Skip to content
Part 44 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Binta Tariq yayi da ido kome yayi tunani oho kayan ya ninke ya mayar leda kafin ya miƙe yabi bayan ta, sai dai ɗakin yana rufe bai buga ba ya koma falo inda ya kunna TV yana nan zaune yaransu suka dawo inda ya mayar da hankalun sa kansu suka hau hira.

Jin motsin yaran nasu yasa ta fitowa fuskar ta ɗauke da annashuwa ba zaka taɓa cewa ita ce Bilkin sun da ke cikin damuwa ba.

Kallon yaran ta yi kafin ta zauna eyye sannun ku masu Dady wato tunda kun ganshi ni ko oho ko, dariya Hidaya tasa “wallahi na ɗauka ma bacci kike wallahi, we are sorry” dariya tasa to maza ku dena damar miji da hayaniya kuje ku dafa mana abinda zamu ci.

Miƙewa sukai tare da yin kitchen itama ta miƙe ya yi saurin kamo hannun ta a ɗan fusace ta jiyo har sai da ya tsorata ya yi saurin sakin hannun ta ba Bilkisun sa ya gani a fuskar ta ba, Bilkisun sa in ya mata irin wannan riƙon langwaɓowa take jikin sa cike da shauƙin so, “Lafiya dai ko?” ta faɗa tana kallon sa.

Haka kawai tsoron ta ya kama shi cikin rawar murya ya ce a’a gani nan kin tashe su, kema kin tashi kinsan bana son zama ni kaɗai dai ko, kallon sa ta kuma yi sai sai wannan karan murmushi take da bai da fassara sai dai a gun Tariq yasan ba murmushin farin ciki bane, a hankali, kan ya ce wani abu tace “ai kasan abinka da wanda ke fama da shauƙin so yana buƙatar a bashi isasshen lokacin da zai dinga tunanin masoyar sa” ta faɗa tare da juyawa ta yi gaba abinta ya bita da ido kawai.

*****
Dr Ƙaraye na barin gidan su Hafsa makaranta ya wuce baima kai motar sa wurin da staff ke aje mota ba ya faka harabar faculty ɗin da sauri sauri yake tafiya duk inda yabi ɗalibai da sauran staff ke gaida shi sama sama yake amsawa har ya isa studio ɗin inda ake gudanar da seminar.

Da yawan ɗaliban da basu gudanar da defense ɗin nasu ba hankalin su ya tashi ganin shigowar Dr Ƙaraye dan sun san da wahala in bai cancelled ɗin aikin nasu ba.

Kusa da professor Sani ya zauna suka ɗan gaisa a gajarce kafin ya aminshi Abstract ɗin Muhammad dake gudanar da presentation a yanzu, kai kace ada Muhammad ba gaban profs yake ba dan sautin muryar sa ma ya nuna tsoron sa.

Sau kusan biyar suka fito daga studio ɗin, Prof. Sani ya dubi Dr Ƙaraye cike da zaulaya ya ce anya kuwa yau cikin ɗaliban nan namu ba waliyyi ko waliyya naga kawai kallon su kake kana murmushi sam banji ka soki ko mutun guda ba.

Murmushi Dr Ƙaraye ya yi ka bari kawai zuciyar ce ta yi wani wuri wallahi, sam hankali na kan Hafsatuna, dariya Prof. Ya yi haba ko da naji shi yasa wato ka makara kenan kana can kana tunanin ta, Murmushi Dr. Ya yi ka bari kawai naje wurin ta ne fa sam na kasa haƙuri in bari sai goben inje.

Jinjina kai Prof. Yayi mutumina wallahi kana da zafin so yanzu da ace auren ta be mutu ba to kayi yaya kawai daga ganin yarinya ka tsundumu cikin kogin sonta.

Kallon sa Dr. Ya yi a ɗan rikice mutuwar aure kuma, Dariya Prof ya yi “kardai so ya rufe ma ido ka kasa kallon ta a matsayin wadda ada take da nata namijin ai cikin biyu ne dole ɗaya ta faru kodai mijin ta mutu ko ya sake ta, kasan dai yadda ka ruɗe ɗin nan dole ada wani ma ya ruɗe ya kuma kaita gidan sa.”

Ɗan ƙaramin tsaki Dr yaja har kasa na tsani koma waye duda dai ni yama kyauta da ya mutun dan nasan ba me haukan sakin Hafsatuna in ya same ta a matar sa.” Dariya Prof. Yasa kai dai Dr. Ka ruɗe kawai if not ni banga wani special thing about her ba. Sukai dariya duka.

*****
Motsin fitowar sa daga bayin yasa ta saurin jan hijabin ta, ta rufe fuskar ta, tamkar me nannauyan bacci, Riƙe da towel Tariq ya fito yana goge kansa da alamu wanka ya yi, idanun sa ya kai kan gadon su da yake tsaf gyare da zummar ya ɗora su kan Bilkisun sa sanye cikin kyakkyawar shigar ta da yake so sai dai wayam ya ganshi juya idanun ya hau yi tare dan neman ta cikin ɗakin yako yi sa’ar ganin ta bisa sallaya tana baccin ta a nutse. Murmushi ya yi tare da ci gaba da gyara jikin sa tana jin sa yana fesa mayataccen turaren sa me rikitaccen ƙanshin daɗi ta kuma lafkewa tamkar wadda ta yi nisa sosai a bacci.

