Skip to content
Part 21 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Ya Salam!

Mutuwar tsaye Zuzee ta yi lokacin da ta yi arba da Khamis a gabanta yana mata waya, cikin ‘yan sakanni ta shiga tambayar kanta,’ Yaushe ya gane ni ce?’

Amsar ita ce, SP Ameer ne yayi ta bibiyar lambar, da farko ba ta kula shi saboda ya faɗa mata ya sa wrong number ne sai ya same ta, daga baya tana jin yana da kuɗi, kuma sonta yake sai ta fara sake mishi. Cewa ya yi ta kawo account number ɗinta zai turo mata kuɗi, aikuwa jikinta na ɓari ta turo da sunan Zuhura Lawal, tabbas ya turo mata kuɗin, hakan ya bata damar bashi cikakken bayaninta, duk a sunan suna soyayya. Khamis na jin Zuzee ce ke mishi wannan tsiyar ya ɗora hannu bisa kai, Allah ya taimake shi bai faɗa mata sirrinshi ba, kuma duk wani sakin layi da wasu mazan ke yi idan sun haɗu da mace a waya baya yi, hakan ne ya bashi ƙwarin gwiwar yin maganinta tunda ba tsarar shi bace.

Aisha ta san labarin Aydah, don bai ɓoye mata komai ba saboda gudun zargi.

Don haka bata san lokacin da ta yi ma Zuzee wata irin maƙara ba tana faɗin,

“Don ubanki amanata kike ci, da mijina kike soyayya?”

Wannan maƙara ta zo ma Zuzee a bazata, don da farko ba ta san Aysha ta gane ba. Kasa ƙwatar kanta ta yi har Aisha ta samu galabar bankaɗa ta ga kujera tare da danneta ta yi ta jibga, zafin bugu na ratsa ta tana faɗin,

“Aisha kin haukace ne da za ki riƙa jibga ta kamar jaka?”

Aisha na huci ta ce,

“Ai kin fi jaka jakanci tunda har ki ka zaɓi cin amanar ƙawarki, na yarda da ke ashe ke kina daga gefe kina munafunta ta.”

Khamis na ganin Aisha za ta lahanta Zuzee ya ɗago ta tare da faɗin,

“Kada ki kashe musu ‘ya fa!”

Kukan kura Aisha ta yi tare da komawa kan Zuzee ta ce,

“Ka barni na kashe ta, tunda ta san babu ragi a tsakanina da duk wadda ta shiga rayuwar mijina.”

Ihun da Zuzee ta fasa ne ya ba su Maryam damar fitowa daga ɗakinta, Hajiyarmu da Rahama kuwa sai cewa suke,

“Lafiya?”

Su Hafsat da Haupha kuwa sun gane dara ce ta ci gida, tunda sun fi kowa sanin Zuzee ce ƙawar Aisha.

Khamis ma amsar da ya ba su Hajiyarmu kenan, inda ya ce, “Dara ce ta ci gida.”

Hajiyarmu ta ce,

“To Allah ya kyauta, amma ku raba su kada su ji ma juna ciwo.” Don yanzu sun kaure da faɗa, suna ta cizon juna. A yadda suke kai ma juna duka tsaf za su bige wanda ya zo raba su, don haka sai dai su Rahama suka ja baya, suna kallon ikon Allah.

Zuzee ce ta samu sa’ar cakumar Aisha, da kumburarren bakinta ta ce ma Aisha,

“Ke shegiya, ai ke da mijin nan har abada wallahi, don watan tonuwar asirinki ya tsaya.”

Aisha na jin haka ta yi gaugawar watsar da makamanta, saboda tana tsoron tonon silili, cike da nadamar abinda ta yi ma Zuzee ta ce,

“Zuzee kada mu yi haka da ke don Allah.”

Sai da Zuzee ta goge jinin da ya biyo mata ta gefen ido sannan ta ce,

“Ke ɗin banza.”

