Skip to content
Part 30 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Tafe suke a mota zuwa filin jirgi inda Hidaya zata koma makaranta, a wurin faka motocin driver ya faka motar, Hidaya ta ɓata rai tare da yin narai narai da ido tamkar zata yi kuka, Hafsa ta ce ” Hajiya ki fita mana kin takura mun rakoki kin san ina da abinyi sai ka ce akwai wanda ya miki dole sai kin je nesa karatun”

Hidaya turo baki ta yi cikin shagwaɓa ta ce ” Maimakon ma kuyi kuka, haka ma fa Ammi tama ƙi rakono”

“Zan fa tura ki waje, a’a to ya zata rakoki lokacin da tace kiyi BUK mai kika ce?” Hafsa ta faɗa.

Tsaki Hidaya ta yi ” you are not helping matters ” ta faɗa tare da barin motar, sai da ta ɗanyi nisa Hafsa ta fito da ɗan saurin ta, ta rungume ta ,”Zan missing ɗin ki, Allah ya kaiku lafiya.”

sun ɗan jima a haka kafin su rabu, kuma sallama sukai kafin tayi ciki ita kuma Hafsa ta koma mota, Malam Musa ya ja su ka ɗau hanya. Wayar ta ɗauko daga aljihun jakar ta, Number ɗin Bilkisu ta hau kira sai dai taƙi shiga Number busy, tsaki ta yi, duban Baba Musa ta yi bata son takura masa sai dai kuma tana matuƙar son ji daga bakin Bilkin.

kai tsaye gidan su Bilkisu tasa ya kaita, a harabar gidan suka haɗu da yaya Ifti, wadda tana ganin Hafsan ta ɗan tsuke fuska, kusan tunda akai abin Bilkisu da Tariq Yaya Ifti ɗin ke jin hsushin Hafsan, Sam bata nuna ta gane tana jin haushin nata ba ta ce ” Ya Ifti ina kwana?, tana nan kuwa”

“Lafiya ƙalau, ni da ba ɗaki guda muke kwana sannan ba faɗan rayuwar ta take ba ina zan sani”

Hafsa bata ce komai ba ta yi shigewar ta ranta fal cike da jin Haushin Iftin, sam abin na bata haushi yadda Iftin ke wa Bilkisun bacin yadda Bilkisun ta damu da farin cikin ƴan uwan ta.

Falon ba kowa wannan yasa Hafsan yin sama nan ɗakunan ƴan matan gidan yake, kai tsaye ɗakin Bilkisun ta nufa, bugu ɗaya ta ce ta shigo. kwance ta same ta rib da ciki ƙafafun ta sun yi sama waya manne a kunnen ta tana zuba dariya. Murmushi Hafsa ta yi tare da samun wuri ta zauna.

“Hafsa ta zo muyi magana anjima, ok zata ji ” Ta faɗa tare da aje wayar ta dubi Hafsa Tariq ne, yace a gaishe ki”

murmushi Hafsa ta yi “ai ba sai kin faɗa ba yadda farin cikin ki ya nuna, nasan shi ɗin ne, ina amsawa, walllahi ganin ki da nayi ya kuma tayar mun da abin da ya kawo ni”

Tashi zaune Bilkisu ta yi “towo mai ya kawo ki, kin san nayi mamakin ganin ki sabida nasan kina da lesson ko an gama?”

Kwafa Hafsa ta yi “uhumm! Wanne gamawa ai abinda ya kawo ni kenan, Bilkisu I am In love”

“Wow! What ke ɗin?” Bilkisu ta faɗa cike da mamaki.

“Eh ni dai Hafsan da kika sai, ina son sa sosai walllahi, problem ɗin Mum bata son sa, that’s not it only kamar shima bai sona, even though he confessed loving me”

Kallon ta Bilkisu ta yi duk ta faɗa, “Matar nan kin ɗauki soyayya da zafi, but batun Momy ke zaki sa ta so shi, shi mai yasa kika ce baya sonki?”

