Skip to content
Part 23 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Hafsa na zaune a falo tana kallo Momy ta shigo riƙe da leda gefen Hafsa ta ajiye, ya yin da Hafsan ya ɗago ta kalle ta kafin ta ce “Momy sannu da zuwa” ta faɗa tana ƙolarin buɗe ledar.

“Yawwa, sannu” kin dawo ashe itama ta tambaya.

“Eh tun ɗazu ma, kuma mai Umman su Basman ta samu?”

Zama kan kujera Mum ɗin ta yi tare da taɓe baki, mace ce, sai wani firiri ta tame wai ita tasa leshin da ya fi nawa”

Murmushi kawai Hafsa ta yi kan ce Momy waye ya baki alkaki?, kamar kinsan kwaɗayi nake ji walllahi”

“Hajiya Babba ce ta baki har na fito ta ce in kawo miki nama ce mata gobe zaki je ganin babin ta ce adai kawo”

Murmushi Hafsa ta yi “woo ni Hafsa mai kakanni” dariya Mum ta yi yo waye baida su ai sai dai in mutuwa sukai, wayar Hafsa da ta yi alamun an turo saƙo yasa ta dubawa Yaya Usman ne, Momy ta kalla tare da yin murmushi.

“Lafiya kike kallona kina wani dariya?,” Wayar dake hannun ta, ta dan haskawa Momin wadda ta Karanta Momy na falo kuwa_ abinda Usman ɗin ya ce kenan.

Rai Momy ta haɗe tare da cewa “cene masa bama na gidan,” Ba musu Hafsa ta rubuta tare da miƙewa ta shige kitchen tabar wayar jikin Momy tana ta sheƙa dariya so take in yazo yaga wayar gun Mum ɗin ya yi tsammanin ita ce ta masa reply.

Daga ɗan nesa ta laɓe tana hangen falon har ya shigo ganin Momy yasa shi ƙoƙarin juyawa ta ce “Kai Usman zo nan”

Jiki ba ƙwari ya matso Hafsa ta fito kamar ba ita ke dariya ba ta matse “lah yaya ka dawo?”

Watsa mata harara ya yi tayi kamar bata ganshi ba ta hau lalube “Mum ina wayata?”

Ɗago wayar Momy ta yi daga cinyar ta, ta miƙo mata, ta amsa tare da zama gefen Momy wadda le faman faɗan mayar da su Khalil da Usman ɗin ya yi, ɗagowa ya yi rai cinkushe ya ce “anma fisabilillahi nida gidan shikenan sai akawo wasu jarirai su takura mun?”

“Eyye sannu issasshe, gidan ku ai ka ce ba gidan ka ba,” Momy ta katse shi.

Langwaɓar da kai ya yi tamkar wani ƙaramin ya ro, “aiko tafkar su zan koma tunda dole sai an kawo su”

Hafsa ce ta ɗago ” Kai yaya dan Allah, kai lokacin da kake zuwa gidan Gwaggo ko Hajiya Babba kana takura musu ai b wanda ya tafke ka, su da gidan Kakan nin su”

Miƙewa ya yi a kufule “na fahinci ke kike zuga Mum kan ya rannan”

Momy ce ta ɗaga masa hannu “Malam dakata, ba wanda yake zugani, tunda abin naka haka ne ka fito da mata kayi aure ka bar yara su huta ai dama kana da abinyi, in kuma kaƙi zan nemo ma koma wace in haɗa ka da ita”

Dariya yasa Haba Hajiya Momy sai kace a lokacin da ai ko Yaya Sadik da ya haƙura da auren dolen da kika masa dan shi ɗan da ne”

Tsuke fuska Mum ta yi ” kana wasa ko to mu zuba” ta faɗa tare da miƙewa tabar wurin Hafsa ta yi saurin bin bayan ta tare da shigewa ɗaki.

Faɗawa jikin kujera ya yi yana dariya Finally faɗan da yake gudu dai sun haɗu da momy ya sha shi.

