*Ko da So…*
*7*
Har Hafsa ta shige zuciyar Muktar bugawa take sosai ya kasa yadda ita ya gani da wani cikin ni shaɗi ya kuma kasa yadda da zancen ta da kunnuwan sa suka ji na aure zatai, yaran ne suka dawo dashi daga hayyacin sa ta hanyar yi masa sannun da zuwa Hannun sa ya kalla wanda Aiman ya riƙo yana masa sannu da zuwa “Abie ashe baka manta damu ba” yaron ya faɗa, murmushi Muktar ya yi ” ah ka taɓa ganin inda Abie zai manta da Aɗfal ɗin sa am busy ne shi yasa”. Faruk ne ya gaishe shi cike da girmawa kafin ya ce “Abie ashe zaka zo?” yaƙe ya yi kafin yace “zanzo mana yanzu ma zuwa na yi in tafi da ku”
Cike da mamaki Faruk ya ce “tafiya da mu kuma?” gyaɗa kai kawai Muktar ya yi “eh kuje maza ku ɗebo kayan ku sauri nake” su Aiman ne sukai ciki cike da murna ya yin da Abdallah ya bi bayan su jiki ba kwari har Faruk ya juya sai kuma ya jiyo ya ce “Abie Aure ka yi?” kallon yaron ya yi sai yaga ya cika masa ido ya kuma girma haka ne fa yaran su girma suke kuma hankali suke girgiza kai ya yi jiki ba kwari “no” kawai ya ce “maza ku ɗebo kayan Please ya faɗa.
Mum na zaune tana voice message da ƙawayen ta yaran suka shigo, bata damu da su ba ballanta ta musu tsawar da ta saba dan yanzu bata jin haushin su kamar da, dama can haushin Hafsa ta nacewa Ubansu ke bata haushi ta hakke kan su yanzu kuwa sam bata jin haushin su.
Ganin suna fitowa da kaya niƙi niƙi yasa ya aje wayar tare da miƙewa “Kai Faruk ina zaku haka da kaya ba na ce se ending month zaku dinga haɗa wanki ba?” kafin Faruk ya ce wani abu Aiman ya yi wuf ya ce “Ba wanki bane Abie ne ya ce mu haɗo kayan mu zai tafi damu” yaron ya faɗa cike da ɗoki da zirgilli iri na yara.
“what! Mum ta zaro ido shi Muktar ɗin ya ce kuzo ku tafi yana ina?” ta fada cike da ɓacin rai, bata jira amsar su ba ta zari hijabin da ta yi sallah ta fita yana tsaye jikin motar da Hafsa ke hawa tunda ta dawo gidan hango Hajiya da ya yi yasa yaɗan fara sosa kai tare da yake wanda ko laɓɓa bai kawo ba, duk nauyi da kunyar ta ya cika shi domin shi ɗin ya haifu dole yana jin nauyin iyayen Hafsa na sako musu diyar su.
Ɗan russunawa ya yi yana gaidata a hasale ta ce sannu isasshen mara mutunci wato rashin ta idon naka har yakai ka nuna mana iyakar mu ka nuna mana bamu isa ba, wato mu riƙe ma yaran tsawon shekara dan wulaƙanci bamu isa ba ka zo ka same mu kace zaka tafi dasu sedai ka gansu a harabar gida kace suzo ku tafi kai mai yara ko?, ce ma akai ita Hafsan bata da haƙƙi kansu ko me, ko kuwa sakin da ka mata be isa ba se ka zo ka tsinka mata zuciya, tunda kuwa in har aka nemi yaranta har biyar ba’a gani ba kan a gano ubansu ne ya sace su ai zuciyar ta bugawa zatai.
zai yi magana ta ɗaga masa hannu “bani da lokacin jin banzayen kalmomin ka wanda ba mutunci bare ladabi ciki kayi gaggawar barin gidan nan, randa ka shirya ɗaukan su ka dawo” fuuu ta koma ciki.
ajiyar zuciya Mujtar ya yi ransa na masa suya ya rasa wannan wacce irin rayuwa ce, shi bega abin da ya yi na rashin kyauwa ba jiya Innar sa ke faɗa masa Mum ɗin tazo tace yazo ya kwashe yaransa, ya zo kwashe sun abin ya zama masifa. Ya jima a tsaye kan ya bar gidan.
