi Zuzee ta ce,

“Mu je.”

Kafin su shiga ciki sai da Aisha ta tsara ƙaryar da za ta yi ma Khamis.

Shigarsu falon ta yi daidai da fitowar Khamis daga ɗakinsa, gefenshi kuma Maryam ce saƙale da hannunshi tana dariya. Take annurin da ke fuskar Khamis ya kau. Tsakanin Maryam da Aisha kuwa ba wadda ba ta girgiza da ganin ‘ar’uwarta ba, Zuzee kuwa girgizarta ta daban ce.

Ƙarasowa suka yi gaba ɗaya inda suka haɗe a tsakiyar falo, cikin kama kai Aisha ta ce,

“Maryam, Abban Haneef, kun dawo?”

Khamis ya ce,

“Eh ba gashi kin ganmu ba?”

Ta ce,

“Eh.”

Ya ce,

“To madalla, daga ina kike?”

“Wallahi ɗinki na je karɓowa na taras da telan baya nan.”

Ya ce,

“To da kyau.”

Maryam kuwa kasa bata amsa ta yi saboda bata da maƙiyiya kamar Aisha, wucewa suka yi, inda suka shiga ɗakin Maryam.

Nan suka barta ita da Zuzee suna ta raba idanu. Zuzee kuwa tuni cikinta ya ɗuri ruwa, don da ta gaida Khamis ƙin amsawa ya yi.

“Ke ni tafiya zan yi.”

Zuzee na kyarma ta faɗi haka.

A sanyaye Aisha ta ce,

“Bari to na ɗauko miki wayarki da ke caji.”

Shigar Aisha ɗaki ke da wuya wayar Zuzee ta fara ruri.

‘Fiance’ sunan da ta gani a jikin lambar kenan.

Ko a mafarki Aisha ta ga lambar Khamis za ta gane. Cikin wani sabon tashin hankali ta shiga karanta lambar.

Kasa yarda ta yi, har sai da ta kira lambar da ta ɗauka a wurin Khamis da wayarta.

Still cikin wayar Zuzee kiran ya shigo.

“Bala’i, me kenan? Waccan tsinanniyar amanata take ci?”

Kiran Khamis ne ya sake shigowa a wayar, fitowa Aisha ta yi daga ɗakin tana ta huci. Zuciya ce ta umarce ta da ta ɗaga kiran, sai da ta zo gaban Zuzee sannan ta ɗaga tare da miƙa mata,

“Ana kiran ki.”

Zuzee bata wani duba lambar da ta kira ta ba ta kanga wayar a kunne. Magana biyu ta ji iri ɗaya, Ga muryarshi a fili, ga ta kuma cikin waya yana faɗin,

“Princess Aydah, ko kuma na ce Zuzee.”

<< Kishiyar Katsina 19Kishiyar Katsina 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×