Skip to content
Part 50 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Tafe suke a mota kowa da abinda yake tunani aransa, dukan sitiyarin Dr ya yi da sauri ta kalle shi, duk ya haɗa gumu, cikin tsoro ta ce Dr baka da lafiya ne, faka motar ya yi yana wuci, so yake ya yi magana anma yasan ko me yace ba zai zama abu mai daɗi ba, fita yayi daga motar tare da fara bugun ƙirjin sa a hankali, muryar Hafsa ke masa yawo a kunne lokacin da take faɗa masa wai Tariq ita yake so, tsoro da tashin hankali duk ya cika shi yaga tashin hankali a idanun ta lokacin da Tariq ɗin ya faɗi kardai son Tariq ɗin take, kishi da tsoron rasa Hafsan duk sun cika shi. A nitse ta fito daga motar ta zagaya zuwa inda yake cikin muryar ta mai sanyi ta ce ” Dr baka da lafiya ne ko kishin ne?” Kallon ta ya yi da mamaki “ki shi kuma ni na ce miki ina kishi” murmushi ta yi “Haba Dr Amaduna Hafsan taka fa ba yarin bace ai na daɗe da karantar ka, yanzu dai mai ke damun ka?” Cikin raunannyiyar murya yace tsoro ne, wallahi hankali na ya kasa kwanciya kar inje in rasa ki ga wancan mutumin”

Numfashi ta furzar kan ta fe “Haba Dr ai kaima kasan ni ta ka ce, sannan ko maza sun ƙare bazan auri minin Bilkisu ba wallahi ko da ace kai da kake type of Man da nake so bazan ma ji ɗarsuwan son ka araina ba sabida kai nata ne bare Tariq wanda He is not the kind of man I envisioned as my partner” shiru Dr ya yi kan ya ce but ɗazu mai yasa kika rikice dan ya faɗi, reaction ɗin ki over him ya tsorata ni sosai fa” murmushi tayi ɗan gajere kafin ta ce “Given our close friendship with his wife , with whom he has children, I could never wish for her to lose her partner and have their children become orphans. Absolutely not.”

Maimakon ya bata amsa sai cewa ya yi “to yaushe zan turo?” tambayar ta zo mata lokacin da bata tsanmata ba, kallon ta yake cike da zargi da alamu so yake ya karanci reaction ɗin ta yayi ƙorafi, murmushi ta yi kan ta ce ” yo in ta nine ai ko yanzu Dr ka turo a ɗaura mana aure ko dan kar ƴan matan Faculty suyi nasarar kwace mun kai, anma ka bari ina zuwa gida zamuyi magana da Abba in yaso sai in faɗa ma randa ya ce” murmushi ya yi cike da jin daɗi har naji sa’ida a raina wallahi, batun ƴan matan Faculty kuma ai kaf ciki babu mace guri na keɗin ke kaɗai nake gani” murmushi ta yi karfa kasa in nutse a gun nan dan daɗi, yanzu dai zaka iya tuƙa motar ko kuwa in tuƙamu” murmushin shima ya yi ah zan iya ai tuni naji ƙarfi da kwarin gwiwa sun cika ni da jin ni ɗin Nimber one ne aran abar sona”

Buɗe mata motar ya yi ta shiga sannan ya kuna zagayowa ya shiga ɓangaren mai tuƙi kan ya ja motar yabar gurin, a ƙofar gidan su Hafsa ma sun jima suna hira kafin suyi sallama ya tafi. Kai tsaye gidan su ya wuce fuskarsa cike da annashuwa duk wanda suka haɗu da shi sai ya fahinci farin cikin da yake ciki, tamkar sun san da zuwan sa kusan ƙannen sa huɗu ne a falon biyu mata biyu maza suma sunzo, da sauri Kalil ɗan ƙanin sa na biyu ya taso da gudu yana ga Uncle ga Uncle, ya yi caraf ya cafe yaron yana dariya “my Darling shine kunzo haka baka sa an kirani ba, yaron ya yi, tun ɗazu nake cewa Hajiya Kaka tasa Dady ya kiraka tace wai a ƙyaleka in taganka ranta ɓaci yake” murmushi ya yi kafin ya ƙarasa jikin Hajiya Kaka wadda ke kishin giɗe gaidata ya fara yi taƙi amsaws tare da rufe idanu tamkar mai bacci murmushi ya yi tare da faɗin oh wannan rayuwa zamanin nan da ban mamaki mata sun dena gudun kishiya duk dan naƙi ƙaro miki kishiya kike kike wannan abin wai” da sauri ta buɗe idanun ta cike da mamaki yayin da ƴan uwan Dr da Ummin su suka kwalalo idanu cike da mamaki wai yau yaya Ahmad ke maganar aure wanda tun Mutuwar matar sa ko fahinta ya yi maganar aure zaks masa yanzu zai bata rai.

