Skip to content
Part 28 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Tunda suka shigo suka gaishe ta sukayi daki don su chanja kaya, Hajara ta yatsina fuska tana kallan Juwairiyya. “Wai me ya kawo ta?” Juwairiyya ta watsa hannu gefe alamun bata sani ba. Ita kuwa Hajara sai haushin yayar duk yabi ya cikata da yake daman sakuwar ta ce ga fada, ga kazanta. Yanzu Inna sai tace daki daya zasu kwana wanda babu yadda zatayi. Amma in akace kwanan zatayi, wannan karan sai dai ita ta dinga kwanan tsakar gida. Gwara taji da sauro da taji da aikin gyaran fitsarin kwance na yaran Yayar.

Hajara ta linke hijab dinta sannan ta daura zani tana tunanin me zai kawo yayar tasu gida. Ita kuwa Juwairiyya kawai daga labulen dakin tayi ta fice ba tare da ta bata amsa ba.

Kusan a tare suka nemi wajen zama kusa da ita suna zama. “Sannu da zuwa Yaya, ya gidan?”

Juwairiyya ta tambaya tana kallon fuskar yayar wadda duk ta fada.

“Hnmm ya akurki zaki ce min dai. Wannan wajen har kya kira shi da gida? Allah na tuba ba gara kwanan bakin titi ba.” Yarinyar ta ta zuba mata ido kamar tana so ta fahimci me uwar tata take fada. Juwairiyya ce ta lura hakan ya sanya ta kama hannun yarinyar.

“Muje in miki wanka…” da haka ta bar wajen ta barsu da Hajara dan ita ba zata iya tankawa yayar ba.

Hajara ta tabe baki. “Toh me kike nufi yaya?”

Rashida ta sosa kai har dan kwalinta yana zamewa gefe wanda yasa Hajara ta lura da tsohuwar kalbar dake kanta. Hajara ta kalle ta da mamaki kamar yadda Mukhtar yayi mamakinta. A gidan ita da Hajara sune yan gayu da kwalliya kuma ba abunda yake hana su yi. Ko rashin lafiya take sai tayi kwalliyar nan. In bata da kudi kuwa a cinikin Inna take sayar hoda da turare dan zubi.

Kullum tas take amma sai gashi lokaci guda ta rikide. Dole ma tayi nesa da aure yanzu.

“Yaji nayi. Ai wallahi ba zan koma ba sai anyi magana da shi. Ace mutum ba ci ba sha kullum sai dai ya dimama katifa?”

Hajara ta sake tabe baki. “Toh dama ai kinsan baya aiki.”

“Ai da yana nema yanzu kuwa bacci yasa gaba. Ni wallahi ba wahalalliya bace. In ya ga zai gyara toh, in ba zai gyara ba wallahi yazo ya debi yaransa ya bar takarda ta na kara gaba. Ai da saura na.”

Hajara ta zuba mata ido. Bakinta yayi nauyi ta rasa abun fada duk haushin yadda Rashida ta zama ya cikata. Ta cigaba da kallonta har ta mike ta dauki buta.

Ta kalli gefe taga yaronta yana bacci har yanzu. A nan take ta lula duniyar tunani. Garba yana da sana’a, shin watarana haka shima zai daina? Shin haka rayuwarta zata koma ita ma? Tab di jam. Ai wallahi ita sana’a zata nema. Ba zata iya zaman wahala ba. Ba zata yarda ta yarda wannan kwalliyar a gidan su ba. Ta ja numfashi saboda nauyin da taji zuciyarta tayi. Tana son Garba, amma bata son rayuwar talauci ko zaman kauye. Bata son ya dauke ta ya kaita nesa. Dole ma ta masa magana tun yanzu suyi yarjejeniyar inda zata zauna.

Rashida ta tako a hankali tana shafa cikin ta wanda babu tsammani ta dauke shi. Ta ja tsaki sannan ta sake zama.

“Wai Inna ba zata dawo bane?”

Hajarah ta murmusa. “Dawowarta kam sai bayan Isha. Gidan Kawu taje.” Su ka danyi shiru na wani lokaci ko wannen su da abunda yake sakawa aransa.

“Yaya wai auren ba dadi ne? Duk soyayyarki da Nura ina ta tafi?”

Rashida ta tabe baki. “ Wace soyyaya kuma babu kudi. Ai wallahi duk yadda zakiyi kiyi aure gidan kudi. Nima kaina sai da mukayi auren naga duk wasu kadarori da yace yana da ita karyace. Kinga kuwa dole ma na kaso auren nan yasin. Ya nemi yar wahala irin sa.”

