Skip to content
Part 6 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Juyawa ta yi tare da yin ƙunƙuni lokacin da ta ji Muryar Momy tana magana daga bakin ƙofa ita dai tasan ba ta rufe ƙofar ba, wannan ya sa ta juyawa tare da jan mayafin rufar ta dan zaton ta mafarki take sai dai jin muryar Momy ta yi a kan ta tana fadin “wai Hafsa ba zaki ta shi ba sai na ɗala miki duka”

A hankali ta tashi tana miƙa, “Mum bafa mu da lecture yau dubi agogon yanzu fa 7 ta yi?”

“Kina jin ta ko” abinda kawai Hafsa ta ji momy ɗin ta ce kafin ta saka mata waya a kunne, muryar yayar ta ji tana faɗa “Hajiya ki shirya kije gidan kakan nin su Kalil ki ɗauko su ki kawo su nan su ƙarasa sati guda ɗin kan a koma”

Mum bata jira amsar Hafsa ba ta fice tana ci gaba da wayar ta ” ai ke kika kyale su mutane sunbi sun mallake miki yara”

“To Mum ya kike so in yi Mansur ya nuna dole sai an kai su, yau ɗinma tun jiya na dira masa mitar nawa iyaye ne baya son su dinga shiga shine fa ya ce to in ɗauko su siyi sati”

“Ai kuwa zaiga sati ki haɗa ma Kalil ɗin uniform ɗin sa in an koma sch din Usman ya dinga Kai shi ita kuma ki haɗomin kayan ta in ga in yana da kunyar zuwa ya ce in bashi su”

Dariya Farida tasa ” thats my Mum” suna gama tattaunawa bayan ta katse wayar “Hafsa!” Momy ta kuma kwala kira bayan aje waya.

Rai a cinkushe Hafsa ta fito tana miƙa da hamma, kai tsaye wurin aje abinci ta nufa tasan tunda Mum ce ta ke son ta fita da wuri ta dafa breakfast, kamar yadda ta zata ta kammala komai tea ta haɗa ta ɗebi chips da soyayyen kwai ta yo falon dan bata son cin abinci kan dining table, cak ta tsaya lokacin da taga Yaya Usman sam bata yi tsammanin ganin sa ba a yanzu, daurewa ta yi ta ce “yaya ina kwana”

Tsaki yaja “mene wannan?” ya nuna mata kayan jikin ta.

“Wai ke Hafsa Sau nawa kike son in faɗa miki ki daina fitowa falon nan da kayan bacci”

Kallon kanta ta yi ” but yaya mene ne matsalar kayan nan?”

Hannu ya kai zai make ta ta yi saurin kaucewa tana dariya, ɗakin ta ta koma mintina baifi ashirin ba ta fito tsaf da ita har lokacin Momy na zaune tana kallo ” yawwa Mum ni na wuce Bala ne zai kaini ko?”

“Eh ki biya ta gidan yayar taki zata baki kayan su”

“Tom” kawai ta ce ta fice

A bakin gate ya parker motar bugu biyu mai gadi ya buɗe ta shiga da Mijin Faridan ta fara cin tozali.

“La yaya ashe ma kana gida?”

Dariya ya yi “yau sarkin rikici ce a gidan namu mukan munyi fushi”

Murmushi ta yi ” a’ah dan Allah, in kun fushi dani ai da matsala, sai in shiga ruɗani, Mun ta shi lafiya ta faɗa lokacin da ta ɗan risina”

“Lafiya ƙalau Alhamdulillah, muje ciki ya ce”

“Ai na ɗauka fita za kai?”

“Ah ai sai nayi wa autar Abba rakiya zuwa falo, kafin in fita” dariya ta yi “woni” suka sa dariya.

A falo ta zauna inda ya shiga ciki, sai dai wanka ya tarar da matar tasa na yi wannan ya sa shi komowa suka ci gaba da hira da Hafsan suna ta dariya Farida ta fito tana taku dai dai tamkar amarya kamshin ta ya mamaye falon, cike da fara’a Mansur ya ɗaga ido ya kalli matar tasa

“Eyye sai anci tarar ki wato da ace Auta bata zo ba duk wannan wankan haka zan missing kike nufi?”

Murmushin da tasan yana rikita shi ta masa cikin salon tata yaudarar ta ce kaima dai ai sai kasa ayi tunanin bana ma gayu fisabilillahi mene cikin wannan shigar kofa mai ban shafa ba” ta faɗa lokacin da taɗan juya idanun ta bayan ta ɗan kalli jikin ta”

Miƙewa ya yi yana dariya ” ke ko Allah in mutin ya biye miki sam ba zai fita ba, ƙanwar mu agaishe mun da su Abba,” dariya ta sa ta bi shi sai ka dawo min tina kaɗan ta dawo tana murmushi.

