Skip to content
Part 32 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

A rikice ta kalle shi Muktar ni kake kora, miƙewa ta yi duda jirin da ke ɗaukar ta ta ƙarasa gabansa ta hau laluben kwayar idanun sa, akai sa’a suka haɗa ido da sauri ya kawar da idanun sa yayin da tayi saurin kamo hannun sa, “dan Allah Abu Abdallah ka tsaya mu fahinci juna.”

Fincike hannayen sa ya yi “na faɗa miki gobe ki tattara su ku tafi na riga na gama magana, kin fi kowa sanin innace bana janyewa,” ya faɗa tare da yin gaba.

Tashin hankali tuni ya rikitata cikin ruɗu tace “inje ina da su, inni ka koreni kana nufin suka ka kore su ko me?”

Cak ya tsaya kafin ya juyo, “ai adalci na miki, matsayin uwa, in tani ne   ko jariri ne abarmin abuna,” ya faɗa cike da kwarin gwiwa kafin ya yi sauri ya bar wurin, yayin da ɓacewar sa da bugo ƙofar ɗakin da ya shiga yasa Hafsa zubewa tare da rushewa da kuka, Abdallah da  yake tsaye nesa da su, shigowar sa falon shine dai dai lokacin da Muktar ya wuce ɗaki fuu, yayin daHafsa ta zube da sauri kuwa ya ƙaraso wurin, “Mami mai ya faru?.”

Duk yadda taso ta daina kukan kasawa tayi, duda bata son yaranta suga gazawar ta, sai dai yau ita da kanta tasan ta gaza, ta kasa wani kwakkwaran tunani, hannun da Abdallah yasa yana goge mata hawaye ya dawo da ita hankalin ta sosai, ganin ta yi shiru yasa yaron kamo hannun ta, “dan Allah Mami kiyi haƙuri ki cire damuwar Abie a ranki, koma maine nasan ba laifin ki bane, kuma zai fahinci haka in sha Allah zai yafe miki.”

Murmushi ta yi tare da cewa, “Allah yasa Abdallah,” shima murumushin ya yi “bari inje in bashi haƙuri,” kasa cewa kar yaje Hafsa ta yi, sakamakon kwarin gwiwa da ya ziyarce ta, lokaci guda zuciyar na ta faɗamata watakil in yaran sa suka bashi haƙuri ya tuna yanzu fa akwai mutane tsakanin su, watakil ya tuna yanzu fa rayuwar ba tasu bace su kaɗai, bin Abdallah ta yi da ido lokacin da yayi hanyar ɗakin Baban nasu.

Miƙewa ta yi tare da sa hannu ta ɗauki wayar ta kai tsaye ɗakin ta ta nufa, wayar Bilkisu ta hau nema, ta jima tana kallon Number ɗin da ƙoƙarin kira sai dai hannun ta ya kasa danna kira, cilla wayar tayi kan gado tare da kwanciya a dandaryar tiles.

Muktar da ƙafafun sa ke rawa, ƙwarin gwiwar sa ke ƙoƙarin barin sa, na shiga ɗaki banko ƙofar ya yi tare da zubewa a wurin numfashin sa na fita da sauri, yayin da jarumtar sa ta kasa riƙe masa hawayen sa, a hankali yake furta “innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,” Allah ma ya sani yana son Hafsa sosai bai kuma san son yakai haka ba bai san ta wuce jini da tsokar sa ba, sai da ya furtar sakin nan.

Abdallah ya jima bakin ƙofar ɗakin kafin ya shiga, kasancewar ba ɗabi’ar su bace shiga ɗakin iyayen su in dare ya yi. Da sallama ya shiga wannan yasa Muktar saurin goge hawayen sa Abdallan ya yi saurin ƙarasawa “Abie kaima kukan kake?”

Girgiza kai Muktar ya yi “ba kuka nake ba,” kamo hannayen sa Abdallan ya yi tare da ƙokarin mikar da shi tamkar zai iya wannan yasa Muktar mikewa ya bi yaron nasa wanda ya zaunar da shi gefen gado kafin ya durkusa gaban sa riƙe da hannayen sa tamkar wani ɗan shekaru talatin ko fi, a hankali cikin sanyin muryar sa ta yara yace “Abie dan Allah kayi haƙuri ka yafewa Mami dan Allah.”

Kallon sa Muktar yayi kafin ya ce “ita ce ta ce ma ta yi mun wani abu?,” Girgiza kai Abdallah ya yi da sauri “ba ita bace kawai tun jiya da mukaje asibiti naga kamar tama wani abu ne.”

