Skip to content
Part 37 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Soyayyar Mukhtar a jinin ta take, a zuciyarta take. Duk yadda taso ta yakice son shi daga ranta ta kasa, daina kuka abun ya gagareta. Cike take da haushinsa amma duk da haka zuciyarta da shi take bugawa a ko wanne sakan da yake wucewa. Nisawa tayi tana sosa idanunta wanda yanzu sun gaji sun bushe. Ta kalli agogo taga biyun dare. Mikewa kawai tayi ta tafi daura alwala. Ko da ta dawo tayi raka’a biyu sai ta janyo wayarta ta buɗo messages dinsu da Mukhtar ta soma karantawa cike da kewar sa da ciwon rai.

Ke zan zaba a ko da yaushe. In an bani zaɓi tsakanin kaina da yaran mu da ke. Ba ki da mahadi a waje na.

Ta karanta message dinsu na karshe. Sakon ya bakanta mata rai, ya sosa mata zuciya. Ta rasa abun yi don hawayenta sun kare. Ko sati ba a yi ba ya tura mata wannan. Ashe dama shima makaryaci ne kamar sauran maza? Duk tsahon rayuwarta dashi ta yarda da cewa shi din ya fita daban da kowa ashe duk kanwar ja ce.

Zuciyarta ta cigaba da harbawa cikin tsananin haushin kalaman nasa kamar a lokacin ya fade su.

Ta fara typing.

“Na tsane ka Mukhtar, makaryaci kawai.”

Har zata tura sai ta goge. Shiru tayi ta ajiye wayar kafin ta sake ɗauka ta budo chat board dinsu again.

“Ko babu igiyar auren ka a kaina, ina kaunar ka. Ko ka tsane ni, bazan dena sonka ba, ƙaunar ka ta riga ta zame mun jini da tsoka.”

Ta jima tana kallon message din da ta tura masa kafin barawon bacci ya sace ta.

*****

Zaune yake yana juya shayin da ya hada wanda har ya huce bai fara sha ba. Babu abunda yake masa daɗi a zuciya da duniyar ma baki daya. Hafsah itace farin cikin rayuwarsa kuma da kansa ba tare da zugar kowa ba ya datse farin cikinsa. Har yanzu ya rasa inda zai dafa. Ji take gaba daya purpose dinsa a rayuwa ya gushe. Dama Hafsah ce alkiblar dukkan wani abu da ya shafe shi. Itace sila da dalilin komai. Sai dai yanzu da ya yanke alakarsu, bashi da wata madafa. Bashi da wani direction. In yaje aiki ya dawo sai ya rasa abunyi.

Sosai yake cike da kewarta amma in ya tuna dalilin da ya sanya shi yanke hukuncin nan tsakanin su sai yaji ba zai iya chanja ra’ayi ba, abu ɗaya ke ƙara ƙarfafa masa zuciya shine ko da so a zukata biyu dan ba’a tare ba’a fasa rayuwa, ya yadda Hafsa da shi a sannu a hankali zasu gudanar da rayuwar su tamkar ɗayan bai taɓa shiga rayuwar ɗayan ba. Rashin ta ba karamin horo bane a gareshi amma duk da haka ya zabi ya jure. Ba zai iya janye kalaman sa ba.

Shayin ya sake kalla wanda shine abincin sa a kwanakin nan ya daga kofin ya shanye. Salam yaji shi kamar yadda rayuwarsa yaji tayi salam. Agogo ya kalla yaga lokaci sannan ya mike yana nemo wayarsa inda ya ga sako ya shigo tun tuni bai duba ba.

A nutse ya buɗe wayar idanun sa suka faɗa kan saƙon Hafsa da ke yawo kan screen,Sai da ya ji zuciyarsa tayi wani irin dokawa a kirjinsa kafin ya zura wayar a aljihu ya tafi aiki.

A hanya zuciyar sa fal take da tunanin saƙon yayin da can ƙasan ransa ke cike da farin cikin me ya karanta kalaman sun masa daɗi…

*****

A nutse Tariq yake sakkowa daga saman sa yana ɗaura agogo ya yi kyau sosai idanun sa ƙyar bisa Bilkisu da ta rafka tagumi idanun ta kan TV duk sai yaji nutauwar sa ta masa ƙaura da sauri ya ƙaraso wurin yaɗan lafota jikin sa bayan ya zauna, cikin murya ta mai son kuka ya ke magana “wai dan Allah Habibty mai ke damun ki?, Karfa kisa hawan jini ya kama ni, da mai kike so inji da tunanin damuwar ki ko da tawa damuwar na abar sona ɗaya dana bawa raina bata yadda dani, ba zata iya daɗan damurta ba?”

