Skip to content
Part 48 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Da ace allura za ta fadi a cikin falon, tsaf za a iya jin sautinta. Shirun da Bilkisu tayi, tunanin mafita kawai take yi. Ya zata yi ne? Kamata yayi ta ji farin ciki amma sam sai taji bata ji komai ba.

Text din ta karanta taga still Hafsah tana fada mata kan zuwan da zasu yi da Dr Karaye. A hankali ta kalli Tariq sannan ta maida kallonta zuwa wayar.

“Ta ce wurinka za ta zo akan karatun ta. Kar ka yi kauron baki dai. Hafsahn ka tana son fruits, bari na dan fita ta na samo mata.” Da kyar Bilkisu ta gaya masa hakan don so take ta fice kawai ta barsu. Bata son ganin yadda abun zaiyi unfolding. Sannan ita kanta bata gaskata karfin zuciyarta ba. Wani irin haushin Hafsah ne ya cika ta fiye ma da haushin Tariq din. Mafi sauqi shine ta nemi excuse din fita.

Shi kuwa yana jin abunda ta ce, a take fuskarsa ta dau haske ya fara washe hakori. “Dadi na dake kina taya ni son Hafsah. Ina son ki Bilkisu.” Ya tashi ya rungume ta. Har ya sake ta bata san me take ji game da shi ba.

“Bari na miki transfer.”

“Zanje na shirya.” Ta wuce daki sannan ta saka hijab ta fito da saurinta. Bata so ta tarar da Hafsah.

Ganin alert din dubu ashirin yasa ta sake kallon Tariq sannan tayi murmushi. Har gate ya rakata yana cewa ta zabo masu kyau. Da murmushi kawai take binsa har ta bar harabar gidan.

*****

“Ita wannan aminiyar tamu, a ina kuka hadu?”

Hafsah ta kalli gefen titi sannan tayi murmushi kafin ta bashi amsa. “Best friend dita ce tun muna secondary school. Maganar da nake ma friendship din mu ya fi fifteen years yanzu. Ta zama yar uwa a gare ni.”

Dr Karaye ya jinjina kai. “Naga alama kam. Ina fata har a aljannah ku sake haduwa.”

“Ameen. Tana da kirki sosai, in mukaje zaka shaida. Ta rasa mamanta da wuri amma sai Allah ya bata miji wanda maye mata gurbin komai na rayuwa. Ina alfahari da irin soyayyar daje tsakaninsu. Kamar dai Layla da Majnu.”

Dr Karaye bai san sanda yayi dariya ba. Kullum yarintar Hafsah na kara burge shi sama da komai. Sannan kasancewar bata da wani corner a maganarta ko abunda ke ranta, yana sake sakawa yaji ta a ran sa.

“Ashe soyayyar tasu bata kai karshen mataki ba in dai kamar Layla da Majnu suke…”

Kafin ya karasa Hafsah ta karbe tace, “kamar Romeo and Juliet toh.”

Ya girgiza kai. “Sam. Dukkan su ba suci moriyar so ba. Duk mutuwa sukayi saboda so. Ni a wurina they are not supposed to be love icons. Ai kaso mutum, ka rayu dashi cikin wannan son, shine riba. Just like us right now. We are about to be bound. In kina son bada example akan love daga yau, sai kice kamar ta mu.”

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Hafsah. In dai words ne, leave it to Dr Karaye. Ya iya zance. Ya iya karbe zuciya. Mukhtar dinta was more of an action guy and ya burgeta a hakan. Yanzu kuma sai taji ashe all these while tana bukatar kalaman. Yadda Dr ya ke sakata hawa gajimarai a zuciyarta yafi karfinta. Soyyayar sa me zafi ce. Ta Mukhtar me sanyi ce. Yanzu take ji tabbas da Dr Karaye ta fara sani, shi zai cinye da kalaman sa.

Kalaman suka saka mata wata nutsuwa dashi. Ta gama yanke shawara. Bilkisu kawai take jira. Ba za’a wani saka dogon lokaci ba tunda dukkan su ba yara bane. Shiru ne ya cika motar banda nuna masa hanya da take tayi.

Suna isa kofar gidan suka parking.

“Ki fara shiga sai ki min flashing na shigo daga baya. Ko ki zo ki shigar dani. Abunki da me neman shiga, dole naji kunyar introducing dina da za’a yi.

Harararsa tayi cikin sigar wasa sannan ta fita da murmushi a fuskarta.

Tana bude kofar gidan ta hango shi zaune akan plastic chair kamar yana jiran wani abu. Da sauri ya miqe, wanda hakan ya dan tsorata ta ganin yadda yake abu kamar hankalinsa baya tare dashi.

******

Zaune yake gaban computer yana editing wasu layouts akayi knocking a kofar office din nasa. Sai da ya gayara murya sannan ya bada izinin shigowa.

