Skip to content
Part 18 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Tsaye Jummai ta yi a inda take, ba kuma komai ne ya tsaida ta ba sai Ahamad da ke can ciki yana wasa, wanda kuma ba zata iya tafiya ta bar shi ba, ko ta tafin ma toh tabbas sai ta dawo.

Babban tashin hankalinta shi ne sanin labarinta da Aunty ta yi, a rayuwarta ta tsani wani ya san labarinta, muddin ba ita ta faɗa mashi ba, domin gani take zai ƙyamace ta.

“Yanzu da wace fuska zan kalli wannan mata da tun da daɗewa ta nuna kulawa a garemu ni da ɗana?” Tambayar da cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta yi ma kanta, lokaci ɗaya kuma tana jin wani irin tashin hankali a ranta, wanda da zaka kalle ta a lokacin sai ka gan shi ƙarara a tare da ita, domin hannayenta da ƙafafunta ba abin da suke sai karkarwa.

Dafa kafaɗarta da Aunty ta yi ne ya sa ta rumtse idanunta gam, ƙasan ranta kuma tana jin kamar ta nutse ƙasa don kunya.

“Kada ki fita kin ji, ki dawo ki zauna”

Aunty ta faɗa cikin sanyin murya.

Ƙin juyowa Jummai ta yi don bata san da wane baki zata kare kanta a kan tuhumar da lallai sai sun yi mata ita ba.

Ameer da ke jin kamar zuciyarsa zata fito ya ce “Ba magana ake maki ba”

Auntyn ta daɗa da cewa “Ki dawo na ce maki Fateema, kada ki fita”.

Sunan Fateema da Aunty ta kira ya ba Jummai mamaki, don ko Ameer bata tunanin ya san asalin sunanta, bare kuma matar da duka wannan ce haɗuwarsu ta biyu.

Abin da bata sani ba shi ne, sai da Ameer ya san komai na ta kafin ya shiga neman ta, saboda ko zata iya canja suna.

Hannunta Aunty ta riƙo, wanda ya bata damar juyowa ta biyo bayanta. Shi kuwa Ameer har a lokacin yana nan tsaye a inda yake. Ba abin da zuciyarsa ke yi sai tafarfasa, domin shi kaɗai ya san irin azabar da neman Jummai ya gana mashi, wanda da babu sonta a ransa, toh da sai ya ɗauki fansar wahalar da ya sha a kanta. Wani mugun kallo mai cike da jin haushi ya riƙa yi mata har ta zauna a ƙasa.

Muryar Aunty dake zaune a kan kujera ce ta sa shi ɗauke idonsa a kan Jummai, tare da dubanta a lokacin da ta ce mashi “Ka zauna mana.”

Ƙarasowa ya yi cikin falon tare da zama a kan kujera, lokaci ɗaya kuma ya dafe goshinsa da hannu tare da lumshe ido.

Jummai ma tunda ta zauna ta jawo gyalenta ta rufe fuska da shi, daga can ciki kuma sai zubar da ƙwallan baƙinciki take, don bata taɓa zaton a irin wannan lokacin zata haɗu da wanda ta sani ba.

Gaba ɗayansu sun yi jugum tamkar ba kowa a falon, a cikin zukatansu kuma suna ta kukan zuci.

Musamman Aunty da a ta tsani taga rayuwar ƴa mace ta gurɓata.

Duban Ameer Aunty ta yi ta ce “Ameer”.

Ɗago da jajayen idanunsa ya yi tare da duban ta, alamu ta yi mashi na ya bata nutsuwarshi, ya fahimci alamun, don haka ne ma ya cigaba da kallon ta yana jiran jin me zata ce.

Sunan Jummai ta kira, amma Jumman ta yi shiru kamar bata ji ba, saken kiran sunan ta yi sannan ta ce “Magana nake son yi da ke, don haka ki bani nutsuwarki a nan”.

Ɗan motsa ƙafar da ta yi ne ya tabbatar ma Auntyn da tana sauraron ta.

Cikin sanyin murya Aunty ta ce “Yanzu Fateema abin da kika aikata kin yi daidai, me ya sa kika bar gidan mahaifanki, kika zaɓi rayuwa wadda babu komai cikinta sai ƙasaƙanci da wulaƙanci, yanzu ina zaki da haƙƙin mahaifiyarki da kika gudo mawa?”

Wannan magana ta yi matuƙar taɓa zuciyar Jummai, bata san sadda ta fashe da kuka ba, me yasa ba’a yi bincike dalilin barin ta gida ba, sannan a riƙa yi mata faɗa.

Kamar Ameer zai yi kuka ya ce “Tunda ita fa ta samu farinciki, mahaifiyarta ai ko oho, wallahi Aunty da ana mutuwa a dawo, toh da sai in ce har mutuwa mahaifiyarta ta yi, domin sai da ta yi sati a I C U, ba tare da ta san me ke wakana a dunyar nan ba, da yake tana da sauran kwana sai gashi ta farfaɗo, amma kin ga wadda ta shiga halin dominta ko a jikinta”.

Itama Auntyn kamar zata yi kuka ta ce “Haba Fateema, ki yi ma kanki faɗa, sannan ki nemi mahaifiyarki, domin tana cikin wani hali”.

Wani irin kuka ne Jummai ta fashe da shi, bisa ga jin halin da mahaifiyarta ta shiga, sai dai bata yadda a dalilinta ne ta shiga wannan hali ba, domin ita dai bata ga alamar tana sonta ba, domin da tana sonta da bata azabtar da ita da yunwa da ƙishirwa ba.

Fiddo da kanta ta yi waje, tana kukan ta dubi Aunty sannan ta ce “Wallahi Aunty ba akaina mahaifiyata da shiga wannan hali ba, domin bata sona ko kaɗan”.

Aunty ta ce”Kamar ya bata sonki Fateema, dama akwai uwar da bata son ɗiyarta ne, ki dena faɗin wannan magana ma”.

Kuka mai sauti Jummai ta riƙa yi, wanda yake ƙara ma Ameer raɗaɗin zafin da ke ransa, a yanzu kam haushinta yake ji, amma kuma kukanta sosa masa zuciya yake.

Aunty ma ko kusa bata jin daɗin kukan da Jummai ke yi, lallashin ta ta shiga yi ta ce “Ki dena kuka, rayuwa kowa da tasa ƙaddarar, amma mahaifiyarki na sonki, kuma ya zama wajibi ki koma wurinta domin ki fidda ta daga ƙangin da kika sanya ta”.

Jummai ta ce “Wallahi ba zan koma gida ba”.

