Skip to content
Part 7 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

A tunani irin na Maryam namiji ba zai iya son mace biyu ko ma fin haka a lokaci ɗaya ba, mafarin ta ke gani kamar dama can Khamis na son Aisha, ita kuma romon baka ne yake mata kawai don ya mori jikinta. Tsaye take a jikin window tana ƙare ma farfajiyar gidan kallo, cikin ranta kuma tana tuna yadda a ɗazu Khamis ya shigo wurinta a gurguje da nufin yi mata sallama, wani irin haushi ne ya ƙara ƙule ta, inda kuma zuciya ta ce mata,

“Mutumin nan fa ya dena sonki, don haka sai kin tashi tsaye.”

Ko zuciya ba ta faɗa mata ta tashi tsaye ba dama tana da niyya, sai dai ta ina za ta fara? Saboda duk wasu dubarun da take da su ta fiddo su waje, amma hakan bai hana Khamis nuna farincikinsa ga ƙoƙarin Aisha ba. Waya ta ɗauka ta shiga WhatsApp domin duba wasu sirrikan mallakar miji da ta ga ana turowa a group ɗinsu na Matan Aure Zallah. Saƙon cousin Sister ɗinta ne ta ga ya shigo, da hanzari ta buɗe ta ga ta rubuta, ‘Ga mu nan a hanyar gidanki, na kira ki ban samu ba.’

Cike da jindaɗi ta yi mata reply da, “Wayyo murna, Allah ya kawo ku lafiya Yaya Hauwa.”

Fasa shiga group ɗin ta yi tare da kashe data. Fitowa ta yi ta zauna kan wani benci a parking space, lokaci ɗaya kuma idanunta na kan gate ɗin gidan tana jiran shigowar su. Ba ta fi minti goma da zama ba kuwa ta ji tsayawar Napep a waje, da hanzari ta miƙe, kafin ta kai bakin gate ɗin har sun shigo. Ya Salam, ka da ka ga murna a wurin Maryam saboda har da Yayarta mai suna Zulaihat, wadda kuma uwa ɗaya uba ɗaya suke da ita aka zo.

Wata irin maƙalƙalewa ta yi musu tare da faɗin,

“Kai Anty Zulaihat, irin wannan bazata haka?”

Yadda take ta murna ne ya ba su dariya, Hauwa’u, wadda suke ma laƙabi da Yaya Haupha ta ce,

“Sai da na ce a faɗa miki za mu zo ta ce a’a.”

Saboda ita Hsupha a nan garin suke, kuma Mamanta Twin Sister ɗin Mamansu Maryam ce.

Anty Zulaihat ta ce,

“Na san halinta fa, muddin ta san da zuwan mu to ko bacci ba za ta yi ba.”

Maryam ta san haka ne, don haka ta dubi kowannen su tana dariya.

Da murnar ganin juna suka ƙarasa cikin falo, inda suka zauna a nan suka gaisa, bayan gaisuwar kuma suka dasa hira suna ta kwasar dariya. Rashin jin motsin Aisha ne ya sa Haupha tambayar Maryam, “Wai ina kishiyarki ne?, Mun kusa rabin awa a nan amma ba ta fito ba.”

Anty Zulaihat da ta tuna wulaƙancin da Aisha ta yi musu ranar walima ta ce,

“‘Yar banzar ba.”

Haupha na dariya ta ce,

“Da wofi ma wallahi, ai ban taɓa ganin jaka kamar wannan ba.” duk murya ƙasa-ƙasa suke maganar saboda Maryam ta musu alama da Aisha na nan.

Tashi Maryam ta yi ta ce,

“Bari na yi mata magana.”

Kwance ta samu Aisha tana ta shirgar bacci, knocking ƙofar ɗakin ta yi da ɗan ƙarfi.

Cike da magagin bacci Aisha ta tashi tare da tambayar ta,

“Ya aka yi?”

Kamar Maryam za ta shaƙaro ta ta ce,

“Yayyena ne suka zo za ku gaisa.”

Kamar Aisha ba za ta yi magana ba, daga bisani ta ce,

“To gani nan.”

Juyowa Maryam ta yi tare da faɗa musu bacci ta iske tana yi, Haupha ta ce,

“An gaishe da kasa, ƙarfe sha ɗaya amma mai miji da ‘ya’ya na ƙumshe a ɗaki tana bacci.”

Jin motsin fitowar Aishar ne ya sa su canza hirar. Aisha kuwa faɗuwar gaba ce ta riske ta lokacin da ta ga Anty Zulaihat, saboda kaɗan ta rage su zagi juna a ranar walima. Haupha kuwa dama ta san ta saboda class mate ɗinta ce, ita ma ɗin ba sosai suke shiri ba ko a makaranta, Khamis na auren Maryam kuma gaba ta ƙullu a tsakaninsu. Ƙaƙaro murmushi ta yi ta zauna suka gaisa tare da tambayar Anty Zulaihat mutanen Katsina. Sosai Anty Zulaihat ta danne tsanar da take mata ta ce, “Duk suna Lahiya.”

Haupha ma maganar wata class mate ɗinsu da ta rasu ta yi mata, cike da jimami Aisha ta ce, “Wallahi ai an yi rashin AJ.” Haupha ta ce,

“Ba ƙarami ba, Allah dai ya jiƙan ta da rahama.”

Baki suka haɗe da faɗin,

“Amin.”

