Skip to content
Part 16 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Kwanakin da Hafsah tayi a gidan Goggo ya saka ta ji daman irin rayuwar da suke yi kenan a gida. Rayuwa ce cikin aminci da kula da juna da bawa kowa muhimmanci. Duk da in aka saka mutum a gaba da fada akan wani abu sai yaji kamar ya gudu, ita dai gidan Goggon yafi mata dadi.

Zaune take tana taya Goggo linkin kaya ta lura Goggon tayi nisa a tunani. Ta kura mata ido sannan tace,

“Tsohuwa ana tunanin mutuwa ne?” Goggon ta murmusa ta kalle ta.

“Ba dole ba. Kowa matafiyi ne.” Sai Goggon ta goge hawayen da ya taho mata wanda yasa jikin Hafsah yayi sanyi. Shiru suka yi na dan lokaci kafin Hafsahn tayi magana.

“Goggo kin iya wainar gero?”

Goggon ta kalleta da mamaki. “Wainar gero kuma bebilo?”

Ta gyada kai. “Da ma wasu abincin gargajiyar. So nake na koya.”

Goggo taji dadi ganin jikarta ta ta soma wayo da sanin kanta. A iya sanin ta in dai ba so take ta burge mutane ba ko ta nuna ta iya, Hafsah bata kaunar girki. Kai, ko wanne aiki ma ba son shi take yi ba indai ba ra’ayin kanta bane.

“Sai mu fara ai. Dama na kwan biyu banyi ba. Yau sai muyi tuwon dawa amma ki shirya daukar mitar mutan gidan nan. Don ba ruwana.”

Hafsah ta saka dariyar da yasa Goggo tayi shiru tana kallonta cike da nazarurruka barkatai akanta. Duk da rabin su alan mahaifiyarta ne ba ita Hafsahn ba.

*****

Tana kwance tana duba hotunan wasu dogayen riguna ne kiran Bilkisu ya shigo wayarta. Rabon da suyi waya ma ta manta kuma ita ma bata lura ba saboda yanayin zaman gidan Goggon. Ko yaushe da akwai abun yi ko kuma abokin hira.

“Hnmm.” Kawai tace da ta kara wayar a kunne.

“Ke an sa result.” Gaban Bilkisu ya fadi. Ta mike zaune.

“Innalillahi, yaushe?”

“Yau dinnan yanzu ake gaya min. Zaki iya zuwa ki dubo mana?” Hafsah ta daga labulen dakin ta leka taga yadda hadari ya hado sosai. Ajiyar zuciyar fargaba tayi sannan tace,

“Hadari ne a garin. Ki zauna kar asthma dinki ta tashi. Bari na kira Ya Usman.”

Da haka sukayi sallama Hafsah tana ta tunanin yadda zatayi. Dole sai dai suje su duba don ita bata so wani ya gano mata. Ta jima a zaune tana tunanin Yaya Usman zata fadawa ko Abba.

Shigowar Goggo ya sa ta daina zarya a dakin.

“Goggo an saka mana sakamakon jarrabawa. Don Allah ki min addua.” Ta fada idanunta cike da hawaye. Goggon ta kamo hannayenta suka zauna gefen gado sannan tace.

“Ki kwantar da hankalinki. Nasan kwanya ta kika yi. Zaki wuce dukka da sakamako me kyau. Oh jini ba abun wasa ba. Mamanku ma haka take yi duk sanda aka yi jarabawa.”

Hafsah ta lankwasa kai tace, “ke kam Goggo kun huta. Ba kuyi boko ba kuma ba wanda zai kalle ku ya muku gorin haka.”

Goggon ta yi murmushi me sauti. “Nayi firamare ai kafin a min aure. Lokacin ai mune manyan matan gari.”

Sukayi dariya kafin Hafsah ta mike ta kira Abba wanda ya tura mata dreba suje su dubo. Hankalinta yafi kwanciya ta kira shi don ko shi yace zai je ya duba mata yaga da matsala ba zaiyi mata fada ba sai dai ya bata shawarwari akan yadda zata maida hankali. Yaya Usman kuwa suna dawowa mummy zai gayawa wadda zata saka ta gaba tayi ta mata fada kan cewa babu abunda ta sani sai aikin bacci da fita yawo da kawaye. Sannan kuma har Yaya Farida ma sai ta san bata yi kokari ba.

****

Fitowar Mukhtar kenan daga wanka yaji maganganun mutane daga soro. Da sauri ya ajiye bokitin hannunsa ya shige daki sannan ya karo kofar. Baya son yadda mutane suka maida musu gida kamar titi. Ko wacce mace ta figo daga makota sai ta fado musu gida kanta tsaye saboda kusan kullum a bude take. Yasan hakan yana da alaka da sana’ar da Inna ta na yi. Zai
so ace ya bunkasa mata sana’ar ta yadda ba sai ana shigo musu gida kasafai ba. in Allah ya yarda da zarar kudi sun zauna masa shago zai kamawa Inna a bakin kasuwa sai ta dauki hayar yaran da zasu dinga zama suna sayar mata da abincin. Amma yawan yadda ake shigo musu gida yana bata masa rai.

Da sauri ya goge jikinsa sannan ya shafa mai saboda jin kiran Inna da yayi alamar tare suka shigo da bakuwar.

