Zaune take tana cin gyaɗar da yake ɓare mata yana bushewa, mayar masa da wadda ya miƙo mata tayi ni ta ishe ni, watsa abarsa ya yi a baki ta miƙe tare da fita minti kaɗan ta dawo da Tiren abinci a hannu tare da ajewa gaban sa tana faɗin wai yaushe su Hajara zasu ne tun ina shiru yau dai na furta, murmushi ya yi zasu zo ne nine na ce su bari ki kuma sabawa sosai tukun, matsawa ta yi kusa da shi ai na ɗauka wallahi dan bamu je bane suka ƙi zuwa, Murmushi ya yi a’a ai gidan amarya kan ta fara yawo ake zuwa, shiru ta yi bata ce komai ba tana tunani a ranta wato su Yaya Farida kenan gidan ta ne ba zasu zo ba, kamar yasan abinda take tunani ya ce anma dai manya su sai an fara zuwa an gaida su yanzu jira nake ku kammala exam sai mu dan jejje gidaje kafin nan ma munyi albashi, murmushi kawai ta yi tare da miƙa masa shinkafar da ta deɓo a cokali ya buɗe baki yana murmushi.
Washe gari da Sassafe Hafsa ta tashi ta haɗa musu kari ruwan da Muktar ya jona a hita ta ɗauka ta shiga wanka, yana kwance a ɗan ƙaramin falon nasu ta shigo tana goge kai, ɗagowa ya yi yana binta da kallo, ganin yaƙi daina kallon ta ne yasa ta tsayawa ganin ta zargu ya ce gani nai kin ɗan faɗa, dan Allah ki daure ki dinga cin abinci, murmushi ta yi tare da kallon kanta, ni banga inda na faɗa ma, abincin ne wallahi ba daɗi, kaga ma sai da na tashi da sha’awar kosai na soya yanzu kuma ya fita a kaina wai wainar shinkafa kuma nake sha’awa, bata ƙarasa ba ya miƙe bari in sayo miki wurin Hadiza, kan ta ce wani abu ya fice, ta bishi da kallo tana murmushi.
Kan ta gama shiryawa ya dawo da wainar sosai ta ci batai ma tsanmanin zata ci haka ba, tare suka zauna suna hira, kasan na zata tare zamu fita sai naga baka shirya ba, murmushi ya yi eh da yake yau asabar banso inje gida da wuri sai wurin goma zan fita in sha Allah, ƙarar hon ɗin mai ɗan sahun da ke kai ta makaranta yasa ta miƙewa tom bari in je ni, ok sai kin dawo Allah ya bada sa’a murmushi ta yi amin ya rabbi ta fice bayan ta rataya jakar ta.
Zaune suke ita da Bilkisu suna hira bayan fitowar su daga lecture wadda fixing ce ita kaɗai ta kawo su, Bilkisu ce ta dube ta kan ta ce kinsan Tariq ya Matsa wai yana son ya turo nama rasa ya zan in faɗawa Abba, ya akai kika faɗawa Abbanku Muktar zai turo ne, shiru Hafsa ta yi kafin ta yi murmushi wallahi ni banma san ya akai ba inajin Abban ne da kansa ya ce ya turo bayan kwanciyata a asibiti, tsaki Bilkisu ta yi ni kuma ba abin in kwanta a asibitiba, suka sa dariya duka, Hafsa ce ta muskuta kinsan mene kira shi Tariq ɗin muyi magana, ok kawai Bilkisu ta ce tare da fara kiran Tariq ɗin bugu ɗaya ya ɗauka tamkar yana jiran kiran kiran nata ne, Rayuwa ta kamar kin san kece a raina yanzu hanka, dariya Hafsa ta yi tare da cewa ba Rayuwar bace wannan ƙawar ta ce, da sauri ya ɗan gyara zama tare da matsar da wayat daga kunnen sa ya ɗan saki ajiyar zuciya muryar tata ta ɗan taso masa da hatsaniyar da zuciyar sa ta shiga kwanaki wadda yake tunanin ya kashe ta tuni da sauri ya yi uziyya dan neman tsari daga shaiɗan, a nutse ya ce ah Mata a gidan Muntari ya gida, cikin ɗan ƙasa da murya da nuba rashin jin daɗi tace a’a bafa mason irin haka ya ake ɓata mana suna, dariya ya yi ah kaga masoya to ya karatun ya faɗa, murmushi ta yi karatu Alhamdulillah, ya akaji da tsoro kuma ta faɗa.
