Skip to content
Part 10 of 48 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Yau cike da farin ciki Muktar ya fito daga makarantar sakamakon albashin da aka biya da kuma extra bonus na extra lesson da suka fara, kai tsaye motar da zata kai shi Mariri ya hau tun da ya fara aikin nan yake son zuwa gidan ƙanwar sa bai samu yaje ba sabida tsoron kar ya yi kuɗin mota gobe kuɗi ya masa short.

Shinkafa kwano uku ya siya tare da wake kwano guda sai mai kwalba guda da magin ɗari biyu ya nufi layin nasu fuskar sa ɗauke da nushaɗi.

“Ga kawu ga Kawu” yaron ɗan kimanin shekaru shida ya rugo yana faɗa murmushi Muktar ya yi tare da aje kedar hannun sa ya ɗaga yaron ba tare da la’akari da dattin da ke jikin yaron ba”Noor ashe zaka ganeni?”

Nana ce ganin an ɗaga ɗan uwan nata ta rugo da gudu tumbur ba riga bare wando tana fadin “nima” dire Noor Muktar ya yi tare da ɗala mata duka kafin ya daka mata tsawa “jeki gida ta sa miki wando da riga” yarin yar ta tsanyara ƙara tare da rugawa da gudu zuwa gida shi kuma ya kama hannun Noor suka nufi gidan.

Kafin su ƙarasa Rashida ya hanga ta fito ko ɗan kwali babu kanta sanye da ɗaurin ƙirji tana faɗin “muje uban waye ya dake ki” ƙarasawa ya yi ta yi turus lah yaya hararar ta ya yi ta koma ciki tana faɗin “walllahi na ɗauka wani azzalumin ne ya dake ta”

“Ni ne nan azzalumin” tsit ta yi ta shige ɗaki takaici ne ya kama Muktar lokacin da ya yi karo da fo ɗauke da kashi wanda da alamu tun safe aka yi dan har ya fara bushewa, ya mutsa fuska ya yi tare da juyawa da zummar zubda miyau sai dai tarin kwanukan da ƙuda kebi yasa shi daurewa ya hadiye abin sa kafin ya shiga ɗakin, ƙoƙarin tattare kaya take dan sama masa inda zai zauna, girgiza kai kawai ya yi ya zauna tare da aje ledar hannunsa.

“Yanzu fisabilillahi Rashida kina kyautawa kenan jibi gidan ki, ke kanki jibeki waye zai ce ke ƙanwa ta ce ba yaya ta ba?”

Ya tsina fuska ta yi ” yaya dan Allah ya zanyi da rayuwa ta ga yunwa ga ciki walllahi bani da lafiya shi kuma bazai gyara ba sai randa na samu ɗan sauƙi in gyara” numfashi ya furzar “anma yanzu shi fo ɗin can ko Noor kika sa ai zai iya zubdawa”

“Wallahi yaya ban san da shi ba, in banda yanzu da Nana ta shigo ban fito tsakar gidan ba, ya aikin ta tambaya a ƙoƙarin ta son kawar da mitar rashin gyaran gidan da yake”

“Aiki Alhamdulillah, yanzu ma daga can nake nace bari in zo mu gaisa ga wannan” ya tura mata ledar gaban sa.

Da murna ta hau buɗewa kai anma ka kyauta Allah ya buɗa, ya ɗaga arziki bari kaga in ɓoye wannan rabi rabi zan nuna masa shima in yace mun kun haɗu in bai ganka ba sai dai ya dinga gani a faranci dan idon sa idon abincin nan zai kwashe ya siyar”

Muktar bai ce komai ba ya miƙe ” ungo wannan ya miƙo mata dubu ɗaya kya dinga siyen ice ni bari in je in yamma ta yi liss tsadar abin hawa” har soro ta rako shi tana ta godiya ya yi titi.

A bakin titin suka Haɗu da Nura mijin Rashida “lah Yaya barka da yamma ya faɗa lokacin da ya ɗan rissina da kai” hannu Muktar ya miƙa masa suka gaisa.

“Har ka fito kenan nima yanzu na fito daga gidan naje sayo gari tun safe Bamu samu mun ci wani abin kirki ba” ya faɗa lokacin da yake ɗan ɗaga ledar hannun sa yana nunawa Muktar.

“Ayya Allah ya cigaba da dafa mana” ya faɗa tare da zaro ɗari biyar ya miƙawa Nuran, ya amsa yana faman zuba godiya tamkar ya bashi millions.

Cike da gajiya ya koma Unguwar su kai tsaye wurin Malam audu mai lemo ya wuce fuskar sa ɗauke da annuri, ” Lemo za’a ban ya miƙa dubu guda”

Mai lemon ya amsa ya “anya ina da ɗari tara kuwa?”

