Dogon nazari Khamis ya yi, sai ya fahimci ƙyale Aisha da ya ɗaukar ma ransa zai yi idan har ta ƙi haƙura ba mafita bace, saboda zaman ba zai ɗore ba alhali suna jin haushin juna, dole ne wani abu marar daɗi ya biyo baya wanda kuma ba ya fatan faruwar sa.
Sosai jikinsa ya yi sanyi, har ta kai ga Maryam da ke maida kaya a wardrobe ta lura. Ɗabi'arsa ce taya ta yin duk wani aiki da ta jawo a ɗakin, amma sai gashi yau bai taya ta ba, bugu da ƙari kuma ya yi. . .