Skip to content
Part 40 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Dariyar da suka yi ta saka su tuno da. Nan suka buɗo shafin yarintar su kafin suyi aure sukayi ta daarawa har sai da sukayi me isarsu. Kamar ba su ba sai shiru ya ratsa a tsakaninsu. Hafsah tayi ajiyar zuciyar da ya zame mata dabi’a duk da zahiri ta bar Mukhtar, ta kuma jingine shi gefe, duk sanda wani abun ya kawo zancen sa sai taji zuciyarta tayi nauyi.

Bilkisu ta zuba mata ido tana jiran abunda zata ce. Hafsah ta kauda kai gefe saboda bata san ta inda zata fara ba, karshe dai ta zabi abun cewa.

“Nazo neman alfarma ne…” ta faɗa cikin sigar tsokana wadda Bilkisun bata lura ba sai dai nutsuwar da ta karayi tana jin cewa ko me Hafsah zata nema a wajenta zata iya yi mata komai wahalar sa.

Hafsahn ta sunkunyar da kai, “dama na yanke shawarar komawa karatun shine nace dan Allah ko Tariq zai nemo min admission…”

Wani kallo da Bilkisu ta watsa mata sai da yasa Hafsahn ta saki dariyar da take riƙewa ita kuwa Bilkisun ta ƙule sosai ta tashi gami da yin tsaki.

“Wallahi kin mugun raina ni. Mtsww dallah matsa.” Da haka ta fice a ɗakin Hafsah tabi bayanta sukai kitchen inda ta fara zuba musu abinci.

“Ba don halinki ba dai.” Bilkisun ta faɗi yayin da suka zauna.

“Ko don halin nawa ma nasan zaki yi min alfarma…” harara Bilkisun ta sake yi mata saboda kalmar alfarma da Hafsah take ambato tana mugun bata mata rai.

“Allah ya baki haƙuri me gadon zinare!”

Murmushi sukayi.

Tariq da ya shigo da motar sane ya yo ɓangaren Bilkisun samun yaran suna karatu yasa shi yin ɗakin matar tasa, daga baki ƙofar kitchen ɗin ya tsaya, yana kallon su, yadda suke cikin nishaɗi sai suka birgeshi, zuciyar da ke ingiza shi ya yi abinda ba haka ba yasa shi yin saurin barin wurin.

*****

Juyi yake tayi akan gadon don tunda yayi asuba ya kasa komawa bacci, idanunsa suka kumbura. Haka ya wuni daga masallaci sai ɗaki. Ya rasa me yake masa dadi a duniya gaba ɗaya. A yan kwanakin nan duk ya rame ya yi duhu musamman ma in ya tuna cewar Hafsah ta gama idda. Tunanin yana saka shi jin kamar yayi ihu don yana tuna masa da cewa yanzu ba matar sa bace haka zalika kuma ko wanne namiji zai iya aurenta. Idan wannan ya faɗo masa a rai sai yaji kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu. Ba don imani ba sai yace duk sallah sai yayi addu’ar kar ta samu miji.

A gefe guda kuma kewar yaransa tana nuƙurƙusar mishi ƙasusuwa ga kunyar iyayen Hafsah tunda har yau bai waiwayi gidan ba kuma babu wanda ya nemi zuwansa. Ba Mummy ba Abba. Ya rasa ta inda zai bullowa lamarin ya samu sa’ida.

Ko da yajewa da Inna zancen ta je ta amso masa yaran sa cewa tayi babu ruwanta. Hajara kuma ta ce bata da lokaci. So yake ko yaya yaga yaran. A wani bangaren na zuciyarsa ma yana son ganin Hafsah yaga ya ta koma.

Ƙarshe dai yaga gara yaje ya sami Rashida ta bashi shawarar da ta dace. Duk da yasan yanayin tunaninta sai a hankali amma ko meye zata faɗa masa yasan zai bashi mafita in ya haɗa da nasa tunanin.

Haka ya tashi ya shirya ya nufi gidan. Cikin mintuna kaɗan ya isa gidan. Gidane ginin zamani, madaidaici. Kana ganin gidan kasan akwai rufin asiri. Ya jima a motar kafin ya fito.

Ko da ya shiga ya tsaya a kofar part ɗin Rashidan sai da ya shafe mintuna kafin ta fito da kasko a hannunsa. A take wani wari ya daki hancinsa ya kalle ta cike da mamaki.

“Wani irin turare ne wannan Rashida?” Mukhtar ya tambaya.

Rashidan ta taɓe baki. “Laaa yaya ban san kaine ba ai. Na dauka yan adawa ne…, Tsari ne na kaɓo a can wani kauye. Kasan yadda zamani ya chanja gashi ana nufar mutum da sharri shiyasa gara ya tsare kansa ko da an mishi barbade barbade ba zai kama shi ba.”

