Ammi na zaune cikin shaddar ta da ta ji sirfani kallo take dan ta mai da hankalin ta kan TV ɗin suka shigo suna dariya da alamu wata maganar sukai wannan ya ja hankalin Ammin kan su "a'ah yau su Hafsatu ne gidan namu?"
Hafsan ce ta ɗan ture hannun Hidaya ta yi gun Ammi da sauri, "Ammin mu ashe kina ƙasa?" Murmushi Ammin ta yi "ina nan kallo ya riƙe ni".
Rissinawa Hafsa ta yi ta gaishe ta.
“Inaa ba ni amsawa na yi fushi sai yau kika ga damar zuwa" Ammi ta faɗa tana ha. . .