Skip to content
Part 29 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Yau cike da farin ciki ya tashi ji yake tamkar ya janyo ƙarfe uku domin ya tafi gidan su Hafsa sosai yake missing ɗin ta, Kasancewa yaji sauƙi sosai yasa shi tashi da niyar komawa koyarwar da yake mata, ta ko ina ya yi missing ɗin yarin yar, bayan ya karya ne ya hau duba kayan da zai sa, muryar ta ce ta dawo kunnunwan sa a lokacin sa ya sanya ƙananan kaya “Uncle kayi kyau” tamkar a lokacin ta faɗa haka ya ji sautin nata, murmushi ya yi tare da ture jakar bakkon da yake sa manyan kayan sa ya janyo ledar da ƙanana suke, shiɗin ba gwanin ƙananan kayan bane, kwata kwata basu fi shida ba, wata blue ɗin riga mai haske ya janyo gami da baƙin dogon wandon sa, baki yasa ya cinge tag ɗin rigar tunda Ibrahim ya nana masa ita ya siya bai kuma bi ta kanta ba.

Aje kayan ya yi a bakin katifar sa wadda ya gyare ta tamkar mace, ɗakin ya share tare da fita ya ɗebo garwashi tare da ɗan turara ɗakin sam Muktar baya son ƙazanta mutun ne gwanin son ƙanshi.

Dariya Juwairiyya tasa lokacin da ya fito riƙe da kasko ” kaima dai yaya sai kace wani mace, ni ban taɓa ganin inda namiji ke turara turaren wuta ba sai kanka”

Banza ya mata tare da aje kaskon can gefe ya leƙa ɗakin Inna, ganin ɗakin wayam yasa shi cewa “ina Innar?”

“Ka manta yau ake sunan Balaraba ta je taya su aiki” juwairiyar ta faɗa lokacin da take juya miyar da ke kan wuta, jira kawai take ta karasa ta fita da abincin.

“Kingani ko na manta shaf walllahi, bari ma kawai inna fita in leƙa” ya faɗa tare da yin waje ba tare da ya jira amsar Juwairiyya ba.

Gida ne matsaikaci kai yasa ya shiga bayan ya yi sallama, matan da ke ta faman aikace aikace suka amsa, ɗaya cikin masu ɗaura zoɓo ne ta ce “ah Muntari ashe jiki yayi kyau jiya nake cewa zan komo in kuma duba ka.”

Murmushi ya yi “walllahi kam jiki ya yi sauƙi, ina kwana” ya gaishe ta.

“Lafiya ƙalau, to Allah ya ƙara sauƙi” ta faɗa lokacin da ta kamfaci zoɓon ta kurɓa.

“Ina mai jegon?” Ya tambaya bayan ya gaggaishe da matan da ke aiki, daga ciki Balaraba tace shigo mata Muntari, a nutse tare da sallama ya shiga, daurewa yayi dan wani irin ƙamshi ko ƙarni zance ya daki hancin sa, kamshin turaren daban ƙarnin jego daban, a daddafe suka gaisa ya ɗan riƙe Jaririyar na mintina kafin ya bawa mai jegon dubu guda ya taso ya fito.

Ƙarfe biyu dai dai ya dawo sannan ya shirya kafin ya bar gidan su, cike da walwala sam fuskar sa ta kasa ɓoye farin cikin da yake ciki, a ƙofar gidan ya tsaya mintina kaɗan da bugun sa aka buɗe Malam Musa ya fito, ganin Muktar ya washe baki “oh ashe ba’a gama karatun ba, har ina cewa Malan ko sallama”

Murmushi shima Muktar ɗin ya yi “walllahi ba’a gama ba banji daɗi bane sam”

“ayya to Allah ya ƙara sauƙi” Malam musa ya faɗa yana bawa Muktar wuri alamun ya shiga, duru duru ya yi da ido yana tunanin ya za’ai Hafsa tassn ya zo, kamar ance juya suka haɗa idanu da Usman wanda ya fito riƙe da makullin mota da alamu fita zaiyi, ƙarasawa Muktar ya yi suka gaisa.

“Malamin Hafsa ko?” Usman ya tambaya.

Gyada kai Muktar ya yi “eh, Allah yasa dai tana na?”

“Eh tana nan but naji tana cewa zasu fita bari in mata magana” ya faɗa tare da juyawa ba tare da ya jira mai Muktar zai ce ba.

Momy na zaune a falo tana kallo, ganin Usman ta ce “ya kuma ka dawo kasan Hajiya Hasina bata son jira fa”

Zama ya yi kujerar da ke kallon ta, “Dama malamin Hafsa ne yazo nace ba inzo in faɗa miki, dan naji kamar zata fita rannan kuma naji kina cewa an dai na,” ya yi ƙarya dan in yace mata Hafsan ta faɗa masa faɗa zatayi mata tace tana kai ƙarar ta gun yaran ta.