Kowa ya lura da yadda Aisha ta kaɗu don Zuzee ta ce za ta tona mata asiri. Tsawa Khamis ya daka musu don bai son jin abinda zai ƙara mishi baƙinciki dangane da Aisha, wanda ya ji kuma ya gani ma ya ishe shi.

Shigowar Abdul ce ta hana Khamis sake yi musu magana. Saboda tunda Khamis ya dawo bai taras da Aisha ba ya kirawo shi, don ya zama shaida a kan hukuncin da zai yi mata.

Ƙarasowar Abdul tsakiyar falon ta yi daidai da lokacin da Zuzee ta ce, “Aisha idan kika ga ban faɗa musu asiri kika yi ma Maryam ta haukace ba to ban haihu ga uwata ba. Ke da Anty Jamsy kuka je wurin boka aka baki maganin da kika haɗa da jinin al’adarki kika ba mijinki ya sha, tun daga wannan rana bai sake neman matarshi ba, har yunƙurin zubar ma Maryam da ciki kika yi, Allah bai nufa ba, amma da yake kwanan ɗan da aka haifa ya ƙare sai da boka ya sa aljanu suka kashe shi.”

Sallallami duk wanda ke wurin ya shiga yi, Khamis da Abdul kuwa ji suka riƙa yi kamar su aka tona ma asiri.

Aisha da taga ba sauran ɓoyo ta ce ma Zuzee,

“Wace shaiɗaniyar ce ta kai ni idan ba ke ba?”

Zuzee ta ce,

“Don kuma kina jaka sai ki ka biye mini ko?”

Wannan lamari ba wanda ya yi ma daɗi, musamman Abdul da Khamis.

Cikin tashin hankali Khamis ya dubi Abdul,

“Ka gani ko?”

Kamar Abdul zai yi kuka ya ce, “Na gani, ka yi ma Aisha duk hukuncin da ka ga dama, ita kuma wannan tsinanniyar ka bar mu da ita.”

Aisha kuwa tuni ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta sadaƙar Khamis sakinta zai yi, ita kuka su Maryam kuka.

Khamis ya juya a ƙufule ta riƙo mishi ƙafafu,

“Abban Haneef!”

Fizge ƙafarshi ya yi.

“Ki daina taɓa ni, don yanzu ba aurena a tare da ke, ki je na sake ki saki biyu wallahi.”

Duk azabar da Zuzee ke ji a gaboɓinta bai hana ta yin shewa ba.

“Burina ya cika na raba ki da Khamis!”

Maida dubanta ga Khamis ta yi, “Dama ƙarasa sakin ta ka yi tunda ita ‘yar iska ce.”

Rufe bakinta ke da wuya Abdul ya wanka mata mari, Hafsat da Ruƙayya kuwa suka rufar mata da duka, saboda ba ƙaramin tausayi Aisha ta basu ba.

Hajiyarmu ta ce,

“Kai wannan yarinyar ‘yar banza ce, ashe dama burinki kenan?” Zuzee ba ta da kunya ko kaɗan, zagin Hajiyarmu ta yi, aikuwa Zahara’u da Asma’u suma suka rufar mata da duka

Sai da ƙanwar babansu Maryam da su Rahama suka yi da gaske sannan suka ƙwace ta, Rahama na kuka ta ce,

“Idan kuka kashe ta ba za ku fita ba.”

Khamis kuwa ji ya yi dama bai saki Aisha a gaban Zuzee ba, tunda burinta kenan. Bisa hannun kujera ya zauna tare da dafe kansa, cikin ransa kuma yana jin kamar zai mutu don baƙinciki.

Zuzee na zaune a ƙasa ta haɗe kai da gwiwa kuma ta ji shigowar motar police. Ameer ne ya turo mota a tafi da ita. Har da Aisha Abdul ya ce a haɗa saboda ta sa an kashe ma Maryam ɗa, hannu ta ɗora a ka tana faɗin,

“Na shiga uku, wallahi ba ni kashe shi ba.”

