Skip to content
Part 6 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Dogon nazari Khamis ya yi, sai ya fahimci ƙyale Aisha da ya ɗaukar ma ransa zai yi idan har ta ƙi haƙura ba mafita bace, saboda zaman ba zai ɗore ba alhali suna jin haushin juna, dole ne wani abu marar daɗi ya biyo baya wanda kuma ba ya fatan faruwar sa.

Sosai jikinsa ya yi sanyi, har ta kai ga Maryam da ke maida kaya a wardrobe ta lura. Ɗabi’arsa ce taya ta yin duk wani aiki da ta jawo a ɗakin, amma sai gashi yau bai taya ta ba, bugu da ƙari kuma ya yi shiru ba tare da yi mata magana ba.

Zuciyarta cike da damuwar sauyin yanayinsa ta rufe wardrobe ɗin. Ɗan dafa shi ta yi lokacin da ta zauna a gefensa kan sofa ta ce, “Yau kamar baka cikin walwala, ko wani abu ya faru ne?”

“Me kika gani?”

Ya tambaye ta bayan ya sakar mata gajeren murmushi.

Ɗan shagwaɓewa ta yi tare da kwantowa a jikinsa ta ce,

“Na ga yau ba ka taya ni maida kaya ba, kuma ‘yar hirar nan mai daɗi da muke duk babu ita.”

Kasa faɗa mata damuwarsa ya yi, sai dai yayi mata hannunka mai sanda ta hanyar faɗin,

“Kin san yau da gobe sai Allah.”

Ta ce,

“Haka ne.”

Ya ce,

“Toh ina da ‘yar damuwa ce, ina kuma son ki taya ni da addu’a.”

Cike da damuwa ta ce,

“In Sha Allahu zan taya ka mijina, Allah ya yi maka maganin abin da ke damun ka.”

“Amin.”

Ya faɗa a taƙaice, saboda zuciya na ta ƙara tsoratar da shi a kan lamarin Aisha.

Ko kaɗan Maryam ba ta matsa mishi da surutu ba, sai dai ta lafe a a gefensa, saboda ta san hakan na mishi daɗi.

Ƙarar wayarsa ce ta katse musu shirun da ya ratsa su, idanunsa da ke rufe ya buɗe tare da faɗin, “Wayata Mairo.”

Da hanzari ta ɗauko mishi wayar akan gado.

“Waye ya kira?”

Ya tambaye ta, idanunta a kan fuskar wayar ta ce,

“A Umar ne.”

Lokaci ɗaya kuma ta ɗaga kiran tare da kanga mishi wayar a kunne.

Hannunta da wayar ya haɗe ya riƙe, sannan kuma ya zaunar da ita a jikinsa.

“Kana sha’aninka ango, wato tunda ka ƙara aure ko wayarmu ba ka son ɗagawa ko?”

Daga can cikin wayar A Umar ya faɗi haka bayan sun yi ma juna sallama.

Dariya Khamis ya yi,

“Sorry abokina, Wallahi na ga kiranka, na so na sake kira kuma sai na shafa’a.”

Daga cikin wayar ya ce,

“Okay, to ina Amarya?”

Idanun Khamis a cikin na Maryam ya ce,

“Ga ta a tare da ni tana sauraren ka.”

A Umar ya ce,

“Kai da kyau, to ta shirya mana girki mai daɗi, don yau a gidanku za mu wuni.”

A wannan karon Maryam ce ta yi magana, cewa ta yi,

“Lallai muna da manyan baƙi, toh Allah ya kawo ku lafiya.”

A Umar ya ce,

“Amiin Amarya.”

Ci gaba da magana suka yi da Khamis, daga bisani suka yi sallama.

A Umar shi ne babban abokin Khamis, wanda suka haɗu tun a primary school har zuwa University, sai dai suna yin Degree suka rabu, saboda Khamis ya fi maida hankali ga sana’ar saida motocin da suka gada a wurin mahaifinsu. Shi kuma A Umar ya ci gaba da karatu ne inda a yanzu yake koyarwa a Jami’ar Maryam Abacha da ke Niger, a can kuma ya haɗu da matar da yake aure mai suna Nana Aisha.