Sai da ya shirya tsaf sannan ya ƙaraso in da take can ka ɗauketa ya ta yi tamkar baccin take tana jinsa ya kwantar da ita bisa gadon ya fi ce tasan ɗakin yaran su zashi don tabbatarwa kowa lafiya kan ya kwanta kamar yadda al’adar sa take, a nutse ta sauko ta dawo inda ya ɗauke ta, ta koma kwanciyar ta, bata fi minti uku da dawowa ba ya dawo ɗakin, numfashi ya furzar shi dai yadan cutar rikirar ƙwaƙwalwa bata same shi ba, bare yace tunanin shirme kawai yake, a hankali yadan yi murmushin gefen baki kafin ya kuma yunƙurin ɗaukan ta sai dai wannan karan bata bari ya ɗauken ta ba ta buɗe ido, fuskar ta ɗauke da murmushi tace a’a kaga mijin Bilkisu ango ga Hafsatu kuma mage sarkin son jiki, dan Allah kabarni anan inaso anjima ne zan tashi in addi?u’a.

Tamkar maras lafiya ya zuba mata ido cikin shagwaba tamkar wani yaro ya ce haba Habibty dan Allah ki taso kinji, kinsan fa bana iya bacci in bakya kusa dani zan tashe ki anjima ɗin, murmushi ta yi tare da langaɓar da kai irin yadda ya yi cikin salon tata shagwaɓar ta ce Pls D. Kaje ka kwanta kaji kar in kasa tashi bacci nake ji, ta faɗa tare da manna masa kiss a kumatu ta koma ta kwanta tare da jan hijabin ta, ba tare da ta jira me zai ce ba, shafa gun ya yayi tare da yin murmushi ya koma gado, tana jinsa yana ta juye juye har waya ya ɗauka ya kunna film, ya kashe duk tana jinsa itama ta kasa baccin sai dai ba zai taɓa ganewa ba dan lokaci lokaci ma yana leƙo kai ya duba ta, ransa a cinkushe, shi ko lokacin da ta haifi Hidaya da taje wankan gida be takura irin haka ba dan yasan bata nan anma yanzu yana ganin ta, ta ce wani addu’a zatai bacin baccin ta kawai take a nutse.

*****
Hafsa na kwance abin duniya ya ishe ta tun da sha biyu ta yi idon ta biyu take ta son ta miƙe ta yi koda raka biyu ce na sallah ta kasa ita kanta tasan tana da matsala in akazo ga addu’a, tana ƙoƙarin ta shi wayar ta, ta buga alamar kira, itakam tun zamanin tana ƴan matanci rabon da wayar ta, ta buga bayan sha biyu hannu tasa ta ɗauko Sharouk Khan taga na yawo kan screen ɗin murmushi ta yi aranta tana faɗin nima fa banda kirki Dr ɗin guda na sawa Sharouk Khan dan tama manta da batun sa bare sunan da ta sa masa.

A nutse cikin muryar ta me daɗi ta ce “Assalamu Alaikum” cikin muryar sa mai cike da kwarjini da daɗin sauraro ya amsa da “wa’aalaikumussalam, Hafsatuna kema kin kasa bacci ko?” ya tambaya muryar sa na nuna jikin sa ba kwari.

Murmushi ta yi tare da cewa “eh” jin murmushin ya yi har cikin ransa yayin da farin ciki ya cika shi tamkar ta ce tana son sa ne, a nutse ya ce “ har naji daɗi kema kewa ta ce ta hanaki bacci ko” kai kai wannan mutumi kwai tambaya ta faɗa a ranta yayin da ta tsinkayi muryar sa na cewa “ sefa haƙuri kinsan abinka da malami tambayar nake abada amsa in maka a biyani” anya ta faɗa tana dariya…

“Anya ba boka bane ko?” ya tambaya.

“Nifa na fara tsoro ya ake kake gano me zance anya…”

Dariya ya yi cikin kwaikwayon maganar ta ya ce “sabida nida ke ɗin zuciyar mu ta fara bugawa tare ina faɗa miki son da nake miki mai girma ne Hafsatu dan Allah ki daure ki buɗe zuciyar ki, ki sani ciki”

Tana murmushi ta ce “ah ai kai naga alamu a soyayyar ma ɗan fashin gurbin zuciya ne ba ruwan ka da amincewar me zuciyar kawai yakin ka ka tusa kanka”

Dariya ya yi sosai har mamaki ta yi wai wannan mutumin da su Zainab ke mugun shakku da ganin ikon sa ne ke dariya haka oh, “ ni fa kin ban dariya da yawa” wato dai kina nufin na fara nasara ko..

Da sauri ta ce nifa ba haka nake nufi ba, cike da zaulaya ya ce “ah nima Hafsatuna da wasa nake, nasan taurin ranki ai, sai na ɗaure damtse kan in ma zo bakin zuciyar bare shiga” maganar ta bata dariya sosai, mutumin nan kwai zaulaya yasan ta kan shawo kan mutun ko dan malami ne oho.

Sosai sukai hira, sai wurin biyu ya mata sallama ta re da roƙan ta, ta tashi ta musu addu’a Allah yasa haɗuwar su ta zama alkairi yasa ta zama matar sa, bai jira amsa ba ya kashe wayar, ta bi wayar da kallo tana murmushi itakam bata taɓa tsanmanin zata kuma murmushi ga batun wani namiji da ba Muktar ba, se gata harda darawa ga batun Dr Ƙaraye, duda tasan ba so bane sedai tanajin a sannu son ma zai samu.

<< Ko Da So 43Ko Da So 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.