Aunty ta ce “Kamar ya ba zaki koma gida ba Fateema, toh ina ki ke da shi ne da yafi gidanku?”

Ameer ya buɗe baki a fusace zai yi magana kenan Jummai ta tsaida shi a sadda ta ce “Aunty a duniya ba gidan da ya fi gidanmu, amma ba zan koma ba domin gwara rayuwar kurkuku da can”.

“Haba Fateema, kin san me bakinki ke faɗa” in ji Aunty. Jummai ta ce “Aunty, Inna bata so na, ta tilasta mani rayuwa a ɗakin da sai da na buƙaci rayuwa a cikin ƙabari da zama cikinsa, sannan ta azabtar da ni da yunwa da ƙishirwa ni da jaririn da bai ji ba bai gani ba, ta yaya zan yadda da cewar tana sona”.

Ido Aunty ta rumtse tana jin wani irin tausayin Jummai a ranta, tabbas a ganinta da ita na farko ta lura tana cikin ƙuncin rayuwa, kuma in dai a irin wannan yanayi ne, toh bata ga laifin Jummai da ta gudu ba.

Ameer ma tabbas ya san kaɗan daga cikin halin ƙuncin da Jummai ta faɗa a gida, wanda a dalilin ganinta a wannan yanayi sai da ya kwashi kwanaki bai iya bacci saboda tausayinta, sai dai kuma gwara ta mutu a wannan halin da guduwa daga gidan iyayenta, domin gudun faɗawa muguwar rayuwa.  

Mur ya sha tare da danne tausayin Jummai a ransa, don ba zai iya goyon bayan ta ba duk da ya san tunzura ta a ka yi.

Ce wa ya yi “Iya wannan ce kaɗai hujjarki ta barin gida, toh faɗa mana wace riba ce kika samu bayan barinki gida”

Sharɓar kuka ta cigaba da yi, don ya mata kwarjinin da ko kallon sa ba zata iya yi ba, bare kuma ta bashi amsa.

Sosai ta ba su tausayi, amma ba yadda za’a yi su goyi bayanta tunda ta aikata kuskure.

Ɗan dafa kafaɗarta Aunty ta yi, sannan ta sake magana cikin raunin murya “Fateema, babu wata hujja da mace zata kafa akan barin gidan iyayenta, duk kuwa irin rintsin da ta haɗu da shi a gidan, me ya sa baki yi haƙuri da ƙaddara ba, me ya sa baki kai maƙura wurin ba mahaiyarki haƙuri ba.”

“Wallahi Aunty sai da na yi taba haƙuri, amma ta ce ganina ma ƙara mata damuwa yake.”

Aunty ta ce “Toh Sai ki ƙyale ta, kina nan zata neme ki da kanta.”

Faɗa sosai suka yi mata akan abin da ta aikata tun daga tushe, sannan suka nuna mata mafi girman kuskure da mace zata yi shine ta bar gidan mahaifanta da sunan neman ƴanci, domin ba wani ƴanci a waje, sai a gidan.

Kuka ta riƙa yi kamar ranta zai fita, wanda ya yi sandin ƙara mata ciwon da kanta yake.

Aunty ta fahimci faɗan ne bata so, cewa ta yi “Tilas a yi maki faɗa Fateema, domin bamu fatan rayuwarki ta sake komawa a cikin garari, ina da yaƙinin sai da kika wahala a garinnan kafin ki fara jin daɗi”.

Kukan da take bai sa sun dena yi mata faɗa ba, sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru.

Sai da ta tsagaita kukan ne Aunty ta tambaye ta “Yanzu a ina kike zaune?”

Shiru ta yi, don ba zata iya faɗa musu a hotel take da zama ba. Ameer da ya tsani shirun da take yi idan an tambaye ta ya ce “Ko ba kya ji ne”.

Cikin rawar murya ta ce “Hotel”.

Ras gaban Ameer ya faɗi, bai san sadda ya rumtse ido tare da dafe kai ya ce “Wai ni Allah” ƙasan ransa kuma yana jin wani irin ɗaci, domin ta tabbata yawon bariki Jummai ta ke.

Aunty kuwa a ruɗe ta ce   “Wane irin hotel kuma, duk gidajen garinnan baki da wurin zama sai hotel, kai kin shiga gararin rayuwa.”

Sake dafa kafaɗar Jummai ta yi sannan ta sassauta murya ta ce “Fateema, zaki iya rayuwa da mu”,  don batun tsegumin hotel ma bai taso ba, aikin gama ya gama, abin da kawai zasu yi shi ne ceton rayuwarta.

A fusace Ameer ya ce “Kamarya tana iya rayuwa da mu Aunty, ai ya zamar mata dole wallahi, ita da muguwar rayuwa kuma har abada wallahi, daga nan kuma gida zata koma, idan ya so ta kashe kanta.”

Sosai Aunty ta goyin bayan maganarshi “Tabbas kuwa Ameer.” Ta faɗa, tare da bin sa da idanu lokacin da ya miƙe ya bar falon, don ya kai maƙurar ƙuluwa da lamarin Jummai.

Maido hankalinta ta yi akan Jummai, sannan ta cigaba da bata magana, tare da nuna mata illar rayuwa ita kaɗai, domin babu irin hatsarin da ba zata iya faɗawa ba.

Bata gushe tana ba Jummai magana ba, har sai da ta yadda zata zauna dasu, domin da farko tutsewa ta yi akan ba zata zauna ba, saboda ta san daga nan sai garinsu kuma, wanda a halin yanzu bata muradin sa.

Hannunta Aunty ta kama suka tashi, sannan ta ja ta zuwa wani ɗaki, wanda asalin sa na yaranta ne Aisha da Salma da suke Level two a B.U.K.

Ɗaki ne mai ɗauke da ƙananun gadaje guda biyu, sai ƙatuwar wadrob, a gefe kuma doguwar kujera ce da kayan kallo.

Jikin bangon ɗakin kuma manne yake da hotunan kyawawan ƴan matan guda biyu.

Kallon hotunan Jummai ta riƙa yi, wanda ta ga fuskar Aunty a cikin tasu.

“Ki zauna a wannan ɗakin, na yarana ne da suke suke karatu a Kano, ki saki jiki anan, ki ɗauka kamar gidanku ne anan kin ji”

Kai Jummai ta ɗaga tare da lumshe ido a lokacin da hawaye suka zubo mata a kumatu.

Cike da tausayin ta Aunty ta ce “Ki je ki kwanta, sannan ki rage kuka don Allah, kin ga ba lafiya gare ki ba”.