Da kyar Mukhtar ya fahimci inda ta dosa da yaga tana magana tana leka ɗayan part din da abokiyar zaman ta take. Ya girgiza kai ya bi bayanta suka shiga falo. Rashida ta dena bashi mamaki sam sai dai kawai ya bita da addua. Murnar da yake yi ma da ya kasance yaranta kaf basui halinta ba.

Mamakin yadda akayi Nura bai taɓa sakinta ba yake yi duk da kuwa halayenta marasa kyau ne. Nura yana son Rashida nesa ba kusa ba kuma yana kula da ita daidai iyawarsa tun bashi dashi. Duk sanda tayi yaji kuma da kanshi zai zo yayi biko har ma ya fadawa Mukhtar ya saka baki.

Shi gashi yana zaune da Hafsah lafiya kalau wani abun ya saka ya rabu da ita. Kenan shi ba son ta yake yi ba da gaske? Ko dai shi kawai rago ne? Ko jarumtakar kenan? Ya rasa amsar tambayarsa ya kalli Rashida da take shigowa da lemo a tray.

Ta ajiye sannan ta taɓe baki. “Sai haƙuri yaya. Tsiyar Nura ba zata bari ya saya mana lemon kwali ba sai na roba.”

Mukhtar yace, “kamar yaya kenan. Wai ke Rashida yaushe zakiy hankali? Mijinki kike kiran sunansa gatsal haka?”

Tayi tafi harda shewa. “Hankali na nawa kuma? Don nace Nura? Ai Nawwara ya kamata na kira shi dashi. Namiji ne amma ba zuciyar maza! Kullum a babu. Ko da ya fara samu kuma aka makala masa waccan banzar me kama da biri. Ni abun kunya ne ma ace ina kishi da kamar ta.”

Mukhtar ya rasa abun cewa sai kawai ya dauke kai. Ko yaushe a cikin kure shi take yi. In da sabo yaci ya saba.

Hakan ya tuna masa da Hafsahn sa. Mace me tarbiyya da iya kula da miji. Zata tsokane shi kamar kakanta amma kuma umarnin sa ko yaushe bata sabawa. Idan magana yake mata me muhimmanci tsayawa take ta saurara ta bashi amsar da ya dace. Idan lefi tayi cikin lumana zata gaya masa ba zata sake ba. Kusan komai nata ya cika goma amma da yake dan Adam ace sai ya zama bata cikan ba, tara take. Ko a zuciyar Mukhtar ma abu daya ne ya hanata cika goma a zuciyarsa.

Abun da ya zamo silar sakin ta.

Ko ita Hafsahn baya jin ta sani kuma ba zai iya sanar da ita ba. Ba zai iya sanar da kowa ba saboda ko shi kanshi in ya tuna dalilin sai yaga kamar sakin ba shine maslaha ba.

Mukhtar ya kai mintuna biyar yana tauna maganar da yazo da ita kafin ya kalli Rashida wadda take danna wayarta yace,

“Na saki Ummu Abdallah…”

Kalaman sa suka saka shi jin wani ɗaci a harshen sa saboda tamkar dafi suke. Zuciyarsa ta tsinke kamar ko yaushe idan ya tuna abunda yayi musu ɗin.

“Ban gane ba?” Abun yazo mata a bazata. Kuma ta kwana biyu bata leƙa gidan ba.

Ya rike kansa don ba zai iya maimaita wannan kalaman masu dafi ba.

“Ta gama idda ma.” Sai yaji wannan din ma sunfi yi masa zafi.

Rashida ta fara salati tana sallalami cike da al’ajabi. Yanzu ashe Mukhtar zai iya rabuwa da Hafsah? A take kwakwalwarta ta ayyano mata cewar Nura zai iya rabuwa da ita kenan. Jikinta yayi sanyi duk da ba wani son Hafsahn take ba. Haka ta jingina da kujerar hadi da jefar da wayar hannunta. Ashe haka maza suke?

“Shawara nazo ki bani tsakani da Allah. Yaran suna wajen ta kuma tun da ta tafi ban je wajen su ba. Ya dace naje ganinsu?”

Bakin Rashida ya mutu murus. Da kyar ta haɗiyi yawu tace,

“Ikon Allah. Gaskiya baka kyauta ba. Kana nufin iyayenta ne zasu kular maka da su ko me? In ba zaka iya zuwa gidan ba ai kasan makarantar da suke. Kaje ka gansu salin alin kafin kayi tunanin mafita don ni kaina a kulle yake. Tabb…”

Aka dan jima bai ce komai ba.

“Tabb.” Rashida ta sake maimaitawa sannan ta mike don gaba ɗaya ya jagula mata lisaafi. Dama kwana biyu taga Nura yana mata wani gani gani. Ai kuwa ba zata bari ya sake ta ta tashi a tutar babu ba. Dole ma tasan abun yi kafin ya shammace ta.