Maryam ba ta san lokacin da ta riƙe Aisha ba tana faɗin,

“Ba inda za ta je, ni ce uwar ɗan da aka kashe, kuma na yafe mata.”

Khamis ne ya janye Maryam, Abdul kuma ya ce,

“Ko kin yafe, shari’a ba za ta yafe mata ba. Ki rabu da ita ta girbi sakamakon cin amanar mahaifanta da mijinta da ta yi.”

Suna ji suna gani aka iza ƙeyar Zuzee da Aisha zuwa Police headquater.

Duk da mugun halin Aisha, amma ba wanda bai tausaya mata ba. Zuzee kuwa zagi ne ta sha shi wurin su Hafsat, sai da Hajiyarmu ta taka musu birki sannan suka yi shiru. Ce musu ta yi,

“Kada wanda ya sake zaginta. Wannan kuma izina ce gare ku, ƙawayen banza ku guje su, sannan ku kiyayi zargi gudun kada wata rana ku zama abin zargi ku ma.” Faɗa mai ratsa zuciya ta yi musu. Aikuwa duk suka yi laƙwas. Jiki a mace suka ƙarasa kimtsa ma Maryam ɗakinta, wanda dama a gyare yake.

Hajiyar su Haupha na zuwa aka bata labarin gwaramar da aka yi, ta ce,

“Na gode ma Allah da ya sa bana nan aka yi.”

Duk wani abu da ya kamata su yi ma Maryam sun yi. Nasiha suka taru suka ƙara yi mata, suka nuna mata ƙarshen yadda makomar Aisha ta kasance, don haka ta kiyaye kanta da zargi da baƙin kishi.

Suna yin Magariba kuma Auwal ya zo ya ɗauki su Hajiyarmu ya kai su gidan su Haupha. Rahama da su Hafsat kuma Khamis ya kai su gida. A hanyar dawowa ne ya biya gidan Abdul ya ɗauko yaransa, don sai da Abdul ɗin ya zo yake faɗa mishi suna can tun jiya.

Sai da ya biya ya yi musu siyayya sannan suka nufo gida. Sosai yara suka yi murnar dawowar Maryam, ita ma ɗin ta yi farinciki da ganinsu. Tambayar shi Haneefa ta yi,

“Ina Mommy?”

Ce mata ya yi,

“Ba ta nan.”

Da ya ga za ta matsa mishi ya taka mata birki. Abinci suka ci, ba a daɗe ba ma suka yi bacci.

A ɓangaren Maryam kuwa, duk da ruɗun da suka shiga, amma hakan bai hana ta yin shiri na musamman domin tarbar mijinta a shimfiɗa ba.

Sanye take cikin night gown mai ɗaukar hankalin mai kallo. Sai da ya yi wanka sannan suka ciyar da kansu abinci mai daɗi.

Sosai Khamis ya ɓoye ƙunar da ke ranshi duk don ya ɗebe ma Maryam kewarsa. Suna gamawa ya ɗauke ta tsam sai kan ƙayataccen gadonta. Rumfa yayi mata yana kallon kyakkyawar fuskarta, wadda ganinta a dab da shi ya yaye mishi kaso mai yawa na damuwarshi.

“Ina son ki Mairo, da na san haka ƙarshen zamana da Aisha zai kassnce da tuni na rabu da ita.”

Hannu Maryam ta sa ta toshe mishi baki da shi.

Harshe ya fiddo ya ci gaba da lasar hannun, daga nan ya zame jikinsa ya kwanta a gefenta. Muradinsu shi ne kasancewa tare da juna, don haka ba su wani ɓata lokaci ba suka shiga nuna ma juna kulawa ta musamman.

A wannan dare sai da Maryam ta toshe ma Khamis baki, saboda sambatun da ya riƙa yi. Dama an ba ta labarin in dai ta yi matsi da MAI KABBARA to sai ta toshe mishi baki, haka kuwa aka yi.

Yana dawowa daidai ya ce,

“Ke wai me ake baki ne idan kika je Katsina?”