Tafiya Jummai ta yi ta kwanta a kan gadon, Aunty na fita ta fashe da matsanancin kukan cizon yatsa, me ya sa karon farko bata bi Aunty ba, kuka sosai ta yi mai isarta. Wani bacci mai nauyin gaske ne ya ɗauke ta.

A cikin baccin ta yi mafarkin Alhaji Lawwali na mata kashedin zama a gidan yana faɗin “Ki yi gaugawar barin gidannan, sannan ki biyo ni mu tafi tare”.

Firgigit ta falka daga baccin, a lokacin ne Ammu ya shigo shi da Ahamad suka ce “Mammy ta ce ki tashi ki yi sallah.”

“Toh” kaɗai ta iya ce musu, bayan sun fita ta rafka uban tagumi, cikin ranta kuma tana tunanin wannan mafarki da ta yi.

Kasa yadda da shi ta yi, don haka ta ba ranta abin da ya faru ne ya sa ta mafarkin.

Yunƙurin tashi sallah ta yi, amma ta kasa saboda muguwar kasalar da ta sauko mata.

Tafi ƙarfin awa ɗayan wurin ba abin da take sai zancen zuci.

Sai da su Ammu suka ƙara zuwa kiranta cin abinci sannan ta taƙarƙara ta shiɗo. Ban ɗaki ta faɗa da nufin yin alwalla, kasa yi ta yi, sai ma ta kafe window da idanu, sakamakon iskan guguwan da ta ji a daidai saitin, a cikin iskan ne ta riƙa jin hayaniya da baɓɓakar dariya.

“Ashe da wasu mutane anan gidan” ta faɗa a ranta.

Alwallar ta yi ta fito, sallar ta kabbara, amma gaba ɗaya rafkanwa ce cike da ita, don sai da ta yi raka’a shida ba tare da ta sani ba, saboda dogon tunanin da ta faɗa.

Tana akan abin Sallah ne sai ga Altine mai aikin gidan ta kawo mata abinci, don a zaton Aunty kunya ce ta hana ta fitowa.

Kasa cin abincin ta yi, sai ma kwanciya, don wani mugun zazzaɓi ne ya rufe ta.

Tana nan kwance har aka kira la’asar, tana son miƙewa ta yi alwalla amma ta kasa.

Aunty ce ta shigo ɗakin tare da zama a kan kujera tana fuskantar Jummai, sai da ta yi kusan minti biyu tana kallon ta sannan ta yi magana cikin sigar tausayi.

“Fateemer ya kan?”.

A hankali ta buɗe idanunta tare dayin magana cikin shaƙaƙƙiyar murya ta ce “Da sauƙi”.

Aunty ta ce “Toh ki daure ki tashi ki yi sallah, idan Ameer ya dawo sai ya duba ki” “Toh” ta ce, sannan ta tashi zaune, kama ta Aunty ta yi ta miƙe, aikuwa juwa ta kwashe ta, Allah ya taimaka Auntyn ta riƙe ta da a ƙasa zata faɗi.

Kwantar da ita ta yi a kan kujera tana yi mata sannu. Kamar ance ta duba abincin, sai taga tun daga plate har ruwa da lemu  ba abin da ta taɓa

“Wai baki ci abinci bama” kai Jummai ta ɗaga.

Ta ce “Toh tashi ki ci” tashi Jumman ta yi, aikuwa da hannunta ta riƙa bata, Jummai na karɓa tana kukan tausayin kanta, me ya samu mahaifiyarta ne da taƙi bata irin wannan kulawar. 

Sai da ta ci da yawa sannan Aunty ta bata ruwa ta sha.

Tana nan zaune har abincin ya lafa, cewa ta yi ta je ta yi alwalla.

Tana shiga ban ɗaki ta ji irin abin da ta ji a ɗazu, guguwa ce ta taso har tana dukan ƙyauren window.

A wannan karon bata tsaya ba, ta yi alwalla ta fito, don ta san bazara ce, tashin guguwa ba wani abu bane, tana gama alwalla ta fito ta yi salla.

Shi kuwa Ameer da wani irin takaici ya bar gidan, don ba zai iya zama ba, ba abin da ke damunsa sai kishi, yanzu ba Habeeb kaɗai ya tsana ba, hada shegun da suka ɗauki nauyin rayuwar Jummai a hotel.

Yana cikin tafiya a mota sai ga kiran Dr. Misau ya shigo a wayarsa, parking ya yi a gefen titi sannan ya ɗaga kiran.

Gaisawa da ƴan maganganu suka yi, sannan ya tambayi Misau ɗin wajensu Asabe, tunda yanzu shi ke kula da su.

Misau ɗin ya ce “Ba laifi gaskiya, yanzu ta rage damuwar nan”.

Ameer ya ji daɗin haka, cewa ya yi “Masha Allah, ai komai ya kusa zuwa ƙarshe”.

Wannan magana ta ba misau mamaki, daga can ya ce “Kamar ya komai ya kusa zuwa ƙarshe, ko kun ji labarin Jummai ne?”.

“Eh toh, ana dai bincike”.

Abin da ya sa ya ƙi faɗa mashi an ga Jummai, saboda tsoron Jumman na iya guduwa, tunda ta fara botsarewa.

Sallama suka yi, ya katse kiran, tare da tada motarshi ya tafi.

Ba shi ya dawo gida ba sai tara na dare.

Aunty ta ce “Muna ta jiranka ka duba Fateema, gashi kuma har ta yi bacci”.

Ɗan haɗe rai ya yi sannan ya ce “Ai sai Monday ko ina duba ta Aunty, saboda komai na asibiti.”

“Toh” Aunty ta ce, don ta san a gida ma akwai kayan aikin, bai dai ga damar duba ta ba.

“Gobe toh sai ka kai su ita da Altine a hotel ɗin su kwaso kayanta”.

“Allah ya kaimu goben” ya faɗa, tare da juyawa ya fice.

Rufe falon ta yi, sannan ta shige ɗakinta ta kwanta.

Washe gari bayan sun yi breakfast suka shirya ita da Altine, dasu Ahamad da nufin zuwa hotel kwaso kayanta.

Tuni Altine da su Ahamad sun fita farfajiyar gidan, suna jiran fitowar Jummai da Ameer.

Fitowa Jummai ta yi cikin ɗan ƙaramin gyalen da ta zo da shi jiya, a lokacin Ameer da Aunty suna magana a falo.

Wani mugun kallo ya jefe ta da shi, wanda ya sanya ta sadda kanta ƙasa, domin a zatonta haushin lafin da ta yi ne ya sanya shi yi mata shi.

sai da ya ce “A haka zaki fita da wannan gyalen”, sannan ta fahimci manufar kallon.

