Skip to content
Part 12 of 53 in the Series Ko Da So by Aisha Kabir


Tunda aka rubuta exam din farko hankalinta bai kwanta ba. Ganin yadda exam din tayi mata ya saka ta hana idonta bacci ta dage da karatun sauran courses din. Sam ta cire wasa da bata lokaci a abubuwa marasa muhimmaci ta maida hankalinta completely kan karatun. Bata son failure a rayuwarta musamman ma ta fannin karatun.

Pencil take fikewa wanda zatayi practicing zanen kifi dashi mummy ta shigo falon.

“Hafsah dai ta bace bat. Wannan bamu san wacece ba.” Mumy din ta fada tana jawo kujerar kusa da Hafsahn ta zauna sannan ta dubi kan table din inda anan Hafsah take wuni.

“Mummy sannu da dawowa.” Haka kawai tace sannan ta cigaba da zanenta.

Kallonta mummyn tayi sannan tayi murmushi. “Allah ya bada sa’a. Daman so nake kije gidan su Hidaya ki karbo min wani lace da na siya.”

“Mummy dan Allah. Exam fa nake. Hidayan ta kawo miki mana.” Ta turo baki sannan ta juya.

Sabanin yadda suka sabayi, mummyn tace, “Toh shikenan Allah ya bada sa’a. Da ace komai na rayuwarki haka kika bashi muhimmanci ai da ba haka ba. Ni na koma daki. Na dafa abinci ma in zaki zuba.”

Yadda Mummy tayi laushi yasa Hafsah taji babu dadi ta kalle ta. “Mummy kinsan zan karbo miki ko?”

Murmushi tayi. “Ba komai. Good luck.” Da haka ta bar wurin.

*****

Yau ma taje makarantar don haka ta yi saurin zuwa kujerarta ta zauna. Tana ta duba takaardun hannunta, fuskarta cike da damuwa fal wadda ta mamaye fuskartata tun ran farko.

A hankali ya tako, hangota da yayi ya saka yaji wani abu da ba zai kira shi da walwala ba. Kawai he felt something.

Ko da ya karaso, Hafsah taso tayi kamar bata ganshi ba don yau ba ta son yin magana amma sai ta kasa.

“Hi.” Tace sannan ta matsa mishi ya zauna. Murmushi yayi ya ajiye flask din hannunsa a tsakanin su sannan ya zauna.

“Hello.” Ya amsa mata sannan ya zauna. Sun jima basu ce komai ba har sai da yaga ba zatayi magana ba sannan yace,

“Bismillah: wainar gero.” Ta dago ta kalle shi da alamun tambaya yayin da shi kuma yake kokarin bude flask din. Nan take kamshin geron ya cika mata hanci taji tana son ci. Sai a sannan ta tuna da rashin jin abincin safe da tayi a ranar.

Amma da yake bata taba ci ba sai kawai ta kalle shi har ya doni kulikuli ya kai bakinsa. Hankalinsa kwance yake taunawa.

“Ban taba ci ba.” Ta amsa shi tana dora indanuwanta akan shi. Duk da tension din karatun da take ciki sai da taji wani abu ya amsa a zuciyarta. Bata san da me zata kwatanta shi ba. Kawai dai in an matsa mata zata ce yana burgeta.

Da mamaki ya kalle ta sannan yayi murmushi wanda bata gani ba saboda dauke kanta da tayi daga kan sa.

“Yau zaki fara. Da dadi.”

Ta kai hannu ta gutsuri kadan sannan ta doni kuli kulin. Sai da ta dan kalli piece din hannunta ta kalla taga baya kallonta sannan ta kai bakinta. Taunar farko, ta gaskata maganar sa sai gashi ba tare da tace komai ba ta kai hannu ta sake dauka. A haka suka cinye ba tare da kowa yace komai ba. Ruwa ya mika mata, ba musu ta karba da murmushinta ta sha. Daidai sannan aka kada kararrawa.

“Thanks. Kuma da dadin sosai.”

Ya murmusa. Wa ya gaya mata daman girkin Innarsa girkin wasa ne. “Inna tace take yi.” Ya fada cike da nuna jin dadin sa a fili.

Ta gyada kai. “Five star.”

Mikewa yayi yana kallon yaran da suke guje gujen komawa class.

“Thanks for lunch.” Ta sake maimaitawa wanda a daidai lokacin Mukhtar ya sake jin wani abu ya shiga zuciyarsa game da Hafsahn. Kalmar dai daya ce, ta burge shi.

Ba tare da yace komai ba ya mata murmushi, ta mayar masa. A daidai wannan lokacin wata alaka ta shiga tsakaninsu. Alakar da babu wanda zai iya mata suna a cikinsu.