Ana bude kofar ya kalli wanda ya shigo.

Sarah ce. Secretary dinsa. Dauke kansa yayi saboda yasan official visit ne. Bai wuce tace kwana biyu da baya nan wasu sunzo enquiry ba. Construction company dinsa yayi suna so ko yaushe a cikin samun clients yake.

“Yaya Mukhtar.” Ta furta a hankali. Har cikin zuciyar sa sai da yaji yadda ta kira sunan da wani irin sanyi. Sannan yaushe ma ta fara kiran sa da Yaya?

Ganin tayi grasping attention dinsa ne ya saka ta cigaba, “you need to take things easy on yourself. Share. Share with your wife. Kwana biyun nan har reply na mails dinka akwai errors.”

Mukhtar ya dan kalle ta kadan sannan yace, “na rabu da mata ta and it’s killing me Sarah. She’s the navigator of my life. Shiyasa zaki ga na samu matsala but do you know how i can move on?”

Zuciyarta tayi breaking. “Ku sasanta.”

Mukhtar sai da yaja wani numfashi da yake jin kamar yana ji masa ciwo. “Ba zai taba yiyuwa ba.”

Shiru sukayi kadan kafin a hankali ya kalle ta for the first time yana asessing dinta. Kyakkyawa ce. Kamar Hafsah. Hasken ta ma kamar na Hafsah ne. She’s a bit chubby and short. Ba doguwa bace amma.

“Thanks Sarah.”

Ta gyada kai sannan ta dauko wani flask ta ajiye masa a kan table din.

“Lunch. It’s past 5 already.”

Ba tare da ta qara cewa komai ba ta bar office din. Idon Mukhtar ya dade akan kofar kafin ya dauke idonsa. Budo message yayi a waya sannan ya budo sunan ta.

‘ Can we talk?’

Haka kawai yaji zuciyarsa ta fara harbi da karfi. Anya zai iya kuwa? Kamar cin amanar son da yake wa Hafsah ne. Nan take kuma ya tuna ita Hafsah ai bata duba shi ba. Gashi har zatayi aure.

A hankali ya danna send yana jin wani baqon yanayi da maimaikon yaji excitement sai ya sake jin wani irin baqin ciki da haushin kansa akan sakin da yayi.

Me yasa baiyi hakuri da abunda kaddara ta zaba musu ba?

*****

“Ya Tariq mene ya faru?” Hafsah ta tambaya tana tsayawa daga inda take. Tsoro take yace mata wani abu ya samu Bilkisu saboda dama call din nasu ya yanke abd Bilkisun bata yi mata reply ba.

“Ma kika gani?” Ya tambaya.

“Your hand is shaking.”

Da kyar ya waske. “Ba wani abu. Shake din love ne.” Ya aro jarumta ya fadi. Bilkisu ta fada masa he should be straightforward in ba haka ba Hafsah ba zata fahimce shi ba.

Tayi murmushi. “Na katse muku hirar love ne kamar ko yaushe?”

Tariq ya danyi nervous darling sannan yace, “wannan karan dai kin shigo gidan dan ki kara mana love…”

Hafsah tayi murmushin rashin fahimta tace, “Saboda mun zo da Dr?”

A razane Tariq ya kalle ta. “Wa kenan?”

Cikin zumudi tace, “My fiancé. Wanda zan aura, stamp din Bilkisu nake jira kawai.”

Wani irin jiri ne ya fara dibar Tariq. Da kyar ya koma ya zauna a kan plastic chair din. Kar dai ya makara?

“Hafsah ina son ki. Bilkisu tana sonki. Don Allah ki tausaya min ki shigo gidana. Our love is so big to accommodate you. I need your love to have a complete life.”

Kamar wadda aka juyewa baron kankara haka Hafsah ta daskare a wajen. Da kyar ta hada kalmomi a bakinta.

“Is this a prank? Ko a April muke?”

Tariq ya sake tashi. “No. I love you Hafsah. Don Allah ki aure ni. Bilkisu is so excited to share me with you.”

“Tariq? Ka samu matsala ne? Kasan me kake cewa kuwa. Dama naga hannunka yana rawa, is that a sign of an illness ko aljanu ne? Ina Bilkisu?”

Hafsah bata san sanda ta fara jero tambayoyin nan ba.

“Ko daya. Na dade ina sonki Hafsah. Taje siyo miki fruits.”

“Maybe I’m possessed.” Ta fadi hadi da yin waje ta kira Dr Karaye shi kuma Tariq ya bita.

“Mine, kaji wai Tariq ne yake so na. Ka karanta mun ayatul kursiyy ko na taka kan aljani a kofar gida. Dama mummy tace bana adhkar kullum. Innalillahi…”

Wani irin kishi ya cika Dr Karaye. Da kyar ya kalli Tariq yace.

