Skip to content
Part 35 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Abba yana shiga dakin ya tarar da Hafsah sai kuka take ita kuwa Mummy ta inda take shiga sam ba tanan take fita ba. Ya sani katse ta zai kara tunzura ta shiyasa ya nemi waje ya zauna. Hafsah ta kalle shi zuciyarta na dada karyewa don tasan zancen sai ya fi karya masa zuciya sama da Mummy saboda yadda ya yarda da Mukhtar sosai. Ta kauda kai kafin su hada ido a sannan Abban yayi gyaran murya.

“Wai me yake faruwa ne na zauna amma sai babatu kike tayi na rasa ta inda zan kama zancen.”

Mummy taja tsaki. “Wannan yaron ne ya sake ta.”

Zuciyar Abba tayi wani mummunar faduwa, tamkar ma ta rabe biyu yake ji. Da kyar ya yi jarumta yace,

“Toh lefin Hafsah ne naga kinsa ta gaba zaki cinye ta danya maimakon naga akasin haka?”

Mummy ta girgizan kai saboda takaici. “Tsabar shi butulu ne ita kuma doluwa ce wai yace ta dauke yaran kuma ta kwaso su…” ta dungurewa Hafsah kai.

Abba ya mike. “Ya isa haka Hadiza.”

Mummy bata ji ba ta cigaba. “Tun baida sisi muka bashi ya, muka rufa masa asiri shine yanzu zai bude mana namu ai wallahi bai isa ba. Shiyasa sam ni bana son talaka don duk randa yayi kudi sai ya nuna bakin hali. Kai takaici ba zai kashe ni ba yau…”

Abba ya lalubi aljihunsa ya ciro mukulli. “Kince dama zakije boutique, a dawo lafiya.” Da haka ya samu yaja Hafsah har falonsa ya zaunar.

Ya kira Sadiq. “Kazo ka dauki yaran Hafsah su wuni wajen ka.”

Cikin mintuna talatin gidan ya dauki shiru sannan Abba ya kalli Hafsah.

“Ki hutawa ranki. Ki kwanta kiyi bacci. Zuwa dare in kowa ya danyi sanyi zamuyi maganar.”

*****

Yanma lis Mum ta dawo, kusan kamar tare suke da yaran dan sunƙi zama gidan Sadik ya dawo da su. Abba yana dawowa daga Masallaci yace Mum da Hafsa su same shi a falon sa.

Tsananin nauyin dake zukatan mutum ukun da suke zaune falon Abba ya zarce misali. Ga wani shiru da ya mamaye falon tamkar babu mai numfashi a wajen. Ko wannen su, kwakwalwarsa cike take da tunanin kala kala game da al’amarin da ya tunkare su yau da safen nan. Da zare zai fadi, tsaf wani zai iya jin kararsa domin ko Hafsah dake durkushe a gefen Abba hannunta kan gwiwowinsa, kukan ta bai da sauti.

Zafafan hawayen ciwon rai ne kawai suke ta faman wanke mata fuska. Idanun nan sunyi kanana sun koma ciki, ga fuskar tayi fari tas, ta yi fayau abun tausayi.

Abba ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya domin ya kawar da shirun da yayi yawa a wajen yace,

“Hadiza kiran sa ya ɗauke yaran nan ba maslaha bace…” Mummy ta tura kai gefe, zuciyarta tana kara ruruwa da haushin Mukhtar. A duk sanda aka soma maganar sai taji tsanarsa tana qara shiga ranta. Wayewar gari daya kawai ya tashi ya mayar mata da ya bazawara. Abun baƙin cikin ma wai duk wannan kukan da Hafsahn take yi bai hana shi janye zancen ba. Sannan yace ta haɗa da yaran kamar dama dasu aka kaita. Don kawai tsabar maqo dan kawai ya ɗaukewa kansa wahalar ciyarwa, sam wannan baƙin hali.

Hafsah ta ɗago dafaffun idanunta ta sauke su akan Mummyn tana jirar amsa daga gareta amma sai tayi kamar ma ba ita akayi wa magana ba. Sanin halin ta ne ya sanya Abba bai sake maimaita maganar ba ya shafa kan Hafsah yace,

“Muje ki kwanta ki hutawa ranki. Wannan ba wata babbar matsala bace da zaki bi ki tadawa kanki hankali. Every problem has a solution.” Ya mike riqe da hannun Hafsah har zuwa tsohon dakinta inda ya tarar kaf yaran sun kwanta a gadon. Ya kalle su a takure da junansu, kwalla ta kusa kwace masa amma ya dake ya nuna mata sallaya.

“Addu’a makamin mu’umini. Ko raka’a biyu ki daure kiyi. Allah ya miki albarka.” Amsar da Hafsah ta bayar a makoshin ta ta tsaya saboda yadda muryarta ta dashe. Ta je tayi alwala sannan ta tada sallah.

Abba yana fita Abdallah ya daga kai ya kalle ta a cikin duhun saboda kashe musu fitila da akayi. Yaga sallah take yau babu hawaye sai ya koma ya kwanta amma duk yadda yaso yayi bacci ya kasa. Yasan idan Mami taji idonsa biyu ranta zai baci, hakan yasa ya sake rintse idonsa yana karanta ayatul kursiyy don baccin ya kama shi.