Tana dariya ta ce,

“Abin daɗi mana.”

Ya ce,

“Wa yake baki?”

Ta ce,

“Hajiyarmu.”

Sai da ya sumbace ta sannan ya ce, “Allah ya saka ma Hajiyarmu da gidan aljanna.”

Maryam ta ce,

“Ita kaɗai?”

Ya ce,

“Har da Mama da Baba.”

Maryam na dariya ta ce,

“Gaba ɗaya mahaifanmu za ka yi ma addu’a.”

Ya ce,

“Lallai kam Mairo, Allah ya taimake su baki ɗaya Amin.”

A wannan dare sai da ya yi ma Babansu Maryam kyautar kujerar Makka, ita kuma ya yi mata alƙawarin canjin sabuwar mota.

Aisha kuwa a Police station suka kwana su uku, don Jamsy ita ma tun jiya Ameer ya sa an kamo ta. Laifinsu shi ne dai kashe ɗan Maryam da Aisha ta sa boka ya yi.

SP Ameer bai so Aisha ta kwana ba saboda darajar Mahaifanta, amma Alhaji Usman ya ce duk wanda doka ta faɗa kanshi a hukunta shi.

Kuka da nadama kuwa Aisha ta yi mai isarta.Tana ji tana gani mugun abin da ta shuka ya ƙare a kanta, ga shi kuma ta bar ma Maryam gidan da mijin tare da ‘ya’yan.

To me ya fi wannan takaici, kin kasa hakuri da kishiya, gashi kuma kin bar mata gidan saboda baƙin kishi. Mu kula ƴan’uwana mata, mu sani nadama ce ƙarshen duk wani kishin da babu tsoron Allah a cikinsa.

Zagi da tsine ma juna kuwa shi ne aikin da suka kwana suna yi, Aisha ta ce ma Zuzee,

“Allah ya isa ce tsakanina da ke.” Wata irin dariya Zuzee ta tuntsire da ita, duk da fuskarta da ke kumbure, saboda dai burinta ya gama cika tunda ta kashe ma Aisha aure, sai da ta gama dariyar sannan ta nuna Jamsy da ke ta muzurai.

“Wannan tsohuwar kilakin za ki yi ma Allah ya isa ba ni ba.”

A fusace Jamsy ta yi kan Zuzee ta ci gaba da mazga, Zuzee ba ƙarfin ramawa, don haka sai da Jamsy ta gaji da dukanta sannan ta rabu da ita. Zuzee dai ta sha jibga marar misaltuwa, shi ya sa fuskarta da jikinta ba abin da suke sai ciwo.

Washegari da Safe sai ga ƙeyar Bokan da suke zuwa wurinshi SP Ameer ya tuso.

Da bincike ya yi bincike sai aka gane babu hannun Aisha a kashe preemie ɗin Maryam. Shi Malamin ne ya wakilta aljanin da aka haɗa da Maryam ya kashe jaririn, saboda zai yi ma wani ɗan siyasa aiki. Abdul da ke tsaye ya ce,

“Duk da haka Aisha ba za ta fita ba, saboda a dalilin aikinta aka kashe yaron.”

Bokan ya ce,

“Kada ku ɗauki alhakin yarinya fa.”

Wannan statement na boka ne ya kuɓutar da su Aisha, amma fa ba don Abdul ya so ba duk da ƙanwarshi ce, shi ya fi son a yi mata hukuncin da za ta shiga taitayinta a gaba.

Zuzee kuwa ana fiddo su ta ɗingisa bakin titi ta tari Napep. Kafin ta shiga ne ta ga motar mijin Jamsy, inda yake ɗauke da Hannah a gaban mota, gani ta yi sun shiga police headquater ɗin, baki ta taɓe sannan ta shiga mai Napep ya ja.

Jamsy kuwa tana hango mijinta riƙe da hannun Hannah gabanta ya faɗi, alamu kenan na karyewar asiran da take musu. Kuma boka ya ce duk ranar da asirin da take ya karye, to watan wulaƙantarta ya tsaya.