Cefane mai rai da lafiya Khamis ya fita kasuwa ya siyo. Cikin ransa kuma yana gode ma Allah da ya sa girkin Maryam ne saboda ba ta da gandar aiki. A kitchen ya same ta har ta yi boiling shinkafa tana tacewa.

“Da kyau Mairo, rashin son jikinki na ta’azzara soyayyarki a zuciyata.”

Murmushi mai cike da jin daɗi ta yi. Buɗa cefanen ta yi, ta ga duk abin da ake buƙata ya kawo.

Tambayarta ya yi,

“Komai ya yi ko?”

Ta ce,

“Eh.”

Ya ce,

“To bari na karɓo drinks.”

Cewa ta yi,

“Akwai drinks anan, kuma zan ƙara musu da zoɓo.”

Sosai ya ji daɗin hakan, saboda dama ba son fita yake ba.

Sai dai kuma ya lura aikin na da ɗan yawa, tunani ya shiga yi ko ya kira Aisha ta taya ta?, Tsoron rashin mutuncin Aishar ne ya dakatar da shi.

Duban Maryam dake rage wutar Gas ya yi ya ce,

“Aikin ya miki yawa ko?”

Idanunta a kan cefanen ta ce,.

“Eh to, ko za ka ta ya ni?”

Da dariya ta ƙarashe maganar saboda da wasa take.

“Sosai ma kuwa zan taya ki.”

Ya faɗa yana nannaɗe hannun riga. Nuna mishi ta yi da wasa take yi, amma ya kafe dole sai ya taya ta.

Datsar kabewa ta bashi saboda ita ce ba ta da yaji, ita kuma ta ɗauki cefanen ta fara gyarawa.

Aisha ce ta doso kitchen ɗin a lokacin da Maryam ta ce mashi, “Ka zama zaƙin zaƙa here.”

Shi kuma ya ce,

“Maigida da fere kabewa ba.”

Dariya suka tintsire da ita, wadda kuma ta ƙara ƙuntata zuciyar Aisha a lokacin da ta ga Khamis zaune akan ‘yar kujera yana ta faman firar kabewa.

Sosai ya kama kanshi, saboda bai taɓa taya Aisha aiki ba, ya san kuma wannan sai ya shiga lissafin abin faɗi a wurinta. Maryam kuwa daɗi ta ji da ta iske yana taya ta aiki, ko ba komai Aishar za ta gane ita ta musamman ce a wurin Khamis.

“Shanyayyen banza.”

Aisha ta faɗa a ranta tare da yi mashi mugun kallo. Ɗaukar kofi ta yi ba tare da ta tanka ma Maryam ba ta juya za ta fice daga kitchen ɗin, saboda tunda ta hana Haneefa kwana ɗakin Maryam suke ‘yar gaba-gaba.

“Madam muna da baƙi fa, su A Umar ne, don haka ki zo mu shirya musu girki.”

Khamis ya faɗa yana dariyar tsokana.

Ta san hada neman magana a cikin zancensa, don haka ne ta ce, “Allah ya kawo su lafiya.”

Sannan ta fice.

Taɓe baki Maryam ta yi, sannan murya ƙasa-ƙasa ta ce,

“A ƙras can dai.”

Khamis ya ce,

“Me kika ce?”

Duk da kuwa ya ji, cewa ta yi,

“Ban ce komai ba.”

Tana ‘yar dariya.

“Uhm.”

kaɗai ya ce yana ‘yar dariyar shi ma.

Sai da suka ci ƙarfin aikin sannan Khamis ya fito. Kiran A Umar ya yi a waya ya ce,

“Mun ji ku shiru fa.”

Rabbatar mishi ya yi da zuwa ƙarfe ɗaya In Sha Allahu za su iso.

Banɗaki ya faɗa ya yi wanka, yana fitowa ya shirya sannan ya nufi school ɗin su Haneef ɗauko su, saboda sha biyu da rabi suke tashi.

A hanya yake faɗa musu cewar su Anty Aisha za su zo, Haneefa na murna ta ɗan leƙo da kanta saboda a baya take ta ce,

“Daddy tare za mu tafi Maraɗi da su ko?”