Kallon bayansa tayi har ya bace mata da gani sannan ta mayar da hankalinta kan takardun ta tana sake jinjina dadin wainar gero din. Tayi mata dadi kuma zata fadawa mummy don ta koya mata.

*****

Bayan kwana biyu an yi exam fiye da rabi, Hafsah tana zaune tana kallo mummy ta shigo falon. Sannu tayi mata sannan suka cigaba da kallon su. Karan kiran da ya shigo wayar mummy ne ya ratsa shirun da sukayi. Mummy ta dauka tana dariya ita kadai.

“Ke dan Allah? Kai kai kai amma nayi murna wallahi.” Iya abunda Hafsah ta iya jiyowa kenan kafin mummyn ta tashi ta bar falon. Ko kadan bata cigaba da tunanin ba ta cigaba da kallon fim din indiyan da ake haskawa a tashar. Tayi nisa gun kallon sai ga mummyn ta dawo.

“Kin san Hajiya Deenah wadda muke sarar laces a wajen ta da na gaya maki rannan?”

Hafsah ta kalle ta, “Matar nan ta Abuja?”

Mummy ta murmusa. “Dadi na da ke baki da mantuwa. Ita ce tazo Kano in fada miki wallahi. Gobe zata zo mu gaisa. Toh kin san dai bai kamata naji kunya ba. Maza maza ki je drawer ta ki nemo leshin da zaki kai a rage miki…” Hafsah tana jin haka ta juya tana kunkuni.

“Yau dai daya ba zan saurareki ba. Wannan umarni ne.” Mummy ta sha kunu wanda yasa Hafsah tayi saurin mikewa don ita barin wajen ma zatayi kafin mummy ta tuno wani abun ta sake saka ta dole. Har ta taka mummy ta dakatar da ita.

“Sannan ki kira Hidaya tazo. Ko kuma bar shi ma zan kira mamanta. A nan zata kwana. Zaku je shopping ne ku siyo kayan girke girken da za’a mata gobe. A nan zata yi lunch.” Ita dai Hafsah bata tanka ta ba. Sai da mummy ta sake daga murya cike da fada.

“Baki ji ni bane!”

“Naji mummy.” Da sauri ta bar falon tana jin wani haushi yana cika ta. Ita sam bata son kalar rayuwar nan kuma bata san me yasa Abba baya hana mummy ba bayan su kullum a cikin yi musu nasiha yake kan kar su dauki rayuwa da zafi.

Mummy kuwa a take ta kira Farida ta sanar mata da kawarta zata zo daga Abuja. “Mummy ki aro chef din Hajiya Maryam mana ta taya su.” Ta bada shawara wadda ta saka mummyn nishadi. Nan da nan ta ajiye wayar ta kira Hajiya Maryam wata business partner dinta tayi sa’a kuma chef din is available. Bayan nan ta kira gidan su Hidaya sannan ta aika driver a dauko ta.

Account balance dinta ta duba taga bata da matsala ko da kuwa nawa zata kashe ba tare da ta taba jarinta ba. Wannan opportunity ne babba a wajen ta. Ta dade tana son kawance da manyan mata ko dan connections da kuma business. Duk kawayen ta kaman ita suke bab wata babbar hajiya da duniya ta san da ita. Cike da zumudi ta tashi ta tafi dakinta tana binciko kayan da yafi ko wanne tsada a kayanta wanda beifi sau daya ta taba sakawa ba.

Drawer gwal dinta ta bude ta ciro wanda daman saboda irin wannan ranar ta tanade shi.

Ranta fari tas ta fara shirye shirye da goge gogen gidan.

*****

Kamshi ne yake ta faman tashi a kitchen din inda chef Roy ta dage wajen nuna bajintar ta ta iya girki sannan kuma tana nunawa Hafsah da Hidaya wasu dabarun girkin.

“Duk sanda kike bukatar wani dandano na musamman a tattare da girkin ki musamman ma nama, marinate it first. Taste din na daban ne. Ki masa hadi sannan ki diga mai sai ki rufe shi na wasu awanni. The resulting aroma is fantastic.” Ta fada musu tana saka marinated minced meat din a fridge don yafi tsimuwa.

Hafsah ta tabe baki ta ce, “girki akwai wahala wallahi.”

Chef Roy tayi murmushi. “Amma akwai faranta ran jama’a musamman ma masoyan ka. Ai girki yana da tasiri sosai akan mutane. In fact hanya mafi sauki wajen janyo hankalin mutane gareka shine ta hanyar abinci me dadi. My advice? Ki daure ki koya.”