Gashi kuma ta yi imani da boka, don haka Hannah tana miƙa mata divorce paper ta kurma ihu. “Hannah miye nan?”

Ta tambaye ta cikin kiɗima, Hannah ta ce,

“Sakamakon muguntarki ne a ciki.”

Mijin kuma ya ɗora da,

“Daga nan sai ki wuce psyciatric, don na san ƙarshenki kenan.”

Aikuwa maganar mijin Jamsy ta zama gaskiya, nan ta baje ƙasa tana ta ihu, fallasa ba irin wadda ba ta yi ma kanta ba. Aikuwa cikin ɗan lokaci sai ga ‘yan jarida sun zo samun labari. Bayan sun gama haɗa rahoto a kanta, sai ga mota daga psyciatric hospital an tafi da ita.

Zuzee kuwa tana zuwa gida ta iske an gitta gawar mahaifiyarta a tsakar gida, jira ake mutane su gama haɗuwa, sai a fidda gawar a sallace ta. Zuzee bata da wani gatan da ya wuce mahaifiyarta, to gashi ta yi sakaci har baƙincikinta ya kashe mahaifiyar. Za ta fara kuka kenan Yayarta ta ce,

“Kada ki fara, tunda kin kashe ta da baƙinciki kin ga shikenan.”

Jiri ne ya kwashi Zuzee ta faɗi ƙasa somammiya. Janye ta aka yi gefe tare da watsa mata ruwa, tana farfaɗowa ba wanda ya sake bi ta kanta. Daga kwancen da take ta shiga kukan nadama tare da neman yafiyar ubangiji, don ta san lokacin wulaƙantarta ya yi.

Abdul da Aisha kuwa a ƙofar shiga falo suka taras da Mommy tsaye, da alamun su take jira.

Aisha kuwa ji take kamar ta tsage ƙasa ta shige, za ta shiga falon kenan Mommy ta dakatar da ita. “Kada ki shigo mini falo, don na cire ki a jerin yaran da na haifa.” Cikin hanzari da kuka Aisha ta toshe ma Mommy baki.

“Ki yi mani duk hukuncin da ya dace da ni, amma kada ki ce mini haka.”

Kukan da ke maƙale a zuciyar Mommy ne ya fito, ita kuka Aisha kuka.

Alhaji Usman na zuwa shi ma sai da yayi kukan wulaƙanta su da Aisha ta yi, cike da baƙinciki ya ce, “Aisha ba zamu yi miki baki ba, amma ga ki ga duniya nan. Kuma tunda kin kashe aurenki, to ki sani baki da sauran gata a gidan nan.”

Haka kuwa aka yi, sai da masu aiki suka fi Aisha matsayi a gidan, babu wani da take raɓa ta ji daɗi, saboda kowa yayi tir da Allah wadai akan tozarta musu ahali da ta yi, saboda kowa ya san Alhaji Usman a gari, kuma duk an ji labarin abin da ya faru.

Sosai duniya ta hora Aisha. Nadama kuwa kullum cikin yinta take. Sauƙinta ma Khamis na aiko Sani ya kawo mata yaranta, kuma bisa ga yadda take ganin yaran da kyakkyawar kamala Maryam na ji da su, don duk sa’adda suka zo sai Haneef ya ce,

“Mammy, Anty tana da kirki.” Haneefa kuwa tambayar ta take, “Mammy yaushe za ki koma gida?”

Wannan tambayar ne ke karya zuciyar Aisha ta yi ta kuka, kuma babu mai lallashin ta bare ya shige mata gaba, saboda burinta bai wuce ta koma ɗakinta don ta gyara kuskuren da ta yi ba.