“Ki buɗa a cikin kayansu Salma zaki samu Hijabs, sai ki ɗauki wadda ta yi maki ki saka”, Aunty ta faɗa idonta na kanta.

Komawa ta yi ta sanyo hijabi, Lokacin har Ameer ya fita, tana zuwa cikin motar ya tada suka nufi hotel ɗin.

Da isarsu ita da Altine suka shiga ciki suka kwaso komai nata suka sanya a boot, sannan ta maida mukullin ɗakin.

Motar suka shiga, Ameer ya kama hanyar ɗayan gidan da zasu kwaso kayan kenan Alhaji Sani, wanda kuma shine yayansa kuma mijin Aunty ya kirashi a waya, cewar yayi gaugawar karɓo mashi saƙo a wurin wani.

Juyawa yayi ya nufi wurin karɓar saƙon, da yake sun yi kusa da gida sai ya ce gobe Insha Allah zai kai su ɗayan gidan.

Da isarsu gida ya buɗe boot ɗin suka fara kwasar kayan, shi yana fiddowa su kuma suna ɗauka, wanda mafi yawa duk kayan wasan Ahamad ne.

Wata jikka ce ya ɗauko ya miƙa ma Jummai, aikuwa tana karɓa handle ɗin jakar ya cire, duk tarkacen dake ciki suka watse.

Mutuwar tsaye su duka suka yi, sakamakon kwalayen condom ɗin da su ne suka fi yawa a jakar.

Jummai kuwa bayan mutuwar tsaiye, sai da ta sauke ajiyar zuciya, domin akwai abin da bai faɗo ba, wanda da Ameer ya ganshi, toh da ƙila dukanta zai yi ta yi.

Juwa na ɗibar Ameer ya yi maza ya koma cikin motar.

Da kyarma Jummai ta shiga tattara kayanta, duk saurinta sai da Altine ta ga abin da take ɓoyo, amma Altinen sai ta yi kamar bata gani ba.

Jakar Jummai ta ɗauka ta nufi cikin gidan, kamar wadda ruwa ya ciwo, ba inda ta zame sai ɗakin da aka kaita, turus ta zauna, ɓangare ɗaya gabanta na wata irin faɗuwa.

Altine kuwa da yake ta ƙware a gulma, tana shiga ta nufi kitchen domin Aunty na can, sai da ta sassauta murya sannan ta ce “Anya kuwa wannan yarinyar kanta ƙalau?”. 

“Me ya faru”

Aunty ta tambaye ta.

“Hajiya jakarta zaƙire take da kwaroron roba da kuma..” kafin ta ida Aunty ta dagakar da ita, don ta tsani gulma

“Na ji don Allah, je ki”, fuskar Aunty a ɗaure ta faɗi haka.

 Sumui-sumui ta fito tare da shigewa ɗakinta.

Fitowa Aunty ta yi daga kitchen ta dawo falo, domin maganar Altine ta ɗaga mata hankali.

Bata samu kowa a falon ba sai Ahamad da Ammu, tambayar su ta yi ta ce “Ina uncle?”

“Yana mota” Ammu ya faɗa.

Ɗan leƙawa ta yi ta window ta ga boot hangame, kira ta kwadama Altine, bayan ta zo ta ce “Wai ba’a gama kwasar kayan ba ne?”

Altine ta ce “Angama Hajiya”

Ɗan ƙara leƙawa ta yi sannan ta ce “Toh ya aka yi boot kuma a hangame”.

Shiru Altine ta yi, don bata san dalilin barin boot ɗin a haka ba. Ɗakin Jummai Aunty ta nufa, Jumman na ganinta tasha jinin jikinta, don a azatonta ta sani. Auntyn ta lura da yanayinta, don haka ne ta ƙara faɗaɗa fuskarta ta ce “Akwai sauran kayan da ba’a kwaso bane a mota?”

“Babu saura” Jummai ta faɗa, lokacin da take wasa da yatsunta.

“Okay” Ainty ta ce, sannan ta fita.

Da kanta ta nufi motar, aikuwa ta samu Ameer ya kifa kansa da stiyarin mota.

Ɗan bubbuga glass ɗin motar ta yi, ido Jajur ya buɗe tare da fitowa.

Sauyin yanayinsa ya sa ta tambayar sa ” Lafiya”.

Kasa magana ya yi sai dai huci, ganin haka ne ya ƙara tabbatar mata da gaskiyar abin da Altine ta faɗa.

Shiru Aunty ta yi, daga bisani ta ce “Ka rufe boot din mana” tana faɗin haka ta dawo ciki.

Rufe motar ya yi sannan ya fita wajen gidan ya zauna tare da haɗe kai da gwiwa.

Wani irin baƙinciki da kishin Jummai ne suka rufe shi, a wannan gaɓar, da zai iya cire son Jummai a ransa, toh da ya huta, domin rayuwar Jummai ta gurɓata da yawa, haka ya ƙaraci zamansa a nan, sannan ya dawo cikin gidan.

Sai da yamma sannan Aunty ta samu Jummai a ɗaki, tare da yi mata magana akan dawowarta gidansu, kamar ta yi bankwana da duk wata baɗala da ta yi a waje ne, don haka ta fara lissafin istibra’i idan ta yadda da hakan.

Alƙawali Jummai ta yi ma kanta cewar ta yi bankwana da duk wata muguwar ɗabi’a, dama neman abinci ne ya sanya ta haka, kuma tunda ta samu, toh shikenan.

Wannan alƙawali ne ya harzuƙa Alhaji Lawwali, don haka a wannan dare ya ɗora ɗambar azabtar da ita.

Tana kwance ta ji kamar an danne ta, daƙyal ta iya buɗe ido, aikuwa a kan idonta wasu fararen tsuntsaye sun tashi tare da bi ta ƙofa sun fita.  Jikinta na ɓari ta kunna fitila tare da duba agogo, aikuwa ta ga duka shaɗayan dare.

Wani irin tsoro ne ya kama ta saboda ita kaɗai ce cikin ɗakin, Ahamad da Ammu suna ɗakin Aunty.

Addu’a, ta shiga karantowa, da ta fara wannan sai ta saki ta kamo wata.

A haka har ɗayan dare. wani bacci mai nauyi ne ya tafi da ita, ba ita ta falka ba sai ukun dare, sakamakon buƙatar shiga banɗaki data kama ta. Saukowa ta yi ta shiga banɗaki ta biya buƙatarta sannan ta fito.