Tashi Aisha ta yi ta shiga kitchen, cikin ranta kuma ta fara zargin ko wani abu suka kawo ma Maryam na asiri, saboda Zuzee ta taɓa ce mata,

“Kina nan za ki ga danginta na zarya, kuma Allah kaɗai ya san me za su ƙullo su kawo mata.”

Basar da tunanin ta yi saboda ta san ba zai barta ta zauna lafiya ba.

Su Zulaihat kuwa ɗakin Maryam suka koma, tun kafin su zauna Haupha ta dubi Maryam ta ce, “Wallahi Maryam aure ya karɓe ki, dududu wata biyu amma kin cika kin batse.”

Anty Zulaihat da itama tun a falo take yaba kyawun da Maryam ta yi a ranta ta ce,

“Ke dai bari Haupha, ƙila kuma an samu babban rabo ne.”

Irin wannan azancin Maryam har ta fara sabawa da shi, dariya ta yi sannan ta ce,

“Wane babban rabo Anty Zulaihat? Ai sai na gama cin amarci tukunna.”

Sosai ta basu dariya. Zama suka yi a ƙasan carpet sannan Haupha ta ce,

“Kina da kishiyar ne za ki tsaya cin amarci ko? To ai sai ki tsaya uwargida ta cika gida da ‘ya’ya, daga ƙarshe kuma ta zo tana miki gori.”

Wurin da ke ma Maryam ƙaiƙayi ne Haupha ta sosa mata, cewa ta yi,

“Gori kuma har na nawa?”

Labarin yadda Aisha ta hana Haneefa kwana a ɗakinta ta ba su, wanda kuma har yanzu ba ta daina jin zafin sa ba.

Baki Haupha ta taɓe ta ce,

“Kishi ne ke ɗawainiya da ita, don haka ki dage ki zuba naki ‘ya’yan ke ma.”

Anty Zulaihat ta karɓe da,

“Wallahi kuwa dai.”

Tambayar ta suka yi yadda zamanta yake da Khamis, wanda idan har za ta buɗe baki ta yi magana akan zamanta da shi, to ba ta san wani abu ba face alkhairi a kansa, saboda ga kwanciyar hankalin da take samu a wurinsa ta fito ƙarara a jikinta, tunda gashi suma sun faɗa. Sai dai kulawar da ta ga yana ba Aisha ce ta fara sace mata gwiwoyi, har take gani kamar romon baka ne yake yi mata.

Ce musu ta yi,

“Gaskiya ba ni da matsala da mijina, sosai yake ji da ni, sai dai damuwata ita ce yadda yake son matarshi.”

Dariya suka ɓaɓɓake da ita, Haupha ta ce,

“Toh ya Hausarki, kin ɗauka bai son matarsa ne ya auro ki?”

Maryam ta ce,

“To Yaya Haupha ba ki ga fa yadda yake faɗa min ba.”

Anty Zulaihat da ke dariya ciki-ciki ta ce,

“Namijin ne za ki yarda da kalaman shi? To kafin ya faɗa miki uwargidansa ya fara faɗamawa, kuma gashi ya mata kishiya da ke, don haka ka da kalmominsa su ruɗe ki har ki manta da ƙalubalen da ke gabanki na kishiya, domin waccan mai kama da ƙarangiyar ba za ta bari ki zauna lafiya ba.”

Jikin Maryam ne ya yi sanyi ta ce, “Toh kenan duk maganganun da yake faɗa mini ƙarya ne.”

Haupha ta ce,

“A’a ba mu ce ba, kawai dai ki ƙara ƙaimi wurin ba mijinki kulawa, ta yadda ko da ƙarya yake faɗa miki, to wata rana zai faɗa miki gaskiya.”

Hanyoyin da za ta zama tauraruwa a wurin Khamis suka ci gaba da ɗora ta, dama gwana ce ita tama, sai ta haɗa da nata ta riƙe.

Lemu da dambun nama ta kawo musu. Suna gama ci suka dasa yi mata faɗa a kan ‘yan kurakuran da suka gani a tare da ita, tunda dama ɗan adam ajizi ne, duk yadda ya kai ga ƙoƙari wata rana sai an ga gazawarsa. Anty Zulaihat ce ta dubi hannayen Maryam da ƙafafunta ta ce,

“Yanzu don Allah ji hannayenki ba wani lalle, baki san idan uwargidansa na ƙunshi ba sai ya fi jin daɗin kallon hannunta akan naki?”

Duba Maryam ta kai ga yatsunta, wanda ba komai a jikinsu sai kufan lalle ga akaifun. Haupha ta ce,

“Hala rabon ki da ƙunshi tun na biki?”

Kai kawai Maryam ta ɗaga saboda jikinta ya fara yin sanyi.

Anty Zulaihat ta ce,

“Kuma a haka kike cewa Uwargida za ta gane kurenta, to kina ruwa wallahi, da ƙunshi kaɗai sai uwargida ta mallake mijinta, ke kuma abarki da yara suna taya ki kwana.”

Maryam ta ɗauka mallakar miji wasa ne, sai gashi cikin ɗan lokaci ta gane akwai aiki a gabanta, burinta kawai shi ne ta san hanyar da soyayyarta za ta mamaye zuciyar Khamis, ta yadda ko yana tare da Aisha zai riƙa tuna ta.

“Don Allah to ku faɗa mini ya zan gyara kaina, sai nake ganin yanzu kamar ban iya komai ba wallahi.” Kamar Maryam za ta yi kuka ta yi wannan maganar.

