Skip to content
Part 38 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Cike da ɓacin rai Bilkisu takara cikin ɗakin tana faɗin ” to ba shi bane haba Hafsa ina kike son kai hankalin ki, anya kuwa, akan namini kike son kassara kanki da kuma rayuwar yaranki?”

“Please Bilkisu….”

Ɗaga mata hannu Hafsa ta yi tare da dakatar da ita, “karki faɗa min komai dan ba zan fahince ki ba, bawai dan ni ban shiga yanayin da kike ciki ba, a’a sai dan kin fara ƙoƙarin fita hayyacin ki da sunan so, haba ke bama zakiyi tunani ba, ai saki ba kanki farau ba, ko shi Muktar ɗin kika kalla ya dace ki gane cewa zaki iya rayuwa ba shi yadda ya rufe idanu ya nuna ba zai rayu da ke ba, ko wannan kika kalla kyama kanki faɗa kema ki nuna masa bashi da gurbi a rayuwar ki”

Cikin kuka Hafsa ke magana ” Wallahi Bikisu ba zan iya ba, ina son sa kema kin sani…”

Tsaki Bilkisu taja tare da takawa inda Hafsan ta ke ta, gefen gadon ta zauna tare sa kamo hannun Hafsan ranta cike da Haushin Hafsan itakam ta rasa wannan wanne irin rashin tawakkali ne, ba kuma tasan lokacin da aminiyar tata ta koma haka ba, ” Dan girman Allah Hafsa ki daure ki buɗe idanun ki, ki kalli rayuwa ko dan yaranki, ki bar su, suji da damuwar rabuwa da kukai ba sai kin ƙara musu wani tashin hankalin ba, ina tabbatar miki wannan abin da kike shin zai ƙara ingiza damuwar su”

Shiru Hafsa ta yi tamkar da gaske tana ɗaukan shawarar Bilkisun sai dai a ranta mita take na dan dai ba ita Bilkisun Tariq ya saka ba, shi yasa take kuri sa cika baki.

Ganin tamkar ta ji maganar ta yasa Bilkisu sakin Hannun ta tare da cewa ni dama zuwa nayi in ce miki an buɗe portal za’a fara registration na post graduate dan ki ɗebewa kanki kewa gwanda ki nemi MS ne kizo kiyi fitar zata sama miki sukuni arai.

Cike da damuwa Hafsa tace “Masters kuma, ni yanzu na yi applying wani abu nan kusa, kar sanadin Haka yasa Muktar ko yayi niyar mayar dani ya fasa, kinsan sabida shi naƙi ci gaba da karatun na kuw ƙi neman aiki”

Wani ƙulu ƙulun takaici ne yazo wuyan Bilkisu ya tsaya tsaki taja mai karfi tare da miƙewa ta harari Hafsa ta yi waje kawai, ba tare da juyowa dan sauraron kiran me Hafsan ke mata ba”

A falo ta tarar da yaran suna kallo, kamar yadda tazo sun takure da alamu ma ba fahintar kallon sike ba, ta kuma jan ɗan karamin tsaki tausayin yaran ya cikata, sai dai mahaifiyar su ta mance da su, Faruk ne yace “Ummi har kin fito”

Murmushi ta yi “eh na fito, nabar su Jawahir su kaɗai,” Aiman ya taso da gudu ni zan biki gaskiya, batai musu ba ta ce Abbadallah ya ɗebo masa kayan sa.

Amsar kayan ta yi, tare da riƙewa yaron hannu sukai farfajiya.

Hafsa bata shirya amsar gaskiya ba, ta zaɓi son zuciyar ta, fiye da zahirin rayuwa, ko Tariq Bilkisu bata kira ba dan yazo ɗaukan ta, titi ta nufa dan bata son ma Hafsan ta fito su tattanka, yadda take jin Haushin ta tas zasu yi rikici.

A ƙofar gate din gidan ta aka ajiye ta, bugu guda Mai gadi ya buɗe, kan ta shiga Aiman ya faɗa gidan da gudu Mai gadi yahau yi mata sannu da zuwa.