“A’a sai an yi hutu zan kai ku har da Haneef tunda bai taɓa zuwa ba.”

Murna Haneef ɗin ya riƙa yi ya ce, “Na gode Daddy.”

Dariya Khamis ya yi tare da dubansa, daga bisani ya maida hankalinsa ga tuƙin da yake yi.

Da misalin ƙarfe ɗaya A Umar da matarsa Aisha suka iso, da murna Maryam da yaran suka tarbe su, saboda Khamis ya ba ta labarin kirkinsu. A falo suka zauna suka yi ma juna sannu. Gaishe da A Umar da ke kan three seater shi da Khamis Maryam ta yi, da fara’a ya amsa ya kuma ɗora da,

“Ya amarci?”

Dariya kawai ta yi sannan ta juya ga Aisha da ke zaune gefen ta.

“Ina yini”

Da fara’a Aisha ta ce,

“Lafiya lau Amarya.”

Haneef da Haneefa ne suka kawo musu gaisuwa. Aisha da ba ta ga mamansu ba ta ce,

“Ina Mammy?

Maryam ce ta bata amsa,

“Tana ciki, ƙila ba ta ji shigowarku ba.”

Khamis ne da kansa ya je kiran Aisha, daga bakin ƙofa ya tsaya tare da faɗin,

“Toh ga baƙi nan, ki rufa mana asiri ki saki jiki, kada ki ba su abin faɗi su tafi da shi.”

Saboda tsaf za ta kama shan ƙamshi har a gane da wani abu, kamar yadda ta riƙa yi lokacin da wasu abokansa suka zo.

Bai tsaya jin gungunin da take ba ya juyo ya dawo falon, bai kai ga zama ba ita ma ta fito, in da ta riƙa kamo fara’a tana aje ta a fuskarta, ita kuma fara’ar na ƙoƙarin ƙwacewa saboda ba abin da ke ranta ke nan ba. Sosai ramar da ta yi ta ɗarsa ayar tambaya a zukatan Aisha da A Umar, musamman da suka ga Maryam da Khamis ɓul-ɓul.Take zuciya ta riƙa hasaso musu Khamis ba ya adalci a tsakanin matansa.

“Haba takwaras, kin bar ma Amarya ni ko?”

Aisha ta faɗa lokacin da Aishar ta ƙaraso inda suke, zama ta yi a hannun kujera sannan ta nemi afuwar rashin fitowarta duk da ta ji shigowar su.

Gaisuwar yaushe gamo ta yi ma A Umar, ta ce,

“Niger dai ta ƙwace mana ku.”

Ya ce,

“Wallahi fa Umman Haneef.”

Juyawa ga Aisha ta yi ta ce, “Ƙawas, na ɗauka kin yi nauyi fa?” Dariya su duka suka yi har da Maryam. Hirar yaushe gamo suka dasa, daga bisani Aisha ta gabatar musu da uwar tsarabar da suka kawo musu. Sosai suka yi murna, musamman Haneef da Haneefa saboda tsarabarsu ta daban ce.

Kiran sallar Azuhur ɗin da ake ne ya sa su miƙewa, Masallaci Khamis da A Umar suka tafi.

Inda Aisha ta shiga ɗakin Maryam domin gabatar da Sallar a can. Sosai ɗinkin Aisha na doguwar rigar atamfa ya birge Maryam, saboda tana son ɗinkin ‘yan Niger. “Ni kam ɗinkinki ya mini kyau.”

Ta faɗa lokacin da Aisha ta fito daga banɗaki.

Dariya ta yi ta ce,

“Ko kina so idan mun koma na aiko miki da shi?”

Kai Maryam ta girgiza tana dariya. “A’a wallahi, ya burge ni ne kawai na yi magana, sai dai zan ba ki kayana ki tafi da su, duk lokacin da za ku dawo sai a taho mani da shi.”

“Okay to, ai kuwa za ki sha ɗinki wallahi, saboda garinmu ba daga baya ba.”