Anty Zulaihat ta ce,

“Maryam duk abin da za mu faɗa miki kin san shi, don idonki ya fi namu buɗewa akan rayuwar aure, sai dai ki dage kawai, kuma ki kula da tsaftar jikinki da muhallinki, ka da ki bari ya ga datti a duk inda zai sa idonsa, banɗakinki da nashi ko basu yi dauɗa ba a wanke kullum, ki riƙa kular mishi da ɗakinsa, girki kuma dama tuni kin ciri tuta sai dai mu ce ki ƙara ƙaimi shi ma.”

Ambaton kula da ɗakin Khamis ne ya sa Maryam tuhumar kanta, don ba ta taɓa ɗaukar tsintsinya ta share mishi ɗakinsa ba.

“Toh ai shi ne ya fi son mu zauna a ɗakina.”

wani sashe na zuciyarta ya wanke ta daga zargin kanta.

Littafin da Haupha ta miƙo mata ne ya sa ta dawo da hankalinta gare su, karɓa ta yi a lokacin da Hauphar ta ce,

“Ki duba waɗannan litattafan, za su taimake ki wurin inganta rayuwar aurenki.”

Murna fal a ran Maryam ta ce, “Ai kuwa na gode Yaya Haupha.” sannan ta duba litattafan tana karanta sunayensu, ɗaya ‘Sirrin Mijinki a Tafin Hannunki’ ɗayan kuma sunansa ‘Habawa! Ni Kaɗai Na San Sirrina, Waɗanda duk Malam Yahaya Ishaq (Arriyadh) ne ya rubuta.

Dariya Maryam ta yi ta ce “Wannan sunayen haka, aikuwa zan yi ta ɓoyon sirrina.”

Haupha da ta san wahalar da ta sha wurin neman su a kasuwa don sun ɓace ta ce,

“Ki ma yi sakaci da su. In faɗa miki yanzu babu su a kasuwa, wannan ma da ƙyar na same su.”

Godiya Maryam ta yi ma ƴan’uwanta bisa ga hanyar da suka ɗora ta. Hirar dangi suka dasa, nan Maryam ta ji hidindimun da aka yi a family ɗinsu na KT, wanda da tana gida duk da ita za a yi. Yunwa ce ta fara taso musu, Zulaihat da ta sauke wata doguwar hamma ta ce,

“Ke wai nan gidan ba a girki ne? Mun fara jin yunwa fa.”

Haupha ta ce,

“Wallahi fa, gara ana yi ana sakawa a bakin salati.”

Dariya su duka suka yi, tashi Maryam ta yi ta ce,

“Bari in duba ko waccan ta gama abinci.”

Sai dai abin mamaki har ƙarfe biyu saura Aisha ba ta gama girki ba.

Zulaihat ta ce,

“Lallai akwai damuwa, kema haka kike kai wa ba ki gama girki ba halan?”

Maryam ta ce,

“Allah ya sauwaƙe, ai ni sai dai girkina ya jira ba dai a jira shi ba.” Suka ce,

“To da kyau.”

A tare.

Ƙarar shigowar Khamis suka ji, fita Maryam ta yi inda suka haɗu a falo ta shaida mishi su Zulaihat sun zo. Cike da Murnar zuwansu ya biyo Maryam suka shigo ɗakin.

Da fara’a ya ce,

“Aunties ne yau a gidanmu, ko da yake ma mun yi fushi ko Sweety, rabonsu da nan tun ranar walima fa”

Idanunsa a kan Maryam ya ƙarashe maganar. Dariya su duka suka yi. Haupha ta ce,

“Bari muka yi ku gama cin amarci.”

Kallon Maryam ya sake yi sannan ya ce,

“Ai mu ba ranar da za mu gama cin amarci ko?”

Kasa bashi amsa Maryam ta yi sai dai ta ci gaba da dariya.

Gaisawa suka yi, sannan ya fita daga ɗakin. Daga nan kitchen ya nufa wurin Aisha ya ce mata,

“Kin ga matsalar rashin gama girki da wuri, sai a yi baƙi a bar su da hamma.”

Sosai maganarsa ta hasala ta, sai dai gudun ta faɗa mishi baƙa ne ya sa ta yi shiru.

Sai kusan biyu da rabi sannan ta gama girkin.

Maryam ce ta ɗauko nasu ita da danginta. Tuwon shinkafa ne miyar taushe, Haupha ce ta ɗan lasa miyar ta ce,

“Bari mu ji ta iya girki?”.

Zulaihat ta ce,

“Don Allah Haupha ki raga ma waccan matar.”

Dariya Haupha ta yi,

“Ai wallahi ba rangwame a tsakaninmu da ita tunda ta wulaƙanta mu ranar walima.” Zulaihat na dariya ta ce,

“To ki yi ƙasa-ƙasa da murya ka da mijinta ya ji mu sha kunya.”

Sosai suka ci tuwon suna ta santi, Maryam ta ce musu,

“Ai ba laifi ta iya girki.”

Haupha ta ce,

“Gaskiya kam mun shaida haka.”

Da yamma liƙis ne suka haɗa kayansu da nufin tafiya. Khamis na hira shi da Aisha a falo suka fito. Yana ganin su cikin shirin tafiya ya ce,

“Kai Aunties ba dai tafiya ba?” Haupha ta ce,

“Aikuwa sai gida.”

