Skip to content
Part 39 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Rabon da ta tsinci kanta a cikin walwala har ta manta. Tun da satin nan ya kama har yazo ƙarshe bata jin ta samu sukuni a ranta ko na sakan daya sai gashi jin muryar Mukhtar gami da ɗora idanun ta kan sa sun sanya ta a cikin farin ciki marar misaltuwa. Ba wani abun yace ba, kawai jin muryarsa babu wannan kaushin ya saka har hardewa take a hanyar zuwa kofar gidan nasu. Tayi sa’a bata tarar da kowa ba a hanyar.

Ta jima tana kallonsa cike da so da kewa mai yawan gaske. Zuciyarta na bugawa da sauri, da kyar ta samu ta nutsu kafin ta ƙarasa.

Kamar budurwar da tayi sabon saurayi ta sunne kai kasa tana masa sallama hade da gaishe shi murya ƙasa ƙasa.

“Mu shiga ciki mana..” ta fada, tana ɗago kanta.

Ya kalleta sannan ya dauke kan sa da kyar. “Nan ma ya isa.”

Take jikin Hafsah yayi sanyi saboda jin amon muryarsa da yake nuna sam yanzu bata cikin burikan da yake son cimmawa amma bata haƙura ba.

“Abu Abdallah, we are above all these…” ta saci kallonsa taga ya zaro wayarsa ya duba sannan ta cigaba duk da tana gani ƙirƙiri hankalinsa baya kanta.

“Dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya…” Kafin Mukhtar ya ankara sai ganin ta yayi ta durƙushe a gaban sa. Takaici ya cika masa zuciya, bai san lokacin da Hafsan sa mai aji ta zama mara zuciya haka ba, da kyar yace ta miƙe.

“Tashi mana Hafsah meye hakan?” Ya maimaita sannan ta miƙe da guntuwar murnar ta. Sai da ta goge hawayen da suka zubo mata sannan ta jingina da jikin motar.

Mukhtar ya kalle ta, zuciyarsa ta karye da ganin yadda duk ta zabge lokaci guda. Don kar ta sake bashin kunya a titi ya ce ta shiga mota akwai maganar da zasuyi.

Ba musu ta shiga gidan gaba shima ya shiga. Sun jima babu wanda yayi magana kafin Mukhtar din ya gyara muryarsa, yana tattaro dukkan jarumtarsa ya dora akan harshensa.

“Hafsah so nake ki nutsu ki fahimce ni. Zama a tsakanin mu ya kare, ba wai don na tsaneki ba. Ke din kina da muhimmanci a gare ni, kuma kin fi kowa sanin bana son naaci da magiya. Daga yau bana son na sake ganin sakon ki makamancin wanda kika turon jiya Hafsah…, Nayi niyar kawai in ƙyaleki ko in yi blocking ɗin ki sai naga ai akwai mutane tsakanin mu innayi blocking ta yaya zan dinga jin wani abu game da yaran, wannan yasa nace bari in zo da kaina zaki fi fahinta fiye da in saƙone”

“Amma Abu Abdallah ko dalilin sakin ai da sai ka….”

Ɗaga mata hannu ya yi ” Aure dai lokaci ne kuma raine da shi, namu lokacin ya ƙare ran kuma ya mutu, dan haka dan girman Allah Hafsa karki kuma turon saƙo irin na jiya, ina ma kin kusa gama idda?, ki cireni a rayuwar ki yadda na cire ki, zai fi miki…”

Kallon sa ta yi tsar so take ta gano Muktar ɗin tane wannan kuwa ko wani mai irin muryar sa ne, sai dai idanun ta shi suke gani, bata kuma cewa komai ba ta buɗe motar ta fice har ta fice ya kira sunan ta, juyowa ta yi batare da ta ce komai ba ya buɗe akwatun gaban Motar ya zaro farar takarda ya miƙo mata.

Kallon sa ta yi da alamar tambaya idanun ta na faɗin me zan da ita?, ” Naga kamar baki yadda na sake ki ba, nace bari in rubuta miki, duda ma kin kusa gama ida, ina miki fatan samun miji na gari,” kamar ba zata amsa ba, ta miƙa hannu ta amsa tare da yin ciki da sauri.

Can bayan gidan ta ɓoye cikin bushiyu tana kuka tana kallon Paper ɗin tabbas rubutun Muktar ne, sharkaf ta jiƙe paper ɗin da hawaye, maganganun Bilkisu kawai ke dawo mata, tabbas bata da hankali da tayi tsanmanin Muktar zai iya mayar da ita, goge hawayen ta tayi tare da miƙewa har ta fara tafiya sai kuma taja ta tsaya takardar hannun ta, ta yayyaga ta watsar aranta tana ji tamkar Muktar ɗin ne ta watsar.

A falo ta tarar da yaran ta sunyi jigum jigum, wuri ta samu ta zauna, ta hau jansu da wasa, duda cewar ranta ba daɗi…

Shi kuma Muktar yana kallon ɓacewar ta ya mari goshin sa tare da faɗin innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, anya ni ne kuwa, ya ilahi, ya jima a ƙofar gidan sai da yaga motar Abban su Hafsan tayo Layij yayi sauri ya yi baya tare da barin wurin, tsananin nauyin Abban yake ji, baima san da wane ido zai kalle shi ba.