Aisha ta faɗa, cikin ranta kuma tana jin son Maryam a ranta saboda fara’ar ta, uwa uba kuma ga tsafta don ɗakin ba abin da yake fitarwa sai ƙamshi mai nutsar da zuciya.

Babbar darduma Maryam ta shimfiɗa musu, kusan tare suka kabbara sallar.Bayan sun idar ne suka dasa hira, inda Aisha take faɗa mata suna da ‘yan uwa a Katsina, da Maryam ta tambaye ta unguwar da’ yan uwansu Aishar suke, sai ta ga ai unguwarsu ɗaya har ta san mutanen ma. Hirar Katsina suka yi sosai, daga bisani suka fito falo.

Abinci Maryam ta kai ma Khamis da A Umar tare da yaran a dining. Nasu kuma su uku ta kawo musu a falo. Sosai suka yaba da girkinta wanda Khamis ya san za a rina.

Daga can kan Dining A Umar ya ce, “Amarya na naɗa ki sarauniyar ‘yan iya girki.”

Aisha kuma da zoɓo ya tafi da ita saboda yaron cikin da take ɗauke da shi ta ce,

“Ai nima na bata wannan sarauta, wannan zoɓon sai kin faɗa min yadda kika yi shi saboda ya min daɗi.”

Dariya su duka suka yi har da Aisha, duk da ba ta so hakan ba.

A falon suka dasa sabuwar hira, sosai Aisha ta saki jiki aka riƙa hirar da ita, sai dai ba ta cika sa baki idan Khamis da Maryam na magana ba, amma su da ta fara sai sun saka baki. Ana kiran Sallar La’asar mazan suka tafi Masallaci.

Aisha kuma ta ce,

“Yanzu kuma ɗakin uwargida zan yi sallah, hakan ya yi ko?”

Dariya suka yi. Ɗakin Aisha suka nufa. Maryam da Haneefa kuma suka nufi ɗaki. Tarin tambayoyi ne a bakin Aisha, waɗanda take son yi ma takwararta akan muguwar ramar da ta yi.

Hannunta riƙe da haɓa ta dubi Aisha,

“Ni kwa Aisha hala da naman jikinki ake miyar gidan nan, kin ga kuwa yadda kika rame tare da yin wani irin baƙi?”

Mai neman kuka ne aka jefe shi da Kashin awaki, Aisha ta daɗe tana fatan zuwan wanda za ta juye ma damuwar da ta daɗe tana dakon ta, saboda Khamis ya hana ta fita, ƙawayenta da ‘yan uwanta kuma sun ce ba dalilin da zai sa su riƙa zarya gidanta yanzu tunda an mata amarya. Damuwar kuma ta yi girman da ba za ta iya faɗa wa mahaifiyarta ba saboda kunya.

“Aisha halin ɗa namiji daidai yake da halittar hankaka. Idan mace na ita kaɗai to zai juyo mata da farin gabansa, da zaran ya ƙara aure zai karkata farin ga amarya, ita kuma uwargida ya juya mata baƙin bayansa mai muni.”

Ko da hausar Aisha ta sha banban da ta ‘yan Nigeria, amma ta fahimci azancin ƙawarta Aisha.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce,

“Aisha ai namiji damisa ne, ba a sabo da shi, sai dai ban ga dalilin da za ki addabi kanki da damuwa har ki rame haka ba.”

“To ƙawata, an raba ni da mijina yaya ba zan rame ba, kin san wulaƙancin da Abban Haneef ya yi mini kuwa? Nuna kasawa ta akan shimfiɗa fa ya yi, wanda a can baya bai taɓa yi ba.”

Duk inda gaskiya take Aisha ba ta tsoron faɗinta, don haka ta ce,

“Toh kin kasa ɗin ne shi ya sa ya faɗi haka.”

Kamar Aisha za ta yi kuka ta ce, “Haba takwara, ni ɗin ce na kasa?” Saboda sun san halin juna a harkar kayan mata.

Dafa kafaɗarta ta yi ta ce,

“Bari in yi sallah sai mu yi magana.”

Alwala suka yi tare da gabatar da sallah.

