Skip to content
Part 41 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Lokaci wani halitta ne da tunda aka hallice shi yake gudu. Baya sauri dan wani, haka kuma baya jiran kowa. Dukkan wani numfashi da dan Adam yake shaqa tafiya yake da lokacin da aka dibar masa a duniya. Haka lokaci ya cigaba da tafiya, rayuwar Hafsah tana sake alkibila. Kamar wasa har ta samu gurbin karatu a jami’ar bayero ta cigaba da karatun da tace ta gama.

Sai dai ita duniya babu tabbas, zaka iya gama tsarin ka kuma ta sauya maka shi.

Zaune suke a ajin suna jiran shigowar malami wata yar ajinsu wadda suka fi jituwa da Hafsah ta kalle ta taga tayi nisa a tunani.

“Umm Abdallah lafiya kuwa?”

Hafsah tayi ajiyar zuciya. Babu abunda yake mata ciwo sama da yadda mummy tasa yaranta a gaba kuma tace kwana uku ta bawa Hafsah ta kira Mukhtar ya kwashi yaran. Tana kallo yadda duk auka takura musamman ma Abdallahn da duk yafi su hankali. Kullum in zata leka su zata ganshi idonsa biyu yana sallah. Da ta tambaye shi me yake nema a wajen Allah sai yace mata bakomai kawai yana mata addu’a ne. Tasan shi da zurfin ciki da son nuna kalau yake.

“Ciwon kai ne yake damuna yau. Kamar ma ba zan iya zaman lecture din nan ba, tafiya zanyi.” Ta fara hada littafanta tana saka su a jaka. Zuciyarta cike fam da tunani tana neman mafita. Babu wanda zata yi shawara dashi sama da Yaya Sadiq ko aunty Ameera. A take ta yanke shawarar zuwa gidan nasu.

“Toh Allah ya sauwaqe.” Amin Hafsah tace sannan suka yi sallama ta tafi.

Fitowarta daga ajin yayi daidai da lokacin da lecturer din ya iso tare da abokinsa. Dr Karaye. Ba tare da izininsa ba idanunsa suka sauka kan Hafsah. Da yake kuma daliban basu da yawa, lecturer din su Hafsah duk ya san su. Ganin yadda Karaye  ya kalleta ya saka shi yin magana.

“Malama Hafsah ina zuwa?”

Ta jiyo ta kalle shi. “Ah Sir ina wuni. Wallahi banji dadi bane shiyasa zan tafi.” Tunda ta fara magana Dr Karaye yaji ta kwanta masa a rai. Rabon da yaji wani abu akan mace ya manta. Tunda matar sa ta rasu babu wata da ta taba burge shi. Yau shekara goma kenan yana zaune babu aure. Dangi sunyi mitar har sun gaji. An daura masa aure da wata yarinya amma karshe sai rabawa akayi saboda rashin jituwarsu da rashin zamansa da ita.

“Ayya Allah ya kara sauki.”

Saurin da Hafsah take yi bai bari ta bashi amsa ba.

“Don’t miss her!” Lecturer din ya dafa kafadar Dr Karaye sannan ya shige aji ya bar shi tsaye nan yana tunanin ko yabi bayan Hafsah ya karbi number ta. Karshe dai yaga hakan bai dace ba tunda duk ba yara bane.

Juyawa yayi ya koma office dinsa yana tunanin sanda abokinsa zai gama lecture. Zaifi ace address sinta ya karba a gun yan ajinsu idan da me shi. A hankali yayi murmushi cike da nutsuwa da kamala irin tasa. Ya sani, ya samu mata!

*****

Kamar wasa kafin ta karasa gidan Yaya Sadiq ciwon kai ya hana ta sukuni. Da kyar ta karasa driving tajw gidan nasa. Kai tsaye ta wuce wajen Ameera ta shiga da yake ta kirata tun a hanya an bude mata kofa. Gidan shiru kamar babu kowa tayi sallama.

“Welcome sis!” Ta tsinci muryar Ameera tana fitowa daga kitchen. Tayi kwalliya sosai kamar ko yaushe, jikinta yana nan da kyaunsa saboda yadda ta yadda da bauta masa. Haka ma kwalliyarta kullum abar burgewa ce kamar bata da wata matsala a rayuwarta.

Suka gaisa da kyar saboda yadda kan Hafsah yake ta ciwo. Karshe dai sai magani tasha ta kishingida a falon don ta samu sauki. Kusan mintu talatin Ameera ta bata ba tare da tayi mata magana ba har ciwon kan ya lafa ta fara bacci.

Cike da tausayi Ameeran take kallonta saboda tasan me yake faruwa. Tayi ajiyar zuciya sannan ta tashi ta kwaso flasks din abinci ta jera su a dining. Sanda tayi sallahr la’asar tazo tashin Hafsah sannan ne Hafshan ta farka.

“Sannu sis…” ta fadi tana ajiye hijabin da ta kawowa Hafsah don tayi sallahr.