“Eh yaron ne, take taken sa basu mun ba”

Murmushi ya yi “Banda abin Momy kwana nawa ne an gama anma fara test da tayi exam ɗin shikenan , kinga ai da yake sunyi dabara both na second semester ɗin da zatayi da wanda zata gyara Level 2 yake mata, kinga babu batun in tazo level 2 ɗin ya koya mata, yanzu in ance za’a samo wani malamin kafin ta yi adapting to his teaching methods wani abin ne daban, in kuka ta faɗi second semester ina faɗa miki her CGP will be bad, irin mumin da zai adai yi shiru”

Shiru Mum ta yi tana haɗa maganar Usman da Sadik wanda ya mata jiya gaskiya suka faɗa, dole ta haƙura kawai a cigaba amma idanu zata sa musu ta faɗa a ranta, “kaje ka faɗa matan yazo ku tayani sa musu ido”

“Tom” kawai Usman yace tare da wucewa ɗakin Hafsa daga bakin ƙofa ya yi Sallama duda ƙofar a buɗe take yaja ya tsaya, “shigo mana yaya, kullun ina faɗa muku inna bar ƙofar a buɗe kowa zai iya shigowa”

Murmushi ya yi ya shiga zaune take tana kallo a system ɗinta gefen ta kuma danbun Nama ne tana ɗan tsakura, ” kinga sauri nake, Malamin kine yazo mun magana da Mum tace zaki iya ci-gaba but make sure kun yi ƙoƙarin covering komai da sauri, kun fasa fitar ne?” ya faɗa.

Sai da ta daure wurin ɓoye murnar ta, bata son ya fara zargin batin mum gaskiya ne barema rannan ya mata batun ko ta fara soyayya ne, “Tom kace masa ina zuwa, eh mun fasa Hidayan ta ce sai gobe zata tafi, duk ma ta damu bata son komawa makarantar”

“Towo ai dama sai da na faɗa karatun naisa ba irin nasu bane, ita mai kwalafucin gida, ace daga shiga level 2 har ta sare, ai shikenan bari inje” ya faɗa

“Tom yaya adawo lafiya” ta faɗa lokacin da ta jawo system ɗin tana ƙoƙarin kashewa, yana fita ta rufe system ɗin ta zari mayafi, a nitse ta fito ji take tamkar ta zura a guje ta ɗora idanin ta kan sa, tuni zuciyarta ta isa harabar gidan tahau kewayon neman inda yake, tana barin falon ta fara duban sa can ɗan nesa da entrance ɗin falon ta hange shi zaune Kasan bishiya bisa kujerar da ke gun, tamkar yasan zumuɗi bai bari ta ɗauko abin zama ba.

Da mugun sauri ta ƙarasa sai dai tana zuwa daf dashi ta tsaya, cikin kala kalar shagwaɓa tace “nayi fushi shine zakayi rashin lafiya baka faɗan ba ko” ta faɗa idanun ta sun kawo ƙwalla.

Murmushi ya yi “banda abin Hafsa ita rashin lafiya ai bata sanarwa, anma amin afuwa”

Murmushi ta yi, ” shikenan ya wuce ya jikin gashinan kuwa duk ka faɗa”
Hannu ya miƙa mata “ban wayar ki,”

Ba musu ya miƙa masa Number ɗin sa ya rubuta kafin ya danna kira tasa tayi ƙara, “Number ta kenan ko mun gama karatun wataran ma dinga gaisawa”

“Kaga zumuɗin ban ɗauko abin zama ba duk na ƙagu in ganka,”

“Ashe bani kaɗai ba, sosai na yi missing surutun ki fa”

Ɗan jan hancin ta tayi, fuskar ta ɗauke da murumushin jin daɗi.

Sai yanma lis suka gama karatun ta miƙe “bari in kawo ma kwanon rannan, kaga ko ruwa ban kawo ma bama”

“Karki damu ganin ki da nayi ma ya wadatar” maganar da yayi a zuciya ta faɗo labban sa sauti ya fita, bata ce komai ba ta yi ciki tana murmushi.

Tunda suke karatun yake tattara jarumtar, so yake ya faɗa mata irin son da yake mata ya kasa, ya rasa mai ke damun sa, ya rasa wanne irin kwarjini yarinyar take masa .

Hangar ta da yayi tayo wurin sa da kwano yasa shi faɗaɗa murmushin sa, ta ƙaro tare da miƙa masa, “gashi na gode sosai a gaisar mun da Inna amin godiya wurin ta”

Murmushi ya yi har ya juya, ya kuma juyo tare da cewa “Hafsa,” ta juyo haka kurum suka samu kansu da faɗuwar gaba.

Matsowa ya yi kusa da ita gaban sa na ƙara faɗuwa, sam ya naimi abinda ya tsara zai ce mata ya rasa.

“Kinsan tunda nazo nake tsara irin yadda zan miki proposing Soyayya ta, anma kwarjinin ki yasa da na kalle ki sai in manta komai”

Har kanta taji batun nasa, daɗin da taji ya yi yawa, sai dai itama ɗin bata san mai zata ce ba, “kaga na manta ban faɗa ma ba kayan da kasa yau sunma kyau” kallon kansa ya yi tare da yin murmushi.

A gaishe da Inna tace tare da shigewa gida, ya kusa minti ɗaya atsaye kan ya fice yana fita ya durkushe yana haki Finally ya fidda abinda ke ransa, murmushi kawai yake, yana kuma kallon rigar dake jikin sa kalmomin Hafsa suka dawo masa “kayan da kasa yau sunma kyau” murmushi yayi kwarin gwiwa ya kama shi cas ya miƙe tare da nufar titi.

Hafsa na shiga ɗaki ta faɗa gado tana bubbuga kai, takaicin kanta duk ya cika ta, har dare in ta tuna ga dama ta samu ta watsar bata bashi amsa ba, sai ta hau tsaki da bugun kanta, da zarar zuciyar ta ce mata what if ya ɗauka rejecting ɗin sa kikai ba, sai taji kamar ta zane kanta, baccin da ya sace ta dakyar shima cike yake mafarkan Muktar ya dangana ya cire ta a ransa.

<< Ko Da So 28Ko Da So 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.