Skip to content
Part 7 of 53 in the Series Ko Da So by Fadimafayau

Tunda dare ya raba Khairi ta dasa kuka, gajiya da rarrashinta da Mum ta yi yasa ta ɗauke ta takaiwa Hafsa wadda ke bacci, kukan Kairin ya tashe ta, Mum ta ɗora mata ita a cinya tare da ficewa daga ɗakin.

Ko dan Hafsan ce ta ɗauko ta daga gidan Kakannin ta oho anma Hafsan na kunna fitila ta kalle ta sai ta yi shiru wannan yasa Hafsan miƙewa ya haɗo mata abincin ta sannan ta bata ta goya ta, ta jima tana jijjigata kafin ta yi bacci, kwantar da ita tayi kafin ta samu itama ta kwanta.

Huɗu saura Khairi ta tashi ta hau kuka, Hafsa na hanma ta miƙe ta kuma bata abinci sannan ta goya sa sai dai taƙi bacci, haka ta sauke ta yarinyar ta hau wasanta yayin da Hafsan ke gyangyaɗi.

Gari na wayewa Hafsa ta shirya itakam ba zata iya ba gidan Yaya Sadik zata tayi Bacci, wanka ma a toilet din falo ta yi dan khairi na Bacci bata son ta tashi Mum tace ba zata ba.

*****

A kwance ya same ta tana daddana waya. Kamar ba zai magana ba, har ya wuce sai dai hango tulin kayan abincin da suka ci jiya da daddare akan dining table har yanzu bata ɗauke ba ballantana a yi batun wankewa yasa shi kallon Lokaci cike da takaici, uku saura idanun sa suka gane masa. Sake kallonta yayi yaga yadda tasha kwalliya kamar ba gobe, jewelries dinta ma duk sunyi matching da kayan da tasa, A kallon farko tayi bala’in burge shi don son kwalliyarta na daga dalilan da yasa ya aure ta, wannan yasa bacin ransa game da kwanukan ya yi sauƙi.

“Ameerah!” Ya faɗa muryar sa cike da emotions din da ba ma zai tantance me yake ji a lokacin ba. A hankali ta dago ta kalle shi kafin ta maida hankalinta kan wayar.

“Haba Ameerah, this is not right. Kalli gidan ki fa!” Bata fuska tayi a ranta tana cewa yanzu zai fara wannan faɗan nasa mara amfani yabi ya cika min kunne.

“Oh sweetheart…” Ta fada a shagwabe lokacin da take ƙoƙarin ta shi zaune duk da bata ajiye wayar ba amma hankalinta na kanshi.

Sai da taga yana kallon ta sannan ta haɗe hannu. “Ban san me yasa kai baka fara kallon abu me kyau ba kafin ka nemo lefi. Look at me, duk kwalliyar nan taka ce! Da ace na tsaya wani wanke wanke i would have wasted alot of my time… Wannan kwalliyar sam ba zan samu lokacin yinta ba.”

Cike da rashin sanin abun fada ya shafa fuskarsa sannan ya nemi wajen zama.

“You can always manage your time Ameerah. Idan kika tashi da wuri kika gama da aikin gidan kikayi kwalliyar you have all the day to press your phone. Wallahi ana shigowa falon nan tsamin miya ake ji.” Ya fada yana mikewa don da ganin yanayin fuskarta ma ba zata bashi amsa me dadin ji ba.

Dining din ya nufa ya kwashe kwanukan sannan Yayi kitchen dasu. Ko da ya shiga kitchen dinma sai yaji kunya ta kama shi saboda kurar da yayi ga wani wari da yake tashi sama sama. Bude fridge yayi ya ga vegetables din ciki sun rube. A take ran sa ya baci sosai. Ya tsaya, ya zaga, ya juya, ya tsaya ya rasa ta inda zai kamo lamarin. Sai kawai yayi tsaki ya fita.

“Okay okay ki taso muyi aikin nan don wallahi saura kadan dai gidan nan ya zama bola. Ki zo muyi aikin, i have something for you. Very special!” Yayi winking a karshe yana kakaro murmushin karfin hali ya yaba a fuskarsa. Tana magana kasa kasa ta taso ba da son ranta ba.

Rahina fa zata zo tayi anjima…” bai tsaya jinta ba yaja hannunta sukayi kitchen din. nade hannun rigaarsa ya yi, inda ya kaɗa kumfa, malama ina wankewa kina ɗaurayewa, ya faɗa lokacin da hau kiciniyar wanke kofi, tsai kawai ta yi da idon ta kansa ita kam bata shirya taɓa ruwa yanzu ba amma tasa in ta yi magana faɗa zai yi, wayarsa da tayi ringing ya da shi jan tsaki hannun sa ya fara gogewa da towel kafin ya zaro ta.

“Toh.” Kawai ya ce sannan ya nufi kofa ta bishi da ido cike da murnar Allah ya cece ta ba zatai wanke wanken nan ba.

