Skip to content
Part 14 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Faka motar da Malam Musa ya yi cikin harabar school of hygiene yasa Muktar buɗewa ya fito, ɗan sunkuyowa ya yi bakin tagar “ina zuwa yanzu zan miƙa in fito” murmushi kawai Hafsa ta yi ya yi gaba, yadda zuciyarta ta kasa yadda cewar wannan Makaranta ce ta gaba da secondry yasa ta buɗe motar ta fito, a nutse take tafiya tana bin tsirarin daliban da ke kai kawo, zagaye makarantar ta yi duka makarantar a idanun ta bata fi Faculty ɗin su ba, sai da ta gama yawon ta sannan ta dawo riƙe da alawar madara da ta gani gurin wata ɗaliba ta siya, Hango Muktar tsaye jikin mota yasa ta yin sauri ta karaso.

“Lah har ka dawo, Na bar ku kuna ta jira ko?”

Murmushi ya yi “a’a nima yanzu na fito” ya faɗa tare da matsawa daga jikin ƙofar motar bayan ya buɗe ta shiga shi kuma ya buɗe ƙofar gaba Malam Musa ya ja motar sukai gaba.

Kasancewar zasu sauke Muktar a Dala yasa Malam Musa bi ta cikin gari, ganin an biyo ta kasuwar kurmi ya sa Hafsa tunawa sunyi da Hidaya zasu so kamar ta ce su tsaya sai kuma ta tuna da halin Hidaya in taji ta zo ita kaɗai akwai rikici, adai dai ƴan Kado suka sauke Muktar yana ta faman zuba godiya kafin su wuce.

Hangar Malam da Hafsa ta yi yana alwala lokacin da suka shigo layin yasata faɗaɗa murmushin ta tamkar ta matso kusa da shi.

Cike da fara’a ta ƙarasa inda ya ke alwalar, shima murumushin yake, rissinawa ta yi ta gai da shi kafin ta ce ” yau zuwan nawa a sa’a na yi tunda ns fara tozali da rabin raina”

Dariya yi “assha ashema rabin rai ne abu bai yi daɗi ni da nake son fadar duka” itama dariya tasa a’a inna saka duka ran ina zan kai su Abba?” Karasowar Malam Musa riƙe da Jakar ta yasa ta amsa ta yi gaba tare da barin su suna gaisawa.

Kai tsaye gidan ta nufa, ƙarami ne ba can ba yafi rabin fuloti anma baza’a ce fuloti bane ginin ya yi kyau sosai dai dai misali ginin siminti ne ba shi da gate anma ba zaka kira shi gidan talakawa ba, gidan masu rufun asiri yafi dacewa da shi, da Sallama Hafsa ta shiga lokacin da ta wuce zauren farko, “a’a muryar waye nake ji kamar Muryar Bebilo” Gwaggo da ke zaune kan ƴar ƙaramar kujera ta mata tana wanke wanke ta faɗa” turo baki Hafsa ta yi lokacin da ta shiga riƙe da Jakar ta ” Ni sai in koma, kurum dan mutun ya tsufa sai ya dinga faɗamin sunan tsoffi”

Dariya Gwaggo ta yi ” kajimin ja’irar yarinya Ba sai ki koma ba, ai kinfi ni sanin hanya tunda ta ita kika bi kika shigo”

Malam da ya shigo riƙe da buta ne ya ce “koma kinji Hafsatu na, kyale ta kishi take”

murmushi Hafsa ta yi kamar dama da gaske komawar zata yi kafin ta ce “to ba inda zani tunds dai wanda nazo gunsa yana maraba”

Dariya suka sa dukkan su sannan suka soma tambayarta mutanen gida.

“Duk suna lafiya. Ina kawu Halipha?” Ta tambaya tana shigar da akwatin ta dakin Goggon. Kamshin turaren wuta ya doki hancinta har yasa ta rufe idonta. Son kamshi a jinin kakarta da mamanta yake amma ita bata wani damu ba. Tana yabawa da kamshi in taji sai dai bai dameta har ta saka da kanta ba.

Da akwatin ta a baya ta karasa shiga ɗakin wanda yake matsakaici ne. Gefen wardrobe ta hanga inda zata saka akwatin nata. Kamar ta tuna wani abun ta daga kai ta kalli jerin tukwane da tangaren da suke saman wardrobe din. A kullum burgeta sukeyi saboda babu inda ta taba ganin irinsu banda wajen Goggon. Kallon jeren take yi, girma girma kuma samfuri daban daban yasa ta soma kirga su.

Tana kirgen ne Goggo ta daga labule ta shigo ta tarar da ita. “Bebilo…” ta kira tana katse Hafsah wanda yasa ta buga kafa.

“Oh Allah, Goggo kin katse ni.” Goggon tayi dariya.

“Seti goma ne dani in fada miki domin ni yar gata ce. Daga baya na saida me ros da me bakin les dina. Ke har kumbo gare ni me sha biyu.” Goggon ta fada tana zama a gefen karamin gadon ta da yake kusa da babban gadonta wanda Hafsah take so.

“Ni ba ganewa nake ba fa Goggo. Wannan gadon naki ne dai nake so ki bani na tafi dashi gida kin ki.” Ta fada tana danewa kai gami da kwanciya a kan filon.

Goggon ta murmusa. “Sai randa kika bar mun miji zan baki.”

Hafsah ta tabe baki. “Toh me zanyi da mijin ki duk furfura? Kan shi ma duk sanko. Ni kuwa wanda zan aura in kika ganshi sai kinyi kishi.”

“Bebilo kenan. Allah ya nuna min ranar nan.” Goggon ta tashi ta fita.

