Dariya suka sa, sai kuma Hafsa ta kuma ta fashewa da kuka, cikin tashin hankali ya ƙarasa wurin ta, “Haba Hafsa mene haka, mai aka yi kuma,” ya faɗa tare da sa hannu ya goge hawayen nata “Please karki bari su kuma zubowa, sai ki sa ni ciki damuwa kinji,” gyaɗa kai ta yi kafin ta ce to anma fisabilillahi ace daga kawo ni jiya Mum har ta fara zuwa….” Saurin rufe mata baki ya yi “na fahince ta wallahi, kinsan inada ƴan uwa mata, muma munyi auren mace I know how it feels idan kukayo kaya aka ɓata, uwa ce dake tayi” kallon sa take sosai bata son gano damuwa a fuskarsa, da alamun yasan mai take tsoro ko kusa bai bata damar fahintar ya damu ɗin ba, zaunar da ita ya yi gefen gado ina zuwa yace tare da yin waje.
Kitchen ya shige tare da fara laluben abinda zai haɗa musu na breakfast, ƙamshin da taji ya fara tashi na girki ne yasa ta miƙewa sam tama manta fa zasu ci abincin, kuma ita zata dafa, duk Mum ce ta ɓata mata plan, ta tsara ranar Farkon ta gidan Muktar dole ma yasan ya yi aure anma ba komai miƙewa ta yi tare da yin waje, kai tsaye ɗan ƙaramin kitchen ɗin su ta nufa yana tsaye yana tsame dankalin dake soyuwa cikin mai ta ƙarasa a hankali tare da rungomi shi ta baya, murmushi ya saki tare da ajiyar zuciya ransa na masa daɗi yau wai shine da Hafsa a haka, ko mafarki ya yi ada ya auri Hafsan ba yadda yake ba dan yasan igiyar raƙumi ta yi kesa da ƙasa sai gashi yau tama zama tasa a hankali yace Alhamdulillah, yadda suke yasa ta jin handalal tasa ha hankali ta juyo da jikin ta saitin sa, suka haɗa idanu tare da sakarwa juna murmushi, ta ce “wato kazo kana ta cinye abincin har ka ƙoshi haka kake zuba Alhamdulillah,” ta faɗa cike da zaulaya.
Murmushi ya yi tare da lakuce mata dogon hancin ta, “ba na ce ki jirani ba shine kika taso kika tawo” turo baki ta yi cike da shagwaɓa abincin naka ne ya cika ƙamshi ya hana in ci gaba da jira, kallon kason sa ya yi da sauri yace kin gani ko abinda nake gudu kenan na ce ki jira nasan kallon ki kusa dani bazai taɓa bari in abinda ya kamata ba, rikitani kike, dariya tayi tare da ɗan masa cakulkuli tace “irin haka?” Yasa dariya ta ɗan zame daga jikinsa tare da kuma masa yai saurin yin ƴar ƙara kinga kinsa na ƙone ko” ya faɗa tare da durƙushewa awurin cikin ruɗu ta ƙarasa tana tattaɓashi tana masa sannu ganin yadda ta ruɗe yasa shi fashewa da dariya Hafsan tasa akwai yarinta inba haka ba tana fa kallo ba wani ƙomewa da ya yi, ja ta yi ta tsaya tana turo baki hannun sa cikin tukunya riƙe da cokali yana juyawa ya sa hannun hagu ya jawo ta jikin sa fushin mene haka karki sa hankalina ya tashi ƙin sakin fuska ta yi a hankali ya manna mata kiss a kan bakin da ta turo dariya suka sa duka mai cike da nushaɗi.
