Idanun Habeeb cike da ƙwalla ya ɗago tare da duban mahaifinsa ya yi magana cikin rawar murya, "Abba don Allah kada ka rabu da mahaifiya ta."
Murmushin da ya fi kuka ciwo Alhaji Mai Nasara ya yi, don ya fahimci in da ya dosa, "Zaka ɗauki Jummai da ɗanta ku tafi kenan?"
Kai Habeeb ya girgiza "Abba ai ba ɗana bane."
Alhaji Mainasara ya ya ce "Wannan ai maganar banza ce, bari in faɗa maka wani abu. Zaman lafiyarka da na uwarka a gidannan shi ne ka ɗauki matarka da ɗanka ku tafi, idan ba haka ba zaku ga. . .