Da yake Goggon ta jima da fita, hakan ya bawa Hafsah damar yin tunani akan maganar da sukayi. Wanne irin miji take so? Shin ita zata taba yin aure kuwa? Ba ma wannan ba, ita bata taba soyayya da kowa ba kuma finding her spec was the biggest challenge ever. Sau da dama Hidaya tana hada ta da mutane amma tana rejecting da taga hotunan su saboda sam basuyi mata ba. Ko saurayin Hidayan ma sam inda itace ko kalle bai isheta ba shiyasa ma bata son kalar hirar da ita.

A wannan tunanin ta tuno da Bilkisu wadda hakan yasa ta danna mata kira.

*****

Zaune suke a tsakar gidan. Fili ne fetal an kawata shi da shukoki masu ban sha’awa da dain kallo. Wasu a cikin su suna da fure me kamshi sosai musamman ma da daddare. Daga gefe guda kuma wata yar rumfa ce haddadiya da akayi ta da itaciyar bambu. Idan mutum ya zauna a rumfar zai iya hango kwalliyar gidan nasu. Sau da dama Bilkisu ta kan fito nan ta zauna tayi karatu iska me dadi tana kada ta.

Hakan yasa da aTariq yace zai zo ta gayyace shi nan. A zuwan sa na biyu wanda shine yau ya saka ta tanadi karamin kafet da ta shimfida kasan teburin wurin.

Lemon da ta zuba masa ya dauka ya sha sannan ya ajiye yana hamdala. “Wannan hadin da su Baba sukayi tamkar amsar addu’ata ne. Ko nace Allah ya amsa min addua ta ta hanyar su. Beel, you’re everything i ever wanted in a woman.” Ya furta mata kan shi tsays duk da yana dan hin kunya. Abu na farko da yasa ita ma Bilkisun taji ta daina jin zafin abun game da shi. Duk inda kamala take ya cika ta sannan kuma a waye yake. Wayewa ta ilimi da expressing kan sa.

Kunya ta lullube ta yasa ta rasa abun cewa. Tun zuwan sa na farko yake lullube ta da kalaman da ba yadda zatayi sai yi musu masauki a zuciyarta.

Ya saci kallon ta, kunyar tana burge shi yace, “Alhamdulillah. Ni kam nayi sa’ar auren hadi. Na samu me sona…”

Bilkisu ta dago ta kalle shi, fuskarsa cike da murmushi. “Nace ma haka?” Ta fada da yar murya.

Ya murmusa. “Haka zuciyata take gaya min. Bata yi min karya.”

Jin haka yasa ta rasa abun cewa. A daidai lokacin kiran Hafsah ya shigo wayarta. A zuciyarta har hamdala tayi saboda escape din da ta samu.

“Heyy…” ta fada tana kara wayar a kunnenta.

“Nayi fushi wallahi tunda lafiya kike sai anjima.” Hafsah ta fada.

Bilkisun ta kalli Tariq taga hankalinsa ma ba kanta yake ba sai ta sake yin kasa da murya. “Haba besty na. He is here. Ki bari zan kira ki…”

“Iyyeh??? Lallai ma! Ke video call zan kira kuma wallahi ki mika masa wayar tun kafin…”

Bilkisu ta katse ta. “Naji.” A haka sukayi switching sannan ta kalli Tariq wanda shima ya kalle ta da murmushi.

Ganin murmushin Bilkisu yasa Hafsah ta saki baki sannan tace. “Sheep in love! Kalle ki dan Allah.”

Tariq yayi dariya sannan yace, “wacece ta katse mana lokacin mu?”

Mamaki ya kama Hafsah. Wannan wani irin abu ne? Shin dama love at first sight da ake cewa da gaske ne? Don wallahi tana jin muryar Bilkisu taji ta chanja. Ganin fuskarta cike da farin cikin da take kokarin boyewa ya sake bata mamaki. Shi love din haka yake daman? Lokaci guda sai ya kama mutum ya maida shi wani abun daban.

A wani tunanin kuma take mamakin yadda duk kusancin su da Bilkisu saboda shigowar wani cikin rayuwarta ya saka har suka dauki kwana biyu basu yi magana ba and Bilkisun was genuinely happy with that. It shocked Hafsah to bones.

Bata fuska tayi don ta nuna how unhappy she was with him sannan tace. “Billy ki bashi wayar.” Fuskarsa tana bayyana a gaban screen din Hafsah ta hade girar ta.

“And who are you? Kasan wacece ita a gare ni kuwa? Cikin kwana biyu kake nema ka maye gurbi na?” Ta tambaya da dukkan gaskiyarta wadda yasa shi dariya.

“Tariq Aliyu. You must be Hafsah. Yanda ta fada haka kike and I’m so thrilled to let you know i have snatched your friend. Na sace ta, tawa ce dukka.”

Hafsah ta sha kunu sannan ta daga muryarta yadda Bilkisu zata jiyo. “Billy ki karbi wayar. Ina da case da ke…”

Bilkisu ta karba. “Besty na don’t mind him.”

“Hnmm.” Kawai Hafsah tace sannan ta harari Bilkisu. Bilkisu na ganin fuskarta tasan yanzun zata fado wata maganar da zata sa taji kunya hakan yasa tayi saurin yi mata sallama ba tare da ta jira me zatace ba ta kashe wayar.

“Hafsah ce…” Ta kalli Tariq.

Ya jijjiga kan sa da murmushi. “A drama queen i guess.”

Tayi murmushi. “You absolutely have no idea. Rigimarta tafi karfinta.”

Shiru suka dan yi ko wannen su yana tunanin makomar rayuwarsu.

<< Ko Da So 13Ko Da So 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×