Murmushi Muktar ya yi “ai yau na du zan siya anma a haɗamun da ayaba”

“Kai Alhamdulillah, yau da raina naga addu’a ta ta amsu” mai lemon ya faɗa tare da miƙowa Muktar lemon ya amsa yana murmushi.

Kasancewar yanma ce yasa shi tarar da ƙannen sa biyu na wanke wanke, Inna zaune tana ferayar kabewa Juwairiyya na tsifa tausayin mahaifiyar tasa da ƴan uwan nasa ya cika shi shikam zaiso ko sau guda ne wataran ya zo ya tarar da su suna hutawa sai dai in har suna son rufawa junansu asiri dole su aikatu.

Sannu da zuwa suka masa ya zauna gefen Inna, “wash Allah na gaji yau ɗinnan” inna ce ta dube shi “gashi nan kuwa ka yi zuru zuru, yanzu nake cewa ko lafiya yau ka kai dare”

“Walllahi nima nagani, da aka tashi ne na biya gidan Rashida duk tana gaishe ku”

Washe baki Inna ta yi jin ya ambaci ƴar uwar tasa ” kai amma ka kyauta walllahi, Allah ya bar zumunci”

“Amin” ya ce tare da miƙa mata lemon da ya siyo ga wannan ba yawa an mana albashi sannan ya bata dubu uku ya miƙawa kannen nasa dubu guda guda, suka hau murna da godiya.

Daki ya shige tare da faɗawa katifar sa Juwairiyya ta shigo masa da abincin sa “Allah dai yasa baki sa mun gashi ciki ba?”

Murmushi ta yi “kai yaya wane gashi abu a rife” bai ce komai ba ya buɗe ta yi waje.

Washe gari sai da ya zauna ya kasa kuɗin sa yadda zasu ishe shi sannan ya wuce shagon Bala ya biya shi bashin sa kafin ya wuce makaranta.

*****

Maganar da sukai jiya da Bilkisu lokacin da take cewa ita bata son hutun nan na mid semester da za’a fara yau Bilkisun ke bata shawarar mai zai hana ta dinga Bin Abba sch ko bata shiga aji tunda tsakiyar term ne ta dinga ganin yara tana jin ɗebewar kewa wannan ya sa yau ta tashi da wuri ta nufi farfajiya dan jiran Abba ya fito.

Tana tsaye a veranda lokaci lokaci suna hira da Baba mai gadi Abba ya fito yana gyara Babbar riga turus ya tsaya ” Hajiya Hansatu ba hutu kuke bane naga kin tashi da wuri haka?”

Ya mutsa fuska ta yi “Abba Hajiya Hafsa nake”

“Ok koma dai mene?, Baki bani amsar tambayar da na yi ba”

Dariya ta yi ” munyi hutu shine nake son binka reading at home is boring,” furzar da iska ya yi “rikici dai Hansatu muje to”

“That’s my Abba, leƙawa ta yi falon cikin ɗaga murya ta ce Mum na bi Abba sch”

Sai da ta fara zuwa ta gaida tsoffin malaman ta da ke makarantar sannan ta koma can ƙarƙashin wata bishiya dake nesa kaɗan filin wasan ƴan makarantar ta zauna.

Tana zaune aka fito break masu wasa suka zo suka hau lilikan da ke makale a filin da take iya hanga nesa kaɗan da ita, murmushi take lokacin lokaci dan tana iya fahimtar wasan da yaran suke.

Kamar daga sama ta tsumayi muryar sa yana faɗin “towo yau an rigani kenan?” ɗagowa ta yi sukai nasarar haɗa idanu ya sakar mata murmushi itama murmushin ta yi, kafin ta ce “ina kwana, Mai aka rigaka?”

Kujerar da take kai ya nuna mata “lafiya kalau, nan wuri na ne kullum nake zama akai during break”

Murmushi ta yi “a’a da kujerar nan na magana da zata faɗa ma kujera ta ce kullum kanta nake zama tun muna student”

“Ah yanzu ai kin bar makarantar bama kujerar ba, yanzu tawa ce” dariya tasa “aikam dai bana tashi a gurin nan, ba dai laifi zamu iya sharing shima dan ina ganin girman ka” ta faɗa tare da ɗan matsawa gefe.

Dariya ya yi “toh ya zanyi tunda an mallakemun guri, wai da gaske kina ganin mutunci na”

“Ga sheda na matsama ka zauna a kujera ta” dariya yayi ba tare da ya ce komai ba ya hau makin ɗin littattafan da ya zo da su in da ta maida hankalin ta kan yaran da ke wasa…

<< Ko Da So 9Ko Da So 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×