Kamo hannun Hajiya Kaka ya yi badai kishiya kike so ba shikenan karki damu ni Ahmadu na yanke shawarar cika miki burin ki fatana kar ki zo kishi kuma yasa ki sai ina rabon faɗa tsakanin ku, dariya ta yi cike da murna da saurin zama yayin da ƴan uwansa suka yo gun da sauri inda Ummi ta kuma zubo musu ido, juyowa ya yi ya dubi ƙanne nasa alamun mene haka suka sa dariya, “iyayan tsugwididi ku fita batun manya ne, Khairiyya ce cikin shagaba tace ya ya…. “Madan  a fice ace mace da auren ta ta ƙi dena shagwaɓa, maza ayi waje” ƙin fita da sukai ne yasa shi cewa wallahi narasa randa kuka rainani haka,” Umar ne ya matso yaya a ina take,” Kallon Ummi ya yi yadda take kallon sa yasan amsa take jira.

Ni Ahmad to a Hotoro take, ɗalibarmu ce a BUK, dama zuwa na yi in faɗa muku zan je gidan Kawu gobe in faɗa masa dan ya yi bincike kafin su ce in turo, duda dai ni gaskiya a nawa binciken ban samu aibu ba, anma kunsan ba yadda zai da nawa binciken ba, ƙannen sa ne suka hau buɗa inda Nura ya miƙe tare da fara kiran yayar su, kafin minti Talatin ta iso gidan, tuni gida ya haure da murna shidai Dr sai murmushi yake dan ya fisu jin daɗi.

*****

Ita kuwa Hafsa tana shiga gida Mum ta gani a falo tana kallo, sannu da hutawa ta mata har ta wuce ta dawo ta ce “Mum Abba kuwa ya dawo?” Murmushi ta yi ” bai dawo ba, menene?” Murmushi Hafsan ta yi kan ta ce ba komai, ta yi ciki, Mum ma murmushin ta yi kan ta ce aranta Hajiya Hafsa kenan yar gidan Abban ta in ya dawo aka faɗa masa maji ta ci gaba da kallon ta.

Sai bayan lisha’i Hafsa ta miƙe ta yi ɗakin Abba yana zaune shi da Abdallah suna hira suna dariya, daga baƙin kofa ta tsura musu ido aranta tana faɗin oh rayuwa kenan ada a irin wannan lokacin tana shekarun Abdallah ita da Abban suke zama, ita sai yanzu ma da ta kalli Abban sosai taga ya ƙara girma ya yi furfura, da sallama ta shiga sannu da hutawa ta ma Abba ta ɗan sa musu baki a hirar tasu kafin Abdallah ya miƙe ya fice sai da suka taɓa hirar siyasa da Abban kafin ta ce dama Abba mutumin da yake zuwa wurina ne ya ce yana son ya turo, nace sai na same ka tukun.”

Shiru Abban ya yi kafin yace ” shi Muktar ɗin shikenan ya katse auren naku? Na yi tsammanin ko dan yaranku zaku haƙura ku sasanta kanku, na yi niyar tun kanki gama idda in masa magana sai kuma na fasa a zatona zai iya hucewa da kansa ya zo”