Sallamar Mukhtar ta saka Hajarah ta hadiye amsar da zata bayar. Har ya shigo da ya zauna gefen su da yar ledarsa a hannu ya ajiye basu sake cewa komai ba.

“Oh har yanzu bacci yake? Ga biscuit na siyo musu.”

“Kai yaya ni kuma me ka kawon?” Ta tambaya tana daukar ledar. Kan ya amsa ta dauki daya ta bare.

Hajara ta kalle ta ta mike. Ta bar wajen kanta cike da tunani kala kala.

“Kinsan wannan zaman ba zai yiwu ba ko Rashida. Ya kamata ki nemi sana’a ki rufawa iyalinki asiri.”

Ta juya keya tana magana kasa kasa. “Ni fa wallahi yaya gara kawai ya sake ni.”

Mukhtar ya sake jinjina al’amarinta. “Nan fa kika ce in ba shi ba sai rijiya.”

“Da ake ma magana yanzu kuwa wallahi kamar sartse nake jin sa a zuciyata.”

Mukhtar ya furzar da iska. “Allah ya gyara. Ke dai na baki kwana daya kiyi tunanin sana’ar da kike son yi na baki jarinta.”

Rashida ta washe baki. Gara dai wasu kudi su shigo hannunta ta samu na siyan tsire tana ci a tsakar gida tana waqen ta na habaici kamar yadda tayi wancan karan da ya bata jari.

“Ba kudin zan baki ba Rashida, don nasan cinyewa zakiyi. Abunda kike bukata zan kawo miki dukka.”

Wayarsa ta fara ringing hakan ya sanya shi ciro ta yaga wa yake kiransa. Salisu ne. Saurin tafiyarsa ya karu sosai sannan ya fice daga gidan ya bar Rashida tana ta mitar yadda shi sam baya goyan bayanta yadda ya kamata. Tana yi tana cin biscuit din da aka kawo wa yaranta ko a jikinta.

*****
“Kar ka zama rago mana, kawai ka sauke nauyin da kake ji a zuciyarta gane da ita tun kafin wani ya riga ka wallahi.” Salisu ya bashi shawara bayan ya zauna a tsakar gidan nasu daidai kofar dakin Salisu.

Mukhtar ya shafa kansa yace, “kai ba zaka gane bane. Nauyinta nake ji wallahi. Kwarjininta yawa ne dashi.”

Salisu ya rike dariyarsa. “Toh shikenan ina fata dai duk randa kaji wani ya dauke ta ba zamu kwantar da kai a asibiti ba.”

Mukhtar ya harare shi. “Bansan raini wallahi shiyasa ma tun farko naki yin shawara da kai.”

Salisu ya make kafadarsa. “Dalla wasa nake. Tashi ka raka ni naje na zuba wa Maryama karatun yau. Kasan sai anayi ana nuna jajircewa.”

Suka fito tare suna tafiya. “Amma wai Salisu da gaske dai ba zaka nemi sana’a ba? Don’t think of it the wrong way. In har sonta kake yakamata ace kana da plan na aurenta.”

Maganar Mukhtar ta sanya a karon farko jikin Salisu yayi sanyi. Shiru yayi har suka karasa layin gidan bai tanka ba. Sai dai suna neman yaron da zai kira musu ita ne mahaifinta ya fito. Kafin kace kwabo, Salisu ya sulale ya arce. Mukhtar ya juya ya kalli gefensa ya hangi dattijo. Da suari yabi bayan Salisu yana tuntsurewa da dariya.

Sai da yayi da gaske ya kamo shi.

“Haba maza, wannan yawa ne.” Salisu ya sosa keya yana nema ya maze. Amma ganin dariyar Mukhtar ba zata tsaya ba ya sanya ya hakura.

“Kuma wallahi idan naji maganar nan a wani wuri sai nayi balangu da kai.”

“Yi hakuri jarumi.”

Salisu ya sha kunu. “Kai wai baka lissafi ne? Yanzu in yace in turo fa ya kake so nayi bayan kasan ban shirya aure ba. Balle kuma ya bincika yaji bana aiki.”

Mukhtar ya gyada kai cike da jin dadin yadda abun ya kasance. Ko babu komai Salisun zai nemi abunyi. In baiyi don Allah ba ko iyayensa, yanzu zai yi saboda soyayya.

Ko da suka koma hanya, gida Salisu yayi. Kana ganinsa ka ga tashin hankali da damuwar da yake ciki. Mukhtar ya mishi sallama sannan shima ya koma gida da Rashida a ransa.

