Skip to content
Part 42 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

LITTAFI NA BIYU

Da gudu Aiman ya shige ɗakin Hafsa tana kwance bisa gado idanun ta na duban fanka da alamu ta yi nisa a tunani Aiman ɗin ya gaji da magana taɓo ta ya yi ta ɗan firgita da girgizawar da karamin hannun ya mata a ɗan nutse cikin muryar damuwa ta ce “Aiman bana hana ka girgiza ni ba.”

ƙasa yaron ya yi da idanun sa ” I am sorry Mami, my mistake, anma ba ke ce ba ina ta magana kinmin banza nama ɗauka kurmancewa kikai” yadda ya yi da yadda sautin Muryar sa yake ya sata yin murmushi tabbas ɗa rahama ne, ita tasan damuwar da take ciki ta yi mata yawa ma ta ma ƙarfin kwanyar ta sai gashi yaron ta yasa ta pure murmushi kuma har cikin ranta taji nishaɗin.

Yunƙurawa ta yi ta zauna tare da kamo ƙaramin mutun ɗin nata da duka hannun ta kafin ta ce “to ayi haƙuri baccin zomo nake shi yasa ido na ke a buɗe anma bana jinka” dariya yaron ya yi “nifa in ce ya faɗa kamar babba” kallon sa ta yi tamkar mahaifinsa ya koma mata kusan da shi da Abdullahi sunfi kowa yanayi da Muktar.

“Au har na manta” ya faɗa tare da dafe goshi haka dai ta kuma ganin Muktar a yaron dafe goshi ya yi da bai yi wani abu ba ɗabi’ar Muktar ce.

Murmushi ta yi kafin ta ce towo me kuma ka manta, wani ne yace ki zo yana kiranki yaya Abdallah ya ce ba kyananan bacin Abie ya hana mu ƙarya.

Gaban ta ne ya faɗi ita ko tana budurwa batai wannan yayin na a turo ana kiran ta ba ballantana kuma yanzu da girman ta da komai, “maza geka kace banan kaji ɗan albarka,” ƙuri yaron ya yi yana kallon ta da alamu so yake yace mata baya son ya yi ƙarya, fahimtar hakan da sanin halin yaron yass ta tsuke fuska tare da faɗin zaka tafi ko kuwa sai na sakko na make ka.

Rai ɓace ya fice wanda ya yi dai dai da kawowar jikin Mumy wurin har ya ɗan buge ta a tsorace ya hau bata haƙuri, sosai yake tsoron dattijuwar kakar tasa, “Mumy ki yi haƙuri mami ce ta min tsawa inje in ce wau bata nan, bacin tana nan”

Mum da batai niyar ce ma yaron komai ba ta yi saurin cewa “waye kuma yake kiranta?,” a fusace ta faɗa dan tsammanin ta Muktar ne kafin ta samu amsar yaron tuni zuciya ta tunzura ta yin bakin tagar da ke iya hasko mata farfajiyar gidan, can ta hange shi tsaye cikin manyan kaya jingine gikin motar sa, irin sirikin da Mum take so kenan nan take taji hankalin ta ya kwanta da shi kamalar sa daban yake duda daga nesa ta hange shi, da sauri ta saki mayafin tare da cewa “Aiman” yaron da ke gab da fita ya ja ya tsaya rai duk a cunkushe “maza jeka kace masa ta zuwa” da fara’a yaron ya fice dan shi kam ya tsani ya yi karya bacin Allah baya bacci yana ganin sa, yana jin tsoro yana kuma jin kunyar Allah.

Da han zari Mum ta shiga ɗakin Hafsan tana kwance sangalalun hantunta bisa goshin ta idanun ta da ke fuskantar fanka a limshe sai dai kallo guda zaka mata kasan ba bacci take ba.