Khamis kuwa sai su Haneef sun yi maganarta ma yake tunawa da ita, saboda Maryam ta tsaya kai da fata wurin hana shi tunanin wata mace idan ba ita ba, ta hanyar kissa da biyayya ta samu wannan dama. Ita kuwa Maryam ɗin kana ganinta za ka gane ‘yar lelen miji ce. Tuni kuma har ta samu wani cikin, wanda Deni ya yi mata albishir ɗin ‘yan biyu da yardar Allah.

Da yammacin wata Juma’a ne Aisha na kwance a ɗakinta ta ji ana knocking, a sanyaye ta tashi ta buɗe ƙofar.

“Laaa takwara ta Aisha?!”

Ta faɗa tare da rungume taƙawarta Nana Aisha ‘uar mutan Nijar, wadda kuma Aishar ke nadamar watsi da shwararin da ta taɓa bata.

Zuciyar Aisha a karye ta shiga ɗakin, tare suka zauna a kan sofa, bayan Aksha ta karɓi babyn Aisha da zai kai wata huɗu da haihuwa.

Cikin muryar kuka Aisha ta tambaye ta,

“Yaushe ki ka haihu?”

Aisha ta ce,

“Wata huɗu kenan.”

Sunan yaron ta faɗa ma Aisha wato Umar, ana ce mishi Faruk saboda sunan kakansa ne.

Gaisuwar yaushe gamo suka yi, Aisha ta ce,

“Aisha kin ga yadda son zuciya da watsi da shawarki suka yi da ni ko?”

Cike da tausayinta ta ce,

“Na gani Aisha.”

Nana ta ce.

“Ki yi mini duk faɗan da ya dace, na miki alƙwarin zan ɗauka. Ni dai fatana na koma ɗakina domin gyara kuskuren da na aikata.”

Nana Aisha kam ba ta da faɗan da za ta yi ma Aisha, saboda duniya ta yi mata, sai dai tana da shawarar da za ta ba ta wadda za ta iya fisshe ta, idan Allah ya so ta da Rahama sai ta koma ɗakinta. Cewa ta yi,

“Ki dage da istighfari da nafilfili, kuma ki kai maƙura wurin kai ma Allah kukanki, idan da rabo sai ki koma ɗakin ki.”

Wannan shawarar Aisha ta bi. Ci gaba da kai kukanta ta yi ga Allah, azumin Ramadana na zuwa kuwa ta ƙara ƙaimi wurin ibada.

Sannan kuma ta riƙa tura ma Khamis mutane su lallashe shi ya maida ta. Daga cikin mutanen akwai KB, aikuwa KB na mashi maganar ya ce,

“Ba ranar komawarta gidana.”

KB ya ce,

“Wai ko saboda ‘ya’yanta fa.”

A fusace Khamis ya ce,

“To ‘ya’yanta suna cikin wahala ne? Yadda Maryam ke kula da su ko ita da ta haife su ba ta kula da su ba, idan za a kawo wani uzurin zan iya karɓa, amma ba na yara ba.”

Saƙon Khamis na koma ma Aisha ta ci kuka kamar hawayenta za su ƙafe, kuma duk da tausayinta da ‘yan gidansu suka fara, amma ba mai iya ba ta haƙuri.

Khamis kuwa ba don bai son Aisha yake ƙin maido ta ba, sai don gudun kada ya sake amince mata ta ha’ince su.

Addu’a da neman zaɓin Allah ya shigayi shi ma. Kwatsam sai ga mahaifiyarshi ta kira shi a kan batun ya maido Aisha. Saboda su Haneef na ce mata ta sa Daddy ya maido musu Mommy, wai tunda ta yi nadama.

Da Khamis ya samu Maryam da zancen ta ce,

“Ni dai ba zan ce ka maido ta ba don jama’a su so ni, amma idan kai ka yi ra’ayin maido ta zan mara maka baya ɗari bisa ɗari.”

Dogon nazari ya yi, sai ya fahimci barin Aisha a wannan yanayin zai iya cutar da ita, tunda har ta yi nadama. A ranar Idin ƙaramar sallah ana tasowa daga masallaci ya wuce da yaransa a gidansu Aisha.

