Kwance take tana bacin ta a nutse bisa Sallaua inda ta dunƙule cikin hijabi alarm nata faman ƙaɗawa anma ko a jikin ta, murmushi Muktar ya yi bayan ya kashe alarm ɗin gyara mata kwanciyar ya yi kafin ya fice daga ɗakin, wainar da Anti Amira ta kawo musu jiya ya ɗauko ya ɗumama, ya soya taliya da kwai wanda kusan ita ce fav. Breakfast ɗin Hafsa, tare da dama musu koko da sauran garasar da ta yi ragowa sai da ya wanke abubuwan da ya yi anfani da su kafin ya koma ɗakin har lokacin baccin ta. . .