Shiru ta yi tana jin Abban sai da ya kai ƙarshe sannan ta ce “Abba batun Muktar ya zama shuɗaɗɗe a rayuwa ta, duk abinda zan kan ya yi haƙuri ya maida auren yaƙi, bansan mai na masa ba, kana gani yaran ma yadda ya banzatar da su, sai fa shekaran jiya yazo Mum ta kore shi wai yazo tafiya da su” shiru Abba ya yi “shikenan ai, shi wannan ɗin a ina yake, kuma kina sonsa ko kuwa haushin Muktar yazo ɗeɓe miki kaya ne yasa kika ce ya fito?” Dariya ta yi kafin ta ce ai Abba kaima kasan ko da banyi auren huce haushi ba ballanta yanzu da na kuma hankali,” dariya ya yi shima “eh to kuma haka ne kin ɗanyi hankali tunda har kika gama biƙin ɓacin ran sakin nan da aka miki banji kinƙi cin abinci mun kwanta a asibiti ba” dariya tasa indai zaulaya ce to Abba Number one a hankali ta ce “oh rayuwa kenan Allah dai kar ya kaimu abinda ba zai wuce ba”

Amin Abba yace kafin ya ce “to shi wannan ɗin a ina yake?”

“Eh to ba wani abubuwa nasani kansa ba, nadai san mutumin kirki ne, sannan Malami ne a faculty ɗinmu sannan yadda ake batun ƙimar mafinsa yasa ban ji ɗar kan tushen sa ba, ɗan gidan Alhaji Ibrahim Maikalanzir Ƙaraye ne” ta faɗa “ikon Allah Abba ya ce aikam mahaifinsa abokin Alhajin mune, Allah ya musu rahama duka.” Murmushi Hafsa ta yi yayin da Abba ya ce ” shikenan zan ɗanyi bincike kafin in ce ya turo din” hira suka sauya wanda Abba keta tsokanar ta wai shi ta gaɗa wurin zafin soyayya.

*****

Da sauri ta bar wajen tana maida kukanta. Ta dade a dakinta wanda har sai da ya bita yaga me takeyi. Yana shiga ya hango ta, tana tsaye tana linke kaya ta baza akwatuna a ƙasa da sai faman zuba kaya take, duban ta ya yi “haba D. daga dawowa sai faman aiki ki zauna ki huta mana,” banza ta masa ta cigaba da zuba kayan ta, bai ce komai ba ya cigaba da kallon ta.

Sai da ta gama tsaf sannan ta ta hau ƙoƙarin fitar da su, cikin razani ya miƙe ” D. Mene haka ina zaki da kaya kuma” cikin kufula ta ce “tafiya zan kuma wallahi na tafi bazan dawo ba, karkayi tunanin dan banda gata Abba ya mutu, sai Mama innaje gida za’amin dariya ace dama ni na ɗaukeka mutun bazan iya tafiya ba, wallahi da gata na kadai san ina da gida, na kuma yi girman da innaje na ɗauki yarana muka zauna ba me mun ciwon baki” da sauri ya riƙo ta cikin tashin hankali yake magana ” Haba D. ni yaushe na ce baki da gata fisabilillahi, dan Allah ko me na miki dan girman Allah kiyi hakuri” ture shi ta yi, “ka faɗa mana aikin ka ya nuna haka, tunda gashi sabida ka ɗauke ni banza wai kaine da kanka zaka ta shi ka ɗorawa wata mace da baka aura ba girki, anya Tariq kama taɓa sona kuwa?”

Sosai ya tsorata da lamarin Bilkisu, ta sani sarai yana sonta kamar ransa anma ta ke tambayar sa haka, yanayin fuskar ta ya kuma tsorata shi, da Bilkisun sa ta da ce da tuni tana kuka suke wannan maganar anma fuskarta ƙamas alamun ta kai maƙura, kamota ya yi ya sanya jikinsa ya shafa kanta, ta yi ƙoƙarin ta ƙwace ta kasa kuka ne ke ƙoƙarin ƙwace mata sai dai ta sa ma ranta ta dena kuka kan Tariq, da ƙarfi ta ƙwace kanta cikin ƙunar rai take faɗin “kasan mai yasa na ƙi tambayar ka saki?” Zaro ido ya yi saki kuma abakin Bilkisu a ransa yace innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, kafin ya ce wani abu ta ce ” sabida haramun ne dan haka ka matsa in wuce in ba haka ba kuma ka sake ni na gaji in yaso zanta istigfari har zuwa ranar da zan duniya”