Tambayar Zulaihat ya yi yaushe za ta koma Katsina, ta ce,

“Sai gobe In Sha Allahu.”

Gaba ɗaya Maryam ta manta da Aisha da ke hakimce a kan kujera tana shan ƙamshi saboda tana tare da miji. Ɗan shagwaɓe ma Khamis ta yi ta ce,

“In ce mun kusa zuwa Katsinar mu ma ko?”

Dariya ya yi sannan ya ce,

“Sai kin shekara tukunna.”

ta ce,

“Kaaaam.”

Cikin muryar shagwaɓa, dariya su duka suka yi in banda Aisha da take ta kallon wayarta.

Khamis ne ya ce,

“To bari na ƙarasa da ku.”

Nuna mishi suka yi ya bari, amma ya ce atabau.

Aisha kuwa kamar ta ce bai zuwa, sai dai ba dama, dariyar yaƙe ta yi musu lokacin da suka yi mata bankwana tare da ficewa daga falon, a parking space suka tsaya suna ta tsigar Aishar. Khamis kuwa ɗakinsa ya koma da nufin ɗaukar key ɗin motarsa. Kira ya ƙwala ma Aisha lokacin da ya duba inda ya aje key ɗin amma bai gani ba. Zuciyarsa cike da takaicin canza ma key ɗin wuri ya dube ta lokacin data shigo.

“Ina key na da ke kan gado?” hannunsa na nuni da saman gadon da tun baccin safe ba a gyara shi ba ya ƙarashe maganar.

“Toh ni dai tun safe rabona da ɗakinnan, ka ga ba ni na canza mishi wuri ba.”

“To sai ki taya ni nema.”

Ya faɗa tare da buɗe lokokikin da ke gefen gadon. Sosai suka ci nema amma basu ganshi ba. Da Aisha ta gaji sai ce mishi ta yi,

“Kai ma to dole ne sai ka kai su, ka barsu su shiga Napep mana.”

Ko kusa maganarta ba ta ba shi haushi ba, sai dai rashin gyaran ɗakin da ba ta yi ba ne ya hasala shi inda ya ce,

“Idan ‘yan uwanki ne za ki faɗi haka?”

“Ni ai ‘yan uwana ba su jiran lift saboda duk suna da abin hawansu.”

Ganin makullin a ƙasan gado ya hana shi yi mata magana, sai dai ya ce,

“Hmm.”

Kawai sannan ya fice daga ɗakin.

Ta lura a ɗan fusace yake, bayansa ta biyo tana magana, amma ya yi gaba kamar bai ji me take cewa ba.

Yana ficewa daga falon ta koma wurin window tana hangen su Maryam. Khamis na isa kuma ta ga ya yi musu magana, kan ka ce me sun ɓaɓɓake da dariya.

Ba wannan ne ya fi ba ta haushi ba, fitowar Khamis daga mota lokacin da Maryam ta yi mishi magana ne ya ƙule ta.

Ba ta ji me suke cewa ba, sai dai ta ga Maryam na diddira ƙafa alamar shagwaɓa. Kafaɗunta Khamis ya riƙe tare da yi mata magana, duk a kan idonta Maryam ta yi ɗan tsalle tare da sumbatar sa a kumci. dariya ta ga ya yi sannan juya ya shige mota.

Idan ran Aisha ya yi dubu to ya ɓaci.

“Munafukar banza.”

Ta faɗa lokacin da Maryam ɗin ta juyo, tashi ta yi ta koma ɗakinta, cikin ranta kuma tana faɗin,

‘Idan akwai mugun gani to shi ne mace ta ga mijinta da wata ko da matarsa ce.’

******

Maryam kuwa ɗakinta ta nufa, litattafan da Haupha ta ba ta ne ta ci gaba da dubawa, take kuwa ta samu sirri mai sauƙin haɗawa, wanda za ta tsuma Khamis idan ya dawo ɗakinta gobe.

******

Abin da Aisha ta gani ɗazu har yanzu yana ci mata rai, da daddare Khamis na zaune a ɗakinta sai ya ga ba wata walwala a tare da ita.Tambayar ta ya yi, “Ranki ya daɗe lafiya dai ko?”

Ba ta da hujjar da za ta ce ba ta jin daɗin ganin shi da Maryam ba tunda matarsa ce, sai dai ta lalubo maganar ɗazu ta ce,

“Ni wallahi ban ji daɗin maganar dazu ba.”

Sake tambayar ta ya yi,

“Wace magana ce?”

Ta ce,

“Akan kai dangin Maryam mana, ban ji daɗi da ka sako dangina ba.”

Shi kam baccin ta taƙalo maganar nan da ba zai sake tunawa da ita ba, saboda inda ya yi ta nan ya bar ta. Haƙuri kawai ya ba ta aka wuce wurin saboda ba ya son dogon zance.

******

Washegari ne Maryam za ta karɓi aiki, don haka tana gama gyaran ɗakinta ta fito. Kai tsaye ɗakin Khamis ta nufa domin share shi, saboda a yau nan take muradin kwana.

Kallo ta ƙare ma ɗakin. Ba laifi a tsaftace yake, sai dai da za a ƙara gyara shi zai fi haka tsaftatuwa. Ba ta wani ɓata lokaci ba ta yaye zanen gadon saboda yana buƙatar canji, zuciya ce ta ruwaita mata ta ɗage katifar domin ganin tsaftar ƙarƙashin gadon.