“Hafsah mata ta ce. Har sadakinta yana aljihu na. Daurin aure kuma wani satin ne. A kula da kula matar wani.”

Ai kafin kace me, Tariq ya zube a wurin.

Tashin hankali duk ya baibaiye su. Hafsah ta dinga rokan Dr sukai shi asibiti.

“Kinsan Allah ba zan dauki wani gardi a mota ta ba. Musamman ma da yanzu ya gama cewa yana son ki. Ki dai kira matarsa ta zo ta taimaki kayanta.”

Sukuku Hafsah ta tsaya tana kallon Dr Karaye. Zata sake magana ya girgiza mata kai, “alfarma daya ba don naso ba shine na jira zuwan matar sa amma ba zan barki ki bi su ba balle kuma na saka shi a motata.”

Kallon yadda Tariq yake a sheme a kasa ne yasa Hafsah ta kauda mamakinta ta dannawa Bilkisu kira.

Cikin kidima Bilkisun tace gata nan zuwa.

Ba a wani jima ba tazo duk a rude. Ashe bai fita a ranta ba. Ashe shi dinne rayuwarta. Kan kace me hawaye sun wanke mata fuska.

“Dan Allah ka kama min shi…” ta fadawa Dr karaye wanda banda tafasa babu abunda zuciyarsa keyi.

“Wuce mu tafi.” Yace da Hafsah sannan yayi gaba. Babu wata maganar kirki suka bar wurin. Har suka yafi Hafsah bata dena ganin yadda Bilkisu take ta kiciniyar daukan Tariq ba.

This life!

****

A hankali ya bude idanuwansa ya sauke su akan Bilkisu wadda take zaune daga wurin kafarsa tana gyangyadi. Bai sani ba ko awa nawa yayi kafin ya tashi. Miqe kafar yayi wadda ta din bige ta, hakan yasa ta farka.

“Alhamdulillah.” Ta furta tana yiwowa kansa ta duba shi. Murmushi ya mata kadan kafin tayi magana yace,

“I am fine me gadon zinare.”

Rabon da ya fadi wannan sunan ta manta. Haka kawai sai sunan ya tuno mata da ranakun farkon auren su. Yadda ya dinga cika ta da kalaman irin son da yake mata. Yace ai shi sunan ta ya dace da ita. Babu wata Bilkisu kamar tasa. Kwalla ce tazo mata ido, ta goge sannan ta kama hannun sa.

“Sannu, meye yake ma ciwo?”

Ya girgiza mata kai. “Babu. Na kan nemi dikkan ciwo na rasa in ina ganin ki.”

Hnmm tace sannan ta nisa, “ba fa Hafsah bace. Bilkisu ce.”

Murmushi yayi mata sannan ya juya kansa. Ba wanda ya sake cewa komai banda fitar da tayi ta je kiran dr. Yana zuwa kuwa ya sallame su tare da warning kan avoiding duk wani abu da zai sa jinin sa ya hau.

Ko a hanyar ma da Bilkisu take driving basu ce komai ba. Dukkan su ba tare da magana ba cike suke da fargabar makomar aurensu. Ko bai gaya mata ba, ta san bai yi nasara ba. Kuma ko bai gaya mata ba tasan ya hakura. Amma da wani irin rashin ta idozai kalle ta? Al’amarinsa ba zai dena bata mamaki ba. A yanzu haka bata san a wani matsayi zata dauke shi ba sam. Bata san me take ji game dashi ba duk da dai tasan wannan son ya na nan

  • Amma ko da so, ana kin mutum. Ko da so, ana kasa zama da mutum. Ko da so… abubuwa da dama suna tasowa.

Har tayi parking basu ce komai ba suka shige gidan wanda suke ci har iskar sa ta chanja.

“I am really sorry…” he trailed off as if he was lost of words. Bilkisu ta kalle shi da alamar tambaya.

“What for? Dr?” Yana jin yadda ta kira shi da Dr sai da gabansa ya fadi. Tun sanda ya kammala phd dinsa ya gaya mata baya son sunan kuma bata sake fada ba.

Cikin helplessness ya riko hanneyen ta. “Please.”

Ta girgiza kai. “Hakurin me kake bani wai?”

“Yau nake realizing irin ciwon da kika ji da na fada miki ina son Hafsah.”

Dariyar bakin ciki ce ta kwace ma Bilkisu.

“Really Tariq? Da bata yi breaking heart dinka ba ba zaka taba ganewa ba ko? Ka dauka ni Dutse ce? Ko kuwa menene ko kuwa duk a cikin raini ne saboda bani da farar fata irin tata?”

“Haba Bil.. i made a mistake. Ki yafe min.”

“You know what? To hell with your apology!” Da haka ta bar wurin kuka yana kwace mata.

<< Ko Da So 47Ko Da So 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×