Kafin mu ɗora muji ya akai akayi auren Hafsa da Muktar, ya akai Mum ta dawo tana son sa, ku biyo mu rayuwar su ta yanzu, nasan baku manta da sakin da ya mata ba, bari muji ko zai mayar da ita ko kuwa
Cigaban Labari
Yamma lis aka sallami Mami Hafsah wadda jikinta da jininta da ya hau ya daidaita. Ko da likitan ya sallameta zaunawa tayi a kan gadon asibitin kanta yana mugun sarawa. Ta rasa tunanin da zatayi a lokacin. Ta rasa inda ta nufa. Ance in bata daina ba jininta zai mugun hawa wanda zai jawo mata wata babbar matsalar. A ganinta babu matsalar da ta kai girman rabuwa da Mukhtar. Sai dai ba kowa bane zai gane. Har shi Mukhtar din da ya jawo musu wannan bala’in.
Ta kalli yaran yadda sukai jigum har sun gaji da tambayarta mene ya faru sunyi shiru. A hankali ta rufe idanunta wasu zafafan hawayen suka sake saukowa. Ta goge su sannan ta mike. Da farko, jiri yaso dibanta kafin tayi gaining balance dinta. Dakin take ganu tamkar ba haske. Hasken rayuwarta ya barta, taya zata ga wani haske a duniya? Ta sake takawa amma sai gashi ta kusa faduwa saboda duhun da take gani a idonta.
Abdallah ya taso ya kama hannunta. Ta kalle shi sannan ta rike hannun nasa da kyau. Da gaske bata jin zata iya yin takun farko ita kadai. Ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a rai gami da shanye kukan da takeji ya kulle mata wuya.
Ta kalli sauran yaran cike da damuwa tace, “Muje, gidan aunty Halimah kafin Abie ya dawo.” Suka gyada kansu, mutum biyu kuwa suka zuba mata ido tunda da dan wayonsu sun san ba kalau ba. In ma gidan aunty Haliman ne Abien ne yake kaisu. Ta rasa yadda zatayi ne. So take taje can saboda kar yaran su fahimci abunda yake faruwa ba don tana tunanin zuwa gidan aunty Halimah mafita ce ba.
Hawaye ya balle mata wanda a yanzu bata boye ba daga idanunsu dake kanta.
Da kyar ta tausasa zuciyarta ta dena hawaye har suka fito bakin titi domin samun abun hawa. A sannan ta tuna babu kudi a hannunta. Wata zuciyar tace kawai ta tafi gida watakila in Mukhtar din ya ganta ya sauya hukuncin da ya dauka akanta.
Tana tsaye tana tunanin ta yadda zata kira wayarsa sai ga direban gidan yazo ya faka kamar yasan jira take. Ba tare da doguwar magana ba duk suka shige cikin Sienna da aka zo daukan nasu.
Kananan suka soma surutu musamman ma da Malam Idi direba ya mika musu ledar alawa. Abdallah yayi shiru yana kallon window yayinda suke tafiya gidan.
Mami Hafsah ta jinginar da kanta a jikin kujerar ta rufe idonta wanda a ranar babu abunda yake mata dadi kamar rufe idon. So take kawai ace mafarki take. So take ta bude idonta ta ganta zaune a gefen Mukhtar tana bashi abinci a baki suna dariya. So take ya zama ba gaskiya ba. Gwara mata ma ace ta sami matsalar da take sanya ta tunanin da ba daidai ba akan ace mata yinin yau da gaske ne.
Da gaske ne Mukhtar ya sake ta.
*****
Tuki yake a hankali saboda yasan idan yayi gudu ba karamin zagi zai sha ba akan titin ko ma yaje ya jawowa kansa asara da hakkin rai. Tunda yake a rayuwarsa bai taba tsintar kansa a yanayi makamancin wannan ba ko kusa. Bai taba yanke hukuncin da ya yanke masa wani sashe na zuciyarsa ba kamar wannan. Danshin gumin da ya zubo daga goshinsa yabi da kallo yaga yadda farar shaddar da ya sanya ta kwanta a jikinsa saboda zufar tunani da tashin hankali.
Zuciyarsa ma nauyi take masa idan ya tuna kalaman da ya furta dazu. Idan ya tuna kalamai ne amma sun fi adda kaifi. Sarai yana sane da yanayin da Hafsah ta shiga. Ba zai manta kalar dimaucewar da ya gani a kwayar idaniyarta ba sai dai kawai bashi da zabi.
Ajiyar zuciya yaso yayi sai dai ji yayi zuciyarsa tayi nauyin da ba zata iya abunda yake so ba. A dole ya nemi gefe ya faka motar gami da dauko robar ruqan dale gefensa ya fita daga motar. A gefen ya wanke fuskarsa sannan ya sha ruwan ko zaiji dadi. Sai dai babu wani sauyi da ya samu bayan hakan.
Akan trunk din motar ya zauna don ya samun sauki kafin ya cigaba da tukin. Sai da yafi minti biyar yana istighfari kafin ya koma cikin motar ya kunna sannan ya cigaba da tuqi. Kai tsaye gidan Salisu ya nufa domin bashi da wani waje da zaije ya samu sauki. Ko gun Salisun ma in yaji mai yayi sai ya mare shi amma zaifi bukatar jinyar radadin marin sama da radadin da yake ji a zuciyarsa.