“Ikon Allah!”

Ta faɗa saboda ƙura ce da ledoji cunkushe a ƙarƙashin gadon.

Sauko da katifar ta yi ta jingina ta ga bango. Sai da ta toshe hancinta da ɗankwali sannan ta fara sharar wurin, amma duk da haka ƙura sai da ta shigar mata hanci, atishawa ce ta ƙwace mata, wadda ta yi sanadiyyar leƙowar Aisha ɗakin.

Tabarmar kunya ce ta shiga naɗewa da hauka ta hanyar tuhumar Maryam ta shigo mata ɗakin miji a ranar aikinta. Wani irin mugun kallo Maryam ta yi mata sannan ta ce,

“Au ke kaɗai ke da mijin da za ki tuhume ni don na shigo?”

“Me ya sa ba ki bari sai ranar aikinki ba, ko wani munafuncin aka zo da shi?”

Saboda zuciya da ba ta da ƙashi ta fara ruwaita mata wani abu ta zo sawa a ɗakin, saboda danginta da suka zo jiya, kuma ma tunda take ai ba ta taɓa jin motsin Maryam a ɗakin ba.

Murmushin takaici Maryam ta yi, don ta gane inda ta dosa, ba ta son biye mata akan wannan batun, sai dai ta ce,

“Kin manta yau ne nake karɓar aiki? Kin ga ya zama dole in fara shirin tarbar mijina ai ko ba haka ba?”

Ba ta tsaya jin baƙaƙen maganganun da Aishar ke cewa ba ta cigaba da aikinta. Tas ta yi ma ɗakin tare da goge duk wata yana dake jikin bangon ɗakin.

Maida katifar ta yi, sannan ta ɗauki zanen gadon ta faɗa banɗaki, wanke shi ta yi, sannan ta wanke banɗakin shima. Fitowa ta yi waje da nufin shanya zanen gadon. Aisha na ɗakinta ta ji motsin Maryam a bayan ɗakinta, sai da Maryam ɗin ta wuce sannan ta leƙa ta window, tana ganin zanen gado a kan igiya ta taɓe baki tare da faɗin,

“Za ki bari ne madam.”

Saboda a ganin ta duk wani iya yi da Maryam ke yi na amarci ne, tana haihuwa za ta bari, kamar yadda itama ta bari.

Maryam kuwa ɗakinta ta koma ta ɗauko wani pink ɗin zanen gado mai kyau ta shimfiɗa a gadon Khamis. Sosai ɗakin ya yi wani irin kyau gami da fitar da ƙamshi mai sanyaya zuciya, jawo ƙofar ta yi sannan ta koma ɗakinta.

Jan lalle ta ƙunsa wa yatsunta.Tana gamawa ta shiga kimtsa kanta don ta ɗaukar ma ranta Khamis sai ya ji abin da bai taɓa ji ba a tare da ita. Da yamma Khamis na dawowa ya ga ɗakinsa ya sauya kama mai kyau.

“Aikin waye wannan?”

Ya tambayi kansa, saboda ya san Maryam ba shiga take ɗakinsa ba, Aisha kuma rabon da ta yi ma ɗakin irin wannan gyaran har ya mance.

Shiru ya yi da bakinsa, ya ce,

“‘Yar gwadal ce za ta nuna.”

Dare na yi ya nufi ɗakin Maryam, ƙamshin da ɗakinta ke fitarwa ne ya tabbatar mishi da ita ce ta gyara ɗakin, saboda iri ɗaya ne da wanda ɗakinsa ke fitarwa.

Rungumo ta ya yi ta baya a lokacin da ta gama shirin bacci ya ce,

“Kin yi kyau Princess.”

Saboda rigar baccin da ta sanya ta musamman ce.

Murmushi ta yi ta ce,

“Na gode babyna.”

Tare da riƙe hannayensa da ke zagaye da ita.

Kansa ya cusa a wuyanta ya ce, “Yau ɗakin Khamis ya tabbatar da ya yi sabon aure, irin wannan gyara haka?”

Murmushi kawai ta yi, cikin ranta tana jin daɗin ta yi abin da Aisha ba ta yi ba.

Juyowa da ita ya yi har suna jin numfashin jun, ce mashi ta yi,

“Ai kula da ɗakinka wajibi ne a kaina, don haka ka daina maganar ma.”

Kasa magana ya yi saboda komai nata tsuma shi yake yi.

Hannunta ya kama zai nufi gado, ƙin tafiya ta yi ta ce,

“Yau a ɗakinka zamu kwana.”

A har kullum yana ganin kama hannun mace su tafi ɗakinsa ɓata lokaci ne, musamman idan yana cikin wani shauƙi na musamman, saɓar Maryam ya yi kamar jaririya. Ƙuri suka yi ma juna na wani ɗan lokaci, kowane yana jin ƙaunar ɗan’uwansa na daɗuwa.

Jiki a mace ya nufi ɗakinsa. Kallon zanen gadon da ke ɗauke da tambarin heart ya yi, sannan murya ƙasa-ƙasa ya ce,

“Ni kam yaushe ne Valentine day?”

Amsa ta bashi da, “February fourteen ne, amma ni da kai kullum Valentine day ɗinmu ne.”

Ya ce,

“Da gaske?”

Ta ce,

“Allah kuwa.”

Dire ta ya yi a tsakiyar gadon sannan shi ma ya hau.

