Ruwa ake yi kamar da bakin kwarya hakan ya saka Mukhtar ko kofar gida bai samu ya fita ba. Zaune yake gaban tv rin falon sa wanda yake ji tamkar a makabarta yake saboda tsabar shirun da duniyar tayi masa. Sosai yake kewar Hafsah da yaransu sai dai ya rasa dalilin da yasa har yanzu ya kasa zuwa ya gansu. Gani yake yi tamkar ganin yaran zai sanya wani dalili ya dawo da Hafsah wanda shi kuma ba zai iya ba.
Kamar wanda ya tuna wani abu, a take ya mike ya tafi dakin su. Bude dakin da zaiyi, warin ruma ya daki hancinsa. Abunda duk shekarun su da Hafsah bai taba jin warin ba. Lallai mace itace fitilar gida! Zuciyar sa ta doka da rashin ta, take wani irin rauni ya lullube shi har ya taka yaje gaban wata drawer ya dauko wani album. Kayan drawer ma duk sunyi kura haka dai ya dauko sannan ya fito falon.
Sai da ya goge album din sannan ya nemi wurin zama ya fara bin hotunan da kallo. Yayinda idon sa ya sauka akan wani picture da Hafsah take kallonsa cike da soyayyarta mara algus, sai kawai ji yayi hawaye na sauka akan fuskarsa. Baiyi yunkurin goge su ba domin kuwa yana bukatar samun nutsuwa a zuciyarsa. Wata irin zuciya ce gare shi me tsaysauran ra’ayi musamman ma a game da sakin da yayi. Akan ya janye sakin Hafsah gwara son ta yayi ajalinsa. Wanda yake ji soj nata ne zai tura shi kasa. Ya zabi rasa numfashinsa a rashinta. Akan zama da ita da numfashinsa.
Hoton an dauke shi ne bayan ta haifi Ayman. Baya mantawa da irin nishadin da suke ciki ranar wanda ya saka har ma suka shirya kiran me hoto.
Kamar ba zai dena hawayen ba haka ya cigaba da kallon hotunan daya bayan daya.
Zuciyarsa ce take ta fada masa har yanzu bai makara ba. Har yanzu zai iya zuwa su sasanta amma da ya tuno dalilin rabuwarsu sai yaji ba zai iya ba.
Zaman sa da Hafsah ya kare.
Wannan shine abunda yake maimaitawa a ransa kullum. Saboda gudun rudim zuciya ma sai ya zaro wayarsa ya kira Rashida me bin shi. Bayan sun gama gaisawa yace,
“Dama nace in kina son furniture din gidana kizo ki kwashe su. Saida gidan zanyi a cikin satin nan.”
Mamaki ya cika Rashidan amma sai tayi saurin bashi amsa kar ma ya chanja ra’ayi.
“Gani nan zuwa Yaya.”
*****
Ganin ruwan da Bilkisu tayi yasa tayi sauri ta kammala girkin dare sannan ta samu ta shige daki. Duba lokaci tayi taga biyar ta gota. Ba shiri taje ta dauro alwala tayi sallah raka’a biyu sannan ta zauna ta dinga zubo addu’o’in samun saukin kishi da kuma cikawa da Imani. Dama biyu ce tayi amfani da ita. Ga shi sa’ar qarshe ta ranar jumu’a gashi kuma ana ruwa.
Sosai taji dadi bayan kammala adduarta domin babu wata mafita sama da addu’a. Yawan addu’arta ne kadai zai kawo mata sauki ita ta sani. Duk wanda zata gaya wa matsalarta babu me fahimtarta sama da Sarkin da ya saukar mata da jarrabawar. Shi ya jarrabeta kuma ta hanyar rokonSa take saka ran cinye jarrabawar. Kullum abunda take nunawa yaranta kenan. Ta kan basu misalai da annabawa da sahhabai a ko yaushe. Duk sanda suka shiga cikin wata damuwa ko matsala, Allah suke fara kira! Allah da kanshi ya ce da annabi Yunusa bai kasance daga masu tasbihi da kiran Allah ba, da ya dawwama a cikin kifi har abada.
Bayan addu’arta sai ta fara istighfari wanda yake taimakawa wajen amsa addua. Tana zaune tana salati ne taji sallamar Tariq wanda yasa a take zuciyarta ta buga. Mutum ce ita, mace ce mai son mijinta kuma take kishinsa. Hakan ya sanya raunin ta ya rinjayeta.
Da sauri ta goge hawayen da ya zubo daga idonta saboda tsabar kishin da yake cin zuciyarta. Duk da kaso me yawa na abunda take ji ya ragu, amma tunda Tariq ya fada mata qudurinsa tayi bankwana da kwanciyar hankali.
Sosai zuciyarta take mata ciwo. Ciwon so. Ganin duk irin zaman da sukeyi hakan bai hana shi hango Hafsah ba. Ko tun yaushe ma yake son ta? Allah masani. Idan ta tuna zai raba komai nasa ne da wata sai taji kamar ta kurma ihu. Kuma ko farincikinsa da zumudinsa baya boyewa.
“Me gadon zinare!” Tariq ya fada yana shiga dakin hannunsa dauke da ledoji guda biyu. Da kyar ta dora idanunta akan fuskarsa sannan ta dauke. Ya sake maimata sunanta cike da tarairaya.
Da kyar ta daga ido ta kalle shi sannan ta kakaro murmushi ta masa. Da saurinsa ya karaso yana me zama a kusa da ita. Sai da suka gaisa sannan ya janyo ledar gabanta.
“Wasu Abaya na gani na siyo muku…” ta so tayi murmushi da nuna zumudin ganin kayan yadda ta saba duk sanda ya musu siyayya ita da yaran.
Budesu ta soma yi sai taga size daya ne, hakan yasa ta kalle shi da alamun tambaya. Ko dai ya manto na yaran ne a can?
“Naga kawarki tana son abaya sosai. Su take sawa shine na siyo muku bibiyu. Ki zabar wa Hafsah nata. Ban san wacce kala ta fiso ba.” Sukuku ta tsaya tana kallon ikon Allah. Tun yanzu? Ko kunyarta ma baiji ba? Wani irin abu ya taso mata har wani daci take ji a bakinta. Anya kuwa kalau yake? Lallai ta yarda namiji ya zarce tunaninta.
Da kyar ta hadiye yawun da take ji ya tokare mata wuya tamkar an sanya dutse a wajen. Hawaye taji suna barazanar taruwa a idonta. Da dukkan jarumtarta ta mayar dasu sannan ta kalli kayan.
“Dukka zasuyi mata kyau. Ka kai mata.” Da haka ta mike tsaye ba tare da ta jira amsar sa. Shima mikewar yayi yana riko ta.
“Me ya same ki?” Kamar sukar mashi taji tanbayar tasa. Bata san sanda wata dariyar bakin ciki ta kufce mata ba. Ta dinga darawa har sai da taji raunin ta zai bayyana sannan ta dena.
“Akwai abunda zan karasa kafin Maghrib.” Ta zame ta fice ta barshi tsaye yana mamakin me ya same ta lokaci guda.