Skip to content
Part 24 of 53 in the Series Ko Da So by Aisha Kabir

“Ashe ma kin iya kika zauna wasa..” Mukhtar ya fadi, yana duba assignment din Hafsah wanda guda daya ne kadai tayi mistake shima daga formula ne. Cike da jin dadi ya sake kallonta yace,

“Kawai dai ba kya maida hankali ne.”

Hafsah ta sunkuyar da kai tana murmushi sannan tace, “ai malamin ne wallahi abun haushinsa yayi yawa. Wai kaga mutum ya sako wata yellow din shadda ga bakin glass kamar dan daba.”

Mukhtar ya kasa rike dariyar sa ya dara. “Allah da gaske. Ni gaba daya sai naji haushi yake ban kuma dama ni ba son physics nake ba.”

Ya kalleta cike da mamakin yanayin tunanin ta da yadda ta dauki rayuwa. “Toh yanzu me ya chanza? Nima dai kalli kiga silifas na saka.”

Hafsah ta leka kafarsa taga silifas dai da ta sani amma sai taji haushin Mukhtar bai kama ta ba.

“Ai kai daban ne, you’re charismatic and just ka hadu kawai…” kamar wadda tayi sabo, sai tayi saurin rufe bakinta ta sadda kanta kasa tana ji kamar ta nutse don kunyar abunda ta fada.

Mukhtar kuwa zuciyarsa ta cika fam da farin ciki. Ya rasa inda zai saka kansa a lokacin, fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi ya maida kallonsa kan littafin dake hannunsa. Sun jima a haka ba wanda ya sake cewa komai. Ko wannen su zuciyarsa tana dokawa da sunan dan uwansa.

Mukhtar ya gyara murya sannan yayi kokarin ture yanayin da ya ziyarce su. Hafsah ta dago ta kalle shi, kafin ta dauke kai sai da idanunsu suka sarqe suka yi murmushi sannan kowa ya kauda kai.

Ya sake gyaran murya yana nemo jarumtakarsa da ta gama bacewa a lokacin sannan ya dauki textbook din gefen sa ya bude.

“Tunda kin gane capacitors, inaga yanzu sai mu fara da resistors ko?” Ya fada wanda ya sanya Hafsah tayi ajiyar zuciya sannan ta kalle shi tana gyada kai. Zuciyarta bata daidaita bugunta ba sai ma kara saurin da take yi.

Ta rasa yadda zata yi ta nutsu ta nuna ba abunda ya faru har sai da kalaman da bata san yadda suka hadu ba suka fito ba, tace “uncle Mukhtar wasa nake fa kawai dai ka iya koyarwa ne.”

Mukhtar ya gyada kai. “Nagode.”

Bata kalle shi ba ta yi shiru. Tunda ya fara bayani kanta kawai take gyada mishi ba tare da ta furta komai ba har suka gama karatun ranar. Daidai sanda yazo tafiya ne yasa yace mata ya kawo mata abu ya ajiye a kofar dakin me gadi.

Cuke da jin dadi da manta wancan yanayin kunyar da ta saka kanta a ciki ta bishi ya mika mata flask madaidaici.

“Wainar gero ce, inji Inna.”

Taji dadi sosai kamar tayi tsalle.

“Nagode sosai. Bari na koma. A gaishe su dan Allah.” Ba tare da ta jira amsarsa ba ta gudu cikin gida cike da farin cikin da tun kwanaki bata san silarsa ba. Kai tsaye kitchen ta wuce don ta zuba wainar in ta huce kuma tayi warming a microwave.

Bayan Mukhtar yayi sallama da mai gadi shima a hankali ya soma tafiya yana tunanin ta. Wani yanayi yana fusgar zuciyarsa game da Hafsah. Ya sani ya kamata ya dakatar da koma menene. Aiki ne ya kaishi ba sabo ba. Ko bayan haka ma sam ita ba kalar wadda zaiyi sabo bane da ita. Watakila kuma shi yake ganin kamar kulawar ta a gare shi ta musamman ce. Watakila kawai kirki take masa with no strings attached. Ya tsaya a bakin titin yana sake maimaitawa zuciyarsa ta daina dokawa Hafsah ko da kuwa dukan da takeyi ba na neman wata alaka bace ta kawayence ko na so. Maimakon yaji komai ya daidaita sai murmushin Hafsah ya sake fado mishi a rai.

A take zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri tana saka shi shima murmushin.

Mota tazo wucewa ya tsayar ya shiga sannan ya samu hankalinsa ya chanja alkibila.

*****

Mummy ta yatsina fuska tana nuna bacin ranta gami da nuna kyama ta kalli flask din da ke zaune a cikin sink. Jikinsa duk ya kode. Ko flask din ma’aikatan gidan bai kai munin wannan ba. Sai ma taji kamar har wani wari wari ne yake tashi daga sink din duk dan saboda flask din.

Ta sake kallonsa sannan ta wanke hannunta ta nufi dakinta saboda wayarta da take ringing.

Ko da ta isa ta tarar call din ya tsinke sai kawai ta ajiye wayar ta fita da tunanin waye ya kawo mata wani flask cikin gida.

A corridor suka ci karo da Hafsah wadda mummyn bata ganta ba tun bayan sanda ta fita daukar lesson.

“Kin yi wata bakuwa ne bayan kin shigo?” Ta tambayi Hafsah.

Hafsah ta girgiza kanta sannan ta kalli plate din hannunta. “Laa mummy wallahi na manta banyi miki bismillah ba. Wainar gero naci.”

