Skip to content
Part 11 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Tsaye take gaban notice board din kamar yadda sauran dalibai suke tsaye da littafan su da biro suna kwafar draft timetable ɗin da aka kafe dazu. Ita kaɗai tazo makaranta a cikin kawayenta yau shiyasa ma take tsayen ita kaɗai.

Hannunta ta kai kan layin course din farko tana karanta da code ɗin cike da damuwa.

“Eh electricity ne. Dashi zamu fara.” wani da ke bayan ta ya faɗa, A nan take taji kafafuwanta sunyi mata nauyi. Ita fa bata shiryawa exam ɗinnan ba. A bazata tazo mata kuma ace course din da bata iya ba dashi za’a fara. Test dinma da akayi kwafa tayi kuma malamin bai ma kawo musu sunga nawa suka ci ba.

Jiki a sanyaye ta bar tsakiyar jama’ar da suke ta faman tofa ra’ayinsu. Idanunta suka ciko da hawayen fargaba. Nan da nan ta kara sauri ta bar wurin. Female rest room kawai ta nufa. Tana shigo ta fara hawaye. Sai da suka gama zuba sannan ta wanke fuskarta ta fito. Driver dinta ta kira kawai sannan ta shiga masallaci ta kwanta tana jiransa. Tunaninta bai wuce yadda zatayi ta tsallake jarabawar nan ba.

Tana kwance kiran dreba ya shigo. Jiki ba kwari ta tashi ta tafi in da yayi fakin.

Ko da suka isa gida babu wanda ta tsaya gaisarwa kamar yadda ta saba. Ji take abubuwan sun cunkushe mata a lokaci guda kuma bata san ta inda zata fara ba.

Dakinta ta fara shiga tayi jifa da jakarta sannan ta fada bandaki inda tayi wanka, tana wankan tana hawaye har sai da taji saukin abun da ya tsaya mata a rai sannan tayi alwala ta fito.

Sallar la’asar ta fara yi sannan ta kwanta. Kugin da cikinta ya fara ne yasa ta tuna bata ci abinci ba. Ba’a son ranta ba ta nufi kitchen. Tayi sa’a babu kowa balle a sakata ciwon bakin magana. Tana bude flask taga dambun shinkafa, nan take mood dinta ya fara chanjawa ta diba ta koma daki.

A hankali take cin abinci wanda duk wanda ya hangota cewa zaiyi wasa take da abincin. Sai da ta gama ta sha ruwa sannan ta dauki wayarta ta kira Bilkisu.

Sai da tayi ringing din farko Bilkisu bata dauka ba. Duk da ba son yin magana take ba haka ta sake kiran wayar. Sai da ta kira kusan sau uku sannan kaninta ya daga.

“Bata da lafiya, kuma ta kulle kanta a daki.” Gaban Hafsah ya fadi, ta rasa abun cewa.

“Hello?” Ta fada don ya maimaita abunda yace ta tabbatar taji daidai.

“Yaya Bilkin ta rufe dakinta kuma taqi magana dani.” Duk da haka Hafsah bata fahimci abunda dan shekara bakwai dinnan yake cewa ba. Mikewa tayi ta nemi abaya ta saka cike da tashin hankali da tunanin me ya sami aminiyarta ta. Banda wayarta babu abunda ta dauka ta fito. Jin shiru sosai har yanzu yasa ta fahimci Mumy bata nan yau. Watakila fitar yamma tayi. Gate kawai ta nufa ba tare da tabi takan dreba ba taga me gadi yana zaune.

“Hajiya Karama sannu da fitowa.” Fuskarta babu fara’a kamar yadda ta saba tace,

“Don Allah ara min dari biyu in na dawo zan dauko maka. Bana son komawa ciki ne, sauri nake.”

Ba musu ya zura hannunsa a aljihu ya mika mata ita kuma tayi gaba tana godiya. A ransa yake tunanin ko me ya sameta. Ko me yake damunta. Yarinyar tana da mutunci sosai da girmama manya. Ba ruwanta da bambancin da ke tsakanin su na nauyin aljihu. Sosai yake jin dadin aiki a gidan sabanin gidan da ya baro inda yaran gidan suke masa kallon raini da rashin sanin darajar dan Adam.