Zama ya yi a gabanta, tare da ruƙo yatsun hannunta da sai yanzu ya lura da ƙunshin da ke gare su.

“Ma Sha Allah, wannan ƙunshi ya dace da fararen yatsunki Mairo, sosai ya tafi ta ni.”

Zaune ta tashi tare da naɗe ƙafafunta suna fuskantar juna.

Ɗora hannunta ta yi a cikin tafukansa ta ce,

“Wannan ƙunshin duk don kai na yi.”

Cike da son ta ya sumbaci hannayen sannan ya ce,

“Ah ya yi kyau kuwa, to na gode sosai.”

Jin daɗin yabon ne ya ba ta damar cewa,

“Uhm, dama ina son zuwa kitso kuma.”.

Sai da ya dube ta sannan ya cire hular da ke kanta, hakan ne ya yi sanadiyyar bayyanar kwantaccen baƙin gashinta da ta ɗaure da ribbon. Hannunsa ya sa kan gashin ya cigaba da shafawa, cewa ya yi,

“Wannan gashin naki mai kyau da ƙyalli ko ba kitso ai yana da kyau Mairo.”

Murmushi mai sauti ta yi tare da ɗan langaɓe kai.

“Idan kuma aka kitsa shi sai ya fi maka kyau ai.”

Ya ce,

“Koh?”

Ta ce,

“Uhm mana.”

“Toh ki bari sai ranar da ba ke ce da girki ba sai ki je.”

Ta ce,

“To.”

Maganar kitson suka cigaba da yi, ya so ta je gidan da Aisha ke zuwa, amma ta ce a’a, daga ƙarshe suka yanke shawarar zai kai ta gidansu sai su Hafsat su raka ta.

Hira mai daɗi suka cigaba da yi, can wurin ƙarfe goman dare ya ce, “Kin ga ban siyo fura ba, kuma cikina abu mai ruwa-ruwa yake buƙata, ko za ki dafa mini ɗan ruwan zafi?”

Fitowa ta yi ta shiga kitchen, cikin ɗan lokaci ta dafa mishi ruwan bunu wanda ya ji kayan ƙamshi, sannan ta sanya sukari tare da matsa ɗan lemun tsami kaɗan a ciki, saboda ya yi daɗin sha.

Sosai ya ji daɗin ruwan bunun, amma ya ce,

“An ce fa lemun tsami yana da ‘yar illa.”

Ta ce,

“Ai ɗan kaɗan na saka.”

Ya ce,

“Okay.”

Bayan ya gama sha ne suka kwanta, bacci mai cike da soyayya suka yi.

*********

Washe gari da Asuba Khamis ya tafi masallaci, ita ma a nan ɗakinsa ta gabatar da sallarta, tana gawamawa ta cigaba da azkar. Wayarsa da ke kan stool tana caji ce ta ga alamar ta cika, miƙewa ta yi da nufin zare wayar daga jikin socket, sai dai hoton Aisha da yaranta da ta gani a fuskar wayar ne ya faɗar mata da gaba.

‘Khamis ne ya cire nata hoton ya sa na Aisha, ko Aishar ce ta cire nata hoto.’ Tambayar da ke ta kai kawo a zuciyarta kenan, lokaci ɗaya kuma tana jin gabanta na wata irin faɗuwa. Idan kuwa Khamis ne lallai ya fara gajiya da kallon ta, tunda da kanshi ya sanya hotonta a fuskar wayar ya ce ko da bai gidan zai riƙa kallon hoton yana jin daɗi.

Wani sashe na zuciyarta ne ya ce, ‘Ƙila kuma Aishar ce ta cire.’ Hakan ya ba ta damar cire hoton Aisha tare da ɗora wani hotonta mai ɗaukar hankali. Jin motsin Khamis ya sa ta aje wayar bayan ta zare ta daga caji.

Yana shigowa wurin wayarsa ya nufa tare da faɗin,

“Ta cika kenan.”

Hotonta ya gani a kan fuskar wayar, ‘yar guntuwar dariya ya yi ya ce a ranshi,

‘Ikon Allah, wayata ta shiga layin kishi kenan.’

Saboda Aisha ce ta cire hoton Maryam ba shi ba.

A daren da Aisha ta karɓi Khamis ne kuma ta ga sabon zanen gado, sanin na Maryam ne ta ce,

“Babu dalilin da zai sa in kwana a zanen gadon masu mugun abu, kai ko ba mugun abu ba zan yi bacci a zanen gadon kishiya ba.”

Murya ƙasa-ƙasa take maganar tare da yaye zanen gadon.

Khamis na shigowa ɗakin ya ga tana ta wurgi da rigar filon a tsakar ɗaki.

Tambayar ta ya yi,

“Me ya yi da za a cire shi?”

Ta ce,

“Nawa zan saka.”

Sake tambayar ta ya yi,

“To wannan wani abu ya yi?”

Ta ce,

“Ko bai yi komai ba ni ba zan yi bacci bisa zanen gadon kishiya ba.”

Sosai ta bashi dariya, don a ƙufule take maganar.

Tattara zanen gadon ya yi ya ce, “Ai sai ki shimfiɗa naki.”

Hakan kuwa aka yi ta shimfiɗa sabon zanen gado itama.