Bai jima ba sai gashi sun shigo da Hafsah wadda ke faman surutu “ashe ma kana gida ai Allah ne ya ci dani da har nace bazanzo yanzu ba sai dare momy ta takuramun” kallon ta ya yi tare da watsa mata ƴar ƙaramar harara aiko fita zan yi kima sa a ranki baki ganni ba, haka kawai sai yarinya ƙarama ta dinga damfara ta, ya faɗa da sigar wasa” hirar da suka shigo suna yi kenan, Ameerah na hango Hafsa fita a guje ta rungume ta.

“I miss you so much Hafsy!” Ta fada tana murmushi.

Hafsahn tayi dariya. “ Anya kuwa Anti Amira ni kikai missing?” Hafsan ta faɗa tana dariya.

“Koma dai mai zaki ce ni nasan ke na yi missing, yanzun ma Allah ne ya debe ni yasan na yi missing ɗin ki ya turo min ke, yayan ki bai son cin abincin Rahina Please ki taimaka kan ki tafi ki dafa masa yau ban jin daɗi” Amira ta faɗa tana ƙasa da murya kamar mara lafiyar gaske.

“Yo to mene marabar abincin nata da na Rahinar duk ƙazanta ce” Sadiq da ya fito da alamar fita zai yi motsa jiki ya faɗa.

Dariya Hafsa ta yi ” eh naji kuma yau dole a ci ƙazan tar ba, ni zuwa nayi ma in yi Bacci wallahi Khairi ce ta hanani sukuni, ni ban kama da Maman ta ba, anma ta maƙale mun” lakuce mata hanci ya yi ” ba dole, au danma tana son ki, kike faɗar haka kamar a kunnen Yaya Farida, in zata tafi ki ɗauko mata kuɗi a envelope a saman drawer ya faɗa kafin ya fice”

Tsayawa Hafsah ta yi tana kallon Ameerah sannan tace, “ba zaki je ki raka shi ba? Ke dan love dinnan ma baki iya ba?”

Harara Ameerahn ta watsa mata kafin tayi wajen itama. Da kallo Hafsahn ta bi gidan tana jin tsami tsami yana tashi sannan ta tabe baki amma still bata ga laifin Ameerahn ba.

Kawai dai tana tunanin Ameerahn ta gaji ne. Tana zaune, sai gashi ta shigo.

“Yauwa ko kefa? Haka ake yi ai. Ko dan ki mallake yayana.” Ta fada cike da tsokana.

Wuri Ameerah ta samu ta zauna sannan tace, “hnmm haushinsa fa nake ji. Duk jikina ciwo yake saboda aikin gidan nan na samu daƙyar ya bari Rahina ke zuwa tayani shima ya ce sai randa bazai wuni a gida ba, girki kuwa duk sanda ta yi sai ya gane ya yi ta fada na rasa ya ake yake ganewa”

Da mamaki Hafsah ta kalle ta. “Wai dama kana jin haushin wanda kake so? How is that possible?” Ta tambaya saboda ita a ganinta in dai tana son mutum sosai ba zata taba jin haushin duk abunda zaiyi mata ba musamman ma in kyakkyawa ne.

“Ke yarinya ce har yanzu.” Inji Ameerah.

“Kai Anty.” Dariya Amira tasa “Umman mu ta ce zata bawa Momy zaƙo nama zata shi kika kawom?”

“Au kinga zan manta dalilin zuwan” Hafsa ta zaro ledar ta miƙa mata kafin ta miƙe mai zan girka muku?”

Jingina sosai Ameera ta yi da kujera “yau kitchen ɗin naki ne ai kin ka fini sanin abinda yake so” ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin saka pin ɗin wayar ta.

*****

A gajiye ya dawo ya tarar ba kowa a gidan saboda haka kawai duba bokitan da robobin ruwan gidan yayi yaga ba ruwa. Yasan yaran nan suna sane suka wuce islamiyya basu cika ba saboda Inna ta cika da kan ta. Haka ya shiga jan ruwan har sai da ya cika su duk sannan ya debi ruwan wanka. Zafi ake sosai shiyasa bai damu ma sai ya kunna wutar dafa ruwan ba.

Ko da ya fito, mai ya shafa sama sama, sai da ya ci ɗanwaken sa da ya tarar an rufe masa a ɗakin sa, sannan ya saka kayan sa ya fice don sunyi da abokan sa zasu hadu a gidan su Salisu. Kai tsaye gidan su Salisun ya nufa. Daga bakin kofar gidan Baban su Salisun yana zaune da almajiransa suna ta karatu.

“Baba ina wuni, ya kokari?” Ya gaishe shi yana durkusawa. Da fara’ar sa Baban ya amsa.

“Ya mutan gidan Mu’utar?” Ya tambaya yana sake yaba hankalin yaron.

Bayan sun gaisa ya nufi cikin gidan da sallama saboda Salisun ma dakinsa a cikin gida yake ba a soro ba.

Umman su ce zaune tana tankaɗe garin tuwo. Ko da ya gaishe ta bata amsa ba.

