Skip to content
Part 47 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

“Allah na gode maka!” Hafsah ta tsinci muryar mummy a kunnenta. Wata irin kunya ta lullube ta saboda sai da tasa yaran suka duba mata ko mummy tana falo kafin tazo shigewa.

Da kyar ta daga kai ta kalli mummy, fuskarta cike da murmushin da Hafsah ta manta rabon da ta ga irinsa a fuskarta. Sosai kunya ta dada kama ta sai dai yadda mummy taja hannunta suka nemi wajen zama yasa tayi ajiyar zuciya ta zub da makamanta.

“Abban ku yace sun gaisa ai wancan satin. Ya yaba da hankalin mutumin.”

Hafsah ta sake sunne kai kasa.

“In har ya kwanta miki, dukkan ku ba yara bane sai ki masa magana.”

Ganin dai Hafsah ba zata ce komai ba yasa mummy tayi dariya sannan ta tashi.

“In dai kece, zaki gaji.”

******

Rabon ta da gidan ta manta amma yau da sassafe ta shirya domin zuwa ta sauke ragowar nauyin dake zuciyarta. Sanye take da leshi mai tsadar gaske kamar ko yaushe. Hannayen ta cike suke da warwaro da zobunan gold.

Ta jima tana kallon kofar gidan kafin tayi ajiyar zuciya ta kashe motar. Ba zata taba son Mukhtar da ahalinsa ba ko me za’ayi amma yau daya dai zata danne wannan differences din nasu ta je tayi musu magana. Har yanzu ranta a bace yake dasu wannan shine babban dalilin zuwanta ma.

Da kyar ta fito tana jin wani abu yana mata yawo a rai har ta kai ga sallama.

Inna tana zaune tsakar gidan da har tiling dinsa anyi yanzu tana jin rediyo da yake dabiarta ce ta amsawa mummy ta shigo.

Da kyar mummy ta boye kallon kaskancin da take watsawa gidan don kawai kamar neman alfarmar su tazo yi ne.

Da fara’a Inna ta taso tana gyara dan kwalinta.

“Maraba lale. Sannu da zuwa Hajiya Hadiza.”

Murmushi mummy tayi sannan suka shiga ciki. Sai da suka gaisa sannan mummy ta fara bayani.

“Dama zuwa nayi da wata magana. A kan yaran nan ne, naga tunda suka rabu bai zo inda suke ba. A matsayinsa na uba hakan bai dace ba sam. A halin yanzu Hafsah ta samu mijin aure kuma kina ganin ko mijin yace zai rike su ya dace ta kwashi yara har hudu ta tafi dasu?”

Muryar mummy was low. For the first time. So kawai take ta raba Hafsah da Mukhtar har abada. Duk da dai yaran jininta ne, zata hadu dasu koya ya amma dai gara su raba hanya. Abun yana mata ciwo ganin zata raba uwa da yayanta amma babu yadda zatayi. Kiyayyar mahaifinsu ce ta shafe su.

Inna ta nisa. “Gaskiya ne. Ai kuwa ba yadda banyi da Mu’utar ba. Tunda Allah ma yasa ta samu miji, ai dolen sa yanzu. Kuma mun gode Allah saka da alkhairi da dawainiya dasu.”

Da kyar mummy ta amsa wani baqin cikin yana tokare mata wuya. Babu wata hira da ta shiga tsakaninsu bayan abunda ya kawo mummy. Haka ta miqe ta fice daga gidan amma har ta kusa isa gida ba ta dena jin nauyin nan ba a zuciya.

Wannan wace irin qaddara ce?

Mukhtar ba kaddarar Hafsah bane, qaddarar ta ne.

*****

Tun ranar da Tariq ya koma gida fuska a hade, Bilkisu ta rasa kansa. Wani irin zazzabi yakeyi da baya iya cin komai. Tun tana daukan abun wasa har sai da aka kira family doctor su ya duba shi yace hypertension ne.

Hankalin Bilkisu ya tashi sosai ganin me zai saka shi damuwa har haka kuma yaqi fada mata.

“Don Allah ka daure kaci. I made it with lots of love.”

Tariq ya kalli pepper soup din da ta ajiye masa da fatira amma sam yaji baida appetite din ci.

Ganin yadda yake ta bata fuska yasa Bilkisu ta gutsuro ta doni romon sannan ta kai masa baki. Kamar karamin yaro haka ya bude ya karba yana bata rai.