Mummy ta kalle ta unbelievably, “wainar gero kuma? A ina kika samo ta Hafsah?”

Hafsah ta murmusa. “Uncle Mukhar ne… Innar…” bata karasa ba mummy ta dakatar da ita.

“Ban gane ba.”

“Innar shi ce…” ta sake katseta da wata tsawa me firgitarwa.

“Innar wa? Meye hadin ki dasu Hafsah? Wato har abincin alamajirai ake kawo miki kina bani kunya ko?”

Hafsah ta zumburo baki tace, “mummy ni nace fa ya kawo min. Wallahi kinga kuma har na saka wata a fridge.”

Mummy ta dafe kanta da taji ya fara sara mata saboda bakin ciki. Ta rasa yadda zatayi da wannan yarinyar. Wato abun Hafsah ya kai har abincin mutane take ci take kawo mata cikin gida. Irin mutanen da bata kauna musamman ma wannan Mukhtar din da kallo daya kawai ta mishi taji baiyi mata ba.

Bata son Hafsah tana harka da irinsu. Mutane ne masu wani irin tunani kuma bata so a gwarayawa Hafsah tunaninta. Bata kaunar kusanci da irin su Mukhtar shi yasa ma tun farko bata ji dadin yadda zai dinga zuwa ba. Yanzu kuma abun ya kai har da abinci ma aka kawo. Allah kadai yasan me ya zuba a ciki don ya cuci yarta.

Har wani duhu take gani yana gilmawa ta idonta. Ba tare da ta ce komai ba ta nufi part din baban Hafsahn ta shiga. Ta san baya nan amma a nan zata zauna jiransa don wannan abun yafi karfinta.

Kujera ta zauna tana rufe idonta. A hankali take kokarin ayyano fuskar Mukhtar amma ta kasa don bata wani tsaya ta mishi kallon da zata gane shi ba. Yanzu kuwa ya zama dole ta saka ido sosai akan sa. Har ma akan Alhaji Muhammad don talakawan nan ba kirki gare su ba yanzu tana zaune sainsu asirce mata miji da ya.

Bari dai ya dawo.

*****

Zaune Hajara take suna hira da Inna tana bata labarin yadda za’ayi bikin kawarta Nafi ba tare da sun kammala karatunsu ba. Nafi kawarta ce sosai da suka shaku har suke lissafin irin burirrikan da suke so su cimma a rayuwarsu bayan sun kammala sakandire. Kwatsam wani Alhaji Gambo ya zo yace yana sonta. Ganin mutuncin sa yasa ta kasa yi masa wulakanci tace yaje ya gaida babanta wanda take tunanin kora da hali ne tayi masa.

Sai dai yana zuwa gidan nasu zance ya chanza musamman ma da ya sakar musu da bakin aljihu kamar bai son ciwon kudin ba. Daga yadda Nafi take bata labari, da gaske sonta yake tsakani da Allah amma ita Nafin bata son shi. Sam ba kalar wanda take tsara rayuwarta bane. Tun Hajara tana nuna mata ta botsare har ta hakura dai take lallashin ta saboda taga alamar aure dai sai anyi shi.

Inna ta gutsuri goron da take ci jefi jefi tace, “toh Allah ya basu zaman lafiya. Su ma iyayen nata hankalinsu yafi kwanciya.”

Hajara tayi shiru tana sake jin haushin Alhaji Gambo sannan tace, “ni kam inna sai nake ganin an cuceta wallahi. Nafi fa ita take yin na daya a ajin mu kuma gashi wanda zata aura yana da mata kuma yace ba zatayi karatu ba.”

“Aure ai wata ni’imace musamman in mace tayi dace da miji me tausayi da sanin kimarta. In dai zai dauke ta da daraja sam karatun ma mantawa zatayi dashi.”

Hajara ta tabe baki. “Tab di jam. Ta dai gamu da wahala.” Inna ta kalle ta cike da mamakin tunanin Hajarar.

“Toh ni Inna wallahi gara min karatun. Gara mutum ya waye ya samu ilimi ya kuma tallafawa kansa kafin auri. Jibi fa Yaya yadda take. Ni banga wani amfanin auren wuri ba.”

Inna ta rasa abun cewa sai kawao ta kara volume din rediyonta ta juya gefe alamun ta gama wannan maganar.

Hajara dai taso Inna ta tanka mata amma tayi shiru. So take ta sako maganar Garba amma ta rasa taya ya.

Sai da ta gaji ta tashi sannan Innar ta bita da kallo.

Zuciyarta ta sosa game da halin da yayar tasu take ciki. Bata mantawa, ra’ayin Rashida baibai yake da ra’ayin Hajara. Sam taki yarda ta kammala karatu ta nace ita sai aure. A lokacin Nuran zaman jiran shago yakeyi sannan ya kan dan saida abubuwa idan yanayin su yazo. Duk yadda aka so a fahimtar da ita bashinda sana’a mai karfi da zai rike ta taki fahimta. Haka suka hakura aka mata auren saboda kwanciyar hankalinsu da nata.

Duk da wannan, bata son ra’ayin Hajarq da dogoj burinta. Tana so ace yaranta dai sun danyi karatun su sannan suna da sana’ar hannu kafin suyi aure in yaso in suna da rabo sayi karatun mai zurfi a dakinsu.

Take taken Hajara ya bata tsoro. A hankali ta furta addua ga dukkan yayan nata sannan ta cigaba da jin rediyon tana ayyanawa a ranta ya kamata ace Mukhtar ya iso gida.

<< Ko Da So 23Ko Da So 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×