Tare suka jejjera kayan abincin kafin ya fita ɗan ƙaramin tsakar gidan nasu zuwa bayi dan watsa ruwa jin da yayi zafi na damun sa. Mintina kaɗan ya fito zuwa ƙaramin fallen ɗakin da suka mayar tamkar falo, tana zaune tana duba waya ya shigo, miƙewa ta yi tare da matsawa inda ya zauna yana goge kai ta amsa tare da fara goge masa kayi lefi shine ka tafi ka barni ina, har ka gaji ne da ganina, dariya yayi maza ki kuskure baki, kinsan zuciyar Muktar da idanun sa bazasu taɓa gajiya fa Hafsan sa ba, kece fa duniyar tawa, daɗi ne ya lulluɓe ta lokaci guda kuma da kunya ganin yadda ya ɗago suka haɗa idanun ta yi saurin rufe masa fuska da shawul ɗin da take goge masa fuskar, gun abincin ta nufa inda shi kuma ya zare shawul ɗin yana dariya, wato har yanzu kunyar nan bata gama watsewa ba, to bazai yiwu ba ya faɗa tare da miƙewa, ganin abinda yake shirin yi yasa ta saurin kai dankali bakinta tana faɗin ah ni abina ta ko ina ɗagwas ai bani ba girki, ga miji ga mai girki, dariya yasa tare da saurin matsawa naƙi wayon zonan ɗan kaucewa ta yi tana dariya sai dai ya fita zafin nama tuni ta jita tsam jikin sa….
Ganin yadda ta sha kunu ne yasa shi sa dariya nifa kinsan ban gaji ba Tom, cike da shagwaɓa tace ni bansan haka kake da mugu… ganin ya tsureta da ido tamkar mai son cinye ta yasata yin shiru tare da fara zuba masa abinci ya gintse dariyar sa, Hajiya Hafsa tawa, ni ta Abba na ce, dariya ya yi Hansatun Muntari kenan yadda ya faɗi sunan da kuma yadda ya yi da muryar sa yasata dariya yayin da shi kuma ya tsura maya idanu ransa cike da sonta wanda ke kuma nunkuwa a dukkanin bugun daƙiƙa guda.
Tare sukai wanke ƴan kwanukan da sukai anfani dashi yayin da shi kuma ya gyara tsakar gidan duda ba dattin da yayi, sai da ta kunna turaren wuta kafin ta koma ɗaki cikin kayan gyaran kanta ta fara dubawa rashin wuta yasata ɗaukan shawul kawai ta fita yana zaune yana fifita ta karasa tare da zama gefensa tahau goge kanta, wanda Kasancewar sabon kitso ne kan ga ruwa da ya taɓa ya kwanta ya yi luf luf gwanin ban birgewa, shikam jiya yaga kyan kitson sosai anma yanzu kitson yafi firgeshi baiyi tsanmanin kitso nama mata haka kyau ba sai da ya ganshi kan Hansan san, ahankali yasa hannu yana shafa kan tayi saurin ɗagowa tana zare ido, dariya yasa Hajiya ya rage idon haka karya faɗo kinsan dai ba tsoro zasu ban ba, kyau zasu mun karkisa inyi abinda ban niyya ba, itakam ta fara tsorata da lamarin Mijin nan nata tamkar bashi ne Muktar ɗin fa zaizo baifi yayi magana biyar ba shima sata dame shi, in aka ce mata zai wani abin da yake yanzu ma zata rantse ƙarya ne.
Iska mai ƙarfi ce ta taso wadda tasa su komawa ɗaki, Muktar ya ce haba ashe shi yasa ɗazun zafi ya da men hadarine a garin, zaune suke suna hira lokaci lokaci Muktar na tsokanar ta, ruwan da ya fara sauka mai cike da sanyi ne da feshi wannan yasa Hafsa leƙawa bedroom ko zamu koma can ɗakin mu rufe nan naga ruwan ɗan gabas ne, dariya ya yi, bakin ƙofar ta leƙa ta yi saurin dawowa da sauri kallon ta ya yi a ɗan firgice, mu zauna kawai anan bazan iya shiga ruwa ba.