“Kawarki tana so ta datse miki rayuwar aure me cike da soyayya, Billy. Wai tana da saurayi. Ni kuma I can’t take it. Kishi yana nema ya kashe ni.”

Wani irin mamaki ya sake dibar ta. Wannan karan hakurunta fled outta the window. Ta kafe shi da ido sannan tace,

“Allah Ya maka rahama. Ina tausayawa yaranka na maraici da zasuyi don ba’a sauya uba…”

Bata jira amsarsa ba ta bar wajen wani irin baqin ciki yana cika mata rai. Wani irin mutum ne Tariq. Did he ever love her or he just settled with her? Me yasa yake nuna mata wannan halin tamkar ita ba mace bace? Me yasa yake kokarin nuna mata Hafsah ce burinsa? Ya manta amniniyarta ce? Koko ya dauka ita Bilkisu namiji ce yanzu?

Kuka ya kwace mata sanda ta isa daki. Wani dan karamin akwati ta gani. Ta debi kaya set biyu sannan ta fito. She was so happy baya falon. Ba tare da ta duba yaranta ba ko ta dauki mota, ta fice.

Barin shi za ta yi. Barin rayuwarsa za ta yi. She’s gonna disappear, forever if it warranted. Ba zata zauna Tariq ya kashe ta ba!

*****

Son da Dr Karaye yake yi wa Hafsah baya misaltuwa. Son ya kai yawan da yayi breaking dinta har sai da ta fara jin zuciyarta tana buga masa. Ko wacce gaba ta jikinta felt alive again. A wannan karan kuma babu fargaba a soyayyar. Wani irin calmness take ji da peace of mind.

Kamar yadda ya saba zuwa, yana zaune daga gefe ita kuma a daya gefen suna hirarsu sama sama ya gyara murya.

“Ni fa na kosa yanzu kuma…” haka kawai taji gabanta ya fadi.

“So nake ayi maganar nan a wuce. Ki nema min izini wurin Abba ya saka min lokacin aiko manya na. I can’t wait to dance with you in the rain.”

Ta kwashe da dariya. “Rayuwa ba fa film bace…”

Ya murmusa. “Sai dai in ba mu ga dama ba. Reality tana da wahala. Babu lefi in wata rana we pretend to be young and we play. Irin wannan su suke refreshing mind din mutum. Life is not supposed to be that boring you know?”

Hafsah ta sake kallon sa ta dauke kai.

“A gaban yaran?”

Zata iya cewa tunda suke tare bata taba ganinsa a yanayin da ya shiga ba cikin sakanni kadan. A take idanun sa suka kada kamar ransa yayi mummunar baci. Duk yadda yaso ya boye ya kasa don ko maganar kirki bai samu ya kara yi ba.

Da kyar ya tashi ya tafi sukuku ya barta ita ma da nauyin zuciya na tunanin mene zai saka shi acting that way lokaci guda.

Tana cikin wannan tunanin ne taji ihun murnar yaran da yake suna guje guje a tsakar gidan. Dago kan da za ta yi, taga Mukhtar.

Mukhtar.

“Mami, Abbiey ne yazo.” Taji an kamo hannunta. Ta rasa abun yi a lokacin. Da kyar ta karasa inda yaran suke ta murna while Mukhtar stood in all his glory.

Ta saci kallonsa kadan taga yadda ya rame, somehow sai taji wani rauni ya ziyarce ta.

Kamar yaran sun sani sai suka basu wuri.

Babu gaisuwa babu wata magana, Mukhtar ya sauke muryarsa qasa.

“Aure za ki yi, Hafsah?”

Bata san daga ina kwarin gwiwa yazo mata ba ta yi murmushi tana kallonsa har cikin ido.

“Eh. In a fortnight in sha Allah.”

Ya yi shiru kamar zuciyarsa zata fito amma bai ce komai ba. Sun dauki lokaci in silence kafin Hafsah ta juya.

Sanda ta isa daki, sai taji wani hawaye yana zuba daga idonta.

Shi Mukhtar, yafi mayen karfe naci a zuciyarta. Ta sani duk wannan lokacin kawai ta chanja fasali ne shiyasa take rayuwa babu tunaninsa, amma as long as she would be the old Hafsah, ba za ta daina son shi ba.

Mukhtar ne rayuwarta.

<< Ko Da So 46Ko Da So 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.