“Gaya mata dai.” Hidaya ta mara mata wadda tasa Hafsah tayi shiru don ta gaskata maganar su. Abinci me dadi yana shiga zuciya yayi abubuwa da dama. Bata manta wainar geron da taci ba, ba ta manta dadinta ba, ba kuma tajin zata taba manta wanda ya bata din.

Da haka suka cigaba da girke girken main dishes sannan suka fara rolling sheets na samosa.

“Zan iya zuwa koyan girki wajen ki?” Hafsah ta tambaya ba tare da ta dago ba.

“Of course, ko yaushe.” Chef ta amsa.

Hidaya ta kurawa Hafsah ido alamun tambaya sai dai ba ta samu damar cewa komai ba mummy ta shigo.

“Dan Allah kuyi sauri. By now ya kamata ace kun fara jera abuncin nan a table. Chef kar ki biye wa yaran nan.”

“Yes ma’am.” Ta russuna sannan mummy ta fice directly zuwa dakinta inda zata shirya. Su kuma suka cigaba da sarrafa snacks din cikin sauri.

*****

“She’s amazing gaskiya.” Hafsah ta fada tana gutsirar samosa tana sake yabawa girkin chef din wadda har ta gama gyara wurin da suka bata ta tafi.

Su Hafsah ma sunyi wanka kenan sunyi kyau sosai sannan suka zauna ciye ciye.

“Ku zo ku gaishe ta. Kuma dan Allah Hafsah kija ajinki.”

“Toh mummy.” Ta amsa don ta gaji da wannan warnings tun jiya. Jikinta ma duk yayi sanyi saboda ta rasa me zatayi don ta burge mummy. Ita she’s not a good actress akan irin abubuwan nan. Da sai yafi ma in mummyn bata nuna tana nan ba.

A hankali suka fito daga dakin Hidaya ta rike mata hannu kamar tana guiding dinta. Sai da suka isa falon, fuskarsu a sake sannan Hidaya ta radawa Hafsah.

“Banda dariya, jin kunya and too much talks.” Saura kiris Hafsahn tayi tsaki.

Cike da nutsuwa suka karasa sannan suka durkusa suka gaida Hajiya Deena.

“Ma sha Allah. Ya kuke?”

Hafsah zata amsa, Hidaya ta rike hannunta a boye sannan ta amsa in a classy way don ita gwana ce.

“Ya sunan ku.”

“Ni Hidaya and ?”

“Hafsah. Sannu da zuwa aunt.” Hafsah ta fada cike da murmushin da yasa kumatun ta ya fara ciwo. A haka ta saci kallon mummy taga fuskarta. And it showed bata kwafsa ba.

“Wannan ita ce Asma, diya ta ce amma bata gani.”

“Ohhh.. I’m so sorry.” Su dukka suka furta a tare suna nuna rashin jin dadinsu a fuskarsu sannan suka kalle ta. A take Hafsah taji tausayin yarinyar ya cika ta har sai da tayi kwalla. Da kyar ta kalle ta again tace. “Hi.”

Suna kallo Hajiya Deena ta kama hannun yarta. “Go with them habibty.” Da haka suka kama hannunta suka fita daga falon jikinsu yayi sanyi sosai. Har suka isa daki ba wanda ya sake magana inda suke ta tunanin ta inda zasu soma yi mata hira.

“Hi, sunana Asma AbdoulJalal. I was born blind. Ban san meye kala ba. And I’m happy.” Hafsah bata san sanda ta rungume ta ba sannan ta runtse nata idanuwan. Duhun da ya mamayeta ya saka ta fara hawaye. She couldn’t imagine life a makance. Bata san ta inda zata soma ba.

“Kowa sai ya dinga jin tausayi na, saboda ban san kalar komai ba. Not even Mamma.” Ta fada sadly amma da murmushi a fuskarta.

Duk sai suka zama bebaye suka kasa magana.

“Amma all the same, the world ia equally beautiful. Komai sai dai nayi imagining. The only thing i am missing is colors. Duhu kawai na sani so komai a duhu nake ganinsa. A duhu nake tunanin sa. Ance I’m beautiful haka ne?”

Da ido suke ta binta tana basu mamaki. Yadda take ta surutu freely. Su kuwa sai faman goge hawayen su suke. Cike da karfin hali Hafsah ta amsa mata.

“Kina da kyau. Ba kadan ba. Kina da mugun kyau. I don’t know how to describe it for you.”

Shiru Asma tayi wanda ya bawa Hafsah daman tashi ta tafi bandaki tana kukan rashin godewa Allah akan dukkan ni’imomin da ya mata. Rashin kula cewa idon ta da ya bar mata ma wata babbar kyauta ce da rahama sa a gareta.

<< Ko Da So 11Ko Da So 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.