Hajiya na shiga ɗaki ta ce su maida kayan ba wanda ya ce wani abu sukai ciki, inda Aiman ya dire kayan rai ɓace lokaci na farko tun mutuwar auren iyayen su da tausayin yaran me tsanani ya kamata, kamo Aiman ɗin ta yi tana bashi baki abun yaro se gashi ya warware yana cikata da surutu.
Hafsa da ke tsaye jikin taga tanajin su ta koma gado yaraf ta zauna hankalun ta tashe me Muktar yake nufi na zai tafi da yara, wallahi bazai yiwu ba inma aure ya yi ba ruwanta dole ma ita zata riƙe yaranta tunda ba shi ya mata naƙudar ba, a karo na farko tun haɗuwar ta Muktar da bata ji ɓacin ran abinda Mum ta masa ba.
Kai tsaye gidan su Dala Muktar ya nufa Inna na zaune tana gyaran Salak ya shiga da sallamar sa amsawa ta yi tare da ɗagowa dan Muryar sa ta yi kama da ta me damuwa, kamar yadda ta zata fuskar sa ta nuna damuwa sosai gefen ta ya koma ya zauna tare da gaishe ta ya yi ta amsa cike da kulawa tare da tambayar meke damun sa.
Numfashi ya furzar kafin ya fara mata bayanin yadda sukai da Mum Salati Inna tasa kafin ta ce ” yanzu dama Muktar baka da tunani ai ko auren ku baka ƙare shi ba ko hutu suka je gidan ansan zaka tafi dasu ace ma kunyi waya ya dace ka shiga gidan kace kaga kazo, bare yanzu da bama a gunka suke ba, ai ko baka san Halin Hajiya Hadiza ba ka shiga kace zuwa kayi kaji yaushe zaka zo ks tafi dasu.”
Ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce ” kuma wallahi seda kika faɗa Inna nagano ban kyauta ba” murmushi ta yi ai yanzu seka san yadda zaka gyara.
*******
Jin da Dr Ƙaraye ya yi garin na juya masa yasa shi komawa gefen titi, ransa na masa suya zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri tsananin son da yakewa Hafsa ke ingiza wutar kishin sa, shikam bai shirya zama da yaran wani ba, hasalima ganin su kawai da yake takaici ke cika masa rai a duk sanda ya ɗora idanun sa kansu tunawa yake Hafsa fa da ta wani ce Bashi ba. Shi inbanda girman son da yake mata ba abinda zai sa auri wadda ta taɓa aure.
Ya jika a gun kafin ya ɗauki wayar sa hoton ta ne kan screen ɗin wayar tana murmushi, ahankali yaji damuwar sa na raguwa, ba komai zanyi kokari in cirewa raina kishin yaran nan abinda ya faɗa kenan a zahiri duda a ɓaɗini yasan abune mai matuƙar wahala, number ɗin ta ya hau nema tare da danna kira sai dai bata ɗaga ba, message ya rubuta na ban haƙuri yadda ɗazu ya tafi bai jira amsar ta ba ya wuce gida.
Kamar ko yaushe gidan shiru ɗaki ya wuce in da ya faɗa gado idanun sa rufe jin da ya yi zuciyar sa na bugawa lokacin da zuciyar ta ke zayyano masa Hafsan lokacin taba gidan Uban yaran ta yasa ya miƙe tsam bar bedroom din, dole ya nemar wa kansa mafita tunma kan ta gano baya son yaranta ko da yake basu ne baya so ba Allah ma yasani tuna masa da Hafsan ta taɓa auren wani ba shi bane ke ƙona masa rai.
**********
Cak ta tsaya lokacin da sukai kaciɓus da Tariq, duda ranta ɓace yake da shi, sai da gaban ta ya faɗi, sam bata so suka haɗuba wallahi, ta so ace zuwa ya yi yaga tabar masa gidan in yaso yaƙari ciwon sonsa ya auro Hafsan su sha soyayyar su, yadda ta shirya bama zai taɓo gano inda zata ba, dan bata shirya zuwa gidan su a mata dariya kan gashinan namijin da ta mayar uba na son mayar ta marainiya ba.