“Nagode. I feel so much better. Now i can admire your sense of fashion. Kinyi kyau sosai.”

Ameera ta dara cike da izza da jin kanta na cewar tayi kyau. Tana so tayi kwalliya a yaba.

“You saw what your brother failed to notice. Shi da wuya yake tanka kwalliyata.” Ameerahn ta fada da alamar abun yana bata mata rai. Kafin Hafsah ta bada amsa ta cigaba.

“Kuma fa na gyara duk abunda yace. Yanzu na iya girki, ina gyara gida but still shi dai ba damuwar sa bane.”

Hafsah tayi murmushi. “Ai maza haka suke. Yan ganin dama.”

Suka danyi dariya sannan Hafsah ta tashi yin sallah. Sai da sukayi sallahr suka ci abinci sannan Hafsah ta gaya mata dalilin zuwanta da shawarar da take nema.

“Nasan Inna tana son su kuma zata kula dasu amma kin san kyan ko wanne yaro ace yana gaban uwarsa.”

Ameera ta dan gyada kai duk da ba zata ce ba tunda bata da yara. Sau uku tana bari. Har ma ta soma dena gwada haihuwar ta hakura.

“Hakane. Zan fadawa Habibi sai ya kirashi duk da shima haushin sa yake ji. Amma haushin da kowa yake ji ba zai bada solution ba. Kuma ki dage da addua da neman zabin Allah.”

“In sha Allah anty Ameera. Nagode…” karar wayarta ya katse godiyarta. Tana ganin mummy ce tayi sauri ta tashi ta yafa mayafinta.

“Kinsan mummy ta koyi fada on top of natural fadanta.”

Da haka sukayi sallama, Hafsah ta tafi gida tana ta tunanin yadda abubuwa zasu kasancewa yaranta harma da ita. Har yau kuma bata dena mamakin yadda komai ya faru ba. Kamar almara take jin abun. Zuwa yanzu ko tuno Mukhtar tayi sai dai tayi murmushi because ya dena spiking emotions dinta sam. Bata jin komai game dashi. Kawai dai ya zama kamar ko wani mutum da ta taba sani.

*****
Dr Mansur na barin Ajin su Hafsa office ɗin Dr Ƙaraye ya nufa cike da zumuɗi domin a zahiri yama ɗaya daga cikin mutanen da suke burin ganin Ƙaraye ya cire Hadiza marigayiyar matar sa a ransa,  sanin halin Ƙaraye na rashin kulle ƙofa yasa kai taaye Mansur ya murɗa ƙofar ya shiga.

Dr Ƙaraye na zaune hannayen sa bisa goshin sa da alamu tunani yake, sai da Dr Mansur ya ɗan taɓa shi sannan ya ɗago ganin Dr Mansur ɗin tsaye yana kallon sa yasa shi sakin ajiyar zuciya tare da faɗin “Dr am In love, mai ke son faruwa dani ne, kasan ban yadda da love at first sight ba anma da alamu shi ya faru dani, yanzu taorona what If she’s married, nasan babu yadda za’ai kamar ta ace bata da aure, and in wani ya aure ta nasan ba zai taɓa gangancin sakin ta ba.”

Dariya Mansur ya yi, “kai dai kawai kace so ya rufe ma ido in seconds anma I see nothing special about her, “ba tare da Ya bashi amsa ba Ƙaraye ya ce “is she married?” Ya  tambaya yana kallon Dr Mansur da alamu zuciyarsa ke bugawa, da alamu cike yake da tsoron kar ya zama tana da auren.

Dariya Mansur ya yi ” ka kwantar da hankalin ka kwanaki da zamuyi wani topic na zuwa ƙauye a Google form ɗin nasa suyi indicating ko da aure ko babu, naga tasa single” ajiyar Zuciya Dr Ƙaraye ya yi, yanzu ya fahinci mai yasa ƙaraye ya kasa mantawa da Hadiza, son da yakewa mace mai zafi ne, ace daga ganin mace yanzu har ya kamu da son ta irin. haka so mai zafi. “Ya ka amso Number ɗin tata?” Mansur ya tambaya

Girgiza kai Ƙaraye ya yi kafin ya ce ” no ina ta tunanin ko matar wani ce”.

‘Hakane ina muje offis ɗina in duba Google Form ɗin akwai address ɗin ko wannensu ciki, sai in baka” Mansur ya faɗa bayan ya miƙe, murmushi Ƙaraye ya yi, “kamar ka shiga raina da ina tunanin koma ƴan ajin su zan tambaya muje ɗin” ya faɗa bayanya miƙe.

Tare suka fito duk inda sukai ɗakibai na gaida su, yayin da ƴan mata ke ƙara gyara salon tafiya da murya a duk sanda suka hangesu kowa burin ta ace Dr Ƙaraye ya yaba da ita, sai dai shi ina ji yake tamkar ya yi tsuntsu zuwa offis ɗin Mansur dan ganin address ɗin Hafsa ɗin.