Numfashi Hafsa ta furzar “tunda ya zo yamin maganar yana sona bai kuma bi ta kaina ba, kuma fa ya fa amshi Number ta, amma ko da wasa bai kira ni ba, he should have chased me at least before given up, ba daga ya faɗa ban bashi amsa ba ya janye is that love?, ni da nake mace kullun sai naji ina son kiran sa, sai in daure at least I have some pride left”.

“He might be busy fa, ko kuma wani abu ya samu wayar sa, ko kuma wani abun daban bawai dan baya sonki ba.” Bilkisu ta faɗa.

Shiru Hafsa ta yi kafin ta ce “kin tabbata, abinda kika faɗa har ranki?” Hafsa ta fada tana Kallon Bilkisun.

Dariya Bilkisu ta yi “ke dai Hafsa na fahinci zafin so ne da ke, ai ba zan faɗa miki what did I not mean.”

“Bari kiga to in tafi kar yazo baya nan nassn tas Mum zata ce ace masa an dena lesson ɗin.”

Girgiza kai Bilkisu ta yi “yanzu kinsan ba zama zakiyi ba kika wahalar da Driver maine anfanin wayar ki,” Bilkisu ta yi complain.

“Wayar taki da bata da anfani na yi ta kiranki, baki ɗaga ba kina can kina soyayya, Hafsa ta faɗa lokacin da ta miƙe kinsan banga Mamin ku ba.”

“Ba ta nan tun safe taje Islamiyya sai uku zata dawo,” inji Bilkisun.

Gyaɗa kai Hafsa tayi “ah lallai ba zamu haɗu bs kya gaishe ta,” ta faɗa tare da yin waje Bilkisun ta bi bayan ta.

*****

Tunda Muktar ya dawo gida ya kasa sukuni gabaki ɗaya satin yin su ya yi sukuku, ji yake tamkar ya jawo Asabar ta zo ya je gidan su Hafsa ya kuma Tambayar ta, yana son kiranta yana jin tsoro kar ta ga ya takura mata, shi bai saba harkar ƴan mata ba, bai san ya ake tafi da su ba.

Bayan ya dawo daga Salla guga ya yi tare da ɗiban kayan sa masu dauɗa ya fita tsakar gida, tun jiya ya kasa haƙuri yau asabar ɗin ta yi, yau kuma da ta yi ji yake tamkar ya yi tsuntsu zuwa gidan su Hafsa wannan yasa shi samarwa kansa abin da zai ja lokacin sa zuwa ranar ta yi.

Ajiye kayan ya yi ya leƙa ɗakin Inna, tana zaune tana jan carbi ya ce “Inna ina kwana, lafiya ƙalau” ta ce, “yawwa wanki zanyi shine nace ki kawo in haɗa da naki.”

“Shekaran jiya fa kamin wankin ba masu dauɗa waɗancan biyun ne kawai,” ta nuna kayan da ke saƙale jikin alharga, miƙewa ya yi tare da ɗaukan kayan ya y tsakar gida, kusa da nasa ya aje sannan ya ɗauki botiki zuwa bakin rijiya ya hau ja, Hajara ce ta fito daga ɗaki tana miƙa ganin yana jan ruwa yasa ta ɗaukan botiki da sauri ta aje gefen sa, “Yaya dan Allah zubamin walllahi na jawo hannuna kanta yake walllahi na jawo.”

Bai ce koma ba ya juye gugan da ya janyo a botikin da ta aje.

Sai wurin biyu ya bar gida yama kasa jira yau ukun ta yi kan ya tafi, uku da mintiina ta masa a ƙofar gidan su Hafsan mai makon huɗu da yake zuwa, akai sa’a itama ɗin tuni ta shirya yau har ɗan girki na dabara ta yi dan shi, duk gidan ta dafa sai dai a ranta ita dan Muktar tayi, tsoron kar Mum tace har girki take masa ta canja shawara ta ce an dena karatun yasa ta yi kowa da kowa.

Tana zaune tana bitar karatun da sukai baya da shi, dan tasan halin sa dole sai ya tambaye ta mai akai in ta yi dai dai a ɗora in ta kakare a mai maita, Mum ta leƙo “Malamin naki ya zo.”