“Ke Hafsa ki tashi ki fita kina da baƙo” shurun da ta yi ne yasa Mum fusata, nasan ba bacci kike ba zaki tashi ki fita ko sai na tsinka miki mari” rai a cunkushe ta buɗe ido “Please mum..” Hajiya ki ta shi ki fita kin bar mutun na ta tsaiwa, ina kin gama idda, ko kina nufin wancan ɗan iskan kike kuma jira? To wallahi badai ina da raiba, in wancan karan kunmin ƙarfa ƙarfa na yadda yanzu ba zai yuwu ba, in koma gidan sa to wallahi cikin biyu ne kodai na mutu ko kuma nabar gidan nan dan wallahi in kika ce sai kin koma gidan sa to ni kuma nawa auren sai ya mutu in kuma ya mutu ki ɗaura ɗammarar neman wata uwar.

Jiki ba kwari kice da ɓacin rai Hafsa ta zari mayafin doguwar rigar da ke jikin ta, kamar yadda ɗabu’ar ta na sanya abaya kusan ko yau she ma tsayin kayan ta yake tana budurwa yanzunma sune dai kayan nata sai dole take sa atamfa leshi kuwa tunda tabar gida bama ta da shi dama Mum ke sai mata.

A fusace take da zummar taje ta mass rashin kirki ta fito sai dai kwarjini da haibar sa sun sa mata girman sa a idanun ta, bata saki fuskar ba ta ce ina wuni, ajiye idanun sa daga kanta ya yi zuwa ƙasa zuciyarsa na harbawa da sauri tun fitowar ta idanun nasa suka maƙale kanta, sanyayyar murta ta dawo shi, a nutse ya ce lafiya ƙalau ya kuma haƙuri da ni. Ya faɗa yana kallon ta. Kallon sa shi ta fara ji ya fara bata haushi sam bata son kallo ita kam.

Kamar yasan abinda take mita a ranta ya sha kai, sai kinyi haƙuri dani ina da zafin so wannan yasa bana iya juya zuciya ta har in iya ɗauke idanuna daga abinda nake muradi bare ke. Wannan rayuwa oh ta faɗa, namiji sai a slow wato daga ganin ta jiya ko shekaran jiya har ya yadda wai son ta yake kuma ma son mai tsanani dariya abin ya bata ita ai ta zata so yana tsanani alokacin da shaƙuwa ta shiga, kuma ɗagowa dan ta ƙara kallok sa suka kuwa haɗa ido karaf, ya sakar mata murmushi, ta yi saurin ɗauke kai wannan wane irin mutun ne, so take ta nemo yadda zata iya faɗa masa magana ta kasa.

Ko fahinta ya yi da kwarjinin da yake mata oho, murmushi ya kuma saki, nifa ban son a dinga shiru, sunana Muhammad Muhammad Ƙaraye, an associate professor, nasan ba lallai ki sanni ba tunda yanzu kuka fara masters ɗin lokacin kuma kuna undergraduate naje masters, magana ta gaskiya Hafsa tunda na ganki na kasa samun sukuni har kawo yau da nake gaban ki.

Daurewa ta yi ta jawo jarumta dakyar sannan ta ce magana ta gaskiya shine yanzu my heart is shattered, kuma sabida so ne dan Allah mubar maganar soyayya pls.

Shiru ya yi na wasu daƙiƙi kafin ya furzar da iska, ki shi ne ya cika shi ya tsani abin da yake so ya zama wani ne cikin ransa bare Hafsa da yake jin tsananin son ta aransa, cikin nutsuwa bayan ya lauya zuciyar sa ya ce “Hafsa” sai da gaban ta ya faɗi a sanyaye ta ce na’am Sir.

Saurin kallon ta yayi a’a Hajiyata Muhammad zaki ce ni ɗin ina son wadda nake so ta faɗi sunana gaskiya inji daɗin sunana daga bakin abin sona.

Kai wannan rayuwa ta faɗa aramta shi kuma wannan shatouk Khan ne, yawwa na kira sunan ki baki ce me zance ba, kan ta ce wani abu ya ɗora “tunda kika shiga problems ɗin da kike batun so ne ya jawo miki shin bakya addu’a”

Kallon sa ta yi da alamu tambayar ta zo mats a banbarakwai, bai damu da yadda ta ɗauki maganar tasa ba yace me kike cewa a addu’a ɗin?”