*****

Zaune suke a falon Faruk yana koyawa Kulsum rubutu yayin da Abdallah ke gefe yana karatu Khalil ya shigo ƙannen sa suka mara masa baya, Kulsum ta miƙe da gudu tana murna ga yaya ga yaya, shima dariyar yake suka riƙe juna, ina “Aiman” ya tambaya.

Sakin sa ta yi tare da turo baki, “ba ya tafi gidan Ummi ba, ni suka barni anan…” Bai bata amsa ba Mum ta fito cike da fara’a a’ah yau su Walidin din ne a gidan ƙaramin ƙanin Khalil ɗin yasa dariya tare da yin gun ta da gudu akai rashin sa’a ya faɗi yuf bayan karo da ƙafar Faruk.

Da hanzari Mum ta ƙaraso ta kwaɗe Faruk cikin faɗa take magana ” kaga azzalumin yaro mai halin Ubansa, wato san tsaɓar mugunta shine zaku harɗe shi.”

Abdallah ne ya tsaya da karatun nasa kamar zai magana ran sa ɓace sai kuma ya fasa yayin da Walid ke ta faman tsanyara kuka, Faruk ne yace “wallahi Mum ba harɗeshi nayi ba,” tsaki taja tare da doka masa harara “eh ai na saba ƙarya, ka harɗeshi a ido na kace ƙarya nake”

Khalil ne ya matso “kai Hajiya Mum kodai kin fara rikicin tsufa ne, ai ba harɗe shi yayi ba”

Harar Khalil ta yi “indai wannan yaran ne da sukai gadon mugun hali to wallahi ba ababen goyo bane, haka uwar su ta je ta goya ubansu ya watso da ita bisa dutse” hannun Walid ta kama muje kaji Allah zai saka ma sukai cikin falon ta.

Khalil ne ya dubi Faruk ka yi Hakuri kaji Faruk ranta ne a ɓace, kafin Faruk yace wani abu Kulsum ta ce “ai mun sani yanzu Mun ta zama masifaffiya shi yasa ma ba ruwan mu da ita” ajiyar zuciya Khalil ya yi tare da yin ɗakin Mum ɗin tana ta faman wasa da Walid Khalin ya shiga da sallama, harar Walid da ya yi ne yasa shi taɓe baki zai kuka cikin kakkausar murya Khalil yace wallahi ka sake kamun kuka sai na bubbuge ka, mara kirki kawai maza fita kaje ka bawa yaya Faruk Haƙuri, mara kirki kawai ai kasan ba shi ya yadda kai ba dan sharri kana ji ana masa faɗa kayi tsit da sai ka ce faɗuwa kayi”

Mum ce ta ce ba inda zashi ai agaban ka ya fyalle shi, Khalil bai ce komai ba sai harara da ya watsowa Walid ba shiri yaron ya fice, inda Faruk yake ya nufa, cikin muryar nadama ta yara yace “yaya Faruk kayi haƙuri kaji” murmushi Faruk ya yi tare da kamo hancin sa ni banji haushin ka ba zonan ya kamo shi ya ɗora shi a cinya.

Nazir Wanda yake kusan sa’an Abdallah ya ce, ai Walid indai sharri ne ba daga nan ba, kaga dai ya baka haƙuri muna zuwa gida zaice kai ka faɗar da shi, dariya Faruk ya yi, tare da faɗin “yaron kenan”

Kujerar da Mum ke zaune Khalil ya zauna tare da faɗin “Hajiya Mum wai yaushe kika canja hali?” Harar sa ta yi kai Ibrahim banson iskancin banza fa, kazo ka kori yaro muna nishaɗi shine zaka tsare ji da ido wato zaka ƙureni?”

“Opps Mum Iskanci fa naji kin anbata, ɗazu ma naji kina aibata Faruk anya kuwa Mum, mu yaran yanzu ba akiramu da sunan banza bama tarbiyar mu sai addu’a ina ga kuma kakarmu duk ta tsine mana”. Shiru ta yi da alamu ta tuna bata kyauta ba.

“Yanzu dan Allah Mun dai dai kike fisabilillahi ki kalli yanda kika sa su Faruk duk suka rakaɓe, in basu sake a gidaj nan ba ina zasu sake, abinda kike fa zai iya ja musu psychological problem fa”

Taɓe baki tayi Uban su ya ja musu, wallahi duk na tsane su, dan tsabar rashin mutunci in bashi ɗiyar tawa ita kaɗai ya haɗota da gayya ince a mayar masa ace ni zan riƙe”

Dariya Khalil ya yi “a’a dai Mum Abba ne zai riƙe, sannan ita zatayi tarbiyyar ta, ke sai dai ki taya ta”

Tsaki taja “Ai walllahi Muktar ya cucen, yanzu da wannan uban gayyar waye ma zai tunanin auren ta fisabilillahi.”