“Gani nan zuwa Inna.” Ya fada yana mikewa daga kan katifar shi sannan ya daga labule ya fito.

Idonsa alan Inna Ladi ya sauka saboda haka ya daure fuska sannan ya saka silifas dinsa yana karasowa inda suke. Sai da ya durkusa sannan ya gaishe ta.

“Muntari kenan, ashe ka samu aiki.” Ta fada, da alamar tana neman dalilin yin wata maganar. Mikewa tsaye yayi sannan yace, “eh alhamdulillah. Inna na fita, zan leka islamiyya.”

Da sauri ya fice ba tare da ya jira amsar su ba.

*****

Ta dade bata ga nisan zuwa makarantar ba kamar yau. Tafiya suke yi amma kamar basa sauri take gani gashi kuma ko kuzarin ce masa ya kara sauri bata da shi. Sosai take tunanin makomarta har tana mamakin yadda akayi ta damu din. Sanda tana sakandire sam bata damuwa saboda yanayin karatun ya bambanta. Da ta shigo jami’a sai komai ya zamar mata sabo. Gashi dai duk karatu ne amma wani iri take jin shi. Ga yawan mutane a ajin.

Kallon bishiyu da gidajen hanyar take tayi tayi tagumi har suka isa cikin makarantar. Ko da suka dauki kwanar agriculture sai da gabanta ya sake faduwa, cikinta ya daure. Jikin ta sam babu wani kwari ta sauko daga motar sannan ta nufa inda ake saka notice board din.

Hayaniyar dake tashi a wajen ta bata mamaki. Ashe dai mutane da yawa sunji labari. Tana bin mutane da ido taji anyi wata kara. Tana kalla taga wata ce ta yanke jiki ta sume, hakan yasa daliban suka yi kanta da gudu har suka bawa Hafsah damar shigewa gaba gaba don ta fi gani.

A kusa da ita wata ta yi ihun murna sannan ta kara wayarta a kunne tace, “baby carryover ta biyu kawai. Alhamdulillah.” Mamaki ya cika Hafsah. Lallai rayuwa wata irin aba ce me mahanga daban daban. Mintina kadan da sula wuce wata ta suma amma ga wata kuma ita murna ma takeyi bata fado da yawa ba. Maimakon ta duba sai ta tsaya nazarin yadda yanayin tunanin mutum ke da tasiri da yadda rayuwa zata zo mishi. In ya dauke ta da sauki, tazo mishi da sauki. In ya dauka da zafi, sai komai yafi karfin sa.

So take ta karfafawa kanta gwiwa kafin ta duba. Nan ta shiga duba reg number din Bilkisu. Ganin babu carryover yasa tayi ajiyar zuciya sannan ta duba GPA din Bilkisun. 3.8. Hankalinta ya kwanta sosai sannan ta duba nata.

Ko da idonta ya sauka akan nata, bata yarda daidai ta gani ba. Ta sake dubawa tana tabbatarwa da cewa carryover din electricity take gani. Take wani gumi ya rufe goshinta. Yatsanta yana rawa ta sauke shi daga notice board din sannan ta sulale daga cikin jama’ar tana jin jiri jiri.

Tafiya take yi cike da heartbreak din faduwa course dinnan tare da kara jin tsanar course din tana shigar ta. Ta rasa menene matsalar. Ta rasa ya zatayi. A gefe guda kuma tunanin yadda zata fadawa Abba take yi tunda yasan an saka musu result din. Hankalinta gaba daya ya tashi don ji take har wani sanyi yana shiga jikinta.

Da kyar ta samu ta karasa motar sannan sula soma tafiya. So take wani ya rarrashe ta. So take wani yace mata that’s not the end. So take wani yace mata its okay to fail. So take tayi magana da wani…

“Ka kaini gida da sauri…” Ta fadawa direban.

Duk da a lokacin ba Bilkisu take so ta gayawa ba, ba ta da zabi sai na kiranta tunda tana jiranta itama taji sakamakon ta.

Tana danna kiran kamar Bilkisun na jira ta dauki wayar. Hafsah ta runtse idonta hawaye na zuba sannan ta samu courage din yin magana. “Result yayi kyau besty. Kina da 3.8 kuma babu carryover…” ihun murna Bilkisu ta tsala sannan cike da farin ciki tace.

“Besty dan Allah wait, bari na gayawa Tariq…”

Hafsah ta sauke wayar sannan ta jinginar da kanta a kan window. Har suka isa gida bata daina tunani ba. Cike da damuwa ta karasa cikin gidan ba tare da tayiwa kowa magana ba. Ko da ta shiga dakinta ma rufo kofar tayi sannan ta kwanta a gefen gadonta ta fara rusa kuka. Sai da tayi me isarta sannan ta tashi ta wanke fuskarta, tayi sallah.

Bayan ta idar ne ta samu nutsuwa sannan ta tuna ma ashe a gidan Goggo take ba gidan su ba. Ko ya akayi ma dreban ya kawota gida ita ba zata iya tunawa ba.

Wayarta ta janyo tayiwa Halimah text tana gaya mata a gida zata kwana.

Har yanzu zuciyarta take ji tayi mata nauyin da sai tayi magana da wani zata samu sauki. A wannan lokacin kuma mutum daya ne ya zo ranta.

Uncle Mukhtar…

<< Ko Da So 15Ko Da So 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×