Khamis na tsokanarta ya ce,

“Ni kuwa Khamis gaba ta kai ni, cikin kwana biyu an gwangwaje ni da sabbin zannuwan gado, ga wasu turarukan ƙamshi da suma ake sanyaya mini zuciya da su.” Saboda ita ma Aisha sai da ta yi ma ɗakin gyara na musamman, duk don ta ga Maryam ta yi.

Harara ta wurga mishi, shi kuwa sai dariya yake tare da rungumo ta ya ce,

“Kuna sa ni Nishaɗi ke da ƙanwarki.”

Ce wa ta yi,

“Ka ce ina sa ka nishaɗi, ita ma idan ka je ɗakinta sai ka faɗa mata ita kaɗai.”

“To Sholy, ina sonki uwar ‘ya’yana.”

Ta ji daɗin wannan magana, sosai ta samu nutsuwar da sai da suka faranta ran juna a wannan lokacin. Da shirin zuwa kitso Maryam ta kwana, don haka tana gama breakfast ta fara shiri saboda Khamis ne zai kai ta, shi kuma ƙarfe taran safe yake fita.

Gama shirinta ke da wuya ta fito falo tana jiran sa. Khamis ɗin ne da Aisha suka fito daga ɗakinsa, yana hangen Maryam da Hijabi ya dubi Aisha ya ce,

“Na manta ban faɗa miki Maryam za ta je ta kitso ba.”

Bata lura da Maryam ɗin ba ta ce, “To ni mene ne nawa a cikin zuwanta kitso?”

Saboda ba abin da ke ruruwa a ranta sai tsanar Maryam, wadda kuma ba ta rasa nasaba da samun lambobin yabon da Maryam take yi a wurin Khamis.

Khamis ya ce,

“Wai in fita haƙƙi ne.”

Ganin Maryam ɗin da ta yi a yanzu ya sa ta faɗin,

“Uhm, wai haƙƙi.”

Maryam kuwa tana ganin sun ƙaraso tsakiyar falon ta fara shan ƙamshi, saboda akan kunnenta duk maganganun da suka yi.

Cike da jin daɗin shiryawar Maryam da wuri Khamis ya dube ta,

“Ke fa sai dai ki jira, amma ba a jiran ki.”

Ɗan ɗauke kai ta yi tare da faɗin, “Toh mene ne amfanin nawa?”

Ya ce,

“Babu.”

Ga ce,

“Toh ka gani.”

Karɓar mukullin motar ta yi ta ce, “Kawo na riƙe maka.”

Wayarsa ya haɗa mata da ita, ba tare da ta kalli inda Aisha take ba ta tafi tana ta juya makullin motar.

Duban Aisha da ta bi ta da mugun kallo ya yi,

“Wai Wannan ɗage-ɗagen kan da kuke ma juna na lafiya ne?”

Sosai ta ji kamar habaici ne suka yada mata, don haka ta yi magana a hasale,

“Da ni da ita waye babba?”

Ya ce,

“Ke.”

Ta ce,

“To tunda ba tsoron ta nake ba, babu dalilin da zai sa na fara yi mata magana.”

Haɗe rai ya yi tare da faɗin,

“Au sai kana tsoron mutum ne za ka fara yi mishi magana? To ku bari wallahi, don bana so.”

Faɗa sosai ya yi mata saboda bai son rabuwar kansu, kuma idan ba tufka ya yi ma hancin ba har ‘ya’yansu.

Baki ta turo ta ce,

“To na ji, ita ma sai ka faɗa mata haka idan kana son kawo gyaran.” ya ce,

“Ai ba sai kin sani ba.”

Fita daga falon yayi ya bar ta nan tana ta gunguni. Mazaunin direba ya samu Maryam ta hakimce, tana hango shi ta ƙara yalwata fara’ar da ke fuskarta, cikin ranta kuma tana shirin tsokanarsa. Sai dai ganin fuskarsa ba annuri ko kaɗan lokacin da ya buɗe murfin motar ne ya sanyaya mata jiki.

“Matsa ki bani wuri.”

Ya faɗa cikin fushi.

Faɗuwa gabanta ya yi don ba ta taɓa ganin fushinsa ba, laluben laifin da ta yi mishi ta fara yi a ranta, sai dai har suka fice daga gidan ba ta samu laifin da ta san ta yi mishi ba.

“Maryam.”

Ya kira sunanta cikin kaushin murya, a ɗan tsorace ta amsa, “Na’am.”

Tare da dubansa.

Haɗa ido suka yi, nan ta ƙara ganin kalar fushinsa kwance a fuskarsa, a hankali ta ɗauke idonta tare kasa kunne don jin me zai ce.

“Me ya sa ba kya yi ma Aisha magana, so ki ke ku kawo mini rabuwar kai a cikin iyalina?”

Sosai kalmar ‘So ki ke’ da ya ce ta taɓa mata zuciya, saboda ba ta fatan yin abin da zai zarge ta. Kamar za ta yi kuka ta ce,

“Ita ma ɗin ai ba ta yi mini magana.”

Ya ce,

“Ke ai sai ki yi mata, har a wurin Allah kin fita.”

Cikin ranta ta ce,

‘Ai kuwa da ta mutu wallahi.”

A zahiri kuma ta ɗan turo baki.

Faɗa ita ma ya yi mata cikin kaushin murya, ya nuna mata duk wanda ya kawo mishi rabuwar kai a cikin gida ba zai ji daɗinsa ba ko kaɗan. Sosai jikinta ya yi sanyi da faɗan da yake mata, haƙuri ta shiga ba shi don ta san ba su kyauta mishi ba idan suka ce za su yi gaba, saboda yana iya ƙoƙarinsa wurin kyautata musu.