Shiru Kalil ya yi dan maganganun sun fara wuce tunanin shekarun sa kome ya tuna kuma sai ya ce ” yo banda abin Mum ai matar mutun kabarin sa wanda zai aure ta ko yara nawa ne zai aure ta, kuma ba lokacin sai a mayar da su ɗin ba, ko a bawa Momin ta riƙe.”

“Abawa me kace?, Ai mayar su zan tana samun miji suje can su ƙarata ganin su ma hawan ji ni zai samun wallahi” ta faɗa rai a cinkushe.

Shiru Khalil ya yi kafin ya ce ” nidai dan Allah Mum ki gyara ko dan kar su taso da tsanar ki a ransu kefa kaka ce ta wurin uwa dan Allah”

Fuskar ta a ɗan ɓace tace shikenan dai in na kallesu banji haushi ba, I won’t react anma indai na tuna da Azzalumin ubansu to..”

“Please Mum koma me kika tuna kawai ki daure kinji” Khalil ya roƙa.

Banza ta masa tare da rufe idanun ta, ya miƙe bari kiga kome na samu ya zama nawa, da sauri ta buɗe ido ” karka sake ka ɗaukar mun komai”

*****

Kwanci tashi iddar Hafsa ta ƙare sam ta aje Muktar a rayuwar ta, ta yi kyau har ta ciko, duda can ƙasan ranta tana jin sa sai dai ta riga ta sa aranta takardar sakin auren da ta watsar shine ta watsar yadda ba abinda ya same ta lokacin da ta watsar tana jin zata rayu ko ba shi.

Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar ta milk da ta sha adon Golden ta yo kyau sosai ga kitso da aka mata jiya ya ƙarawa fuskarta kyau, ba zaka kalle ta kace ta haifi Kursum ba, bare kuma Abdallah ko yayan sa Faruk.

Yaran basa nan suna farfajiya wurin Malamin da ke musu Lesson weekend, ɗakin Mum ta nufa, Mum ɗin na zaune tana hutawa ta shiga, “Mum sannu da gida,” Hafsan tace.

Ba yabo ba Fallasa Mum tace “yawwa sannu” dan ta rage yi mata hayaniya yanzu da alamu zuciyar ta yanzu ta fara sanyi kan zafin da ta ɗauka.

“Yawwa zani gidan Bilkisu ne, kan batun admission ɗin da mukai Tariq zai nemo min,” da yake Mum gwanar son yaran ta su ci gaba ce jin batin ci gaba da karatu wanda ada tayi tayi Hafsa ta yadda taƙi sai ta saki murmushi, “Tom sai kin dawo, duk a gaggaishe su”

Tana fita Harabar gidan Aiman ya taso da gudu shi sai bita, cikin dabara tace, “kasan dai kwanaki nayi rashin lafiya ko, to likita yace kar in dinga yawo da yara”

Kallon ta ya yi fuskar nan cike da disappointment, kafin yace ” shikenan adawo lafiya in kin ji sauƙi sai in dinga binki ko?”

Gyaɗa kai ta yi alamr eh, ya koma salalo salalo zuwa inda suke karatun, yayin da Hafsa ta yi sauri ta fice kar ya canja shawara tasan halin sa da wayo da ya yi tunanin ba haka bane zai ce sai ya je, kamar kuwa yadda ta zata, har ya kusa sai ya tsaya cak da sauri ya juyo, ganin bata nan yasa shi yin kwafa ya koma ya zauna.

Kasancewar a ɗan sahu ta je yasa ta tsaya bakin ƙofar tana bugawa, tsayawar motar Tariq a ƙofar gidan yasa ta dena bugawa, fitowa ya yi yana murmushi “a’a Mamin yara kece da yamma haka, murmushi ta yi wanda ya ƙara mata kyau, da sauri Tariq ya ɗauke kansa sabida wani abu da ya jima da yaƙar sa da yaji ya taso masa, yayin da Hafsa tace kabari kawai ai wai nan so nake in same ka ne shi yasa.

Makullin gidan yasa ya buɗe, yana faɗin “inajin ko sun aiki Musan, tunsa kika buga bai buɗe ba,”

Bata ce komai ba ta shige ciki, yayin da ya koma dan shigo da motar sa, Yaran suna Falo malamar su na musu ƙari kasancewar yaran Bilkisu duk mata, suna ganin Hafsa suka fara murna, cike da murna suka gaidata, Chocolates ɗin da ta kawo musu ta rarraba musu, kafin ta wuce ɗakin Bilkisu, a kwance ta same ta tana bacci, haka kawai rayuwar yarinya ta dawo mata, hannu tasa ta ɗakawa Bilkisun duka tana dariya.

Firgigit Bilkisun ta farka ganin ta yasa ta miƙewa tana dariya, ” kefa Mami wallahi bakya girma nasan burin ki in miƙe in biyo ki da gudu ko,” dariya Hafaa tasa wallahi kamar kin san haka suka sa dariya duka…

<< Ko Da So 38Ko Da So 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×