Wata irin ƙara ta fasa sakamakon ganin Alhaji Lawwali zaune a kan kujera yana kallon ta.

Daga nan ta sulale a inda take, tabbas hankalinta bai gushe daga jikinta ba, sai dai kuma bata iya ko ɗaga yatsanta.

Baki ta buɗe tana son yin addu’a a lokacin da ta ga ganshi duƙe saitin fuskarta, bata ga tasowarshi ba, amma sai dai ta ganshi a gabanta.

Cikin wata irin murya mai razanarwa ya kira sunanta “Gargaɗi na ƙarshe na zo yi maki, akan ki bar gidan nan, domin kin riga da kin zama mallakinmu, idan ba haka kashe ki zamu yi”.

Wani irin kallo ta riƙa binsa da shi, cikin ranta kuma tana son sanin manufar sa.

Kamar ya san me take nufi ya ce “Dubi can,” inda ya nuna matan ta duba.

Aikuwa ta ga komai na ɗakin ya ɓace, sai wani mugun daji mai duhun gaske.

Wasu irin halittu ne masu ban tsoro ta gani a gaban wuta, sai ɗaukar mutane suke suna azabtar da su da wutar.

A ɗayan ɓangaren kuma ta ga wasu mutane zaune a ƙarƙashin itaciya ta ƙaya, su Hajiya mai gidan Abinci ne zaune cikin jajayen kaya.

Kasa ɗauke idanunta ta yi akansu cikin ranta tana son fahimtar abin da hakan ke nufi.

Wani abu ne kamar mashi ya zungure ta da shi sannan ya ce “Mu matsafa ne, aikinmu shi ne shan jini da cin naman mutane domin samun kuɗi, waɗancan da kika gani ana azabtarwa, sune masu yi mana taurin kai, waɗancan kuma da kika gani zaune, su ne waɗanda suke cikin tafiyarmu.

Zaɓi ya zame naki, ko ki shiga a tawagarmu a tafi dake, ko kuma ki shiga sahun waɗanda zamu cigaba da azabtarwa”.

Kallon tsana ta jefeshi da shi, ƙasan ranta ta ce “Allah ya tsare ni da shiga ƙungiyarku”.

Ya fahimci kallon da take mashi, “Akwai alamun taurin kai a tare da ke, don haka ki fara aje shi tun yanzu”.

Yana faɗin haka ya daka mata wannan mashi a tafin hannu.

Ido ta rumtse tare da fasa wata irin ƙara a ƙasan ranta, don bakinta ba zai iya buɗuwa ba.

Tamkar electric shock haka dafin mashin nan ya riƙa shiga jikinta, tun tana iya tantance komai, har ta kai ga bata san inda kanta yake ba.

Yana ganin hankalinta ya gushe, ya biya buƙatarsa da ita, wadda ba don sha’awa ya yi haka ba, sai don ya zuƙi jinin jikinta.

Asali dama duk sadda ya kusance ta toh sai ya sha jininta, sai dai ba a yadda zata cutu ba.

Yana gamawa ya baɓɓake da wata mahaukaciyar dariya, wadda ta sa ta farfaɗowa daga sumar da ta yi.

Kallonshi ta yi a lokacin yana tsaye a kanta, da jajayen idanunta, cikin ranta tana nadama da baƙincikin sanin Alhaji Lawwali a rayuwarta.

“Ashe dama mugu ne,”  ta faɗa tare da fashewa da kukan takaici, don ta ji a jikinta ya kusance ta.

Ido ya zaro mata sannan ya ce “Tafiya zan yi, gobe zan dawo, don haka ki yanke hukunci”.

Yana faɗin haka ya shafar mata fuksa, take wani bacci ya ɗauke ta.

Daga nan gidan tsafinsu ya nufa, Hajiya mai gidan abinci ta ce mashi “Gargarɗin da ka yi mata yayi, sai dai kada ka bari ta faɗa ma mutanen gidan abin da ke faruwa, domin zasu iya ɗaukar mataki akanmu.” Tana gama faɗin haka ta miƙo mashi wani sabon ƙoƙo.

“Zubo jinin anan”,  Jinin da ya zuƙa a jikin Jummai ya amayar a cikin ƙoƙon tare da miƙa mata.

Kai ta kafa ta sha, sannan ta miƙa mashi ya sha, haka sai da aka zagaye kowa ya sha.

Ruwa aka zuba a ka karkaɗe ƙoƙon da shi, sannan aka watsa a cikin wutar.

Muryaryar Jummai ce ta fito a cikin wutar tana ta kuka. Wannan kuka da take da gaske ne, domin wata irin azaba take ji a jikinta, yunƙurin tashi ta shiga yi amma ta kasa.

Sai da asuba ta ƙarato ta ji kamar an kwance ta daga ɗaurin da aka yi mata.

Da ƙyal ta iya tashi zaune, “Me ya faru da ni ne” ta faɗa tare da fashewa da matsanancin kuka, domin tabbas abin da ta gani ba mafarki ba ne,”Idan kuwa gaskiya ne, toh Alhaji Lawwali ka makaro wallahi, ko kashe ni zaka yi ba zan shiga ƙungiyar asiri ba”. Cikin tsananin fushi ta faɗi haka.

Taƙarƙarawa ta yi ta miƙe, sai ta ji kamar ba ita ba, don ba ƙarfi ko kaɗan a jikinta.

Da ƙyal ta faɗa banɗaki ta yi wanka gami da alwalla ta fito.

Tana cikin chanja kaya kenan aka bugar da ita ta faɗa kan gado, daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba, sai da Ammu da Ahamad suka shigo, saboda Ahamad na falkawa ya kama nemanta yana kuka.

Gadon su duka suka haye, ammu ya shiga bubbuga ta, aikuwa tana buɗe idanunta kanta ya wani mugun sara.

“Wayyo Allah” ta faɗa tare da dafe kan.

Hannu Ahamad ya sa ya janye mata hannu ya ce “Amma” cikin muryar kuka.

Hawaye ne Ammu ya gani suna bin kumatunta.

Aikuwa da sauri ya dira kan gadon tare da rugawa ya faɗo ma Aunty cewar Jummai na kuka.

Da hanzari Auntyn ta shigo ɗakin.

Zama ta yi gefen gadon damuwa bayyane a fuskarta ta ce “Fateema me ya faru kuma?”.

“Aunty kaina ke ciwo” Jummai ta faɗa tana kuka.

Sannu Auntyn ta yi mata tare da faɗin “Anjima sai ku iske Ameer asibiti ya duba ki”.