Ko da Abba ya koma falonsa inda Mummy take zaune tana karkada kafa ya kalli agogo yaga har yanzu takwas ce tayi. Ranar tayi musu wani irin tsawo gashi anyita cikin tashin hankula da tunani. Ya tausasa muryarsa sosai amma sai ya sanya amonta ya zama umarni yake badawa ba wai lallabata yake da niyyar yi ba.

“Yaran nan a nan zasu zauna zuwa har sanda zan yanke hukunci. A yanzu ba zan iya zartar da ko wani irin hukunci ba saboda zafin da zuciyoyin mu suke ciki. Zan kuma kira Mukhtar yazo ya same ni amma ba gobe ba. Bana so na sake ji kin daga zancen nan…”

Hawaye suka wanke fuskar Mummy. Ta goge sannan ta kalli Abba. “Tsakani da Allah abunda yaron nan yayi ya kyauta mana? Haba don Allah saki fa ba wani dalili kwakkwara…”

Abba yayi shiru ya mike kafafuwansa alamun ba zai amsa mata ba.

Bata hakura ba. “Wallahi shiyasa tun farko na gaya maka talaka bai da rana…”

Abba ya bita da kallo, tunanin sa yana wanawa zuwa wasu shekaru da suka shude. Watakila matsalar ma daga nan ta soma. Shekarun baya tun kafin a haifi Hafsahn…

*****

Mukhtar ya yi sallama a empty falon wanda bai taba shigowa yaji shi tsit ba. Ko yaran basa nan Hafsah tana nan, in bata nan wata a kannensa tana nan. Yau ne ranar ko daren farko da zai fara yi a gidan cike da zulumi da dumin rai. Ya shiga dakin sa ya yi wanka sannan ya hau gado ya kwanta. Rufe idonsa ke da wuya hawaye suka fara zuba a idonsa, bai hana su ba domin yanzu su kadai ne zasu rage masa ciwon da yake ji. Ya rasa ta inda zai soma. Gana daya ji yake rayuwarsa ta rasa direction da magnitude. Tun safe yake jiran dare yayi ko dan ya samu ya runtsa kafin wata safiyar tayi ya san abunyi don a yau ma ya rasa tunanin yi. Ga Inna ma sam bata bashi wani goyan baya ba. Kwata kwata ma.

Yaso yaje yaji ta bakin Rashida amma a yanzu baya bukatar shawarar da zata kawo masa mishikila ko ta sake hargitsa masa tunani.

Filo ya janyo ya rungume cikinsa saboda yunwar da take kwakwalar hanjinsa amma sam baya son tauna komai. Har sanyi sanyi yake ji. Ga yunwa ga kewar yaran. Bai manta maganar da sukai da Faruk ba kafin su tafi da safe wanda sam yaki bari ya fito su hadu da Bilkisu.

“Abie me yasa zamu tafi? Me Mami tayi maka?”

Mukhtar din bai manta yadda tambayar tayi masa saukar aradu ba. Da kyar ya bada amsar da baya jin amsar ta kyautu.

“Ba abunda tayi min kawai bana bukatar kowa ne yanzu.” Bai manta yadda Faruk din ya kalle shi ba. Kallon da zai ce bai taba ganin ko tsammanin yaro zai iya yinsa ba ko da kuwa an bata masa rai ne sosai. Sai dai yana ji a jikin sa wannan amsar da ya bayar ta samu mazauni a zuciyar yaron nasa wadda har ya mutu ba zai yafewa kansa ba na gayawa Faruk haka. Faruk din baice komai ba ya fice. Bayan sannan Mukhtar yana leken su har suka fice kuma bai ga alamar Faruk ya gayawa Abdallah ko Maminsa ba. Da alama shi kadai zaiyi jinyar kalaman.

Mukhtar yaji kamar ya fita daga gangar jikinsa ya zane kansa na kurakuren da yake ta tafkawa. Ya janyo wayar sa yaga karfe tara. Yayi tsaki ya kara komawa farkon gadon yana rufe idonsa inda hawaye suka cigaba da zuba a idonsa.

“Dan Allah kar kayi mana haka…” ya tuna muryar Hafsah tana rokarsa amma sam ya rasa me ya hau kansa ya kasa janye kudurinsa. Ya tuna ko bayan nan ta sake zuwa rokarsa bai saurareta ba kuma ko yanzu baya jin zai iya dawowa da ita. Anya kuwa ba aljanu bane suka hau kan zuciyarsa suka danne masa bangaren tausayin Hafsahn sa ba? Sannan suka hana shi yayi mata yadda take so ya dawo da ita?

“Wallahi na fika son ka domin ni babu wani dalili a duniya da zai sa na barka sai mutuwa. In dai rana da wata suna haskawa kuma ina numfasawa, wallahi son ka yana nan daram a ruhi na. Da ruwan sonka aka hallice ni Mukhtar. Dan Allah ka min alkawarin mutuwa ce zata raba mu…”  kalaman Hafsah ko yaushe basa gazawa wajen nuna masa soyayya. Ya sani yana son ta, tana son shi sai dai kawai zaman ne ya hakura dashi. Ba zai iya ba. Abun ya masa yawa. Gara ya sota daga nesa kawai.

Mukhtar ya cigaba da tunani da fatan cewa bar mata yaran da yayi ya zama sassauci a gareta don yasan soyayyar dake tsakanin su mai girma ce ba kuma zai so ace tunda ya datse wadda take tsakaninsu ba ya datse ta yaran ma.

<< Ko Da So 34Ko Da So 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×