Skip to content
Part 22 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

“Sabbin kaya zasu iso nan da sati daya saboda haka ya kamata muyi clearance sales don mu rabu da tsofaffin.” Hajiya Hadiza, mahaifiyar Hafsah ta gayawa me kula da boutique din nata.

Matashiyar ta amsa. Sannan ta dora da, “how many percent off, ma?”

Hajiya Hadiza ta danyi shiru tana ajiye biron hannunta. “Zan yi lissafi.”

Da haka ta cigaba da dudduba kayan tana jotting din abunda ya kusa karewa da abunda yafi yawa. Taku take daidai tana jin dadin nasarar da ta samu a kan kasuwancin nata. Duk abunda ta saka a gaba bata kyale shi sai ta cimma nasara.

Kiran waya ne ya katse mata tunani yasa ta dubi wayar sannan ta tabe baki kafin ta dauka.

“Lafiya, ina boutique ne. Toh shikenan.” Ta fadi sannan ta kashe wayar ta jefa ta cikin jaka. Abunda aka fada yasa ta juya zata tafi don anyi mata ba zata. Matar uncle din Hafsah ce ta haihu shine maman Hidaya ta kira ta fada mata suje barka anjima.

“Wani abu ya taso min. Zan shigo da safe.” Ta fadawa Saratu sannan ta fice tana nufar motar ta tare da tunanin wacce irin shiga zatayi. Bata son shigar da zata jawo mata raini.

*****

Babban gida ne sosai da bangarori da dama. Ko da mummy ta faka motar ta a harabar gidan sai da ta tsaya tana tunanin ko tayi kyau ko batayi ba. Karshe dai ta hakura ta cire mukullin sannan ta fito. Kofar bangaren Amina me jegon tayi tana taku a hankali. Tana budewa sanyin kamshin turaren wuta ya bugi hancinta.

Ta kalli corridor din da zata kaita main parlor din taga yadda aka yi masa ado da frames kala kala. Ga runner carpet nan har karshe. Ta cire takalmin ta ta saka a rack din da aka ajiye a wurin.

Sama sama take jin hirar su har ta karasa da sallamar ta. Cike da takama da nuna ita ma ta isa ta samu wajen zama sannan suka fara gaisawa da mutanen wurin. Dukkan su dai facaloli ne.

Maman Hidaya ta kalle ta ta murmusa. “Hadiza leshin ki yayi kyau wallahi.” Kanta ya kumbura, amma sai ta basar kamar ba wani abu ne mai muhimmanci ba tace,

“Kuma kawai na siya ne randomly saboda shan iska.”

Ta kyalla ta kalli leshin jikin Amina taga babba ne sama da nata. Haushi ya cika ta wato ita Amina zata nunawa sutura. Ai kuwa dai babu abunda mijinta yafi nata.

“Yayi kyau kuwa.” Aminar ta fada itama tana yabawa. Hajiya Hadiza tayi yake tana ganin kamar magana kawai Aminar take so ta yaba mata.

Ta dan kauda kai sannan tace, “ina babyn?”

“Yara sun dauka. Ai ita kam wannan yayyin ta sune iyayenta.” Suka kwashe da dariya.

Maman Hidaya tace, “toh abunka da kalan hanji.” Aka sake yin dariya. Amina ta maze duk da bata dauka da komai ba. Tunda ta samu cikin ake nata tsiya kala kala wai ta tsufa. Da farko ma taso ta cire likitan yace mata babu wani risks sosai.

“Daga ita na kulle dai balle a samu nayi.” Ta fadi sannan suka shiga wata hirar daban.

*****

Ganin a kwana biyu Bilkisu tana ta boye matsalar da take ciki ya saka Hafsah yanke shawarar take gidansu. Ko da ta shirya zata tafi mummy bata ce komai ba hakan yasa taji dadi ta kama gabanta.

A dukkan tsananin mummy bata takura mata idan wajen Hidaya zata je ko wajen Bilkisu. Ta yarda dasu da mu’amalar su da Hafsah din.

Tana isa gidan tayi sa’a bata tarar da kowa ba ta wuce dakin Bilkisu. A kwance ta same ta ta kurawa sama ido hawaye nata fita daga idanunta a gefe kuma wayar ta tana ta ringing.

Hafsah ta yi sallama sannan ta zauna gefen ta ta daga wayar taga Tariq ne.

“Ki barshi kawai.”

Bilkisun ta fada tana tura bakin haushin sa da ta kasa boyewa. Hafsah kuwa daukar wayar kawai tayi tace masa yazo yanzu. Tana sauke wayar, Bilkisu ta kalle ta ta fashe da kuka.

Muryarta na karyewa ta shiga bawa Hafsah labarin yadda sukayi. Ko da ta gama maimakon taji Hafsah ta fara rarrashinta, dariya ta mata.

“Ke yanzu abunda kike wa kuka kenan?”

Bilkisu ta juya. “Kema ba carryover kika gama yiwa zazzabi ba.”

“Bakiga yadda tayi mishi bane and he didn’t stop her.”