“Allah yasa lafiya.” Bai ma san sanda ya fada ba a fili saboda abun ya dame shi.

Ko da Hafsah ta isa titi kafar ta tayi budu budu saboda saurin da take yi.

Me adaidaita sahu ta tsayar ta shiga sannan ta fada mishi unguwar da zai kai ta. Sauri yake amma gani take kamar ya rage saurin adaidaitar.

“Malam dan Allah ka kara sauri.” Ta fada tana kallon gefen titi. A ranta take tuno wacece Bilki. Ta san duk abunda zai hana Bilkisu zuwa makaranta ba karamin abu bane domin ita din jaruma ce kuma mutum ce mai kwazo da yarda da kanta. Ko kadan bata da wani weakness da Hafsah zata iya cewa gashi. Komai nata a tsare yake, komai nata a lissafe take yin sa. Komai Bilki ta kan kalle shi da zuciya me kyau. Abunda zai karya ta ba karamin abu bane.

Duk da ta kasance a hannun kishiyar maman ta tashi wadda take tamkar uwa a gareta, Bilkisun bata taba kallon cewa rayuwarta nada wata tawaya ba saboda rashin uwa. She was always positive about her life. Komai zafin abunda ya same ta alhamdulillah zaka ji ta fara fada. Ko mitaar dan Adam yau da gobe Hafsah bata jin Bilkisu tana yi.

Tayi nisa a tunani ta tsinci muryar me adaidaita sahun yana tambayarta ina zaiyi. Hanyar ta kalla taga har an wuce kwanar tana ta faman tunani.

“Mu koma baya dan Allah. Yi hakuri. Kwanar ita ce kafin wannan.” Tayi sa’a ba masifaffe bane, ba musu ya koma bayan. Suna shiga tace yayi ta sauka tana mika masa kudin. Ko chanjin da yake nufin bata bata tsaya karba ba.

Ko da ta isa gate din gidan nasu turawa kawai tayi ta shiga. Directly part din yaran gidan ta nufa. Bakinta dauke da sallama ta shiga falon amma babu kowa. Corridor din falon tabo inda ta samu yayyin Bilkin suna zaune suna hira kamar babu wani abu da ya faru.

“Ya Iftee ina wuni…” ta gaishe ta. Sai da taja aji sannan ta amsa. “Lafiya. Ta kira ki kenan? Tana sama.” Da haka ba wanda ya kara magana. Akwai rashin jituwa tsakanin Bilkisu da yayyan nata wanda suka hada uba daya. Bilkisun ta taba gaya mata cewa suna jin haushin ta kan cewar baban su yafi kula da lamarin ta.

Yanzu ma abunda take wa kuka haushi suke ji.

Hafsah ta kai minti biyu tana buga kofar amma bata bude ba.

“Bilkisu ki bude min this minute. Wannan wani irin abu ne? In kuma in koma toh?” Ta tambaya tana hararar kofar. Karar mukulli da taji ne ya sanar da ita da Bilkisun zata bude mata.

Tana budewa taja Hafsah ciki ta rufo kofar gami da sake rushewa da kuka.

Rungume ta Hafsah tayi tana jin tausayin Bilkisun. Kuka takeyi da dukka zuciyarta wanda yasa Hafsahn ita ma ta fara tayata. Sai da tayi me isarta sannan sukayi shiru ta goge hawayen, idanta jajir.

“Abba ne. Aure zai min wai. Tariq zai aura min…” Ita kanta Hafsah sandarewa tayi. Bata san waye Tariq din ba amma dai tasan Bilkisun tana da crush duk da sam babu auren a plan dinsu.

Shiru sukayi ba wanda yayi magana.