Kallon Yadda Jummai ke ta nishi ta shiga yi, da taga abin yayi yawa sai ta kama hannunta suka dawo falo.

Kwanciya Jumman ta yi akan kujera tana ta juye-juye.

Anty kuma tana tsaye kanta tana mata sannu.

Ameer ne ya shigo cikin shirinsa na zuwa Asibiti.

Ganin Aunty tsaye kan Jummai ya ce “Me ya faru?”.

“Kanta ke ciwo”. ta bashi amsa.

Kallon Jummai yayi sau ɗaya sannan ya ɗauke kai, ko kusa bai ji tausayin yadda take ta wai-wai ba, don a ganinsa ciki ne da ita.

Aunty ce ta ce “Anjima zasu iske ka sai ka duba ta”.

“Okay” kaɗai yace, tare da sake kallon Jummai a karo na biyu. Sai da ya gama kallonta sannan ya ya ɗauki Ammu dake cikin shirinsa na zuwa makaranta suka fita. 

Ɗan shirun da Jummai ta yi ne ya sa Aunty tafiya kitchen.

A hankali Jummai ta ji an bubbuga jikinta, buɗe idanunta ta yi don ta ɗauka Aunty ce.

Abin da ta gani ne yasa ta ƙwalla ƙara, wadda kuma ba wanda ya ji wannan ƙara.

 Hajiya mai gidan abinci ce tsaye gabanta ita da Alhaji Lawwali cikin jajayen kaya.

Bayansu kuma wasu mutane ne, waɗanda zata iya shaida fuskokinsu a gidan abinci, suma duk cikin jajayen kaya.

Dariya Hajiya mai gidan abinci ta baɓɓake da ita, aikuwa sauran suma suka amsa, gaba ɗaya ba abin da ke fita sai dariya.

Ita kuwa duk ta ruɗe, ba abin da jikinta ke yi sai karkarwa.

Tsawa Hajiyar ta daka mata, tare da zagayowa a wurin kanta ta tsaya, “Jummai, Asibiti zaki ko, toh ki je ki ga idan zaki samu lafiya”.

Cikin tsananin tausayin kanta ta ce “Me na yi muku ne da kuke wahalar da ni”.

“Son ki muke, don haka ki shigo cikin ƙungiyarmu”.

Roƙonsu ta kama yi “Don Allah ku rabu da ni, ni bana sha’awar ƙungiyarku”.

 Dariya Lawwali ya babbake da ita, sannan ya haɗe rai kamar ba shi ba.

“Kin makaro yarinya, ko ki biyo mu, ko mu kashe ki”.

Ƙuri ta yi ma Alhaji Lawwali tana mamakin yadda yake.

Dawowar Aunty cikin falon ne yasa Jummai nemansu ta rasa, sai dai sautin muryar Hajiya mai gidan abinci, tana faɗin “Zamu dawo, duk inda kike muna tare da ke”.

Ido ta rumtse jijinta na ta ɓari, a gigice Aunty ta taɓa ta don ta ɗauka suma ta yi “Fateema”.

Buɗe idon ta yi tare da kafe Aunty da su, sai da Aunty ta ƙara taɓa ta sannan ta ƙyafta.

“Har yanzu ciwon kan?”

Jummai ta ɗaga kai.

Sannu ta yi mata sannan ta ƙara da cewa.

“Breakfast nan Altine zata kawo, ki daure ki ci, sai kiyi wanka, zata raka ki asibitin”

Tana gama faɗin haka ta kama Jummai ta tashi zaune.

+Breakfast ɗin Altine ta kawo, matsa mata Aunty ta yi, ta ci da ƙyal.

Aikuwa Tana gamawa Amai ya tuƙo ta, da hanzari ta nufi ɗakinta tayi aman a banɗaki, sannu Aunty ta riƙa yi mata.

Wanke Aman ta yi, sannan ta yi wanka ta fito.

Kaya ta chanja, sannan Aunty ta bata Hijabi ta sanya.

A lokacin Altine itama ta fito da shirinta. Drivern gidan ne ya ɗauke su a mota suka nufi Asibitin da Ameer ke aiki.

Sun kusa kaiwa kenan ta ji ƙamshin turaren gidan Alhaji Lawwali ya game cikin motar, wata irin faɗuwa gabanta ya yi don a sadda suka shigo motar babu ƙamshin.

Ji ta yi Altine ta taɓo ta, ta juya da nufin yi mata magana kenan ta ga fuskar Hajiya mai gidan abinci a fuskar Altine.

Wasu irin Zaga-zagan haƙoran da ke bakinta ta washe, lokaci ɗaya kuma miyau mai sirki da jini ya riƙa jalala a daga bakinta, “Dama na ce maki zamu dawo, don haka ki fito mu tafi”.

A firgice Jummai ta ta juya zata buɗe murfin mota ta gudu.

Ruƙo ta Altine ta yi ta ce “Ke lafiya, ina zaki”.

Sake duban Altinen ta yi, sai ta ga ita ce ba Hajiya ba.

Fauzewa ta yi, ta cigaba da kallon gabanta har suka isa Asibitin.

Da fitarsu a motar Jummai ta ji ƙamshin turaren ya sake shiga hancinta, a wannan karon bata kalli Altine dake gefenta ba, sai dai ta kalli gabanta.

A cikin kunnenta ta ji ance “Rako ki muka yi Asibitin”.

Ido ta rumtse gabanta na wata irin faɗuwa har kuwa ta kai ma wata pillar karo.

“Ke kuwa kamar baki gani” Altine ta faɗa tare da riƙo mata hannu suka tafi.

Mahaɗa suka yi da Ameer, sannan suka shiga office ɗinsa da ita, Altine da Ahamad kuma suka zauna waje.

Tunda ta zauna ko kallonta bai yi ba cigaba da danna computer, bayan ya gama ya juyo gare ta fuska murtuke ya ce “Me ke damunki?”.

Kamar zata yi kuka ta ce “Ni ban san me ke damuna ba.”

“Kamar ya baki san me ke damunki ba” ya faɗa mamaki bayyane a fuskarsa.

Shiru ta yi tana kallon window office ɗin, wanda kuma wata fuska ce ta ke gani a jikin window tana mata dariya tare da faɗin “Ai ba zaki taɓa sanin damuwarki ba, har sai kin zama ƴar tawagarmu”.

Inda take kallo Ameer ya kalla, aikuwa ta gafuskar ta ɓace daga daga wurin.

“Wane kalar ciwo ne kike ji a jikinki” Ameer ya katse mata kallon wurin.