*****
Ko da suka shiga falo, yaran suka watse sai taji gidan yayi mata wani mugun sanyi don har tsikar jikinta tashi take. A hankali ta nufi dakinta wanda ada babu inda yake sakata farin ciki sama dashi sai dai yau tana shiga kawai sai ta fashe da kuka. Bazata taba manta ranar da suka koma gidan ba.
Da yake ko da wasa bata taba sanin Mukhtar yana gini ba. Yana sane ya boye mata har sai ranar da ta haifi Ayman. Daga asibitin yayi mata albishir da push gift din da ya tanadar mata. Zata iya cewa gidan ya zamto kamar wani gishirin karin farinciki a zuri’ar tasu baki daya.
Ta matsa tana shafa gadon dakin wanda dashi aka yaudareta gaba daya tunaninta bai wuce zai sabunta mata kayan daki ba in ya samu wani contract da yake nema. Mukhtar bai taba boye mata komai ba sai don yana son yayi surprising dinta. A haka dai yayi ta boyewa ya sami contract din har sai da gidan ya kammalu ta ganshi sannan kuma nasarorin fa ya samu suka fito fili sosai. Waje ta samu ta zauna tana bin tunanin abubuwan da suka wakana a lokacin wai don ta gani ko shine dalilin rugujewar farin cikinsu a dan tsukin nan.
Kiran sallah ne ya katse ta. Tashi tayi, tayi alwala sannan ta fara gabatar da farilla, ta leka tayiwa yaran tuni kafin ta soma nafilfilun samun sa’idar ruhi da zuciya.
*****
Sallamar da Mukhtar yayi ce ta jawo hankalin yaran da suka zaune suna kallo a TV. Ayman kuwa a gabansa popcorn ne yake ci yana kallo. Kallon yaran ya dan sanyaya masa zuciya amma ganin basu taso da gudunsu ba yasa jikinsa ya kara sanyi.
“Hiii kids! Abie ya dawo, na dawo fa.” Ya fada yadda ya saba idan hankalinsu yana kan TVn da dole tasa aka saka musu screen time a rana.
“Sannu da zuwa Abie.” Sannan suka mike suka nufe shi yayin da Abdallah ya bi dayar hanyar ya bar falon. Mukhtar ya bishi da kallon mamaki amma sai ya mayar da hankalinsa kan wanda suke gabansa.
“Abie Mami kuka takeyi. Tun gobe take kuka.” Ayman ya fadi yana tabe baki tare da cika hannunsa da popcorn din.
Kursum ta dauka, “And she won’t speak to us. Ni wallahi ban bawa almajiri abinci na ba yau. Mami tace duk randa na bayar da abincin break dina zatayi rashin lafiya.”
Murmushi Mukhtar yaso yayi saboda yadda Kursum take magana in all her innocence. Ya sauke Ayman ya bar su a wajen don babu abunda zai iya ce musu a matsayin amsa. Kaf yaran duk yadda suke son shi, sun fi son Maminsu. In dai ba daga gareta suka ji ba, ba zasu taba yarda dashi ba.
Ko da ya karasa bakin kofar dakinta sai da bugun zuciyarsa ya karu sama da ko yaushe. Har ya murda kofar wani sabon tunanin ya doki kwakwalwarsa. Dole tasa yayi ya juya ya bar wajen kan sa yana bugawa ga idanunsa sunyi jawur.
Da kyar ta karasa adduar da takeyi ba tare da wani kukan ya subuce mata ba. Ba tare da ta cire hijabin ba ta nufi falon Mukhtar da niyyar sulhu. Ba zata iya ba. Ba zata iya rayuwa in babu shi ba. Ba’a yi ta don ta rayu ita kadai ba. Duk da kalaman da ya furta tamkar dafi ne a gareta ba ta sare ba.
Zaune ta hange shi ya kurawa ceiling ido yayinda karatun qur’ani yake tashi kadan kadan a falon. Jin karatun ya kara mata karfin gwiwa. Tayi sallama ta shiga ba tare da jiran amsar sa ba. A gefe ta samu waje ta zauna tayi shiru. Shima Mukhtar martanin shirun ya bata.
Sai da ta janyi ajiyar zuciya sannan tace, “Abu Abdallah…” yanda ta fada da sanyin murya yasa dago ya kalle ta har suka hada ido. Ganin yanayin da take ciki ya kara masa rauni sosai amma sai ya kauda kai gefe.
“Dan Allah…” bai bari ta cigaba ya daga mata hannu alamun babu wata magiyarta da zai saurara. Ganin haka yasa tayi shiru ta mike kafafunwanta ta rufe idonta. In ba zai saurareta yanzu ba, anan zatayi ta zama har ya samu lokacin da zai saurare ta din.
Sanyin AC din falon bai hana Mukhtar zufa ba. Sai da tattaro dukkan jarumtakar sa sannan a cikin kakkausar muryar da take nuna tsantsan umarni yake badawa yace,
“Ki kwashe yaranki ku bar mun gida na. At most, karfe bakwai na safe.”
Cike da tsananin mamakinsa ta bishi da ido hawaye suna fita a idonta.