Basu tashi akan dardumar ba Aisha ta ɗora da faɗin,

“Ƙawata da ciwo ace mijinki ya faɗa miki kasawarki, amma bai kamata ki yi fushi ba, saboda don yana son ki gyara ne ya faɗa miki.”

Sosai maganar Aisha ta tattaro da hankalin Maman Haneef wuri ɗaya.

“Ko?”

Ta tambaya.

“Ƙwarai kuwa, jajircewa ya kamata ki yi wurin gyara kanki, har sai da kanshi ya ba ki lambar yabo akan gyaran. Kuma hakan zai ƙara mishi son ki saboda kin nuna ya isa ya yi miki gyara, idan kuwa kika ƙi gyarawa kika kama fushi, to ba zai sake yi miki gyara ba duk girman gazawarki kuwa, sai dai kuma zai canza miki ta yadda ba za ki sake jin daɗin zama da shi ba.”

Sosai ta nuna mata mamakinta akan wasu matan, da zaran namiji ya ce basu iya ba sai su ɓata rai, musamman idan yana da sabuwar Amarya, sai su riƙa cewa daga yin aure ya fara wulaƙanta ni, sun manta sai abu biyu sun haɗu ne ake gane banbancin kowanne, don haka ƙaimi ya kama su ƙara wurin gyara ba fushi ba, don kaɗan za a kuskure sai amarya ta fi su matsayi. Kamar yadda Aisha ta tabbatar da Maryam ta fi ta matsayi a wurin Khamis, mafarin da damuwarta ke daɗuwa a kowane lokaci kenan.

Hanyar da za ta dawo da matsayinta Aisha ta ci gaba da faɗa mata. Ta ce,

“Ki watsar da duk wasu makaman yaƙi ki ba mijinki kulawa, daga yau kada ki sake rufe mishi ƙofa, idan ya so ma ke ki nemi shirin da kanki tunda durƙusa ma wada ba gajiyawa ba ne. Sannan kada ki ba amarya ƙofar raina ki, don tana lura ba ki da matsayi a wurin miji to za ta samu hanyar raina ki, da ta ga kuwa miji na martaba ki, to kin fi ƙarfin raini a wurinta.”

Karatu mai yawan gaske ta ba Aisha, wanda har ta ji ta huce daga fushin da take yi, ɗaura ɗamarar gwagwarmaya da Maryam ta yi a wurin ba Khamis kulawar da ta dace.

Godiya ta yi ma Aisha ta ce, “Na gode da fidda ni daga duhun da kika yi, yanzu kayan mata irin naku na Niger za ki bani.”

Dariya Aisha ta yi, ta kuma ɗora da ba ta sirrikan samun kan miji. Daga ƙarshe kuma ta ce,

“Kuma ki ji tsoron Allah, ko da wasa kada ki yi abin da za ki cutar da amarya ko da ita ta cutar da ke.”

********

A can ƙofar gida ma magana ce ke cin A Umar a rai, ya so ya binne ta amma ya kasa.

Duban Khamis ya yi tare da faɗin, “Kai mugu! Me kuke ci kai da Amarya wanda ba ku ba Uwargida, anya kana adalci a tsakanin su kuwa?”

Dariya Khamis ya ɓaɓɓake da ita, duk da ya ɗan ji sosuwa a ransa “Me fa muke ci wanda ba mu ba ta, kawai ta ɗauko ma kanta baƙin kishi ne.”

“Kishi da kuma zafin da kake ɗora mata ko, Allah kuwa Khamis ka ji tsoron Allah, Aisha dai ba ta da damuwa.”

Jinjina kai Khamis ya yi ya ce, “Sanin da ka yi mata, yanzu kam ta canza, magana kaɗan sai wulaƙanci.”

Bai taɓa faɗa ma A Umar damuwar da ta shafi iyalansa ba, amma ya zama dole yau ya faɗa mishi ko don ya wanke kansa daga zargi. Sosai ya labarta mishi halin da Aisha ta tsuro wanda har a lokacin bai iya cewa ga inda ta koyo shi.