Hafsah ta ce, “yo ke babu class ma sam a lamarin ki. Nice ke ta ruwan sanyi zan rama. Amma duk ba wannan ba gaskiya Tariq bai kyauta ba.”

Bilkisun ta gyada kai. “Toh kin gani. Yanzu ya zanyi.”

Hafsah tayi shiru sannan tayi tafi. “Ina da wani tsari amma gaskiya sai kin goge hawayen nan. Kuma ji be ki. Je kiyi wanka mu shiga kitchen.” Kamar mutum me rimot haka ta tashi ta fada wanka, bata jima ba ta fito.

Sai da ta daura robe a jikinta sannan Hafsah tace, “zabo kaya kala biyu muje mu tambayi Ya Iftee wannan yafi dacewa ki saka.” Bilkisu ta kalle ta alamun bata amince da plan din ba.

Hafsah ta tashi da kanta ta nemo kayan sannan taja ta har dakin Ya Iftee. Sukai sa’a tana zaune tana zana jagira da alama fita zatayi.

“Hi Ya Iftee! Dama Tariq ne zai zo shine muke so ki taya mu zaban kayan da yafi kyau.” Hafsah ta daga mata kayan. Tana kallo Ya Iftee ta bata rai amma ta basar.

“Eh Ya Iftee. Wanne zan sa? Yace na mishi kwalliya.” Ta sake tabe baki tana tunanin yadda zatayi.

“Ke yanzu saurayin kike wa wannan rawar jikin?” Ta tambaya tana yatsina fuskarta saboda ta kasa boye bacin ranta.

Hafsah tayi kwafa ciki ciki. Kamar Bilkisun ba zatayi magana ba tace, “Ni ba komai bane a wajena. We love each other so much.”

Hafsah taji dadin amsar tace ita suke jira tayi musu zabi. Tsabar takaici ma yasa ta kasa magana har sai da suka gaji suka bar dakin. Suna fita tayi wurgi da jagirar tana tsaki me cin rai. Ta tashi bazar bazar ta nufi bandaki inda zatayi ihu ba tare da an jiyo ta ba.

Ko da suka koma daki, ajiye kayan sukayi sannan suka tafa. “Kinga fuskarta kuwa?”

Hafsah tace, “ai haka akeyi daman. Ke in kika zauna ranki ne zai baci.” Suka dara sannan suka tafi kitchen.

Meatpie kawai sukayi sai zobo da suka dafa. Sanda Bilkisu ta gama kwalliya sannan Tariq ya iso.

Tare suka fito fuskarta dauke da fara’ar da Hafsah tace mata ta makala. Suka zauna sannan suka gaishe shi.

“Kawarki ta guje ni. Na rasa dalili.”

Hafsah ta kalli Bilkisu alamun bata san komai ba. “She didn’t say a word.”

Da mamaki ya kalli Bilkisu. “Babu komai kawai wayar ce kwana biyu bana taba ta. We’re good. Na zuba ma lemo?” Ta tambaya fuskarta cike da murmushin gaske. Har mamaki take yadda ma ta sake dashi har haka taji haushin nasa yana bacewa.

Ya kalli lemon. “Kuma ba poison a ciki?”

Hafsah tayi dariya. “In ma akwai sai dai poison din love ta saka ma.” Ya kalli Hafsah sai kuma ya dauke kai da sauri yana kallon Bilkisu.

Ta zuba masa lemon ta mika shi kuma ya kalli zobon da aka ajiye yace shi zai sha. Ta zuba masa tana kallonsa. Da kyar ya sha duk da dadin da ya masa.

“Wallahi babu wani abu tsakanina da Iftee.” Ya fada. Hafsah tayi wani boyayyen murmushi.

Bilkisu ta girgiza kai. “Yayata ce fa. Me ya kawo zancen ta? Nace ma wani abu ne?”

Ya jijjiga kai. Hafsah ta saci kallonsa taga duk ya rasa yadda zaiyi sai ta mike tace,

“Dama fita zamuyi. Na baku aron minti biyar..” da haka ta bar wajen sannan ta koma cikin gidan ta nemo wayarta.

Ko da ta dauko tunowa tayi ashe bata da number din uncle Mukhtar. A lokacin ji tayi kamar ta kira Abba ta tambaye shi ya bata.

Zama kawai tayi tana tuno yadda yake kallonta. Lokaci yana cika ta koma ta hango su suna dariya. Har ranta taji dadin yadda suka dinke. Hakan yasa ta sulale ta bar gidan cike da farin cikin ganin Bilkisu a farin ciki.

Sai bayan sallahr isha Bilkisu ta kira ta mata godiya. Cike da jin dadi ta mata fatan alheri. Har ta kwanta bacci ta tuna da assignment dinta duk da tayi.

Daukowa tayi ta sake dubawa ta gani ko yayi. Ta mayar ta koma ta kwanta amma taji kewa ta cikata. Ko baccin ma ya gudu.

Tashi tayi ta fita tsakar gida inda suka zauna. Ta zauna a wurin ta daga kanta sama tana kallon taurari tana murmushi.

<< Ko Da So 21Ko Da So 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×