Muktar yasani Abdallah akwai kaifin basira tun yana yaro, sosai yake gane abubuwa bare yanzu da ya fara zama mutun, a ƙoƙarin sa na son ƙin saka yaran su cikin matsalar su yasa shi cewa “Abdallah cikin kaushin murya dubu agogo yanzu yo 11 bana ce duk inda 10 ta yi ba ya zama kun jima da bacci what are you doing outside?”

“Walllahi na kwanta Aiman ne ya tashen zai yi fitsari da nakai shi yayi shine kuma yace zai sha ruwa, shine na fito ɗibar masa, tsai Muktar ya kalle shi ba alamun ƙarya yaron yake ko da yake yasan Hafsa tama yaran su tarbiyya sun san aibun ƙarya sosai, shi ina Yayan ku Faruk da bazai fito ya dibar masa ba eyyi.

“Yayi Bacci kuma yace zai daki duk wanda ya tashe shi.”

“Maza ɗebi ka kai masa, shi yasa nake cewa kan ku tafi ku dinga tafiya da ruwa da abincin Aiman ɗin, tunda kunsan halin sa,” Muktar ya faɗa tare da miƙewa yana ƙoƙarin cire Babbar rigar saman sa, miƙewa Abdallah ya yi har ya kai bakin ƙofa sannan ya tsaya, “Abie dan Allah ka yafewa Mami,” cikin tsawa ya juyo “zaka tafi ka kwanta ko sai nazo na make ka,” da sauri ya bar ɗakin a tsorace dan shi kam ko da wasa ba zai iya tuna sanda Abie ɗin su ya musu tsawa ba.

Ganin Mami bata falon yasa shi zuwa fridge ya ɗebi ruwan a cup tare da ɗaukan yogurt ya yi ɗakin nasu, Aiman na zaune kan gadon Abdallan ya yi tsuru tsuru, duk tsoro ya cika shi duda ga Faruk kwance yana bacci yana ganin Abdallah yasa dariyar murna, shii! yace masa ahankali yace kar yaya ya tashi.

Ruwan ya bashi ya sha sannan ya miƙa masa yogurt din “ungo jeka gadon ka sha”, kallon gadon nasa ya yi kafin ya maƙale kai “ya ni tsoro nake ji,” Abdallah bai ce komai ba ya kwanta Aiman ya maƙale jikin Abdallan yana kurɓar madarar sa, sai da ya sha da yawa sannan ya taɓa Abdallah “yaya Abdallah rufe mun,” amsa kawai Abdallah ya yi ya rufe tare da ajewa gefe. Munsharin Aiman da yaji yasa shi miƙewa ya ciccibe shi ya dora shi gadon sa, kafin ya koma ya kwanta idanun sa kawai ya rufe cike da damuwar tunanin ya Mamin su take ciki in banda dare ya yi da sai yaje ya gani ko ta yi bacci ta dena kukan.

Washe gari da sassafe Hafsa ta tashi, ko wanka batai ba ta zura doguwar riga ta fito daga ɗakin ta a falo suka haɗu da Muktar da alamu daga masallaci yake, dan ta san in yana cikin damuwa sai gari yayi sha yake dawowa bayan yayi Addu’oin sa.

Kawar da kai ya yi kamar bai ganta ba, yayin da ita kuma cikin shaƙaƙƙiyar muryar ta da ya sha kuka tace “Abu Abdallah ina kwana?,”

” Lafiya ƙalau yace, mai ya samu muryar ki?, Hafsa karfa ki sa damuwa ta illata ki?, kalmomin da ke cikin zuciyar sa suka sauka laɓɓansa tare da bada sauti.

Ranta ne ya ɓaci, shi yanzu har yana da bakin ce a kar ta damu bacin shi ke da damar yanke mata damuwar, sai dai kafin ta ce wani abu ya wuce ranta ya kuma ɓaci, kwafa ta yi tare da yin ɗakin yaranta duk suna bacci dama ta sani indai suka dawo daga sallah in ba makaranta bacci suke komawa indai ba tare suka dawo da Baban su ba, in tare suka shigo ne yake sasu suyi Musaffa tare da shi.

Tausayun su ya kamata, a hankali ya shafa kan Aiman katin ta juyo ta fito, zuwa harabar gidan motarta ta shiga bayan ta buɗe gate a nutse ta fice daga gidan ta fito ta rufe.