Agogo ta kalla yau ya shammace ta sosai tayi tunanin sai huɗu zai zo yadda ya saba, Allah yasa na duba sosai ta faɗa tare da miƙewa ta yo falon, ganin Mum a zaune sai taji tsoron zuwa Dinning din tace zata zuba masa abinci, rai ba daɗi tayi hanyar waje.

“Tunda yazo da rana fatsar fatsar haka ko zaki zuba masa abinci?”Taji muryar Mum ta faɗa.

Sai da Hafsa ta yi murmushi sannan ta juyo kamar ba ita ke son zuba masa abincin ba, a flask ƙarami ta zuba masa ta ɗebi lemon kwakwa da yaji madara shima a ƙaramin jug ta ɗora a matsaikaicin tire tare da plate da cokali ta fice, can nesa ta hange shi yau sai taga duk ya fi mata kyau kamalar sa da haibar sa ta fito sosai a idon ta, da Sallama ta ƙarasa sukai ma juna murmushi wasu kayan nata ya amsa suka ƙarasa inda suke zama, “Daddumar na jakar” ta faɗa ya buɗe ya ɗauko tare da shinfiɗa musu ya amshi tiren hannun nata suka zauna sannan ta gaishe shi.

Sun ɗan fara karatun aka fara kiran sallah tace “bari ta shiga ciki nayi,” daga ɗan nesa ta tsaya tare da juyowa, “yawwa wallahi kaci abincin tun ɗazu nake cewa kaci kaƙi, inma kunya ta kake ji to kan in dawo ka cinye,” ta faɗa tare da yin ciki ya yi murmushi kawai.

Bayan ya dawo daga Sallah zuciyarsa ta yi ta faɗa masa yafa ci abincin nan, dan zuciyar Hafsan ta ji daɗi, jan tiren ya yi ya zuba, ga mamakin sa sosai yaci abincin sabida daɗin da ya masa yana cikin tsiyaya lemon a ƙaramin kofi ta ƙaraso wurin, gefen sa ta zauna, “ko kaifa har naji daɗi” ya yin da ya kurɓi lemon ya ce “karfa ace santi nake amma abincin ya yi daɗi.”

Murmushi ta yi “ai dama ni ɗin ba daga nan ba wajen girki.”

Dariya yayi “sa’a dai akai yau yayi daɗin ku Autoci mai kuka iya banda shagawa,” itama dariyar ta yi “aikam ni na fita zakka.”

Tunda suka fara karatun Hafsa ke baza idanu da kunnuwa taji ya yi maganar so amma shi ya mayar da hankalin sa ne kawai ga yin calculations, duk ranta ya ɓaci ta dena ganewa zuciyar ta sai ingiza ta take ta masa maganar wani jarumi cikin ranta na hanata na faɗa mata ita ɗin mai aji ce.

Tambayar da ya saba mata bayan ya gama koya mata ya yi, sai dai ba kyakkyawar amsa, kallon ta ya yi sai da gaban sa ya faɗi da suka haɗa ido ya yi saurin kawar da kai kafin ya ce, “yanzu fisabilillahi Hafsa haka zamuyi da ke ga dare ya fara kawo kai gashi ina son muyi managa, gashi ba ki iya karatun ba.”

Jin ya ce zasuyi magana yasa ta mai da hankali, “gobe in sha Allah ma ƙara mai maita karatun” ya ce.

“Tom” kawai ta mayar masa.

“Kin san kuwa baki bani amsa ta ba ko?”

Kamar bata san mai yake nufi ba ta ce ba kace “gobe zamu maimaita ba in sha Allah goben zan iya.”

“No ba karatu ba, yanzu duk maganar da zamuyi ba ta karatu bace, ta soyayyar da na kawo ƙoƙon bara ce, nasan ba dai dai bane begging for love but I have to, dan Allah Hafsa ki daure ki so ni, ko ya ɗan rabin da nake miki ne, kinji” ya faɗa yana tsare ta da ido.