“Ciwon kai ne mai tsanani, sai kuma kasala, wani lokaci sai in ji kamar ba ni ba ce”.

Kallonta ya shigayi, a matsayinsa na likita yana son gane meke damunta.

Mai makon ya gano, sai kuma wani abu na daban, domin kyau da kwarjini ta ƙara masa, wanda ya farfaɗo masa da sumammen son da yake mata.

Ido ya lumshe na wasu daƙiƙu tare da faɗin “Jummai na da kyau, sai dai a yanzu bana iya cigaba da sonta”.

Buɗe idanun ya yi sannan yayi mata awon bp.

A zatonsa zai ga jininta ya hau, sai ya gaya yana matakin da ake sonsa.

Tasowa ya yi ya zo gabanta sannan ya ce “Zan duba cikin idonki, don haka ki gyara”.

Gyarawa ta yi, ya buɗa idanunta, faɗuwar gaba ce ya samu kansa a ciki, wadda bai rasa nasaba da kusanci da ya samu kansa da ita.

Ƙuri ya yi ma ƙwayar idonta, amma bai ga komai a ciki ba.

Wurinsa ya koma ya zauna.

Cikin wata irin murya ya ce “Baya ga abin kika lissafa, kina jin wani abu?”.

Kai ta girgiza, aune-aunen jini ya rubuta mata  tare da tura ta lab.

Da yake da wuri ta je, ta samu duka an ɗiba jinin.

Dawowa ta yi wurinsa da nufin karɓar magani.

Miƙa mata magungunan ya yi sannan ya ce “Toh ki tafi, zan karɓi result ɗin in duba”.

Kuka ta fashe da shi, ya ce “Kuka kuma? “

Ta ce “Don Allah yaya ka kaimu gida”.

Haɗe rai ya yi “Ba tare driver kuke ba”.

“Eh” ta ce, ya ce “Toh kuma shine zan katse aikina in kaiku gida,  idan ba zaki bi drivern ba ki zauna nan”.

Yana faɗin haka ya cigaba da danna computer.

Idanunta na fitar da hawaye ta fito daga office ɗin, tsoronta kada ta sake ganin abun tsoro.

Tashi Altine ta yi suka nufi mota, aikuwa abin da bata son shi ta gani, domin daga drivern har Altinen sun koma mata waɗannan mutanen.

Gida ma data koma a matsayin Hajiya mai gidan abinci ta riƙa kallon Aunty.

Shi kuwa Ameer gaba ɗaya tunanin Jummai ya hana shi aiki, Lallai irin son da yake mata ba zai iya cire ta a rai ba.

Ganin haka ne ya sanya Alhaji Lawwali harzuƙa, saboda har gobe yana sonta, mafarin bai bari aka kashe ta ba.

Sai dai tsananta mata azaba da yake yi, duk don ta dawo cikinsu, wanda kuma idan ta dawo sai ya aure ta.

Toh ita kuma ta sanya kafiya, duk sadda suka bayyana gare ta da manufarsu sai ta ƙiya.

Mafarin suke ta wahalar da ita, duk gwaje-gwajen da aka yi mata ba’a gane ciwonta ba.

A ranar da suka kai ta daji ne suka ɗaure a jikin wata bishiya, sai dai wata daga cikinsu ta dangwalo wuta ta manna mata a jiki.

Ita kuwa ba abin da take sai kuka.

Aunty dake gabanta a falo duk hankalinta ya tashi. Domin suna ganin Jummai, amma basu ganin irin halin da take ciki sai kuka.

 Waya ta kira Ameer, da yake yana kusa sai gashi ya shigo.

 Hankalinsa tashi ya yi bisa ga yadda Jummai ke kuka.

“Aunty, anya wannan ba iska ne ke damunta ba”.

“Wallahi nima abin da na zata kenan Ameer, ka ga dai ba irin awon da ba’a yi mata ba, amma ba wata cuta a jikinta”.

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke tare da faɗin “bari na nemo mai ruƙiyya Aunty”.

“Toh” Aunty ta ce,

Ya juya ya fita.

Ɗan tsagaita kukan Jummai ta yi, a lokacin da ta yanke hukuncin shiga cikin ƙungiyar, don azabar ta ishe ta.

Dariya suka ɓaɓɓabke da ita, musamman Alhaji Lawwali, ƙyale ta suka yi, tare shirya inda zasu haɗu da ita cikin dare a roundabout.

Gani Aunty ta yi, ta yi bacci.

Altine dake gefe ta ce “Ai Hajiya tun ranar da muka je asibiti na fahimci haka”.

Shiru Aunty ta yi, don ta san da ta bata dama, toh gulma ce zata shigo. Ameer ne ya shigo shi kaɗai tare da shaida musu mai ruƙiyyar bai nan, amma sai zuwa gobe.

Wuri samu ya zauna, suna ƴar hira jefi-jefi da Aunty.

Kiran magarib ɗin da aka fara ne yasa suka tashi.

Ameer ya ce “A tada ta tayi sallah,” Aunty ta ce a ƙyale ta tunda ta samu bacci.

Nan suka barta, suka yi shirin sallah, har aka yi isha’i tana nan kwance.

Bayan Aunty ta fito ne ta tada ta, lafiya lau ta tashi ta ci abinci, sannan ta koma ɗakinta, Maimakon ta yi salla, sai ta koma ta kwanta.

Can biyun dare ta ji ana kiranta ana cewa “Ke muke jira ki fito”,  a ggauce ta tashi ta canja kaya kamar wadda zata unguwa.

Sanɗo ta fara, aikuwa ta samu sa’ar buɗe falon, saboda an manta mukullin a jiki.

Kamar wadda bata son taka ƙasa ta riƙa tafiya.

Ta kai bakin gate kenan ta ji muryar Ameer yana faɗin “ke ina zaki je”,

Ashe ya ga sadda ta fito ta window, a lokacin ya yana shirin kabbara nafilar da ya saba yi duk dare.

A tsorace ta waigo don azatonta ba mutum bane.

Wani wawan mari ya sauke mata a fuska, ya ce “Wato guduwa zaki yi ko”.

Hannunta dafe da kumci ta gigice tare da rasa abin da zata ce.

“Ni ba guduwa zan yi ba, wurinsu zan je,”.

Ras gabanshi ya faɗi, “Wurinsu wa?” ya tambaye ta cikin fushi.

ta ce “Sune suke kirana, sun ce idan ban je ba kashe ni zasu yi”.

Kora ta ya yi ta koma ciki, don a zatonsa ƙarya take.