Washegari da wuri Hafsa ta shirya zuwa makaranta, lectures ɗaya sukayi ta safe sai kuma ta 2 to 4 da Malamin ya mayar 12-2 ana fitowa daga Morning lectures ɗin kasan benen ASN suka nufa ita da Bilkisu domin siyan takardun da aka bayar sunyi sa’a babu mutane sosai wannan yasa suna zuwa aka sallame su, har sun wuce gaban exam office suka dawo ganin tabarmar shinfide ba kowa suna zuwa Hafsa ta faɗa kai tana faɗin kai har naji daɗi, yayin da Bilkisu ta mike ta hau duba fuskar ta jikin madubin da ke manne jikin bango.

“Gaskiya wanda ya sa madubin nan ba karamin technology ya kawo ba” inji Bilkisu da ke faman kamar fuska tana goggogewa.

Dariya Hafsa ta yi tare da tashi zaune ta ja jakar Bilkisu ta ciro janbaki tare da miƙewa, “To Hajiyar Janbaki walllahi baki isa ba bani abuna da tsada na siya.”

“Koma nawa kika siya, walllahi sai na sa” ta faɗa tare da fara shafawa tana mita “mutun sai rowar tsiya haka rannan nayi nayi kiban ruwa kika ƙi sai ledar kika ban kawai ƙyale ki na”

Dariya Bilkisu ta yi “yo daga wasa shafe shima duka Hajiyar Mita”

Shabiyu saura minti biyar suka nufi ajin su Malin chemistry ɗin na tsaye jikin bene idanun sa na kallon ajin lokaci lokaci yana kallon agogo da alamu jira yake 12 ɗin ta yi ya rufe, ganin yadda duk wanda ya hawo keɗan yo gudu ya shiga yasa sums yin gudun, suna shiga ya bi bayan su ya rufe.

Ganin Ibrahim zaune kujerar su yasa Bilkisu yin baya yayin da Hafsa ta ja ta tsaya kan sa tana faɗin wurin mune, mursisi ya ƙi tashi, cikin fushi ta ce zaka tashi ko sai na girgiza kujerar”

Kamar dutse yaƙi motsawa sam Hafsa bata son zaman baya wannan ya bata kwarin gwiwar gaza jin tsoron malamin da ya tsura mata idanu tun bayan goge allo da ya yi ya juyo yaganta shi bai ce ta zauna ba, bai kuma ce ta fita ba da alamu mamakin karfin halin ta yake dan wanda ta tsaya kan nasa ya girme mata, ganin yadda Malamin ya tsura musu ido yasa Ibrahim tashi Hafsa ta yi kwafa tare da zama.

Ajiyar zuciya Malamin ya yi ya juya har ya fara rubuta ya juyo ” Bansan akwai maza masu tsoron mata ba sai yau”

Aka sa dariya, duban Hafsa ya yi Hajiyar rikici fatan dai yau ba zaki mun bacci a aji ba,” kunya ce ta kama Hafsa dama Bilkisu ta faɗa mata yasan kowa suma yasan su gashi kuwa ya san kullum baccin ta take a class in nasa musanman in Khadija da suke surutu tare bata zo ba, dan ita Bilkisu in ana lectures to mantawa take suɗin aminai ne maida hankali take sosai bata surutu.

Sai wurin biyu da rabi ya fita duk Hafsa ta gaji idanun ta tun da ya fara batun course ɗin suka fara lunshewa sai ta yi kamar zatai bacci sai ta ɗago ta kalle shi ta fasa.

Sai da suka biya ta coke village suka sayi shawarma dan tun jiya Hafsa keson cin ta coke village ɗin a mota suka ci abinsu aka sauke Bilkisu inda Hafsa ta wuce gida, ta yi niyar daga makaranta zata wuce gidan Hajiya Babba taga babin Ummi sai dai gajiyar da ta yi yasa ta bari sai anjima da yamma kawai ta je.

*****

Kasancewar litinin ce ta ƙarshen wata yasa Muktar tunda ya tashi suka gaisa da Inna yake faɗa mata “in ayi albashi zai wuce gidan Rashida naji rannan kince da na faɗa miki zaki aika mata da sako.”