“Aunty Jawahir nine fa nazo” Aiman ya faɗa lokacin da ya shiga falon da gudu yana murna, Jawahir da ke faman danna waya ta miƙe tana dariya, Darling A welcome” ta faɗa tana ware hannu ya faɗa jikin ta suna dariya.

Walida ce ta harare su, kun cikani da ihu, ta faɗa da salon wasa, Aiman ya kalle ta lah ashe Aunty Walida kina nan shima da tsokanar, kuma harar sa ta yi, “to da ina zani Aimanu?” Turo baki ya yi ni ba sunana Aimanu ba ko yaya Jawahir.

Murmushi Jawahir ta yi kyale ta Darling A, wai dan kafi sona take kishin, gyaɗa kai ya yi irin ta yarin ta yana Murmushi.

*****

Suna zaune baka jin sautin komai sai na Tv da fanka, Kursum ta dubi yayin nata “ni gaskiya nima ku kaimi gidan Ummi, mai yasa baku kirani na lokacin da zata tafi da Aiman.”

Harar ta kawai Abdallah ya yi in da shi kuma Faruk ya ce “sai ki tashi ki bita ai, karki kuma mun magana” sanin halin duk su biyun yasa yarinyar sunkuyar da kanta zuwa abinda take kan tayi maganar tana murmushi.

Shigowar Mum ya sa duk suka maida hankalin su kanta, fuskar nan a ɗaure tamkar ba ita ce Mum ɗin da ke ɗokin su ada ba, jiki ba kwari suka mata sanu da zuwa ba tare sa ta amsa ba ta dubi Abdallah cikin faɗa take faɗin ” kai wannan wane irin iskanci ne da zaka ɗoran kafafu kan kujera, ko kuwa tarbiyar da ubanka maras tarbiyya ya ma kenan?”

Kallon ƙafafun sa Abdallan ya yi shikam ko ya makance ne dan kuwa bai ga kafafun sa kan kujera ba, Kursum ce ta ce “Mum ki kalla fa, ba’a kai kafar sa take ba” watso mata baƙar harar da ta y ne yasa ta yin shiru yayin da Abdallah din ya sauko daga kujerar, tsaki Muk taja tare da yin gaba Kursum tace kagani ko yata shi yasa nace bana son gidan nan yanzu Mum ta tsane mu.

Juyowa Mum ta yi cike da fushi tamkar da babba zatai magana tace “to dan ubanki ai sai ki haɗa kayan ki, ki tafi, shegiyar yarinya mai gadon baƙin hali…”

*****

Tunsa Muktar yazo office yake kallon saƙon Hafsa har ya fara mata typing reply sai kuma fasa ya janyo file ya hau dubawa sai dai kuma tunanin saƙon ya tsaya masa a rai, yasan in baiyi wani abun ba kallon saƙon zai iya sawa yayi abinda bai niyya ba, hannu yasa ya danna delete ya jima yama shakku kafin ya danna confirm.

Ganin ba zai iya komai ba a offis ɗin ya shi miƙewa ya bar office ɗin kai tsaye inda yake aje mota ya nufa, kunna motar ya yi ya nufi gidan su Hafsa.

Tana zaune tana tunani wayarta, ta dawo da ita ganin sunan Muktar na yawo kan screen ɗin yasa ta washe baki, ina ƙofar gida taji yace ba tare da ya jira sunyi gaisuwar da suka saba ba, bata damu ba ta miƙe cike da murna ta zari hijabi dan a shirye take, har ta fito ta dawo ta kuma kallon fuskar ta a mudubi, man leɓe ta ɗan murza sanin yana son ganin sa a laɓɓan ta, farin cikin da take ciki tamkar cewa yayi ta fito su tafi, kai tsaye ta nufi ƙofar gidan can ta hangeshi jikin mota harɗe da hannayen sa a jikin kirji ta kuma washe baki kafin ta nufi wurin…

<< Ko da so 37Ko Da So 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.