Skip to content
Part 27 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Ganin shiru shirun da Hafsah ta dauka kwana biyu ya damu mommy sosai. Duk yadda ta kada ta raya kuma Hafsah ta nuna mata sam shirunta bai da alaqa da Mukhtar. A zuciyarta taji sanyi amma duk da haka bata jin zata iya barin sa ya cigaba da hulda da Hafsah saboda gudun bacin rana.

Mug din tea da take sha ta ajiye tana hamdala. Shirun gidan ya mata yawa yau saboda bata da niyyar fita ko ina. Hafsah ta kwalawa kira wadda ta fito tana hamma.

Mummy ta kalleta ta tabe baki kadan. Yau hira takeji shiyasa ma ba zatai mita game da yadda Hafsahn take ba.

“Mummy ina kwana.” Ta samu waje ta zauna. Ta kalli TV taga a kashe sannan ta kalli mummy wadda sanye take da wata doguwar riga mara ado sosai. Hannunta kamar ko yaushe dauke yake da zobunan gwal guda biyu da awarwaro uku wanda sai zata kwanta da daddare kawai take cire su.

Yanayin shigar mummyn ya tabbatar mata da yau ba inda zata je.

“Lafiya lau. Kin tashi lafiya?”

Hafsah tayi murmushi. Yau wace rana ba’a fara amsa gaisuwarta da mita ba. Ta gyara zama tana matsawa kusa da mummyn.

“Lafiya lau mummy.”

Suka danyi shiru cike da rashin abun fada don basu saba hira ba haka kawai sai dai in wani abun ne ya tashi.

“Yau ba zaki fita ba?”

Mummy ta gyada kai. “Hutu nake. Gyaran daki na zanyi daga nan inyi tsifa na wanke kai.”

Hafsah ta murmusa. “Toh mummy muje in taya ki gyaran dakin sai in miki tsifar ma.”

“A’a gara dai ki tayani gyaran dakin. Ba ruwanki da gashi na. Haka kawai a yanke min dan abun adon nawa?” Suka kwashe da dariya.

Abu ne da dukkan su basa mantawa. Akwai lokacin da mummy ta taba saka Hafsah da Hidaya suyi mata tsifa lokacin basu kai haka ba. Da yake tana da cika da tsawon gashi sai yasa suka dade sunayi har suka gaji. Hafsah ta kalli Hidaya tayi qasa da murya sosai don kar mummy taji,

“Dama akwai reza mu dan rage tsahon jelar.” Karaf kuwa sai a kunnen mummy wadda ba shiri ta kwace kanta ta hau su da fada. Tsifar da basu karasa ba kenan kuma basu sake ba.

“Mummy an fa dade. Kuma gajiya ce tasa na fada haka.”

Mummy ta girgiza kai. “Ba zan yi wannan gangancin ba. Tunda kika furta, zaki aikata. Ki ja min asara ki jawa babanku.” Suka sake yin dariya wanda tayi daidai da shigowar Sadiq.

Sallama yayi basu ji ba sai da ya sake yi. Ganin rahar da suke ciki ya faranta masa rai sosai har shima sai da ya murmusa.

“Ya Sadiq ina kwana.”

Hafsah ta gaishe shi.

“Ba wannan ba. Hado min shayi.” Mummy ta harare shi. Ya za’ayi mutum ya fito daga gida yazo neman abinci. Sai da Hafsah ta wuce sannan mummy ta amsa gaisuwarsa tana cewa,

“Ina Amirar take?”

Ya sosa keya. Kwana biyu abun nata kara gaba yakeyi don ko kwalliyar jikin ma da take bata lokaci tana yi masa bata yi yanzu. Bar ta dai tayi ta kwanciya tana ta gaji. Abun yaso ya dame shi musamman da yaga in zasu fita tana yin kwalliya iya kwalliya sannan ta ware sosai amma da sun dawo gidan sai ta sauya kamar ya kawo ta makabarta.

Boyayyiyar ajiyar zuciya yayi sannan ya niisa. “Bata jin dadi ne.” Da gaske kuma yau yaji alamar zazzabi a jikinta shiyasa ya danyi share sharen da zaiyi ya barta tayi bacci ta huta sannan ya fito.

Mummy bata wani gamsu ba tace, “Toh Allah ya kara sauki.”

Daidai sannan Hafsah ta shigo dauke da ruwan zafi a flask ta ajiye. Mummy ta kalle ta tace,

“Ki soya masa bread. In yaga dama kar yaci.”

Jin haka yasa ya fasa yin mitar da zaiyi na cewa jagwalgwalo ne Hafsah zata kawo masa kawai. Ganin kallon da mummy take masa ne ma yasa ya fara tunanin ko lefin me ya mata bai sani ba. Yaji kamar ya fasa zancan da ya kawo shi amma ba ya so ya rasa damar yau kasancewar tana raha.

“Mummy tana karatun kuwa?” Ya tambaya da alama yana nufin Hafsah.

“Hnmm gata nan dai ta bi tasa tsanar physics a ranta.” Ta tabe baki.

“Ai na dauka an yi solving wannan issue din.”

Mummy ta girgiza kai. “Yaron ne sam bai yi min ba. Shiyasa na dakatar da shi.”

Sadiq ya gyara murya, an zo wurin. “Me yayi mummy? Bai da kamun kai ne?”

Ta juya kai. “Kawai kasan talaka da jin kan sa. Sam kawai zuciyata bata aminta dashi ba.”