Bayan ya gaisa da mahaifan Aisha ne ya ce yana son a bashi damar keɓewa da ita.

Khamis na mata albishir ɗin komawa ɗakinta ta fashe da kukan godiyar Allah, wani irin tausayinta ne ya kama shi, amma sai ya ce,

“Wannan shi ne last chance ɗinki, saura igiyarmu ɗaya, idan kin yi riƙo da ita bisa ga tsoron Allah, to mutuwa ce za ta raba ki da ɗakinki, idan kuma kika yi wasa da ita, toh wallahi tsaf za ki dawo gida.”

Ai ko Khamis bai faɗa mata ta riƙe aurenta ba, dole ta riƙe. Ɗora ɗamarar zaman amana ta yi da mijinta da kuma kishiyarta.

Duk wani masoyin Aisha sai da ya taya ta murnar komawa ɗakinta. A ranar da ta tare ne Maryam ta rako mata Khamis, gefenta Maryam ta zauna tare da ruƙo hannunta,

“Amarya ga amanar mijina nan na kawo maki. Aisha na tuna yadda ta yi ma Maryam a can baya ta rungume ta,

“Na karɓa Mairo, kema na karɓi taki amanar, ki yafe mini zaluncin da na yi maki, yanzu ni ce abin zargi ba ke ba.”

Maryam ta ce,

“Nima ki yafe mini duk lafin da na yi miki.”

Khamis da ke kan stool ya rungume su baki ɗaya,

“Nima ku yafe mini don Allah.” Dariya su duka suka yi. Har ɗaki Khamis ya raka Maryam tare da bata magana, don ya ga kishi na shirin sanya ta kuka. Sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya nufi ɗakin Aisha.

*****

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Maryam ta haifi yaranta kyawawa mace da namiji. Macen an sanya mata sunan Hajiyarmu wato Zainab, Namijin kuma an sanya mashi sunan Abdullahi wato mahaifin Khamis, ana kiransu Hassan da Hussaina.

Kuma a sabon gidan da Khamis ya gina mai ɗauke da part biyu suka koma, a can aka yi taron sunan ‘ya’yan Maryam.

Kuma kowace ita kaɗai ce a part ɗinta, hakan kuma ya musu daɗi, domin kowace za ta wala son ranta.

Aisha ma tana ɗauke da matashin cikinta. Kuma tuni ta gane illar zargi, kuma ta fahimci kissa ce nagartacciyar hanyar mallakar miji ba asiri ba, don haka yanzu Khamis na jin daɗin zama da ita. Batun ƙawaye kuma Nana Aisha ce kaɗai suke tare, saboda tana ba ta shawarar yadda za ta maido martabarta a idanun mijinta.

Tuni kuma aka sanya ranar bikin Auwal da Hafsat, sai mu ce Allah ya ida nufi Amin.

Zuzee kuma da farko ba ta karaya ba, tana jin labarin Aisha ta koma ɗakinta sai ta fantsama asiri, da yake yanzu Aishar ta riƙe Allah sai ya kare ta. Daga ƙarshe da ta ga asirin da take ma Aisha ya ƙi ci sai ta saduda. Yanzu dai ta auri wani Alhajin ƙauye, tana can matanshi da ‘ya’yanshi na juya ta.

Tammat Bi Hamdillah

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani damar kammala wannan littafin lafiya. Ina roƙonsa ya amfanar da mu alkhairan da ke cikinsa. Ina kuma neman gafararsa akan kuskuran da na yi a cikinsa.

Godiya ta musamman ga masoyan littafin KISHIYAR KATSINA, yawanku ba zai bari na lissafa ku ba. Amma wallahi ina sonku, kuma ina jin daɗi yadda kuke sharhi a kan littafinnan.

Sai mun haɗu a wani littafin In Sha Allah. 

Maman Mu’azzam da Abdallah

<< Kishiyar Katsina 20

4 thoughts on “Kishiyar Katsina 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×