Kallon ta ya yi D. Ina zuwa haka da kaya niƙi niƙi, hararar sa tayi kan ta ce, tafiya zan I’m tired of this marriage!” a tsorace ya ce what?
Bata bashi amsa ba ta ce Please matsa zan wuce banso in yi dare a hanya, riƙo hannun ta ya yi tare da amshe jakar ya aje gefe ya yi saurin kulle gidan, yadda ya barta tsaye nan take har lokacin.
Ganin ba zata shigo gidan ba yasa shi aje jakar a bakin falonsu ya dawo ya kamo hannun ta, fuzgewa ta yi, so take ta yi kuka sedai sam ta dena bari yaga gazawar ta, tunda bama damuwa yake ba, matsalar sa kawai Hafsa ce.
Kamo ta ya yi yasan ya ta jikin sa ya ɗan shafa bayan ta kamar wata yarinya, sun jima a haka kafin ta ture shi ta yi ciki abinta.
Bin Bilkisu Tariq ya yi da Kallo shi dai yasan ba kishi take ba, tunda yafi kowa sanin yadda suke da Hafsa yasan zata fi kowa murna da ya auro mata Hafsan dan abotar su ta kara kauri to ko ciki ne da ita ya yi tunani yasan yadda cikin ke sata nunƙufurci murmushi, ya yi dan shikam yana son ƴaƴa a nutse ya bi bayan ta tare da ɗaukan jakar da ya aje duda yadda jin jikin sa ba kwari tun tabbatarwar da ya yi Hafsa na da mai zuwa wurin ta ɗakin Bilkisun ya nufa, tana zaune wayar ta a hannun ta ko ke take kallo oho.
Gefen ta ya zauna tare da kamo hannun ta D. Nifa na kasa gane miki kwana biyu ko dai ciki ne da ke. Fuskar ta a ɗaure ta ce ni kuma ciki, ai na gama haihuwa biyar ɗin da na haifa Allah ya anfana, a ɗan tsorace ya kalle ta ban gane kin gama haihuwa ba. Murmushi ta yi eh na gama so kake mu tara ma yara ka rasa yadda zakai da su na haifi biyar ga biyar ɗin Hafsa goma, ka bari in tazo se ta haifo ma wasu tunda dai ka auri mace ai kwa tara zuriya tare.
Zaiyi magana Ringing ɗin wayar ta ya katse shi, duban wayar ya yi ganin sunan Hafsa yasa ya zuba mata ido kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga tare da yin Sallama, daga ɓangaren Hafsa ta hau tambayar ya ta ji muryar ta sukuku, murmushi Bilkisu ta yi tare da cewa ba komai kawai ta na ciwon kaine.
Sannu Hafsan ta mata tare da cewa “kina gida ne?,” Duban Tariq Bilkisu ta yi kamar ta ce a’a sai kuma ta daure ta ce “eh ina nan” daga ɓangaren Hafsa ta ce tom shikenan gani nan Please kisa Hidaya ta jejjefa mub ɗan wake daga sch nake.” Tom kawai Bilkisu ta ce ta aje wayar.
Tariq ne ya miƙe jiki na rawa “bari kiga inje in jejjefa mata tunda in akace se su Hidaya sun dawo sai tazo yunwa ta dame ta”
Takaici yasa ta kasa cewa komai ya yin da shi kuma ya fice ya yi kitchen, wayar ta da kuma ƙara ta miƙa hannun ta ɗauka ɗan ƙaramin tsaki ta yi ganin sunan Hafsa again duda tasan ba ruwan Hafsan a duk abinda Tariq yake anma Haushin ta take ji, sauran ƙiris kiran ya katse ta ɗaya cikin sauri Hafsa ta ce kinga Dr ne yaji nace zan biyo tanan dama maganar sa zan zo muyi shawara ya takura yana son ya fito, to shine yace baku taɓa haɗuwa ba so tare zamu zo,” rasa farin ciki Bilkisu take ko kuma tausayin mijin ta, samun kanta ta yi da kasa cewa komai dan jin shiru yasa Hafsa tunanin ko network neta katse kiran tare da turo mata sako.