Ya ji daɗin hakurin da ta bashi, sai ya ji ta ƙara burge shi a ransa.

Shiru ce ya ratsa a tsakaninsu, inda kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

Bai sake dubanta ba sai da suka zo a ƙofar gidansu, gani ya yi duk ta sha jinin jikinta, dariya ya yi aransa gami da faɗin,

‘Ashe tana tsoron faɗa.’

A zahiri kuma cewa ya yi,

“Sauka daga nan, idan kin gama kitson ki kira ni zan zo na ɗauke ki.”

Jiki a mace ta fito daga motar, “Allah ya kiyaye.”

Ra ce mishi sannan ta rufe murfin motar. Sai da ya ga shigewarta gidan sannan ya ja motarsa ya tafi.

*****

Sa’adda ta shiga gidan ba kowa a falon sai Salima, da murna ta maƙalƙale tana faɗin,

“Oyoyo ga Anty Maryam.”

Hakan ya ba sauran yaran damar fitowa da gudu suna ta murna da ganinta.

“Ina Umma?”

Ta tambaye su lokacin da ta zauna akan kujera, tana rufe baki sai ga Umma ita da Hafsat da kuma Ruƙayya sun fito. Hafsat da Ruƙayya ma sun yi murnar zuwanta don za su samu ƙafar yawo, Hafsat ce ta ce mata,

“Har kun iso.”

Maryam ta ce,

“Wallahi kuwa.”

Gwiwa biyu a ƙasa Maryam ta gaida Umma, cike da fara’a Umma ta amsa tare ta tambayar ta su Aisha.

Maryam ta ce,

“Duk suna nan lafiya.”

Tsarabar sweet ɗin da ta yi ma yara ta ba su, daga bisani Hafsat da Ruƙayya suka raka ta gidan kitson. Da zuwansu ta ga mai kitson na ƙunshi, aikuwa ta ba da kuɗi aka siyo mata baƙin lalle, ana gama kitson a ka ƙunsa mata.

Sosai ƙunshin ya ƙawata farar ƙafarta, Ruƙayya na santin ƙafar ta ce,

“Anty Maryam ki riƙa saka safa kada a cinye miki ƙafa.”

Saboda duk wanda ke gidan kitson sai da ya yaba kyawun ƙunshin.

Sallamar mai ƙunshin suka yi sannan suka fito, a hanya ne suka ga wata mai suyar dankali, tsammaninsu har da awara, sai dai suna tambaya aka ce ba awara, saboda waken suya ya yi tsada.

Hafsat ta ce,

“Wallahi don dai ban iya awara ba da na yi.”

Maryam ta ce,

“Na iya, ki zo sai mu yi.”

Da wasa suke maganar awara, sai gashi ta zama gaske.

Ɗubu ɗaya Maryam ta ba Ruƙyayya kuɗin wake, suka kuma fidda ranar da za su je can a yi awarar.

Da isarsu kuma suka taras da Khamis har ya zo ɗaukar ta. Abinci kaɗai ta ci, sannan suka tafi.

Sai da suka zo wani titi da ba mutane ne ya tsaida motar. duban shi ta yi ta ga yana mata wani shu’umin kallo mai nuna alamun ya huce daga fushin da yake yi da ita ɗazu.

Tambayar sa ta yi,

“Lafiya?”

Sai da ya kamo hannunta sannan ya ce,

“Ƙunshi zan gani.”

“Ma Sha Allah.”

Ya furta a fili, lokaci ɗaya kuma ya sumbaci hannayen ya ce,

“Ya yi kyau Mrs. Khamis.”

Murmushi ta yi ta ce,

“Na gode.”

Kallon saman kanta ya yi ya ce,. “Saura kitson.”

Ba ta wani ɓata lokaci ba ta ɗage hijabin daga gaba. Sosai ƙananun kitson suka burge shi, shafar kan ya yi daga gaba har baya sannan ya ce,

“Lallai kam kitso ya fi ƙawata wannan gashin mai kyau da sheƙi.”

A gida ma haka ya riƙa santin wannan kitso da ƙunshi, Aisha na ganin haka kuwa ta tambeye shi ita ma za ta je a yi mata.

Da yake ranar girkinta ne sai ya ce,

“Ki bari sai ranar da ba ke ce ke da girki ba.”

Tunawa ta yi da can baya take ita kaɗai ai duk sa’adda ta so ta ke zuwa kitso, na me kuma yanzu zai tsiro da sai ba ranar girkinta ba.

Ce mashi ta yi,

“Ikon Allah, can baya da nake ni kaɗai fa?”

Ya ce,

“Yanzu da baya ba ɗaya ba ne.”

Ta ce,

“Kai Abban Haneef, don Allah da na gama girkin ba abinda zan yi fa, don Allah ba sai in tafi ba.”

Ido ya ɗan zaro,

“Wa ya ce ba abin da za ki yi?”

Ta ce,

“To me zan yi?”

Ya ce,

“Tausa za ki yi mini idan na dawo.”

Dariya mai cike da takaici ce ta yi, matsa mishi ta yi, aikuwa ya kafe, kan ka ce me ta fusata, da ya lura sai ya bar mata gidan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kishiyar Katsina 6Kishiyar Katsina 8 >>

1 thought on “Kishiyar Katsina 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×