Bubbuga ma Aunty ƙofa ya yi, baya ta fito ya nuna mata Jummai dake ta zare ido ya ce “Ga ta nan, ba don Allah yasa idona biyu ba, toh da ta gudu”.

“Wallahi Aunty ba guduwa zan yi, cewa suka yi zasu ƙyaleni idan na je”.

“Su wa kenan?” Aunty ta tambaya hankali a tashe.

Jummai ta buɗe baki zata yi magana kenan ta sulale.

“Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un” Aunty ta shiga faɗi tare da riƙe ta.

“Wata sabuwa Ameer, me hakan ke nufi”

Kai ya dafe tare da sauke ajiyar zuciya ya ce “Allah ne Kaɗai mafi sani Aunty”.

Jijjiga ta Aunty ta shiga yi tare da kiran sunanta, amma shiru bata motsa ba.

Ruwa Ameer ya miƙo mata ta yayyafa mata, nan kamar ba rai ajikin Jummai.

Rungumeta ta yi tare da fashewa da kuka “Ameer yanzu ya zamu yi da ɗiyar mutane, ka da ta mutu a hannunmu”.

Gabanshi na wata irin faɗuwa ya ɗuƙa tare da ɗago hannun Jummai, jijiyar ya ɗan danne, sai ya ji tana harbawa.

“Kada ki damu Aunty, Kamar iska ne ya bugar da ita”.

Ruwan da ya ɗebo ne ya fara tofa ayatul kursiyyu a ciki, aikuwa yana watsa mata ta fasa ƙara.

Wata irin gigita Aunty ta yi don tsoron iska take, duk kuwa da shekarunta.

“Iska ne Aunty, gobe Insha Allah sai a kira Malam Ali”.

Zamar da ita Aunty tayi, sannan ta ɗauko fillow ta tada mata kai, don tsoron Rungumeta take a jikinta.

Ɗan nesa kaɗan da ita ta zauna, Ameer ma akan kujera ya zauna suka sa ta a gaba, suna jiran safiya ta yi a kira Malam Ali mai ruƙiyya.

A kuma wannan dare ne Alhaji Mainasara yake ta shirin tafiya UK, domin an sanar da shi Habeeb na can asibiti rai a hannun Allah.

A yadda hankalinsa ya tashi bai ƙi ya buɗe idanu ya ganshi gaban ɗansa ba, wanda ya daɗe yana kewa.

Zaune yake a kan gado ya yi tagumi, Uwani ce ta dafa shi tare da yin magana cikin damuwa ta ce “Alhaji ka kwantar da hankalinka, Insha Allah abin bai kai yadda ake zato ba”.

Hannunsa ya ɗora akan nata sannan ya yi magana cikin raunin murya “Toh Allah ya sa haka, ni dai in tsoron rasa Habeeb”.

Wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo mashi sakamakon nadamar tsananin fushin da ya nuna ma Habeeb a can baya, duk da kuwa ya chan-chi hakan, amma kuma abin ya yi yawa, domin fin shekara bai sake bi ta kansa, duk da kira da kuma saƙunan nadama ban hanƙuri da Habeeb ɗin ya riƙa tura mashi.

Haƙuri Uwani ta cigaba da bashi, amma ko kusa ziciyarsa bata ɗauka ba.

A cikin wannan yanayi suka kai har asuba. Sallah ya fita a masallaci ya gabatar, ita kuma Uwani ta koma bedroom ta yi tata.

Bayan an gama sallar yana ta kyarmar shigowa gida ya ga duhun mutum a ƙofar gidansa.

Fitila yasa ya haska, abin mamaki sai ya ga Hajiya Mairo ce tana shirin ƙwanƙwasawa.

“Alhaji” ta faɗa tare da ƙarasowa gabanshi ta tsaya.

“Ke ce a irin wannan lokacin?” ya faɗa tare da ɗan ja da baya.

Kamar zata yi kuka ta ce “Ni ce Alhaji, maganar Habeeb, don Allah yaushe za’a shirya ganinsa?”, saboda ta riga shi sanin ma Habeeb bai da lafiya. Kuma tun a ranar da ta sani ta so tafiya, sai dai rashin kuɗi ya hana, domin har yanzu Hajiya Sa’a bata biya ta kuɗinta ba. Sannan ta nemi bashi a duk inda take zaton zata samu, amma ba wanda ya bata, da ta rasa yadda zata yi ne ta zo wurin Alhaji Mainasara. 

Numfashi ya sauke sannan ya ce “Ni kam dai yau nake shirin tafiya Insha Allah”.

Ta ce “Don Allah toh me zai hana mu tafi tare Alhaji”.

Mur ya sha tare da faɗin “Dawa, hanyar jirgi daban da ta mota Mairo”.

Magiya ta kama yi mashi akan ya taimaka ta su tafi tare, saboda yanzu bata da kuɗin da zasu kai ta UK.

Shigewarsa yayi gida, don ƙagare yake yabar garin.

Ko Uwani bai faɗa ma ya ga Mairo ba, ya kama shiri, bayan ya gama ya rungume Ahalinsa tare yin bankwana ya fito.

Driver ne ya ɗauke sa, suka kama hanyar Airport. Hajiya Mairo kuwa kamar mahaukaciya ta koma gidan da ta ke haya, kuka sosai ta riƙa yi kamar ranta zai fita, gani take ma kamar Habeeb ya mutu.

Matar da suke haya a gida ɗaya ce ta fito tare da tambayrta me kuma ya faru.

Tana Kuka ta ce “Lami na rasa yadda zan yi, so nake in ga halin da ɗana yake ciki, amma ba dama, ƴan kuɗaɗena mutane duk sun cinye”.

Lallashinta Lami ta shiga yi, amma kamar tana zuga ta, da Lamin ta gaji, sai ta shige ɗakinta ta barta nan.

Gari na ƙara haske ta shirya kamar mahaukaciya ta tafi gidan wata ƙawarta neman rance.

Yadda ta je, haka ta dawo ko asi bata samo ba, ƙarshe ta shige ɗaki ta yi ta kuka, don ta fara nadamar kashe aurenta, tunda da yanzu ita da shi zasu tafi.

Alhaji Mainasara kuwa da asubar washe gari jirginsu ya sauka UK, zuwa ƙarfe bakwai ya hallara a asibitin da Habeeb yake kwance.

Kai tsaye ICU ya nufa, kasantuwar shine mahaifinsa ne aka bashi damar shiga wurinsa.

Kuka ya fashe dashi a lokacin da ya ga ba alamar rai a tare da Habeeb, “Wace irin cuta ce haka ta samu ɗana.

Maman Mu’azzam

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 17Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×