Ruwan da aka tafka jiya da daddare zuwa asubahin yau yasa kayan da Muktar ya wanke basu bushe ba, takaici da ɓacin rai duk yabi ya cika shi sam baya son saka ƙananan kaya gashi kaf manyan kayan jiya ya wanke su, cike da ɓacin rai ya buɗe jakar bakkon da ke gefen katifar sa wadda yake sa ƙananan kayan sa shi bama zai iya tuna yaushe ya sanya su ba.
Rai a cinkushe ya shirya ji yake tamkar bai sanya kaya ba, ruwan da aka maka yasa Inna ta makara batai kosai ba, sai fanke tuni an zuba. . .