“Hnmm unmm…” ta faɗi sannan ta mike.

“Ka gaida gida.” Ta shige ɗaki ta kullo kofar.

Ko kaɗan Mukhtar baiji komai ba ya tashi ya tafi.

*****

Sai yamma lis Hafsah tazo tafiya da yake bata zo da mota ba, ɗaki Bilkisu ta shige tana faɗin ina zuwa, Tariq na zaune yana taɓa waya ta shiga, yana ganin ta ya buɗe hannu alamun tazo ta shiga, ta maƙe kai, “kajika Hafsa na waje tana jira na kasan bata son jira” murmushi ya yi “nikam dai ba’a kyautamun ba, bakiji yadda nake missing ɗin ki ba walllahi” Dariya ta yi “nidai yanzu taimakawa zakai kazo ka kaita, bata zo da mota ba” miƙewa yayi an “gama tawan” sai da ya zo daf da ita ya jawo ta jikin sa, suka sa dariya duka, kaiko na faɗa ka jira take sai da ya manna mata Kiss a goshi sannan ya fice ta bi bayan sa. Hafsa da ya ɗora idanun sa kan Fuskar ta yada shi jin wani iri, rage dariyar yayi kafin yace “Madam munbar ki kina ta jira ko?”
Murmushi Hafsa ta yi, “ai indai kune na saba jira.”

Duk yadda Hafsah tazo zillewa don kar ta shiga motarsa sai da Bilkisu ta kureta. Gudun ɓacin rai yasa ta yarda ya kaita din.

Sunyi sallama har ta shiga motar sun fito. Banda AC da takeyi baka jin sautin komai. Gaba ɗayan su ba wanda ya sake a motar. Ita Hafsah tana ganin rashin dacewar shiga motar wani daga shi sai ita shi kuwa yayi nisa a tunani yana yi yana satar kallonta wanda tunda ta shigo idonta yana ga window.

Tariq ya gyara murya sannan yace,

“Ya yaran?”

Idon Hafsah akan window ɗin ta murmusa. Indai kana son ganin farincikin ta ka tambayi lafiyar yaranta.

Murmushin nata ya taɓa shi, a hankali yace ya rabb, yayin da Hafsa ta ce “Lafiya ƙalau.”

Suka sake yin shiru. Tariq ya rasa abun cewa, duda yadda yake son suyi magana ɗin, sai dai ya kasa wannan yasa kawai ya kunna rediyo. Waƙar indiya ta shigo wadda a take tasa Hafsah ɓata rai. Ta juyo da rauni a fuskarta. Karaf suka haɗa ido. Gaban Tariq ya faɗi, bai yi tubanin zata juyo ba, wannan yasa idanun sa duk sakanni in ya kalli Titi yake dawo da su kanta.

“Don Allah ka kashe?” Kamar ma tambayarsa take. Tariq ya kashe sannan yace “mai yasa, ba daɗi ne?” ya tambaye ta dalili.

“No It reminds me of him. Baya son waƙar indiya amma yana son wannan kuma yana rera min.” Ta juya kanta tana tausasa zuciyar ta akan son Mukhtar da ya manne mata. Ta nemo dukkan dalilin da zaisa ta tsane shi ta sakawa ranta sannan hawayen suka koma. Ta bar shi har abada amma son shi? Bata jin zai barta.

Shiru Tariq ya yi kafin kuma ya ce “Kyanta kiyi taji har sai ta dena tuna miki dashi. Sometimes we have to help ourselves go over someone.”

Ta gyaɗa kai. “Na sani nima so nake na manta shi a zuciya. I’m done with him amma zuciyata is obsessed. Karatu ma zan koma…”

Jin haka yasa Tariq yaji dadi sosai, yayin da tunani iri iri ya mamaye masa rai.

“An zo fa..” ta fada da dan dariya sannan ya faka motar shima yana dariya.

“Zan faɗawa Bilkisu tayi ma a hankali. Ta sace zuciyarka da yawa a waje ma tunaninta kake. Nagode.” Bata jira amsar sa ba ta buɗe motar ta fice.

Ya bi bayanta da kallo, son ta yana sake sabunta a cikin ransa. Lokaci yayi da zai sanar da ita, ba zai iya yin kasadar barin taba kamar yadda ya yi abaya, dole tasa ce Hafsa, yanaji aransa sabida hakane ma ƙaddara ta rabota da gidan ta dan ta zama tasa, amma kafin nan yana bukatar amincewar Bilkisu. Zai yi istikhara sannan ya fada mata, duda bai san ta inda zai fara ba, anma tsananin son Hafsa aransa na bashi ƙwarin gwiwa, tsoron rasa ta a karo na biyu na sanya masa jarumta, dolema zai faɗawa Bilkisu da wannan tunanin yaja motar sa ya bar ƙofar gidan su Hafsa…

<< Ko Da So 39Ko da so 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×