Table ɗin sa Mansur ya nufa inda ya kunna computer ya hau dube dube kafin ya ce ” yawwa gashi nan da sauri Ƙaraye ya ƙarasa ya hau dubawa idanun sa suka faɗa kan hoton Hafsa dake manne jinin screen ɗon computer ɗin gaban sa ya hau faɗuwa, tabbas wannan tasa ce, haɗuwar ta takai iya haɗuwa, she is his ideal type, a hankali yake bin bayanan ta da kallo yana haddacewa”

Murmushi ya yi tare da Dafa Mansur,mutmina this ur form ya mun anfani sosai, Thank yanzu ma dam tace bata jij daɗi me da wallahi yamzu zan nufi gidan” dariya sukai duka Mansur yace Allah dai yasa kayi mata, gaban Ƙaraye ne ya faɗi, a zahiri kuma yace amin.

Washe gari da yanma lis ya nufi gidan su Hafsa, ya kyau sosai sanye yake manyan kaya kamat ko yaushe, milk color shadda ce da ta ƙara masa haiba a harabar gidan ya faka mota, dan kamalar sa tasa mai gadi buɗe masa directly, ba musu, su Faruk suna harabar gidan da alamu shaƙatawa suke da girmamawa suka gaida shi, yace Hafsa yake nema.

Abdallah ne ya haɗe rai da jin Mamin tasu yake nema, murya a cinkushe ya ce bata nan, Aiman ya matso rike da ball tare da faɗin ” Yaya Abdallah ba Abie ya hanamu ƙarya ba, bari in kira ta,” yaron ya faɗa tare da yin ciki da gudu, Abdallah ya tsuke fuska tare da yin ciki rai ɓace.

******
Hira sukeyi cike da annashuwa da kwanciyar hankali. Akan ce ko wanne aure yana da kalubale amma Bilkisu zata iya rantsewa bata sami komai a rayuwar aurensu ba sama da farinciki da kwanciyar hankali. Sabanin da suke samu baya wuce awa daya kowa ya yafewa dan uwansa.

Bata taba zubar da kwalla saboda Tariq ba tunda sukayi aure. Bata taba kwana da bakin cikinsa ba. Rayuwar aurenta babbar kyauta ce daga Allah wadda kullum take kara godewa Allah da yayi mata wannan kyauta mafi girma da za’a yiwa mace a gidan duniya.

Yaranta ma sai sam barka. Dukkan su masu biyayya ne. Basa bata wahalar da aka san teenagers dasu. Basa rashin kunyar nan me cin rai sai abunda ba’a rasa ba. Tabbas ita kam alhamdulillah.

Tariq ya dubeta a ran shi yana tunanin abunda yake shirin gaya mata. Anya kuwa zai iya? Ba zai fi ace ya hakura ya danne bukatarsa ba ko dan wanzuwar wannan farin cikin a rayuwarsu? Amma ai Bilkisu tana kaunar Hafsah. Tana sonta kamar yar uwarta kuma yasan zatayi murna idan ta samu miji.

“Me ya faru?” Ta lura da yanayinsa yadda yayi nisa a tunani. Ganin bai ji taba yasa ta fara masa cakulkuli suka dinga dariya har suka gaji ya jawo ta ya kwantar da kanta a kirjinsa.

“Kinsan ina son ki ko?”

Bilkisu ta gyada kai.”Kaf duniya babu wadda ta kaiki matsayi a zuciyata. I hope you know that?” Jikin Bilkisu sai yayi sanyi.

Wannan words of affirmation and reassurance tsoro suke bata maimakon su kwantar mata da hankali.

Ta daga kanta sannan ta zame daga jikinsa.

Idanunsu suka sarke, take nata suka cika da hawayen fargabar da take mamakin yadda ta kamata. Haka kawai take jin wani irin tsoro ya mamaye zuciyarta. Haka kawai taji kafafuwanta sunyi sanyi kalau.

“Aurrree za..ka yi?” Kalamanta suka fito daga bakinta a rarrabe.

Da kyar ya gyada mata kai. “Shawarar ki nake nema game da neman auren Hafsah.”

Dif komai na duniyarta ya tsaya cak. Rawar da jikinta yake yi a take ya tsaya. Shi kan shi Tariq sai yaji kamar wani abu yana barin jikinsa bayan ya furta kalaman. Kamar da sanye yake da wani lullubi me dumi ko da yaushe. A yanzu yaji wani sanyi yana shiga har kashin sa. A yanzu yake jin wani bakon yanayi yana tsargawa a tsakaninsu. A yanzu yake ji kamar an daga musu wani labule a rayuwar su.

Alhamdulillah Ƙarshen littafi na ɗaya Shin Tariq zai auri Hafsah? Ya ya Bilkisu zata ɗauki al’amarin?
Shin Mukhtar zai yi nadamar sakinta ko sai ya makara? Mene ne dalilin sakin? Ya ya makomar yaran Hafsah zata kasance?

<< Ko Da So 40Ko Da So 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×