Sun jima suna hira da Hafsa kafin ta ɗauko mata kayan yaran ta bar gidan zuwa gidan surukan nasu, tamkar wata babba ce ta zo haka sukai ta nan nan da ita yayin da Khalil ke ta faman murna da tsalle tsakanin jikin Hafsa da Gwaggo wato kakar sa.

Khairat Bacci take Gwaggo da kanta ta saɓata a kafaɗa tasanya ta cikin mota tana faɗin ” Allah dai yasa ta zauna dan tun da aka kawo ta yayen nan bata yadda da kowa sai ni”

“In taƙi yadda ba sai a mayar wa da Babar ta ba” Hafsa ta faɗa suka sa dariya duka inda suka shiga mota Khalil na ɗagawa gwaggo hannu aka ja motar.

*****

Duk da cewar an musu orientation haka kawai tsoro ya cika shi tunanin yadda zata kasance masa da da ɗaliban yasa gaban sa ke ta faman faɗuwa, yau shigar manyan kaya ya yi sosai haibar sa ta fito, nutsuwa da kyansa suka kuma bayyana, kallo ɗaya zaka masa kasan shi ɗin nutsattse ne.

Inna na bakin wuta tana mulmula tuwon siyar wa na safe ya fito, ɗauke da kwano da alamu na abin cin da ya yi kari ne, Inna ni zan wuce asamu a addu’a walllahi tun ɗazu gaba na ke faɗuwa ji nake tamkar bazan iya ba.

Ɗagowa ta yi tana murmushi ” kaima dai Muntari yo ai in Sha Allah tinda ka samu damar tsallake ɗaukan aikin zaka iya ne shi yasa suka ɗauke ka”

Ajiyar zuciya ya yi ” kin san yaran masu kuɗi koyar da su sai anyi haƙuri”

“Ba fa su da matsala ba ga sunan ko ina muna ganin su ba, in zanma misali da yaran gidan Alhaji Sani in ka dubi yadda suke da nutsuwa da tarbiya yaran talakawan ma basu da ita”

Murmushi ya yi ” wallahi Inna har kin kwantar min da hankali bari in je kar in makara”

Miƙewa ta yi har soro ta biyo shi, “Allah ya tsare min kai ya bada sa’a yasa a fara a sa’a”

Cike da kwarin gwiwa ya fice bayan ya ce “amin”

Da kwarin gwiwa ya tura gate ɗin makarantar ya shiga ɗauke da littattafan da aka bashi dan zuwa ya yi nazari ya kuma haɗa lesson plan dan David yaƙi yadda ya bada lesson plan in wurin sa.

Kai tsaye SS 3 ya wuce nan yake da period ɗin farko, sam baiyi tsanmanin ganin ajin da ɗalibi ko guda ba, dan yadda ya sha ji ana faɗe shine yaran masu kuɗi makarar su ta yi yawa.

Cike da girmawa suka gai da shi ya gabatar da kansa matsayin sabon malamin Physics kafin ya koma kujerar zaman malami ya zauna, ya hau tambayar sunayyen su duk cikin jiran takwas ɗin ta yi a Kaɗa kararrawar fara lesson, kafin takwas ɗin har hankalin sa ya kwanta har son yaran ya shiga ransa sosai suke ɗan taɓa hira ana kaɗa kararrawa duk suka nutsu suka hau fiddo da littattafan su, tsarin yaran ya birge shi sosai ba yau ya fara koyarwa ba domin yana voluntary a unguwar su, nan Makarantar ƴan mata ayi shiru ma kawai ya ishi malami.

Motion shine topic ɗin da aka ce ya ƙara yi musu da alamu malamin su na da ya iya koyarwa dan kuwa bai wani sha wahala ba dan sun gane topic din sosai tun daga yadda suke watso masa tambaya da kumma bashi amsar tambayar da ya mu.

Lokacin bada class work aka kaɗa wannan ya sa shi rubuta tambayoyin sa ya koma ya zauna lokacin lokacin wa su na masa tambaya.

Rike da littattafan na su ya fito dan malamar Chemistry tuni ta hallara har ya fita wani ɗalibi ya ce ” Sir pls Mai ka karanta?”

“Juyowa ya yi yana murmushi abin da ka ce ɗazu kanasonn karanta”

“Wow ɗalibin ya ce u mean engineering no wonder naji Ina son ka”

Dariya kawai Muktar ya yi ya bar ajin sai da ya kai takardun nasu office sannan ya dawo zuwa SS 2, tun a wurin orientation aka faɗa musu ƴan SS 2 sai sun yi haƙuri da su, sai dai sam bai ga matsalar ba in ka ɗauke surutu ƙasa ƙasa wanda shi tun a GGSS Dala ya saba da wanda ya fishi yadda ma ya fahinta sunfi SS 3 ɗin ƙoƙari…

<< Ko Da So 5Ko Da So 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×