Ina zuwa yace tare da fita tayi saurin jawo shi, karka shiga kar zazzaɓi ya kama ka dariya yada tare da cire hannun ta a hankali daga nasa da ta kamo, kim manta inda kika ɗauko mijin naki ne?, ba abinda dukan ruwa zai min ina zuwa ɗakin ya bari ya barta da tunani tunda suke bai taɓa maganar Background gap dake tsakanin su ba zaton ta ma bai yadda akawai gap ɗin ba, tana tsaye ya shigo da rigar ruwa a hankali ya sanya mata tare da janta waje wasa suke sosai cikin nushaɗi aɗan ƙaramin tsakar gidan nasu, sai da suka gaji sannan ya shanya kayan sa a igiya sukai ɗaki Hafsa ta aje rigar ruwan a ƙofar ɗaki tare da shigewa ɗakin tana dariya, though ruwan bai dake taba sabida dukan rigar datasa anma tayi enjoying ɗin wasan nan su karo na farko kenan da zata ce ta shiga tayi facal facal da ruwan sama, dan Mum sam bata bari kaf ɗin suma tsoron ruwa suke.
Jiki ba kwari ya tashi zaune tare da fara goge hotunan Hafsa daga wayar har wanda sukai tare da su Bilkisu da yake da su ya goge dai dai dana bikin Hafsan sai da ya goge, jiki ba kwari ya tura wayar gefe ya sauko daga gadon tare da yin waje, falo ya nufa Hajiyar su na zaune tana karatun wani littafi na turanci ya shigo ta aje tare da duban sa, anya Tariq kana kyauta a kanka kuwa jibi yadda ka faɗa nayi nayi kaje asibiti kaƙi tunfa satin da ya wuce da ka dawo baka fita ba anya.
Ɗan zaro ido ya yi wato har yayi sayi haka ne fa tunda ya dawo daga ɗaurij auren Hafsa da Muktar ya rasa mai ke masa daɗi, wallahi Hajiya lafiyata lau mai aka dafa?, Bata bashi amaa ba ta ce to ko Bilkisun ce baka so? Da sauri yace wallahi ina son sa har zuciyar sa na bugawa da sauri, yasani yana son Bilkisu sosai in ya rasa Hafsa wadda ya yi son maso wani bazai taɓa son ya rasa Bilkisu ba wadda suke kaunar juna, murmushi Hajiya tayi to ai shikenan ga abincin ka can ka ɗauka kaci, girgiza kai ya yi nama fasa ci bari in je mu gaisa da Bilkin nasan zata kawon abin da zan taɓa sai yafi mun daɗi kin san abu daga hannun masoyi daɗin ɗanɗano gare shi, dariya kawai Hajiya ta yi amma kaiko…dariya ya yi bari in je in shirya.
Tsaf ya shirya ya fito falon har lokacin Hajiya na zaune yace Hajiya ya kika ganni, dariya ta yi to kaɗanyi kyau dariya shima ya yi kawai tare da cewa ya tafi, tsaye yake bakin Motar sa yana jiran fitowar Bilkisu, tana zaune tana gyara ɗauri ƙanin ya shigo ya sanar mata da zuwan Tariq janbaki kawai ta shafa ta fice, kasa cire idanun sa ya yi a kanta tayi kyau sosai sanye take da black lace mai adon ja a hankali yace Subhanallah shi kansa yasan yana son Bilkisu bai san wacce irin zuciya Allah ya masa ba da taso mutun biyu a lokaci guda, wani barin ne ya ce masa shaiɗan ne yaso ka ɓata zumunci, basar da tunanin ya yi tare da mayar mata da murmushin da take masa, a nutse suka gaisa kafin ta fara ƙorafin mai ya same shi ya faɗa, a barkwance yake ce mata rashin ta kusa ne, sun taɓa hira kafin ta koma ta kawo masa abinci, sosai yaci, sun sha hira kafin ya tafi ya barta cike da farin ciki.