Sana’a rufin asiri ce ga kowa komai kuwa kankantarta. Mutum bai san ta ina Allah zai buda masa ita ba. Ga Innar su nan yana kallo. Albarkar dake sana’arta ce ta taso dasu dukkan su har ma suka zama abun kwatance.

Dole Rashida ta dauke ta a matsayin abun koyi ba ta zauna tana ta mita ba. Sosai yake so ya sake kebencewa da ita ya nuna mata muhimmancin sana’ar da yake so tayi. Ba wai don Nura ba kadai. Don kanta. Shima Nuran zai je ya same shi ya nuna masa sai ya zama namiji zai samu daidaito a cikin gidansa. Zaman gidan da yake kullum ba mafita bace a gareshi saboda kullum Rashida zata ganshi ne ta kara raina shi.

Tabbas yana tausayin ta da yadda rayuwarta ta koma amma yafi ganin lefinta.

*****

Safiyar ranar da zafi aka tashi hakan yasa ko wannen su ya fito tsakar gida aka shimfida tabarma ana fifita tun bayan asuba. Yaran Rashida kuwa suna can gefen bishiya suna wasa bayan Juwairiyya ta yi musu wanka don suji dadi su ma.

Mukhtar ya kalli lokaci a karamar wayarsa sannan yace, “bari na sake wanka na tafi aiki.”

Mikewar sa ke da wuya, Hajarah da Juwairiyya suma suka tashi suka tafi dakin su don shirin tafiya makaranta.

Inna ta kalli Rashida dake kishingide tana gyangyadi tace,

“Rashida ki tashi muyi magana.” Tana goge idonta ta zauna ta bata fuska.

“Komai na duniya da kike gani hakuri ake dashi. Sannan ita rayuwar nan cike take da kalu bale da jarrabawa kala kala. Na sani ke da Nura kuna son junan ku har gobe, saboda haka bai kamata ace kun bari sauyin rayuwa ya jawo tangarda a rayuwarku ba. Dukkaninku masu laifi ne. Kinji dai fadan da na miki jiya…”

Hawaye suka zubowa Rashida. Ita sam ba haka taso ba. So tayi a nuna masa tafi karfin sa. Amma sanin halin Inna yasa bata tanka ba ta gyada kai.

“Shi raini da bakaken maganganu da kika dauka babu ranar da zasuyi miki. Mijinki shine shugaban ki saboda haka ki zama mai hakuri dashi a ko da yaushe. Na sani, zaman babu bai da dadi shiyasa akace miki ki nemi abun yi, zaki rage jin radadin babun.”

Rashida ta sake goge hawayen da yake ta faman zarya a kumatun ta.

“Mukhtar ya kira Kawu jiya kuma sunyi magana da Nuran. Anjima kafin azahar zai zo ya dauke ki ku koma. Dan Allah ki dinga godewa Allah akan duk abunda ya same ki.”

“Inna wallahi ina kokari na.”

Inna ta tashi. “Na sani, ki kara akan wanda kike, wataran sai labari. Muje mu daura karin kumallo.”

Kafin Rashida ta amsa Inna ta tuna abu tace, “kuma don Allah kazantar nan da kika dauka ki jefar da ita a hanyar komawar ki. Tashi ki wanke kan na kitse miki shi.”

A kace ko wanni mutum yaro ne a gaban mahaifan sa. Sai gashi Rashida ta tashi ta wanke kanta inda Inna ta kitse mata kan tsaf, tayi wa yarta ma. Bayan kowa ya bar gidan kuma Inna sun kammala gyare gyare sai ga Nura yazo. Da fara’ar sa ya shigo alamun son ta yana tare da shi kamar ko yaushe.

Ya zauna Inna ta hada su biyun ta kuma yi musu nasiha akan muhimmancin hakuri da karbar kaddara duk yadda tazo wa bawa. Nura ya yi mata godiya ya kama hannun yaran ya koma waje yana jiran Rashida.

Inna ta debo kwano daya na shinkafa da wake danye da wasu kayan abincin ta mikawa Rashida. “Gidan ki shine garkuwar ki. In kin yi da kyau kiga da kyau. Kije, Allah ya muku albarka. Mukhtar zai zagayo miki in an musu albashi.”

Rashida idonta ya cika da kwalla. “Nagode Inna.” Da haka ta fita daga gidan tana jin nauyin da ta shigo da shi gidan yana raguwa.

Tana fita taga Nura tsaye yana magana da yaran. Yasa su gaba suka fara tafiya don samun abun hawa.

<< Ko Da So 27Ko Da So 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×