Ƙara lafewa ta yi jikin sa, cikin muryar shagwaɓa tamkar wata ƙaramar yarin ya tace haba Zaujey wai kaima cikin damuwa kake?” Ɗan ture ta ya yi na wasa “kema kinfi kowa sanin cikin damuwa nake, kalli yadda na rame fa”

Tsai ta kalle shi da gaske ya ɗan faɗa, a hankali ta kamo hannun sa, ka daina damuwa ba kai bane kasani damuwa tunanin halin da Hafsa ke ciki nake nasan halin ta inta sawa zuciyar ta abu, ni kuma ba iya zuwa zan kullum ba dan lallashin ta” kaf ya maida hankalinsa kan Matar tasa, yasan Hafsa. Nada matsala tun randa tazo da sassafe sai dai shi ba gwanin tambaya bane, yayin da ita kuma Bikiisun ba gwanar bashi labarin sirrin wasu bace.

A hankali cikin kasalalliyar murya mai cike da takaici Bilkisun ta ce “Muktar ya saki Hafsa”

Wani abune da baisan mene ba ya ziyarci ransa, A ruɗe Tariq yace what Saki kuma anya Habibty ba Mafarki kikai ba ya faɗa a ruɗe.

Girgiza kai ta yi “wallahi ba mafarki bane ya sake ta” ta kuma jaddada abinda ta ce

Cikin tashin hankali yake fadin “innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, saki fa, yaushe Muktar ya fara shaye shaye, waye ya faɗa masa har yanzu muna zamanin da ake saki, ya kuwa san me yake anya?…”

Yadda taga ya zage yana ta banbamin masifa kan sakin sai ya kwantar mata da hankali, Tariq ɗin da ke gaban ta yanzu bai mata kama da mutumin da zai iya banzatar da ita ya sake sakin wulaƙanci irin na Hafsa ba maras dalili.

Sun jima suna tattauna kafij ya ce ta je ta shiryo kar su makara, dan yaga yau ba zata iya tuƙin ba, miƙewa ta yi zuwa ɗakin ta kasancewar tayi wanka kaya kawai tasa suka bar falon a farfajiya ma shi ya buɗe mata gaban mota suka wuce.

A Faculty of Agriculture ya faka motar inda take PHD ɗin ta, kamar ko yaushe da hanzari ya fito tamkar wani driver ya buɗe mata Madam mun ƙaraso ya faɗa yana murmushi, tare da miƙo mata hannu, shamiƙe hannun ta tayi ” kai dai baka girma wallahi kwanan fa zaka fara surukai matsa ni in fito,” Dariya yasa ” ni ina ruwana da surukai, in dai ina tare da ƴar yawalwalar matata to tsufa bani ganin sa.”

Girgiza kai ta yi “tom sai na dawo,” ta faɗa tare da yin gaba cikin ƴar muryar so da ya saba mata yace nifa ba’a sallamen ba, juyowa ta yi tana murmushi tasan me yake nufi, aikuwa sai dai ka kwan anan ta yi faba ko me ta tuna sai ta juyo ” na manta in na fito da wuri zani gidan su Hafsa,” ta faɗa kawai ta yo gaba.

Murmushi yasa yabar wurin yasan Halin Abarsa in zai ɗige a wurin ba zata masa kiss a public waje ba, sai da ya ja motar sannan tunanin Hafsa da mutuwar auren ya dawo masa rai.

Wurin biyu Bilkisu ta isa gidan su Hafsa Mum bata nan, dama bata yi tsammanin ganin ta ba, tasan Mum da neman kuɗi, yaran duk sunyi jigum jigum a falo da alamu lokacin suka dawo daga boko, Aiman na ganin ta ya hau murma, cike da girmamawa suka gaishe ta, “lafiya Faruk ina Maman naku” ta tambaya.

“Anutse ya ce tana ɗaki tace kar mu dame tane” shiru Bilkisu ta yi kafin tace kunci abinci ne?”

Abdallah ne wannan karan ya yi magana, “a’a Mamin muke jira ta dafa, jiya Mum tace kar mu sake mu shiga kitchen mu haɗa mata gobara in Mami ba zata dafa mu ƙarata…” Ko mai ya tuna sai ya yi shiru.

Ajiyar zuciya Bilkisu ta yi tare da yin ɗakin Hafsan, wadda ke kwance tana kallon sunan Muktar da message ɗin da ta tura masa jiya, gashi dai alamu sun nuna ya gani anma reply yaƙi shigowa.

Jin alamun an shigo ɗakin yasa ta ɗago a fusace wai “Abdallah dan Allah mai kake so dani ne?, Nace ka kyale ni bana jin daɗi.

<< Ko Da So 36Ko Da So 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×