Cikin rikicewa gami da faɗa ya ke magana “kinsan Allah Bilkisu ba zan sake ki ba, kome zakiyi, inkina jin auren da ake cewa takalmin kaza mutu ka raba to namu ya wuce nan, dan har a lahira muna tare ki tafi in tafiyar ta fiye miki, anma ki sani da aurena kika tafi, wanda kuma kinsa fitar mace bada izinin mijin ta ba na nufin tsinuwa, ba zan gaji da roƙon ki yafemin ba, in har kinga ba zaki yafe ba to ki daure dan Allah ki zauna dan girman Allah da kuma darajar yaranmu” jakar hannun ta aje ta riga ya cuce ta tunda ya haɗa ta Jallah wato Allah,” ajiyar zuciya ya yi yasani dama indai zaice Allah to zata haƙura, yasan lagonta tuntuni duk iya fushin ta in ance Allah an gama mgn.

Jakunkunan ta ɗauka ya mayar mazaunin su, tare da buɗe babbar ya mayar mata da kayan da take sawa a wardrobe ya jere kafin ya fice, Fruit ya yanko da haɗo mata da madara ya kawo mata,cikin faɗa ta ce ya ɗauke ya kaiwa Hafsa, tsuru ya yi yana kallon ta “Nima ka kyale ni zan zauna a gidan nan ne sabida girman Allah da kuma yarana” kaima kayi zaman yaranka in ka auro Hafsan in yaso sai ku fara zaman aure… Numfashi mai ɗumi ya furzar yau ya yadda mai haƙuri bai iya fushi ba, yasan babban aiki ne gaban sa dole sai ya jure, zai aje cikin faɗan da yafi na ɗazu ta ce kar ya ajiye, da sauri kamar da gaske yaji tsoron ta ya ɗauka ya fice, a ƙofar ɗakin ya tsaya yana kallo ɗakin yayin da ita kuma ta fashe da kuka.

*****

Abba na zaune Sadik yayan Hafsa ya shigo da Mum suka gaisa kafin ya mata bayanin kan Dr da Abba yace ya yi bincike yazo cike da Murna ta ce Abban nasu na falon sa ya je ya same shi, da Sallama ya shiga, Abban ya amsa, bayan sun gaisa ne Sadik ɗin ya ce ” dama Abba kan mutumin da ke zuwa wurin Hafsa ne na yi bincike ta fannin asali baida wani aibu, haka halayya, sannan yana da aikin yinsa, ya taɓa aure sai dai yanzu bai da aure matar ta rasu gun haihuwa tun lokacin bai nemi aure ba sai yanzu” murmushi Abba ya yi kan yace “Allah kenan girman sa yafi gaban wasa ko anan ma ai ya nuna dalilin mutuwar aren Hafsa tunda in har tana gidan Muktar ba zata taɓa auren wani ba, shikenan kuje ku fara shirye shirye tunda duk su biyun ba yara bane ni dai daga wurina gaskiya bana son aja lokaci sai dai in iyayaj nasa sunzo in sunce bai shirya ba, sai ajira din” murmushi Sadik ya yi kan ce ” tom Abba Allah ya basu zaman lafiya” “amin ka turon Hafsan ” Tom ya ce kan ya fice.

Tana zaune tana duba takarda yayan ya shigo suka ɗan taɓa hira yana tsokanarta wai yaji ta fara ƙamshi na amare tana dariya kafin ya ce ta je inji Abban.

Tana shiga Abba ya ce ah kaga manyan amare yana ga har an fara glowing dariya tasa ta rufe fuska, kaga Abba kana ban kunya wallahi, shima dariyar ya yi kajiki Hafsan ce takejin kunyar Abba, zama ta yi sannan ta masa sannu da hutawa, bai daina tsokanar ta ba, sai da ta marairace tamkar zatai kuka kafin ya ce mata ta faɗawa Dr ya turo, daɗi ne ya cikata sai dai taɗan maze, cike da zaulaya Abba yace “a’a Hajiya fito da farin cikin nan kar ya cika miki ciki muji durum” dariya suka sa duka.

Sai da sukai hira sosai kafin Hafsa ta koma ɗaki, tana shiga ta kira Dr yana saune yana marking papers na student tana yana ganin sunan ta kan screen ya hau murmushi kalmomin ta suka ƙara faɗaɗa murmushin sa, daga muryarsa kana iya jiyo murna da farin cikin sa, kai kace wannan shine auren fari da zai yi a rayuwar sa.

 

<< Ko Da So 49Ko Da So 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×