Skip to content
Part 53 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Soyayya ta kankama, kamar babu gobe… Cikin ƙanƙanin lokaci aka sa auren Hafsa da Muktar yau aka shirya ƴan uwan Muktar zasu kawo lefe nan gidan su Kausar akai zasu kai Mum har da ita sai dai da aka ce gasu nan sun zo ne yasa ta shige ɗaki dan da kunya ace harda uwar diya a amsar kayan lefe. Bayan lokaci bakin suka karaso da kayan Hafsah wadda tana can cike da farinciki.

A wulaƙance suke ɗaga kayan tamkar kashi yana yin yadda aka amshesu yasa suka sha jinin jkin su, da alamu dangin Hafsa dai sun raina kaya dan gefe ma aka tura akwatunan bayan ɗaga atamfa biyu zuwa uku, gwaggon Muktar ce ta miƙe kamar sauran jira suke suma suka miƙe, Hajiya Umma ce ta ta buɗe jaka, yawwa ga tukwici kar in manta ta faɗa fuska a shaƙe bandir ɗin ƴan ɗari biyar biyar ne guda huɗu, kasancewar abune na aure kuma al’ada yasa Gwaggon Muktar amsar kuɗin inda ba haka ba wallahi cewa zatai su barshi, plates ɗin snack ɗin ƴan matan dake ƙaramin falon suka fito da su suka bi bayan masu kawo lefen, suna kaiwa bakin falon wata cikin dangin Hafsan ta ce kuma fa amsa sukai ba kunya ba tsoron Allah, dariya gwaggon Hafsan ta yi yo ba dole su amsa ba kuɗi ne fa, kamar Gwaggon Muktar zata jiyo sai kuma ta fice daga falon.

Sai da Mum ta tabbatar sun fita sannan ta fito falon tun daga kan design ɗin akwatunan ran Mum ya ɓaci, kusan tun shekaru da suka wuce akai ya yin su, Hajiya Balaraba ce ta jawo kayan Bari in kuma gani, ni yadda ake faɗar yaron beda aikin yi ma se naga ya yi ƙoƙari har da su kwaddebuwa fa yasa, Hajiya Hansatu ce ta ce ke Hajiya ta ƙaramar ce fa, murmushi Hajiya Balara ta yi Haba Hansatu kina nufin zaki fini sanin zani ne nida nake da mall ta faɗa tare da fito da atamfar, lah aiko Babbar ce sai dai kalar ƴan ƙauye ce, kuma fa wai a haka ɗan Dala ne ko?.

Ran Mum yaɓaci sosai ko hannu kasa kasawa ta yi kayan yayin da Sauran matan keta ƙorafin kayan ni kunsan me yaban dariya? Hajiya Fatima ta tambaya, suka maida hankalin su kanta, yadda suke ta wani rawar ƙafa mana su fa zaton su wani uban kaya suka kawo” Dariya matan suka sa wata can da ke zaune ta ce ai uban kayan ne a gun su akwati shida ke ko zani turmi Talatin,” hmm Mum ta yi kwafa kawai kan ta ce ai wallahi Hafsa ta cuci kanta wannan zannuwan nasu Allah na tuba ba gwanda suyi mata kala biyar kwarara ba.

Dangin Muktar na barin harabar gidan suka hau ƙorafi ko wannensu ya fusata, aiko suna zuwa gida suka dira mitar wulaƙancin da aka musu Gwaggon Muktar ɗin ce ta ce ai wallahi, Suwaiba Muktar ya cuci kan sa ya kuma cucemu haka kawai da mutuncin mu da komai ya sa ana mana kallon kamar wasu almajirai, ita dai Innar su Muktar Haƙuri ta yi ta basu, sam bata wani ɗauki abin da zafi ba dan tasan daman biki ya gaji haka dole sai shaiɗan ya shiga ya in giza komai duk ƙanƙantar sa.

Ita ko Hafsa Farin ciki ta yi sosai da ganin kayan da masoyin nata ya yi, tausayin sa ya cika ta haka sonsa ya ƙaru a ranta dan tasan ba duk namiji ba, musanman in ta haɗa matsayin sa da kayan tabbas ta san ya yi koƙari iya ƙoƙari.

Yau take kamu kuma party tare aka haɗa za’ayi dangin Hafsa sune suka kama wurin biki, tun daga yadda akai arranging din wurin zaka san cewa biki na dagin amarya ne, sam dangin Muktar tamkar wasu almajirai haka suka zama a wurin sai Hafsa ce da kanta ta amshi abin magana ta ce su hawo stage ɗin, basu wani yi mintina ba wata cikin Gwaggon Hafsan ta zo da mutanen ta liƙin da suke yasa MC mantawa da batun dangin ango suka koma gefe, ƙannen Muktar tuni sun Hassala, daga su har angon sam ba’a ta tasu, kalar abincin da aka basu ma daban da na masu taro gashi sunyi gayya duk sun tunzura. Hakuri Muktar ya yi ta basu yana nuna musu ba lefin masu biki bake masu rabone tunda ai basu san kowa ba.

Kamu da MC ya yi shelar za’ai dangin ango su fito ne yasa Muktar komawa ya zauna yadda MC yake magana, ya kuma ƙasƙantar da dangin ango, dan dai dai da turaren da suka fesa sai da ya tanka da cewa haba kukuwa amaryar tamu fa mai tsada ce ya kuke feshe ta da turaren wankin toilet, kufula iya kufula ƙannen Muktar sunyi ana gama kamun, MC yace yanzu za’a gane maras gata tsakanin ma’auratan.