“Umma ina wuni.” Ya sake gaidata. Amma ta yi biris dashi. Jikinsa yayi sanyi sai kawai ya fice ya tsaya daga kofar gidan. Yana kallo Baban ya taso yana tambayarsa.

“Baba dama wajen Salisu nazo.” Ya fada yana sosa keya. A boye Baban yayi murmushi saboda yana ganin yadda Mukhtar din ya yi yasan me dakinsa ce ta koro shi da hali. Har yau abun dariya yake bashi saboda yadda take kishi da mahaifiyarsu Mukhtar din har ma da yaranta saboda kawai Baban ya taba nuna yana son Innar inda Innar taki yarda da auren sam. Shekaru sama da goma kenan amma ta kasa cire kishin nan a ranta.

Shigewa Baba yayi ba tare da yace komai ba. “Sa’a sarautar mata, ta mallam Gambo!” Ya fara mata kirari tunda ya lura da yanayinta.

Ganin cewa watakila Salisun yana jin su yasa ya daga murya, “kai Salisu, Mu’utar na jiran ka a waje.” Ya fada yana daukar buta ya zagaya yana jinjina kishin matarsa duk da sun tsufa.

Mukhtar yayi nisa a tunanin yadda zai cigaba da harkokin sa tunda ya samu aikin nan Salisu ya fito yana ta baza kamshin turare don kamshin ne ma ya dawo da Mukhtar hayyacin sa.

“Haka dai, kullum cikin tunani.” Abunda ya fara cewa kenan wannan ya sa Mukhtar din murmushi.

“Dan malam yaki halin malam. Wannan kwalliyar fa?” Muktar ɗin ya faɗa lokacin da ya ɗora idanun sa kan Salisun

Juyawa Salisun yayi alamun shi ya hadun nan sannan yace, “haba dan Allah kullum kazo sai ka tsaya anan kamar wani barawo sai kace baka san ɗakina ba a cikin gidan.”

Mukhtar bai amsa masa ba suka fara tafiya cikin layin.

“Toh ya ake ciki ne mutumina. Ya aikin?” Ya tambaya bayan yaga alamar ba zai samu amsa ba.

“Komai normal, Alhamdulillah ana ta ƙoƙari dai.”

“Toh Allah ya taimaka amma nikam Allah ya kiyaye nayi teaching kuma a private degree ne fa dakai na BUK kuma. Kamar ni dai ace nike da result ɗin ace ina teaching Ina? Nooo…” inji Salisun ya fada yana saka hannunsa a aljihu.

Murmushi Muktar ya yi. Kai ai ɗan gata ne kana da uba, ni kuwa wasu ke jira in samo in basu, ƙannena fa huɗu aƙa yanzu duk mata, in ban basu ba ai bana ce su zasu ban ba”

“Nima ɗin ai ba shi Malam ke min komai ba kaima ka sani” Salisun ya faɗa lokacin da yaɗan haɗe rai.

“Amma dai shi ke ciyar ka ko?”

Banza Salisun ya masa tare da yin gaba, iska Muktar ɗin ya furzar kafin ya ɗan ƙara sauri ya taddo shi.

Shiru sukayi saboda kowa da kalar tunanin da yake yi har suka isa majalisar tasu. Kamar ko yaushe in daya ya bawa daya haushi sai su chanja wajen zama. Suna zama kuwa sauran abokanan nasu suka lura.

“Oh ku dai ba kwa girma.”

Mukhtar ya bata rai. “Bar sokon mana. Matar sa ta gamu da wahala, tunda har yanzu ya gaza hankali ya gane a Nigeria ko me ka samu zaka haka zakayi indai ba haram bane”

Fusata Salisu ya yi, ” waye maras hankalin ai kai kasan ba hankali ka fini ba, ko dan kawai mutane na fade kana da nutsuwa kake tsanmanin da gaske suke?”

Dafa shi Muktar ya yi “sorry my guy wasa nake, yo banda abun ka ai abokin ɓarawo ɓarawo ne, abinda ya ni shi ya yi ka, ko me nace kamar akaina nake faɗa”

Hararar sa Salisu ya yi “Karka raina mun hankali fa”

Dariya Muktar yasa, nan Salisu ya kuma ƙuluwa

Ibrahim ne wanda ya ce “Haba guys, ya kuke mana haka ne? Please Muktar ka dena dariyar haka” An danyi shiru ana tunanin topic din magana kenan Mukhtar ya leka gefen Salisu cike da zolaya yace,

“Kuma fa kayi kyau yau mutumina. Ya kamata Maryama taga kwalliyar nan ta yaba.”

Banza Salisu yayi kaman bai ji ba.

Miƙewa Muktar ya yi bari in je gida inason kwanciya da wuri sabida tashin safe, har ya yi nisa ya ji Muryar Salisu tsayani zanje Gidan su Maryam suka jera tare suna tafe suna hira tamkar ba sune sukai rikici ɗazun ba ko da yake dama Salisu ne sarkin ruko shi Muktar da ya fahinci abin zai zama faɗa zai mayar wasa in kuma ya zama da anyi shikenan ya wuce.

<< Ko Da So 6Ko Da So 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×