Aranta tace “wanne rabi, ina jinma naka guntun wanda nake ma ne,” a zahiri kuma ta yi shiru kawai so take itama ta ɗan gwada jan ajin nan duda zuciyarta mara zuciya na hanata, ingiza ta kawai take ta ce yes.

“Kin san Allah tun randa na tafi kwana da yini kallon Number ɗin ki nake, ina son kiran ki ina tsoron shirun nan da kikai nasan zuciyata zata iya bugawa na tunanin shirun na nufin a’a Hafsa ki tausayamun kinji dan Allah” ya faɗa da muryar tausayi.

“Ai da ka kira” ta faɗa kafin ta miƙe “mai kika ce?” “sai na yi tunani” ta ce ta hau haɗa kayan ta shima mikewa ya yi ya ninke mata Daddumar tare da sawa a jakar da ta zo da ita ya miƙa mata, ta yi gaba yayin da ya yi saƙaro yana kallon ta, ƙafafun sa ma sun kasa motsawa bare subar wurin, juyowa ta yi ta ga yana nan tsaye, ta gama gamsuwa yana matukar son ta, tana iya ganin hakan a idanun sa da Muryar sa, murmushi ta sakar masa lokacin da suka haɗa ido tare da aje tiren cikin iska ta rubuta masa ” is ok, I love you too” ta yi sauri ta ɗauki tiren ta tayi ciki tana murmushi kamar wanda kwanyar sa ta daskare sai da tayi ciki kuma kansa ya dawo masa da abinda ya karanta, cike da murna ya ce yes! “Ya Allah Alhamdulillah” ya faɗa tare da barin gidan.

Kitchen Hafsa takai kayan sa’annan ta leƙa tace Mum ta dawo.

Muntinan ta kaɗan da shigowa taji muryar Aunty Halima ƙanwar Momy da gudu ta fito tana murna, farin cikin yadda taga sonta ƙarara gun Muktar da zuwan favorite Aunt ɗin nata suka garwaye, har sai da Halima tace “anya Hafsa farin cikin gani na ne kawai?”

Dariya ta yi “kema kin san shine.”

Shiru Halima ta yi “ina zuwa ba mu gaisa da Anti maganar da kika ce zamuyi randa kika zo ɗaukan kaya na biyo sahu.”

Dariya Hafsa ta yi “kai Aunty Halima kedai kwai son labari tom ina ɗaki ina jinki.”

Mum na bed room ɗin ta suka gaisa ta ce “wato yarin yar nan bakya son zumunci, yaushe rabon da kizo gidan nan sannan yanzu ki tashi zuwa kizo da yamma lis fatan dai kwana zakiyi?”

Dariya ta yi a’a kinsan Gwaggo ba ta jin daɗi in bana nan,” harar ta Mum ta yi in kin tashi aure ki tafi da su, dariya tasa ta fice zuwa ɗakin Hafsa.

“Yawwa bani na sha tawaje na,” Halima ta faɗa lokacin da ta faɗa gadon da Hafsa ke kwance, murmushi ya kasa ɗaukewa a fuskar Hafsa cike da zumuɗi tace “Aunty Hafsa I am in love,” sai kuma Murmushin ya ɗauke “Mum bata son sa dan talaka ne” kafin Halima ta yi Magana Mum da ta shigo ta fara.

“Innalillahi wa’innailahirraji’un dama, abin da na guda kenan yanzu sai da ɗan iskan yaron nan ya yi nasarar saka miki sonsa? To walllahi ya yi kaɗan ba’a haifi talakan da zai aurar min ɗiya ba.”

“Anma Anti…” Ɗagawa Haliman hannu ta yi “Malama dakata banso jin wani abu bacin ku kuke zugata.”

“Allah Mum ba wanda….”

Mari ta kaiwa Hafsa “yi mun shiru shasha maras tunani, lesson ne an dena in ma abinda yafi Carry over zakiyi I don’t care, duk randa na ƙara ganin sa a area ɗin nan ba ma gidan nan ba zai sha mamaki sai ya gane bai da wayo walllahi” fuu ta fice Hafsa ta rusa kuka

<< Ko Da So 29Ko Da So 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×