“Towo kaima dai Muktar da rashin azanci kake, tun jiya ba sai ka faɗamun ba, yanzu in ka makara fa”

Shafa kansa ya yi ai “bansan sakon zai ɗauki lokaci ba, ki in bari sai gobe naje”

Mikewa Inna ɗin ta yi bari muga ta shiga madafar su, daga inda yake yana juyo burun burun ɗin ta na taɓa kwanuka, kamar minti uku ta fito rike da buhun samo, dana bakko, gashi tsaki ne da su kuka da garin tuwo da na ɗan wake, “kace mata kanwar tana da zafi dan karta zabga ta ɓata mata abinci.”

Tom ya ce mata ya ɗauki kayan ya fice, aransa yana jin daɗi aikin nan nasa bawai iya ɗebe masa kewar zama wuri guda yake ba har ƴar uwarsa ya taikama tunda ada kuɗin zuwa gunta ma bashi dashi.

Koda aka tashi siyayya dai dai gwargwado ya mata ya hau mota daga Hotoro zuwa Mariri, adai dai lokon su aka sauke shi ya saɓi buhun da ya haɗe kayan duka a kafaɗa zuwa gidan Rashidan, yau baiyi katarin haɗuwa da yaran Rashidan ba duda kuwa tarin yaran dake ta wasa a lokon.

Tun daga zaure yake jiyo Hayaniya mutan gidan yayin da kukan yara ke tashi, sallama ya hau yi ba wanda ya tanka masa daurewa ya yi ya shiga kamar kullum yauma gidan kaca kaca, riƙe take da kwalar rigar mijin nata wanda ke faman faɗin ta sakar masa riga.

Ganin yayan nata yasa ta sakin sa ta fashe da kuka, “yaya ni gaskiya na gaji ka tafi dani dan Allah
Ajiya zuciya ya yi muje daɗi kai kuma lallashi yaran, ya faɗa suka shiga ɗaki da Rashida wadda keta faman kuka.

Sai da ya bari ta sha kukan ta sannan ya ce ta taimaka ta yi shiru, wanda dakyar ta yi.

“Mai ya faru? haba Rashida kin ban kunya bansan rashin mutuncin naki har yakai ki iya riƙe kwalar mijin ki ba kina faɗin maganganu marasa daɗi”

Kuka ta kuma sawa “yanzu yaya kaima goyon bayan sa kake”

Girgiza kai ya yi kema kin san ko zan goyi bayan kowa ke zan goyi baya tunda kece jinina, kawai sa kema kin san baki kyau ta ba, ita kuma gaskiya in ban faɗa miki ba, bansan wanda zai faɗa miki ba”

Cikin shessheƙar kuka ta ce yaya sam Mutumin nan bai san daraja ta ba, baya tausayi na, baisan cina ba baisan sha na ba, sai dai in ciyar da shi abinda kawai ya sani shine ya hakke mun na gaji nayi nayi ya sake ni yaƙi.

Leƙowa Nura ya yi yace “bawai kawai naƙi sakin ta bane dan ta ce cikin dake jikin ta zata zubdane ina sakin ta ta sake aure, ni kuma har ga Allah ina son abinda ke cikin, shi yasa naƙi sakin ta tunda sai na sake ta zata zubar”

Salati Muktar yasa “zubda ciki Farida, dan sunna ɗin? Yo ko na zina ne ai ba kya yi kisan kai ba”

Kuka ta rushe da shi, “ni nagaji ga uwar yunwa, ga wahalar cikin nan nagaji, walllahi nagaji”

Dakya Muktar ya samu ya lallashe ta ta haƙura ya haɗa su ya yi ta musu Nasiha, ya basu kayan da ya kawo, sai yamma liss ya tafi gida dan sai da ya tabbatar sun shirya abin mata da miji kan ya tafi sai wasa da dariyar su suke, Nura ne ma ya kwaɓa ɗan wake ya jejjefa musu.

Muktar na tafe a unguwar su ƙanwar tasa yana tunanin sana’ar da Nura zai iya yi har ya fito bakin titi ya hau Mota bai iya fidda shawara ba…

<< Ko Da So 22Ko Da So 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×