Batai niyar bada amsa ba sai dai yadda ya zuba mata manyan idanun sa masu sata jin wani irin yanayi yasa ta cewa “ina yi cewa nake Allah ya sauƙaƙamin ya zaɓan mafi alkairin,” that’s it ya nuna ta da yatsan sa, gashi kuma Allah ya amsa addu’a dinki kike ƙoƙarin masa butulci, butulci kuma ta faɗa tana kallon sa.

Yes ai shi damuwar so tafi saurin tafiya a lokacin da ka samu sabon masoyi da ke ƙoƙarin cire wanda ke ranka ya sa kansa ciki, bacin haka kince alkairi kike nema kowa be zo ba sai ni, kika sani ko nine alkairin.

Murmushi tayi wannan karan pure smile ne, ya ƙara mata kyau yayin da shi kuma gogan ya ƙara narkuwa da soyayyar ta, yanzu dai kana nufin baza mubar batun soyayya din ba ko.

Yawwa ta waje na, kin fahinta, ya fada a wasance, sukai dariya duka.

Hannu yasa s aljihu ya cire wayar sa tare da miƙa mata, samun number ɗinki, ganin taƙi amsa yace Please Hansatu a taimaki bawan Allah, girgiza kai kawai ta yi tare da amsa wato namiji sedai in ba a gaban wadda yake son ya ma wayo ya tura mata son ta yake ba, mutumin da ko dariya bai cika ba bare magana ya zage ya na zuba mata zance.

Hannu tasa ta amshi wayar tare da rubuta masa number ɗin, ya amsa, zan kiraki bari naje zamuyi wani taro ne, da bs yanzu zan tafi ba, yadda nakejin kamar in ta zama ina kallon ki. Girgiza kai kawai tayi tare da cewa to na gode ka gaida gida.

Baice komai ba ya shiga motar sa sai da ta tada ta sannan ya zuro kai to Hafsatun Muhammadu sai na kira dan Allah ki ɗaga da wuri kar jiran jin sanyayyar muryar ki yasa zuciyata ta buga, bai jira amsar ta ba yaja mota yabar wurin.

*****

Kallon sa Bilkisu ta kuma yi so take ta gano Tariq ɗin ta ne ko kuwa wani ne, tabbatarwa da shi ɗinne yasa ta kuma binsa da kallo so take ta gano a hayyacin sa ya mata magana ko kuwa ya sha wani abinne duda tasan ko fanadol sai ciwon kai ya ci ya cinye shi, sannan in ta masa dole yake sha, kamo hannun ta da ya kuma yi tare da ƙoƙarin sa idanun sa cikin nata yana roƙar ta cikin murya rikitacciya mai nuna tsananin buƙatar da yake na ta amince da abinda yake roƙanta ya tsorata ta, kasa magana ta yi yayin da wani ƙululun takaici yazo mata wuya wai yau ita Tariq ke faɗawa ya kamu da tsananin son wata mace ba ita ba, kuma of all women ya rasa waye zai so sai Hafsa, tabbas Tariq na shirin rusa zumuntar da Allah ya haɗa, zumbur ta miƙe tare da kwace hannun ta, samun kansa ya yi da kasa miƙewa bare ya yi jarumtar bin bayan ta, dan faɗa matan ma ba ƙaramar jarumta ya yi ba, ido kawai ya bita da shi yayin da ta shige ɗakin ta da sauri, kansa ya jingina jikin kujerar da yake tare da riƙe goshin sa, kansa ke sarawa a yayin da zuciyarsa ke bugawa da sauri, a duk bugu guda son Bilkisu da Hafsa ke ƙara nunkuwa ciki, yasani yana son Bilkisu sosai haka ma yake jin yana son Hafsa sosai duk su biyun zuciyar sa na faɗa masa rayuwar sa ba zatai daɗi kuma tai dai dai ba in ba su.