Ya murmusa a boye. “Amma Hafsah tana gane karatun sa?”

“Eh da alama. Shiyasa ma nake tsoron tasirin sa akanta.”

Sadiq yasan inda zancen yake. Yaga babu amfanin yiwa mummy kwana amma kuma don dai ya karkatar da tunanin ta zai gwada.

“Tab mummy ai babu wanda yake da tasiri akan Hafsah sama da ke. Shi waye? Yayi kadan ya sauya mata tunani. Kawai karatu ne tsakanin su shikenan. Na sha kallonsu daga nesa kuma abunda na fuskanta kenan. Kuma tunda anyi sa’a tana ganewa yanzu ai ke abun alfaharin ki ne mummy.”

Mummy ta murza zoben hannunta tace, “hakane kuma. Kawai ina tsoron kar wani abu ya tsarga a zuciyarta ne kasan halin ta da taurin kai yadda naga tana rawar jiki in yazo.”

“Watakila rawar jikin ma duk dan saboda tayi karatun ne ta burge ki. Kaf gidan nan babu wanda yake kokarin ya burge ki sama da Hafsah. In muka zauna kullum zancen ta kenan saboda mummy.”

Mummyn taji dadi. Take zuciyarta tayi wasai. Itama duk da basa jituwa da Hafsahn daban take jinta a ranta kamar yadda take jin Sadiq din daban. Shi kadai ne yake iya kwantar mata da hankali akan kowa. A take ta dauki maganar sa.

“Toh zan duba in sha Allah.”

Bai amsa ba Hafsah ta shigo tana ajiye tray din a gabansa.

“Kuma wallahi nafita iya abinci.. ci kaji!” Suka kwashe da dariya.

Mummy ta kurawa Hafsah ido sai taji wata kwalla ta taho mata. Ta maida ta sannan tayi murmushi gami da mikewa ta bar falon ta bar su suna musu.

*****

Jikin Mukhtar yayi kyau don har ya tashi ya koma aiki ma. Yamma ce lis yana ta faman wanki yaji sallama. A zabue ya juya saboda jin muryar wadda take sallamar. Suka hada ido da Rashida da yaranta biyu dukun dukun dasu kamar yan gudun hijira. Ya kalli gefenta yaga Ghana must go. Gaban sa ya fadi. Ba dai ta kaso auren ba?

Tsame hannunsa yayi daga wankin yana amsa sallamar su ita kuma tana karasa shigowa.

“Ban dari biyu dan Allah na bawa dan iskan nan.” Ta roka. Mukhtar yaji takaici ya cika masa zuciya amma ya ciro ya bata inda ta fita ta wullawa me adaidaitar gami da yin tsaki sannan ta dawo cikin gidan tana mita.

“Aikin banza. Ya dauka dari biyun wata abar arziki ce.” Mukhtar ya bita da ido har ta shige dakin inna ta dire kayan nasu sannan ta fito.

Ya matsa zai dauki yaronta yaji zarnin fitsari ya doki hancinsa.

“Fitsari yayi?”

Ta tabe baki. “Bar shegen yaron nan mana a hanya ya sakar min shi kamar baida baki.” Ta talle keyarsa ai kuwa ya tsala ihu.

Mukhtar ya ja shi gefe yana tafiya dasho bakin rijiya. Ya cire masa kayan ya dauraye masa jiki yana jinjina kazantar Rashida da yadda gabaki daya ta chanza daga kalamai har dabi’u. Bai taba sanin cewa inda mutum yake zaune nada tasiri gameda yadda zai yi rayuwarsa ba sai akan Rashida. Ya dauka sanda tayi aure tayi girman da babu wani abu da zai chanja mata halaye.

Da yake ana rana sosai ruwan da ya yiwa yaron wanka yasa yaji dadi har gyangyadi ya fara. Rashida dai sai kallonsa take tana tabe baki. Har ya gama wankin, ya shinfidawa yaron dadduma gami da lullube shi da zanin Inna kafin kayan su bushe bata ce uffan ba.

Sai da yaron ya fara minshari ta kalle shi. “Sai katon kai kamar na uban sa.”

Mukhtar ya samu wuri ya zauna. “Wallahi Rashida ki gyara hali.”

Ta murguda baki. “Ina Inna?”

Sanin halinta yasa ya bata amsa. “Ta fita. Su Hajara suna Islamiyya yanzu zasu shigo.”

“Toh ai gwara dai su dawo don abunda yake damuna mace ce kadai zata fahimta. Mazan nan duk halin ku daya.” Ta tofar da yawu a gefenta sannan ta mike.

“Bari na zagaya.”

Mukhtar yabi bayanta da kallo yana ji kamar yayi kuka. Wannan wace irin rayuwa ce ta daurawa kanta? Bata jima ba ta dawo.

“Ba wani abun jefewa bakin salati ne?”

“Bakin zagi dai.”

“Me kace?” Ta fada tana lekawa kicin din Innar ko zata samu abu. Mukhtar ya mata shiru bai ce komai ba har ta samu wuri.

“Wai yanzu yaya ba zaka tambayeni me aka min ba?” Mukhtar ya tabe baki.

Sallamar su Hajara yasa yayi hamdala sannan ya mike yana barin gidan cike da bacin ran da duk randa ya ganta sai ta cusa masa. Shi kenan da yake dan uwanta bare kuma mijinta.

<< Ko Da So 26Ko Da So 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.