Tsoro kuma ya maimaita yeh gashi ka kasa tunkarar su Abba kace ayi bikin nan kodai har yanzu baka gama yanke hukunci bane, dariya ya yi habawa ai nafi ƙarfin a kirani da matsoraci kawai dai na ɗauka mace ke cewa Abban ta masoyin ta ya shirya shi kuma sai yace kazo ko, shiru Hafsa ta yi sai dai fahintar yadda basu san yadda ake ba haka shima Tariq yasa ta saurin cewa no ba haka bane, kaine zaka je ka ce ka shirya sai a kirata a tambaye ta, dafe goshi ya yi omo, kinsan sam I don’t know haka ake ina zuwa tom dama naga ɗazu Abban yazo wurin Dad bari in same su ya faɗa tare da kashe wayar Kallon juna sukai da Bilkisu tare da yin murmushi Bilkisu tace wato maza ko suɗin dole ace musu maza ni ina zan iya zuwa in sami har mutun biyu ince musu na shirya aure gwanda ma Abban mu anma Abbansu Tariq fa baya dariya, dariya Hafsa ta yi kafin ta amsa kiran da ya shigo wayar ta ce ai wallahi Aunty Halima na yi fishi ace tunda aka kawoni ba waya bare kira, daga ɗayan ɓangaren ne Haliman ta ce ayi haƙuri a sakko yanzu na kira, cikin ɗan ɗaure murya ta yadda Haliman zata ji fishin ta a sautin ta ce ai ba wani saukowa da zan duk kunsa inama kaina kallon marar gata kicewa Hajiya Kaka na dena kakar da ita, gwanda ma Malam naɗan masa guntun uzuri nasan zafin an kasa shi ne…. Bata ƙarasa ba taji Muryar Kaka na faɗin Malama kizo ki buɗe mana ƙofa muna ƙofar gida, miƙewa ta yi tamkar tana cikin gidan ne dan Allah fa ta faɗa a cike da murna, sai kuma ta tuna tana fa cikin Faculty of Agric ne a new site Buk, salati ta saka, Malam ya yi saurin cewa lafiya dai dafe goshi ta yi tamkar suna ganin ta ina makaranta ta faɗa jiki ba ƙwari.
Bilkisu ce ta taɓota Muktar fa ta faɗa murya can kas, agogon dantsen ta Hafsa ya kalla ganin goma da kwata yasa tace bari in kira shi Allah yasa bai fita ba, bugu ɗaya ya ɗaga ta ce su Kaka ne wai suna ƙofar gida dan Allah in bakai nisa ba ka dawo ka buɗe musu, kinganniba Titi bari in sauri in koma ya faɗa tare da katse wayar bayan ya dubi mai mashin ɗin da ya tsayar ya ce masa dan Allah yi haƙuri kaje wani abu ya tasomin.
A kofar gida ya tadda su suna ta hira cike da murna da girmamawa ya tarbe su, gidan ya buɗe inda suka bishi a abaya ya buɗe musu falon su suka shiga yayin da ya shiga kitchen ya kawo musu lemo da snacks, agogo ya duba yasan kan Hafsa tazo sha biyu zata yi wannan yasa ya shiga kitchen ya ɗora abinci inda ya koma falon suka hau hira tamkar shine jikan nasu bawai jikar su yake aure ba, duk rashin son maganar Muktar sai gashi suna ta hira.
Dad da Abban su Tariq na zaune suna hira Tariq ɗin ya fito sanye da manyan kayan sa kamar yadda ya saba ko yaushe kasancewar sun gaisa ɗazu da Abban su Bilkisu ɗinne yasa ya rasa mai zaice sai da Dadin su ya ce Malam kazo ka saka mu a gaba ko so kake kaji mai muke tattaunawa, shafa kansa ya yi tare da ɗa ƙasa da murya, eh dama Mun magana da Bikisun kamar yadda kuka ce…Dadin ne ya kuma cewa in baku dai dai ta bane ba abu ne dole ba zaka iya tafiya, kamar yadda na faɗa ma lokacin da nace kaje ka ganta baku ne kuka haɗa mu abota ba so dan baku dai dai ta ba hakan bazai raba mu ba, da sauri Tariq yace No Dad munfa dai dai ta zuwa nayi in faɗa ma ka tura, dariya Dad ɗin ya yi tare da duban Abban Bilkisu to kana jin dai ɗanka ko yaushe zaku turo ne?
Dariya Abban Bilkisu ya yi bari zan magana da shi inji yaushe yake so, da sauri Tariq yace ai Abba koma yau ne a ɗaura in yaso shirin a yi a gaba, Dad ɗin su Tariq ɗinne ya ce eyye kaji min maras kunya maza bamu waje sai ma munji daga bakin ta in tace bata amince ba magana ta koma baya, miƙewa Tariq ya yi yana ta murmushi yana komawa ɗakinsa ya kira Bikisun, suna cikin mota ita da Hafsa suna hira wayar ta tayi ƙara ta yi saurin ɗagawa cikin zumudi yake faɗa mata yadda sukai sa su Abba, itama daɗi ya cikia ta, har suka sauke Hafsa tsare tsaren bikin suke.
Da Hanzari Hafsa ta shiga gidan ta murna biyu ke cinta gata zuwan Kakannin ta ga ta bikin Bilkisu da Muktae ta fara cin karo riƙe da tire zai shiga ɗakin da fara’a ya amsa sallamar da ta yi cikin ɗangaɓewar murya ta ce ya ilahi Sannu da gida na barka da aiki ko, murmushi ya kuna yi tare da faɗin ki shiga suna ciki, da murna ta faɗa ɗakin tana faɗin gaskiya nayi dushi wallahi se yau.
Halima ce ta gashi yau ɗinma Munzo bakyanan abinda akau ta guda kenan aka tare weekend tunda kullum kina school, tsaki taja ai wallahi na tsani school ɗin nan kawai dai dan ba yadda zan ne, rissinawa ta yi ta gaidasu duka kafin ta zauna su hau hirar tare. Sai yanma lis Muktar ya kira mai Ɗan sahun da ke kai Hafsa makaranta ya mayar da su.