“Tariq fa ex din Ya Iftee ne. This union is as good as nothing. Kuma wai auren hadi. Abba bai tsaya yaji ta baki na ba fa…”

Ta sake fashewa da kuka. Janyowta kawai Hafsah tayi tana bubbuga bayanta alamar rarrashi in da a ranta take tunanin makomar da kuma dalilan tashin hankalin Bilkisun.

*****
“Na ce ba, Muntari ka cire wani abu a kaiwa Baffan ku.” Inna ta fada tana samun wajen zama kusa da inda yake marking.

Sai da ya bata fuska sannan yace,

“Haba Inna ni fa bani da wani Baffa. Haka kawai sai kiyi ta makala mana mutanen da ba son mu suke ba.”

Kalaman nasa suka bata mata rai saboda sam baya jin fadan da take yi masa shekara da shekaru. “Ahir din ka! Baka da wasu yan uwa sama dasu. Dangin mahiafinka ai sune dangi.”

Rufe littafin yayi sannan ya lumshe idanunsa yana tuno wasu abubuwa da suka faru wanda ba zai taba mantawa ba.

“Inna…”

Ba ta jira yace komai ba ta tare shi da amsa. “Ko dubu biyu ce ka kawo ni zan kai musu. Zumunci ba zai bata dorewa ba in har zaka dinga duba abunda ya faru a baya.”

Shiru kawai yayi saboda ba zai iya musa mata ba. Har zaice sai wani watan toh amma saboda gudun bacin ranta yace toh zai bayar sannan ya dauki littafin ya cigaba da maka wa yana jinjina hazakar daliban makarantar.

*****

Bayan kwana biyu Bilkisu ta ware ta cigaba da harkokinta bayan Hafsahn tayi ta faman zuwa gidan nasu kullum tana bata baki ko dan exam din da take tunkarar su. Yau ce ranar farko da zasu rubuta physics duk da Objectives ce. Suna zaune suna amsa past questions Bilkisun tayi shiru har sai da Hafsah tayi snapping fingers before her face.

Ajiyar zuciya ta yi. “Kin san me? Tariq din ya zo jiya and he seems nice. Ni matsalata bai wuce yadda Umma ta fara min acting ba ita da Ya Iftee. They turned their backs against me bayan they’re my rocks. I bask in their glory.”

“Hakuri zakiyi har su fahimci ba laifin ki bane.”

Bilkisun ta maida kwallar da tazo idonta. “Sun sani. Cewa sukayi haka jinin mu yake ni da mahiafiyata, snatching mazajen mutane muka iya. He was her ex fa for God’s sake.”

Takardar hannunta Hafsah ta ajiye sannan ta kama hannun Bilkisu. “It’s not just about that. Akwai wani dalilin da ya sa suke miki haka kuma shawarata a gareki shine ki zama Billyn da na sani. Grow a thick skin…”

Kafin Bilkisu ta bada amsa wani lecturer yazo wucewa da booklet da answer sheet.

“Innalillahi…” Hafsahn ta furta tana mikewa ta cigaba da duba takardun hannunta. Ita bata yarda ba sai cramming answers take saboda ance su dinne dai ake maimaitawa a hargitse duk shekara.

Har dalibai suka fara shiga halls Hafsah bata nufi kofa bama. “Hafsah drop the papers kar a hana mu shiga.” Bilkisun tayi gaba Hafsah na binta a baya tana ta cramming.

A karshe dai ita ta shiga last aka raba musu papers din. Sai dai me? Wannan karan ko question daya bai dawo daga past questions ba.

Hall din yayi tsit, cikin dalibai kamar Hafsah ya debi ruwa tsabar tashin hankali. Sam Hafsah taki yarda ma question paper din su ce. Watakila mistake akayi hakan yasa ta daga hannunta alamun tana son magana.

“Sir, ina tunanin question din yan level three ne.” Ta fada tana wuri wuri da idanuwa.

Dariya yayi kadan. “Level 100, Electricity and magnetism. Read that again and don’t talk again. In baki da abun rubutawa you can submit.”

Da haka ya sha kunu inda Hafsah ta kurawa paper din ido rai a cinkushe.

<< Ko Da So 10Ko Da So 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×