Muktar da zuciyar sa ke tunzura shi yaje ya rungume matar sa ya ce mata ba komai, yace mata komai ba komai bane ya janye sakin ya zube ƙas zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri lokacin da Hafsan ta rufe gate ɗin da ta buɗe, tunda ta fito a kan idanun sa

Ta jima a bakin hanya kanta bisa sitiyarin motar cike da tunanin ina zata, Bilkisu ce ta fado mata a rai, kai tsaye ta murza sitiyarin motar zuwa gidan Bilkisun bugun da ta yi ba’a ɓude ba yasa ta fara kiran Hafsan kafin ta ɗaga mai gadi yazo ya buɗe, cikin rawar murya yake bata hakurin bai san ita ba ce ta ce ba komai tashiga harabar gidan.

Bilkisu da ke kwance gefen Tariq tana Bacci motsin wayar ta ya tashe ta a hankali ta miƙe ta ɗauka ganin sunan Hafsa na yawo jikin screen yasa ta ɗauka “Hajiya da sassafe haka?”

Hafsa da ke tsaye a harabar tace “ina harabar gidan ki” da sauri Bilkisu ta fito Tariq da ya farka tun sanda ta amsa wayar ya yi saurin bin ta a tsorace dan bai san mai ta fitarwa haka ba.

Yadda Bilkisun taga Hafsa ya tsorata ta, idanun ta sun kunbura, fuskar nan ta yi jarir alamun ta sha kuka iya kuka, rigar jikin ta duk ta yi alamun rashin guga, yayin da ita kuma Hafsan tana ganin Bilkisu kukan da take boyewa ya kwace mata, da sauri Bilkisu ta ƙarasa ta rungume ta, tana lallashin ta.

Tariq da ya biyo Bilkisu ya juya zuciyar sa cike da tunanin mai yasa Hafsa kuka haka, mai ya baro da ita daga gidan ta da sassafe haka, ya jima a tsaye a ɗakin sa kafin ya shiga bathroom.

Dakyar Bilkisu ta samu Hafsa ta dena kukan, kamo hannun ta tayi “dan Allah Hafsa ki faɗamin mai ke damun ki karki sa curiosity yasa zuciya ta bugawa ina cikin ruɗani.”

“Muktar ya sakeni ya ce in bar masa gidan sa” ta tare da rushewa da kuka.

“Innalillahi wa’inalaihirraji’un saki Hafsa dan Allah ki cemun ba gaskiya bane, dan Allah Ki ce mun mummunan mafarki nake” Bilkisun ta faɗa.

“Nima abinda nake son ji kenan, nima so nake in samu mai tashi na daga wannan mugun baccin.” Hafsan ta faɗa tana cigaba da kukan ta.

Dafe kai Bilkisu ta yi tama rasa mai zata ce, saki fa kuma Muktar ya yi, lallai maza abin tsoro ne ita kanta Soyayyar da yakewa Hafsa na birgeta, anma ace shi yayi saki, itakam da badan Hafsan ta faɗa mata tace shi yayi sakin ba tabbas ba zata yadda ba.

“Bilkisu ki faɗamun mai zanyi yace in tafi.”

Ran Bilkisu a ɓace yake, takaici da Haushin maza duk ya cika ta, cike da ɓacin rai tace ” Hafsa ai ko baice ki tafi ba in yace ya sake ki yana nufin ki tafi, in baki tafi ba mai zaki masa?”

“Nasani Bilkisu kawai bana son gida suji su tsani Muktar.”

Numfashi mai nauyi Bilkisu ta furzar, “ni dai magana ta gaskiya da zan faɗa miki shine ki kwashi yaran ki ku tafi gida, ko ki je gidan Yaya Sadik kiyi Idda can duda dai kin san zaman ki can lokaci kaɗan ne gidan sun sani.”

“Bilkisu mai zanyi ya mayar dani shi nake son ji.”

Dafe kai Bilkisu ta yi tasani kome zata ce Hafsa ba zata fahinta ba, so sa ƙaunar Muktar sun riga sun rufe mata idanunta.

Kamo hannun ta tayi “Hafsa ki nutsu ki buɗe idanun ki abinda zai sa Muktar ya sake ki tun jiya yaƙi maida ke banji zai mayar, indai ba zama zakiyi gidan sa kiyi idda ki cigaba da bashi haƙuri ba ba wata mafita, ni bama na baki shawarar zama Allah ma yasani, inda kin ɗebo yaran ki da yanzu Bama zaki koma…..

<< Ko Da So 31Ko Da So 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×