A Umar ya ce,

“Allah ya kyauta, shi ya sa nake tsoron ƙara aure wallahi.” Shawara ya ba Khamis irin wadda mahaifiyarsa ta bashi, daga ƙarshe ya nuna mishi ya ba ta haƙuri akan duk wani kuskure da ta ce ya mata madamar ya san ya yi, hakan zai sa su zauna lafiya, godiya Khamis ya yi mishi sannan suka shiga gidan.

Sai gab da Magarib su Aisha suka fara shirin tafiya, inda suka tafi suna kewar juna, saboda zuwansu ba ƙaramin farinciki ya samar ma mutanen gidan ba. A daren ne kuma Khamis zai koma ɗakin Aisha, sai dai zullumi ya hana shi tafiya, sai ma ya yi kwanciyarsa a kan cinyar Maryam suna ta hira.

“Wai sai yaushe za ka tafi ɗakin Uwargida ne?”

Idanun Maryam a kan agogo a lokacin da Ƙarfe taran dare ta buga ta faɗi haka.

“Sai na sha fura tukunna.”

Saboda al’adarsa ce shan furar dare, wani lokaci ko abincin dare ma bai ci sai ita.

Knocking ƙofar suka ji ana yi, cike da mamaki Khamis ya tambaya, “Waye?”

Muryar Haneefa suka ji ta ce,

“Ni ce, Mommy ta ce a nan zan kwana.”

Kallon juna suka yi, kowa da abin da ya taso mishi a zuciya, Khamis dai murna ce fal a ransa wadda har ta fito fili, saboda ko shakka babu hakan na nufin Aisha na buƙatarsa. Maryam kuwa Kishi ne ya turnuƙe ta, wato sun shirya ko kuma an zuge ta, take ta tuna aikin Aisha ne.

Zumbur Khamis ya yi ya buɗe ƙofar, Haneefa na shigowa Maryam ta ƙara haɗe fuska saboda kayan bacci ne a jikinta. “Koma ki ce na ce ba za ki kwanar mini a ɗaki ba.”

Kallon ta Khamis ya yi,

“A’a.”

A fusace ta ce,

“Wallahi ba za ta kwanar mini a ɗaki ba, sati nawa uwarta ta ɗauke ta, sai yau da jarabarta ta motsa za ta wani turo mini ita, to ba na buƙata.”

Mamakin yadda Maryam ta zage tana tijara ne ya kama shi har ya kasa magana.

Tsaye Haneefa ta yi tare da turo baki, tsawa Maryam ta daka mata a karon farko tunda ta zo gidan, “Na ce ki tafi ɗakin Uwarki ki kwana.”

Lokaci ɗaya kuma ta nuna mata ƙofa.

Dakatar da Haneefar ya yi lokacin da ta juya tana kuka,

“Dawo ki kwanta Mamana”.

Juyawa ya yi kan Maryam da kishi ke ta tsuma ta ya ce,

“Haka kike da faɗa?”

Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba, ya san Aisha ba ta kyauta ba da ta hana Haneefa kwana a can baya. “Ka da ki biye mata, ki yi haƙuri ta kwanta a nan.”

Ba ta son su fara musu, don haka ne ta haƙura, amma cikin ranta har shi haushinsa take ji saboda ta lura so yake ya je wurin Aisha.

Kan sofa ya kwantar da Haneefa, sannan ya ɗauko furarsa da kansa, miƙa mata ya yi.

“Zuba mini a kofi.”

Karɓa ta yi ta zuba mishi, aikuwa Haneefa ta taso,

“Daddy nima zan sha.”

“Toh bari na rage miki.” Maryam kuwa ji ta riƙa yi kamar ta maƙure Haneefar. Yana gama sha ya dawo gefen Maryam da ke ta haɗe rai ya ce,

“Sorry, ba na son ganin fushi a fuskarki.”

Kwantowa ta yi a jikinsa ta ce,

“Me ya sa ba zan yi fushi ba, ban san me ya sa ƙaddara ta haɗa ni zama kishiya ba, bana son ka yi nisa da ni.”

Lallashin ta ya riƙa yi da maganganu masu tausasa zuciya, daga bisani ya kwantar da ita da Haneefa ya yi musu addu’a.

Kashe fitilar ɗakin ya yi sannan ya fice.