Bilkisu na shiga ɗakin bathroom ta shige, hannu tasa ta murɗa makullum dan ma bata son ya shigo ya same ta duda yanayin sa bai mata kama da na nawanda zai iya tashi ya biyota ban baki ba.

Ta jima a zaune ranta na mata suya, wannan wacce irin masifa ce, tabbas namiji ya gama bata mamaki da abinda Muktar ya yi da kuma yau da Tariq ke faɗa mata ya kamu da son aminiyar ta wanda ita amanar ƙaunar ta da ta bashi batai tsanmanin ko ita ce ta samo mace ta kawo masa zai kalla ya amsa ba, bare shi da kansa ya nemo ya sanya zuciyarsa som ta.

Sam ta kasa kuka takaici da baƙin ciki sun tare mata a ƙirji, ganin tama kasa kuka ta kasa tunani yasa ta miƙe ta ɗauro alwala sallah raka’a biyu ta yi ta ɗaga hannu rasa me zata roƙa ta yi, ta jima hannun ta ɗage kafin ta fara faɗin ya Allah ka sanyayamun zuciyata kamar yadda ka sanyayawa Annabi Ibrahim wutar da aka sanya shi, tafi mintina tana faɗar haka kafin kuka mai tsanani ya kwace mata, sosai ta yi kukan har sai da dan kamta ta bawa kanta haƙuri sai kuma ta miƙe ta wanko fuskarta, tabbas kuka rahama ne haka kuma addinin musulunci ni’ima ne duda har yanzu kishin mijin ta na cin ta sai dai ƙuncin da ta shiga ɗazu duk ya baje a nutse ta fita zuwa falo, yana zaune tamkar yadda ta barshi duk sai taji tausayin sa ya kamata duda tana tausayin kanta musamman in ta tuna da wace zatai kishi tasan Hafsa nada shiga rai bare yadda tunma kan batun soyayya ko zaman aure ya haɗata da Tariq ya ruɗe haka akan sonta inaga in yasan daɗin zama da ita.

Ajiyar zuciya ta yi tare da jan ƙafar ta daƙar ahankali tana furta la’illaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalim, Hasbunallahu wani’imal wakil, lahaula wala ƙuwwata illah billa, ciki bata san wanda take fara furtawa ba kawai dai tasan furtasun yasa tana kuma samun nutsuwar zuciyar ta duda kishin nan nata maras iyaka dake zullon sawa ta kasa juya zuciyar tata, wanna yasa take son saurin dakatar da duk wani abu da ke yawo a zuciyar tata maras daɗi.

Hannu tasa ta sauke mass hannun daga goshin sa, a hankali ya buɗe idanun ya kalle ta, yadda ya ganta sai ya kuma jin haushin zuciyar sa, duda tsananin tausayin ta da yaji yakasa iya sarrafa zuciyar tasa ta yadda zai iya haƙurin rashin Hafsan.

Murmushi ta sakar masa, tare da sauke numfashi, kace Hafsa kake so ko, karka damu indai ni ce baka buƙatar in baka dama, ban isa in hanaka abinda Allah ya harramanta ba shi yasa ka auremu fiye da guda a halak ya kuma sanya Hafsa ta zama ƙawa ta, da yaso sai yayo ta jinina wadda bazaka iya zama damu a tare ba, sai bai yo haka ba, kaga ni ban isa na haram ta zaman mu matsayi mata da miji gurin ka ba.

Fatana Allah yasa ta amince kuma Allah ya bamu ikon faranta ma, kaje ka same ta duk yadda kukai ni mai shige ma gaba ce, ciwon kan ya nema ya rasa, cike da farin ciki ya kamo hannun ta yana zuba godiya, tunawa da yayi dole zataji ba daɗin zumuɗin da yake yasa shi hau yi mata addu’a da nuna bawai ko kaɗan son ta ya ragu a gunsa bane.

<< Ko da so 41Ko Da So 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.