Amarya yasa ta fito ya kira masu son ta su mata liƙi daga jaka guda zuwa sama har da masu dala a likin yayin da ango sai da ya jima tsaye, miƙewa Hafsa ta yi ganin mijin nata shima duk ya ji ba daɗi da habaifin da MC ke masa, amsai abin maganar tai tace tasan kowa yasan ayanzu ba wanda ya fita son mijin nata dan haka ita yafi cancanta da ta nuna masa gata, kuɗi kawai take zarowa tana san masa, mintina kamar uku ƴan uwansa suka fito, suna ji wasu na cewa wai seda suka harhaɗa kuɗin, su Rashida zasu sauka ta kamo hannun ta ku tsaya muyi hotuna, mai hoto ta yiwa alama ya zo ya musu hotuna daga kan stage ɗin dangin Muktar sukai waje dan sun gaji da wulaƙancin da ake musu, yayin da dangin Hafsa sukai surutun dangin ango basu da mutunci sai wani shan kamshi suke, tamkar alfarma sukai musu dan ɗan uwansu ya auri ƴar su.

Kamar ran kawo lefe yau kwana gidajen biyu sukai suna mitar yadda yaran nasu suka jawo musu wulakanci,ɓacin ran dangin Hafsa na yadda Dangin Muktar suka ɓata musu biki ne da rashin iya shiga sunce duk kauyawane da yadda suka bar gun bikin a fusace, Hafsa sai barin ɓangaren Mum ta yi koma ɓangaren Dad ita da ƙawayenta su Bilkisu dan ta fara gajiya da kushe mata miji da ake.

Washe gari ran kafi kamar yadda al’ada take can baya dangin Hafsa ne suka tafi gidan da Muktar kama haya, sam gidan bai musu ba, sukai ta masifa wai sai kace kurkuku, Gwaggon Hafsa ce ta kira shi cikin faɗa take cewa gida ya yi kaɗan kujeru ba zasu shiga ba, su kuma kayan su masu tsada ne dan haka bazasu karya kaya ba, kawai ya canja gida tunda dama ai haya ya kama, haƙuri ya yi ta basu kafin ya zo, sukai ta masifa shidai yana bada haƙuri dan Allah ya sani bama shi da dubu biyar a yanzu bare kuɗin kama irin gidan da suke so.

Ganin ba zai bi maganar su ba ta canja gida yasa Gwaggon sawa mai motar ya kai kayan gidan su Hafsa ƴan biki kuwa akai ta magana. Kamar ko wanne kafi dangin ango ne suka dafo dafaduka wadda taji nama da ganye kwano daban, gami da lamurje, a wulaƙance ƴan kafin suka amsa ada mitar ƙarantar dangin Muktar suke basu kawo musu komai na nan take mita ta juya zuwa arasa mai za’a kawo sai ƙandas ɗin abinci da wani garau garau ɗin lemo.

Abban Hafsa ne yasa aka maido da kujerun ya tare da sawa Muktar ya kira kafinta a karya kujerun ba shiri ya yi yadda Abban yace aka sanyawa Hafsa kujerun ta a falo, nan da nan guri ya yi kyau na amarya sak, kasancewar tun ɗazu dangin Hafsa sun tafi Muktar ɗin ne ya share ko ina kan ya fice yabar gidan dan baya son ƴan kawo amarya su tadda shi.

Yadda ƴan kawo amarya ke karo da juna da hankaɗe juna kana gani kasan da gayya suke duk dan su nuna gidan ya yi matsatsi da yawa ne, Ƙarfe tara daga Hafsa sai Bilkisu da Kausar a gidan tara da mintina Muktar suka shigo da abokan sa su Salisu sai zuba ƙanshin suke kasancewar daga Bilkisun har Kausar ɗin ba maganan nu bane yasa ba ai wani dogon surutu ba suka bar amarya da ango, sune suka sauke su Salisu a hanya insa suka wuce nasu gidan cike da taya ƙawar tasu murnar cikar burin ta.

*****

Washe gari Mum ce ta tashe su da sassafe aiko ta shigowa ta hau Muktar da faɗa kan dan mene zai sa a karya musu kujeru, ko kuwa zalunci ne, Hafsa dake ɗaki abin duniya ya ishe ta ne ta danna kiran Abban ta minti kamar sha biyar ya iso gidan ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba tas ya ƙarewa Mum ya kuma ce indai tanason zaman lafiyar nata auren to ta fita sabgar auren Hafsa, rai a bace ta bar gidan ko motar ta bata ɗauka ba, barw jiran Abban ta nufi Titi. Haƙuri ya yi ta bawa Muktar din kafin yabar gidan ko Hafsan bai naima ba. Hafsa najin futar su ta karaso gun Muktar ɗin tare da faɗawa jikin mijin nata tana kuka tana bashi haƙuri, maimakon ya amshi haƙurin ko ya nuna ya damu lallalshin ta ya hau yi gani ba zatai shiru ba yasa shi taɓe baki da fara kukan wasa, dariya tasa ya sumbace ta goshi haba da duk kinbi kinsa na ruɗe pls karki kuma kuka gaba na indai ba sokike zuciyata ta buga ba.

Kama kunnen ta ta yi alamun ban haƙuri, noƙe kai ya yi alamun ba wannan yake so ba a hankali ta sunbaci kuncin sa ya yi luuu cikin wasa kamar zai faɗi tasa dariya kar ka faɗi kasa amarya jinya, shima dariyar yake, ai ki bari kawai tsabar daɗi, tuni Hafsa ta nemi damuwar ta ta rasa sukai ɗaki cike da annashuwa.

<< Ko Da So 51

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×