A buɗe ya hangi ƙofar ɗakin Aisha, baki washe ya shiga ɗakinsa ya yi wanka, yana fitowa ya shafa mai gami da turare mai ƙarfi da kuma ƙamshi, sannan ya sanya rigar bacci.

Ɗakin Aisha ya yi tsinke, inda tun a bakin ƙofa ya ji ƙamshi na dakar masa hanci. Da Sallama ya shiga, inda ya hange ta zaune a kan sofa cikin shigar bacci mai ɗaukar hankali. A komai na sa ba ɓata lokaci, don haka farinciki fal a ransa ya ƙarasa gabanta tare da durƙusawa a kan guiyawunsa.

Ita kuwa so da kewar mijinta ce ta taso mata, kallon mun yi kewa suka ci gaba da yi wa juna, hannayenta Khamis ya ruƙo tare da kai su gefen hancinsa. Ido ya lumshe ya cigaba da shaƙar ƙamshin da ke fitowa a cikinsu.

Buɗe idanun ya yi ya ga ta kasa ɗauke idanunta a kansa,

“Ranki ya daɗe, na san an karɓi tubana.”

Haƙuri ya ba ta ya kuma tabbatar mata da ba zai taɓa wulaƙanta ta ba, saboda ta wuce haka a wurinsa.

“Ba komai mijina, ni ma na fahimci kuskurena, In sha Allahu kuma zan gyara.”

Ya ji daɗin haka, gefenta ya koma da zama tare da rungumo ta, a kunne ya raɗa mata,

“Rigarki ta min kyau, turarenki kuma ya min daɗi.”

Cewa ta yi,

“Mu je a ɗakinka na ba ka kyautar rigar. “

Ya ce,

“Da gaske?”

Ta ce,

“Allah kuwa. “

Dariya suka yi, aikuwa Khamis ya ɗaga ta sama. Ja ma Haneef ƙofar suka yi, bai dire da ita ko ina ba sai a kan gadon ɗakinsa.

A wannan dare Khamis ya yi mamakin Aisha matuƙa, emergency kayan matan da Aishar A Umar ta ba ta sun yi aiki.

Wannan canjin ya san ba yin kanta ba ne, amma duk da haka ya ji daɗi, a kunne ya raɗa mata,

“‘Yar alewar Khamis.”

Hakan kuwa ne ya tabbatar mata da ya gamsu da ita.

Washe gari tunda safe ta faɗa kitchen, breakfast mai rai da lafiya ta yi musu. A wurin zaman breakfast ɗin ne Haneef ya ce, “Mommy jiya na farka fitsari ban gan ki ba.”

Aikuwa Maryam kamar ta haɗiye zuciya, dama ga takaicin Khamis sai dai ya leƙo ya ce mata ta fito amma bai shigo kamar yadda ya saba ba. Magana Aisha ta yi ma Haneef,

“To da ba ka ganni ba sai ka yi yaya?, yaro ka koya ma kanka bacci kai kaɗai ma.”

Khamis ya ce,

“Aikuwa ba, ko kuma ya riƙa tafiya ɗakin Anty.”

Akan idon Maryam da gululun baƙin ciki ya zo ma wuya ya ƙarashe maganar.

Cikin faɗa-faɗa Maryam ta ce,

“A’a bana buƙata, ɗayar ma wurin uwarta za ta koma.”

Baki Aisha ta taɓe, sannan ta yi ‘yar shewa tare da faɗin,

“Ashe ba daɗi.”

Khamis ya lura da rikici suke son tada mishi, don haka ya ce,

“Ah ah!” tare da yi ma tufkar hanci.

A cikin kwanakin aikin Aisha kuwa ba ƙaramar kulawa ta samu a wurin Khamis ba saboda ya samu yadda yake so a wurinta. Hatta girki sai gashi a kitchen suna yi tare. Hakan kuwa ba ƙaramar damuwa ya saka Maryam ba, domin wannan zaryar da yake a ɗakinta ya rage, tambayar kanta ta soma yi.

“Dama yana son matarsa ne? Zantukan da yake mini anya ba romon baka ne ba?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kishiyar Katsina 5Kishiyar Katsina 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×